Sashe 108
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai tana shiga kai tsaye video É—in a kan faskan Leo dake tsaye bayan wata katuwar bishiya yana kokarin canza bullet na bindigarsa ta fara nunawa, ga harbin bullet sai sucewa ta gefensa yake yi, da alama musayar wuta suke yi, ALLAH sarki, kwanaki biyar kenan yau da tafiyarsu, sun yi kwana biyu a hanya kafin su kai in da mutanen suke, da isarsu da kwana É—aya network na wajen ya jagule saboda musayar wuta, a haka Arya ta rasasu har aka harbi drone É—inta, yanzu wanda ta sake turawa ne suka yi sa'ar ya kama network É—in.
Ai tsabar farinciki idanun Arya cikowa da kwallah ya yi, su V kuwa rungumar juna da su Angelina suka yi, thank God ba'a kashe masu jami'ai ba dik da basu da tabbaci sauran suna raye ko aa, amma ganin Leo yasa sun ji kamar sauran suna raye.
Da sauri ta shiga drone control É—in, hannunta har yana kerma sosai. V ce ta ce. "Arya ki bibiyi sauran soldiers É—inmu muga ko suna raye?". Tamkar zata yi kuka ta faÉ—a, zuciyarta na harbawa da karfin gaske, tana tsoron wani abu ya sami Noor É—inta.
Arya na kokarin juya akalar drone ɗin izuwa arear wajen dan ta duba sauran sojijinsu sai gani suka yi Noor ya bayyana a gaban drone ɗin, da karfi ya rungumi Leo suka faɗi ƙasa. Suna faɗuwa bullet ta wuce ta kansu, da gefen wuyan Leo bullet ɗin zata fasa Noor ya cecesa, shi hankalinsa yana can yana ƙoƙarin canza bullet ya zuba sabbi daga waɗan da suke waist ɗinsa a ɗaure.
Ai wani irin yawu da Arya ta haɗiye sai da sautinsa ya bayyana a fili, dikkansu jikinsu tsuma ya fara yi, suna jin ina ma ace suna wajen. Miƙewa Leo ya yi yana faɗin. "Thank you bro". Ya faɗa yana yi wa Noor alamar jinjina da hannunsa.
Noor dake kwance a ƙasa cikin ciyayin dake wajen ne ya miƙawa Leo hannunsa ɗayar da bata rike da bindigarsa, ya shagwaɓe fuska yana faɗin. "Ɗagani"........ Hararansa Leo ya yi tare da cigaba da abin da yake yi na zuba ƴaƴan bullet a cikin bututun bindigarsa. Cigaba da kwanciyarsa Noor ya yi, wai ba zai tashi ba sai Leo ya ɗaga sa.
Watau Noor yana da iya shege, a filin yakin ma sai ya yi. Shagwaɓa ya fara zubawa Leo yana shi dole a ɗagasa.
Leo na ƙoƙarin juyowa zai yi mashi magana sai ganinsa ya yi ya yi wani irin tashi cikin zafa, ya yi tsalle ya taka bishiyar da Leo ke tsaye a jikinta tare da ɗaga hannunsa dake rike da bindiga ya saita ta bayan wuyar Leo ya saki wuta, kan ya faɗi ƙasa ya yi harbi biyar a jere kuma dik sun samu mutanen da ya hara, dan kuwa ƴan ta'adda ne suka ɓuya a cikin ciyayyin wajen, su suka harbo bullet da ya so taɓa Leo Noor ɗin ya cecesa.
A tare suka faɗi ƙasa da waɗan da ya harba ɗin. Sake bajewa ya yi a ƙasa yana mayar da numfashi tare da cewa. "Wayyo my dad, my Juliet, i missed you more". Ya faɗa yana rugumo bindigarsa.
Hararansa Leo ya yi tare da cewa. "Tashi mu bar nan dan ba tsaro, mun shiga sansaninsu dayawa"......... Miƙo mashi hannu Noor ya yi yana faɗin. "Ɗagani, karfina ya kare". A shagwaɓe ya faɗa.
