← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 227

Sashe 77

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kallo ɗaya zaka yi wa yadda suke aikin nan kasan cewa kwararrun likitoci ne na gasken-gaske, in short su likitoci ne da irinsu basu wuce a kirga ba ma a duniya, matakin kaifin ƙwaƙwalwa da bincikensu ya zarce yadda kuke tinani, they're gifted, amma dik da haka cikin taka tsantsan suke aiki yadda zaku san aikin mai haɗari da wahalar gaske ne suke yi, idan aka samu matsala kaɗan komai na iya lalacewa su tabka babban asarar da ba zasu taɓa son hakan ba!.

A cikin wannan kwalba DR JAMES ya sanya wannan mahaifa, sai da ya tabbatar zamanta ta yi daidai sosai, sannan ya kunna wata naura dake jikin kwalbar dan canzawa mahaifar yanayi izuwa yanayin cikin mace, take cikin kwalbar ta kawo wuta sky blue mai É—an haske, ta fara fitar da siririn sauti mai bada vuuuuu kamar vibrate na waya.

Da sauri DR JAMES ya juya ya rungumi DR KAMAL alamar sun yi nasara, matsawa DR MARK ya yi shi ma suka rungumi juna sosai, sannan suka raba jikinsu. A natse suka fara takawa suna bin dik kwalaben dake cikin wajen suna dubasu, tamkar suna duba wani abin haka. Sai da suka tabbatar komai normal sannan suka nufi hanyar fita a tare. Kai tsaye side na dabbobin dake cikin wajen suka nufa, suna tafiya ne a kai É—aya.

Kewaye suka fara yi a wajen dabbobin, yana da girma sosai wajen, guards dake tsaron wajen kawai sun fi mutum 20, kun ga kuwa ai wajen da girma. Kowani dabba da irin abincin da yake ci, ga kwanon abincin kuma a gabansa an zuba mashi, waÉ—an nan guards É—in suke baiwa dabbobin ruwa da abinci, har macizai dikka suke ciyar da su, shiyasa aka samu jiga-jigan guards madaka karti masu rai da lafiya dan kula da su.

Sosai suka yi yawo a cikin wajen, suka tabbatar da komai yana nan yadda ya dace, sannan suka fito suka nufi office ɗinsu. A kan hanyarsu na komawa office suka ci karo da wasu kyawawan nurses guda biyu dake sanye cikin kayan aikinsu, sun yi matuƙar kyau tsab-tsab da su. Face ɗinsu da nose mask suma. Har ƙasa suka durkusa suka gaida Dr's ɗin cikin girmamawa.

Kai na gaji da rubutun, haba, ku ce Princess dakata ki bari haka, ya isa ki huta mana! Amma dik kun yi shiru sai typing nike yi kamar ba'a sona! To sai Monday idan mai dikka ya kaimu!.

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

STEP 1🔥

2025-11-24.🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E_____________22 & 23

Sosai suka yi yawo a cikin wajen, suka tabbatar da komai yana nan yadda ya dace, sannan suka fito suka nufi office ɗinsu. A kan hanyarsu na komawa office suka ci karo da wasu kyawawan nurses guda biyu dake sanye cikin kayan aikinsu, sun yi matuƙar kyau tsab-tsab da su. Face ɗinsu da nose mask suma. Har ƙasa suka durkusa game da sunkuyar da kai suka gaida Dr's ɗin cikin girmamawa.

Hannu Dr Mark ya ɗaga masu alamar sun ji kafin su wuce ba tare da yi masu magana ba. Miƙewa nurses ɗin suka yi suna binsu da kallo har suka kurewa ganinsu, dawo da kallonsu a kan juna suka yi, ɗayar ta ce. "Sister Maya kin san wani abu ne?"........ Kai Maya ta girgiza alamar a'a bata sani ba. "Dr James ya haɗu over, kin san da cewa son gaske nike mashi?". Ta faɗa tana ɗan ciza laɓɓa......... "Sister Zinta i think ai kin same shi kin gama, ko bake kika ce mun ya yi inviting ɗinki zuwa waiting toom ɗinsa a yau da yamma ba?".

"Haka ya ce in same shi a waiting room É—insa bayan tashi daga aiki, amma kuma ai ban san dalilinsa na kiran nawa ba! Maybe ma wani aikin zai sanyani, kin san shi baya rabuwa da sanya mutane aiki". Ta kai karshen maganar tana É—an tura baki a cikin mask É—in.

"Amma ai idan aiki ne baya taɓa cewa a same shi a waiting room kai tsaye haka, sai dai office, ni a nawa ganin kamar ya kyasa dake ne, in kuwa haka ne ki shirya faɗa da sister Lazy, dan ba zata taɓa yarda wata ta raɓesa ba"........ Siririn tsaki sister Zinta ta ja tare da wucewa gaba tana faɗin. "Idan har na samu hankalinsa ya dawo kaina wacece kuma wata Lazy? Ba dik taƙamar da take mana da nuna ta fimu ɗin saboda shi yana kulata bane? Dame ta fimu? Kada ki manta ita ma fa ɗalibar lafiya ce kawai kamarnu".

"Uhm ni dai ina ji maki tsoron balainta, dan mafaɗaciya ce"......... "Ita ɗin banza, dik taƙamarta dan tana aiki a karkashin office ɗinsa ne, shiyasa nima na zage ina son komawa karkashin office ɗin nasa".