"Zaka tashi ne ko sai na ƙara maka nauyi?". Leo ya faɗa on a serious note. Shagwaɓe fuska ya yi yana turo baki, ya ce sam shi sai dai a ɗagasa bashi da karfi. Leo zai yi magana suka ji motsin a kewayen nasu. Kallon juna suka yi.
V da Arya sun gama haukacewa a zaune gaban laptop ɗin, Arya da yake bata son wasa a wajen aiki sai take jin tamkar ta shaƙo Noor, yana ɓata masu lokaci, a cikin ranta tana cewa in dai wani abin ya samu my sterious to kai ne sila, kuma ba zan barka ba. Ita kuwa V kome Noor zai yi burgeta yake yi, salon yaƙinsu ya gama tsumata, har wani nishaɗi suke bata.
Gera guda Leo ya ɗagawa Noor kafin ya miƙa mashi hannu. Kama hannun nasa Noor ya yi tamkar zai miƙe, Leo ya gama sakin jiki Noor zai miƙe sai ya ji Noor ɗin ya fisgisa da karfin gaske ya tafi gabaɗaya ya faɗo kansa. Take bullet ta wucesu fiw.
Dunkule hannun Leo ya yi ya daki Noor a shoulder, alama ce ta jinjina da sojoji ke wa junansu. A wannan karon a tare suka miƙe cikin zafa, jingina bayansu da jikin juna suka yi, Leo na fuskantar gabas Noor na fuskantar Yamma. Kafin su yi wani yunkuri sai gani suka yi ƴan ta'adda sama da 100 sun yi wa wajen zobe a cikin ciyayyin, kuma kusan dikkansu suna rike da bindigu.
Leo ne ya ce. "Bullet nawa ce a bindigarka?". Can ƙasa ya faɗa yadda babu wanda zai ji. "Jaka ɗaya". Ya bashi amsa. Yana nufin bindigar a cike da bullet ya zo da ita, wanda ya harba guda biyar ɗin nan ne kawai suka fita, dama ya gama sanya bullet ne ya zo wajen. Shi ma Leo kunga yanzu ya zuba sabbin bullet..
"What next?". Noor ya faÉ—a a hankali. "Fire!!". Leo ya amsa mashi da shi. Haba yana rufe baki suka fara É“arin wuta, take miyagun suka fara mayar masu da martani, hakan yasa suka rabu suka nemi mafaka, Noor ya É“uya a bayan wata Æ™atuwar bishiyar É“aure, shi kuma Leo ya kutsa cikin daji. Æarin wuta suke babu kama hannun yaro.
Daga bayansa Noor ya ji an saka mashi bindiga a kai, wani É—an ta'adda ne da fuskansa yake rufe da rawani, É—ana kunamar bindigar ya yi, babu imani ya nufi fasa kan Noor. Sai dai kafin ya harba Leo ya rigasa, wani irin wawan harbi Leo yai mashi a gaban goshi, farat É—aya tafiya É—aya kenan. Shege take ya zama mushe.
Ɗago kai Noor ya yi, suka haɗa ido da Leo dake tsaye a bayan wata bishiya da Noor ɗin yake fuskanta. Sara mashi Noor ya yi kafin ya juya suka cigaba da ɓarin wuta. A lokaci guda bullet na bindigarsu ta kare ga ƴan taaddar basu kare ba. Kallon juna suka yi, da ido suka sanarwa da juna bullets ɗinsu ta kare.
Ai su Arya na ganin maganar da suka yi da ido na cewa bullets ɗinsu ya kare dik suka ɗauke wuta, musamman V da ta fashe da kuka ne ma. Ita kuwa Arya dafe saitin kirjinta dake barazanar tarwatsewa ta yi. Ƙoƙarin sanya bullets a bindigar nasu suka yi, sai dai kafin su motsa miyagun sun yi masu zobe, dama sun shigo cikin sansaninsu sosai ne, kwana biyu da suka wuce a waje-waje suke musayar wuta, yau Leo ya ce sai ya matsa gaba, shi ne ya shigo.
Saitasu da bindigu suka yi suna faɗin kada su motsa, sun kewayesu ta ko'ina ba hanyar tsira. Basu da zaɓin da ya wuce dole su ɗaga hannu, kallon juna suka yi, da ido Leo yai wa Noor magana kan ya miƙa kansa. Da farko Noor ya so yin gardama, amma da ya tuna cewa Leo baya abu haka kawai sai ya yarda suka miƙa kansu, suka yi surendar.
Matsawa ƴan ta'addan suka yi, mutum biyu suka kwace bindigun hannun su Leo, sannan suka kwace bullets dake waist ɗinsu, suka haɗesu suka tasa ƙeyarsu kan su wuce izuwa cikin ainahin sansaninsu, sai murna ƴan ta'addan suke yi kan sun kama sojoji, zasu kashesu su ɗauki videon yadda suke kashesu su turawa ƙasa dan a kara tsoronsu.
Arya da V tamkar zasu haÉ—iyi zuciya, kuka V ta fashe da shi, ita kuwa Arya jikinta har kerma yake yi, idanunta sun kara ciccikowa da kwallah, da sauri ta bar gaban laptop É—in ta fito waje cikin tsananin tashin hankali. Manassa ce ta biyo bayanta, V kuma ta juya ta faÉ—o jikin Angelina tare da fashewa da kuka mai tsuna zuciya, tana faÉ—in shikenan mutuwa zata yi idan aka kashe Romeo É—inta.
Su kansu sauran sojijin dake wajen suke tsaronsu sun girgiza na ganin an kama su Noor, han kulansu ya tashi. Waje suka yo suma. Ita kuma Angelina ta yi ƙoƙarin control na drone na Arya dan ta duba ina su Zash suke ta ankarar da su an kama su Leo idan hakan zai yiwu, tana rungume da V tana rarrashinta.
----------------------🔥
WS-H.
Dr Kamal ne ya yi wani irin shu'umin murmushi kafin ya ce. "To amma ai in baka son Lazy kana son Zinta kam ko? Kuma nasan kasan tana sonka tin ba yau ba!"......... Wani irin shu'umin one side smilling ya saki kafin ya ce. "Kwarai, shiyasa nike son dawo da ita karkashin office É—ina"........ "Kana son haÉ—a jini da Muhammad kenan?". Dr Mark ya faÉ—a.
"Hmmmm". Dr James ya faÉ—a, like shi kaÉ—ai yasan me yake ransa.
Jama'a bari in ɗan baku ƙaramin surprise a nan kafin mu wuce. Wani abin da baku sani ba a nan shi ne, da Maya da Zinta dik an kyankyashesu ne daga sperm na daddyn Lion, su Dr James suna da sperm ɗinsa da suka mashi tiyata suka ɗeba, kun san ana iya yi wa namiji tiyata a ɗebi sperm ɗinsa ai.
Ana mashi ƙaramar tiyasa a shiga percutaneous epididymal sperm aspiration ɗinsa a ɗebi sperm ɗin. To su Dr James sai da suka san yadda suka yi suka ciro sperm ɗinsa, yanzu haka suna da ragowa sun mashi babban killacewa da matakan tsaro, a cewar Dr James zai kyankyashi matar da zai aura da wannan sperm ɗin, sannan idan ya mallaki matar zai yi mata dashen wannan sperm ɗin da kwayayen haihuwarta domin ta haifo mashi magaji mai kaifin kwakwalwar daddyn Lion wanda zai iya irin aikin da yake yi, shiyasa ya kyankyashi sister Maya and sister Zinta, a cewarsa Zinta matarsa, Maya ma'aikaciyarsa, nan gaba kaɗan zai sauke Lazy, da Maya zai maye gurbinta saboda shi masu basira kawai yake so a kusa da shi. Bai son daƙiƙu!.