Maya zata yi magana daga bayansu suka ji an ce. "What are you doing here at this time da yakamata ace kuna bakin aiki?"........ Da sauri suka juya, wata malamar lafiya ce dai kamar su, tana sanye da kayan aikinta, kana ganinta kaga irin masifaffun nan masu zubin taliya ƴar murji, idanun nan a tsaitsaye, gashin idon kamar wacce aka shuka shinkafa a ƙasa, suna tsaye zara-zara ga tsawo.

"Sorry sis Lazy". Suka faɗa a tare suna haɗa baki kafin su wuce su cigaba da tafiya zuwa in da zasu ce. Can ƙasa sister Maya ta ce. "Bana faɗa maki ki guji balain sister Lazy ba, kina ganinta tamkar wacce ake yi wa loading na masifa a kanta kowacce rana, kullum da sabon salon balain take zuwa". Cike da tsoro Maya ta karisa maganar.

"Sai kuma ta yi, kawai yanzu inai mata biyayya ne saboda a karkashin office É—in Dr James take aiki, amma ba wai dan ta fini da wani abu ba". Sister Zinta ta faÉ—a......... Suna tafiya suna hira har suka shiga wani sashe a cikin hospital É—in. Wani glass room suka shiga mai É—auke da tarin chemical dayawa, an shisshirya chemical É—in a cikin transparent glass, kowani chemical da sunansa a manne a jikin kwalbansa.

Lap gown and hand gloves suka sanya a jikinsu tin daga bakin kofa kafin su karisa cikin wajen, ga tarin computers daga gefe dayawa, kayan gwaje-gwaje suma akwaisu dayawa a ciki.

One thing about sister Maya and Zinta, dik cikin W-S-HOSPITAL ɗin nan sun fi kowa hakuri, hankali, natsuwa, kamala, kame mutunci da kuma kula da kansu, basa da faɗa, basa zuwa wajen hayaniya, akwai girmama manya, akwai tausayi da sanin darajar ɗan adam, sai dai kuma akwaisu da balain son yara, dik in suka ga yaro rasa natsuwarsu suke yi, su yi ta faman ɗauka, sun taɓa ganin jariri a hannun sister Lazy, suka dinga rokonta ta basu su rike, har da durkusawa ƙasa suka yi mata, ta ce masu babyn Dr mark ne, in suna so su je su rokesa, in ya yarda a basu to zata basu su rike.

Su kuma suna balain tsoron waÉ—an nan 3 doctors É—in, dan haka suka hakura, amma har ruwan hawaye sai da suka yi, rauninsu shi ne yara.

Wasu kyawawan ƙananan transparent glass bottle suka ɗauko, a cikin wani katan baff, suka zauna a saman wasu chairs dake gaban manyan glass na chemical ɗin, a hankali suka fara ɗibar kowani chemical suna aunawa suna zubawa a cikin bottle ɗin daidai misali, sai sun auna kilonsa kafin su shirya shi cikin kwali, idan kwalin ya cika sai su ɗauka izuwa wajen da ake shirya chemical irinsa su hau shiryawa cikin glass ɗin.

Sun sanya eye protection a idanunsu kafin su fara aikin, suna yi suna hira a in da sister Maya ta ce. "Kin san wani abu sister Zinta?"...... Kai ta girgiza a lokacin da take É—ibar nata chemical É—in. "Ina son DR MARK sosai, yana burgeni, amma ban san meyasa yake mugun bani tsoro ba, ko motsinsa na ji sai hantar cikina ta kaÉ—a".

"Uhm watarana komai zai wuce, mu dake mu yi aiki tukuru mu koma karkashin office ɗinsu, kin san basa ɗaukar wanda ba kwararre ba a karkashin office ɗinsu, shiyasa kika ga na kara dagewa dan in zama irin nurses da suke aiki tare da su, kamar dai wancan fitinanniyar Lazy, amma ke ina ga tsoron matar DR MARK kike ji shiyasa kike shankarsa over har haka"..................... "Hmmmm, bana tsoron matarsa, saboda ban taɓa ganin tana masifa ko wani abin mara kyau ba a cikin makarantar nan. Ni babban abin takaicina ma shi ne yadda basa ɗagowa su kalli mutum".

Zinta da shegen son gulma ce tai ƙasa-ƙasa da murya wajen cewa. "Kuma na ji an ce Dr James har hugging na Lazy yana yi, har kiss da sauransu".......... "Ina fatan shiruna ya zame mun alkhairi". A cewar Maya da bata cika son zaman gulma ba, dan ma dai Zinta best friend ɗinta ce yasa idan tana gulma bata tashi ta bar wajen, amma tana ƙoƙarin hanata gulmar, banda haka ita ba'a gulma da ita, kunji ta ce tana fatan shirunta ya zame mata alkhairi, dan tasan abin da Zinta bata sani bane, abin da ya fi kiss Dr James yake yi da Lazy, amma ba zata faɗa ba ko dan ma kada zuciyar Zinta ɗinta ya buga.

"Matsalata dake kenan Maya, komai sai ki ce kina fata shirunki ya zame maki alkhairi, to da kike wannan magana wani zanje in faÉ—awa ne? Ko dai kina tinanin wani na jinmu ne?"...... Kai ta girgiza tana cigaba da gwada chemical É—inta, a natse ta amsa da. "Ba wani zaki faÉ—awa ba, kuma babu mai jinmu, kawai dai manta da maganar, ya batun shirin partyn da zamu yi next month na kammala karatun ajin farko?".
Chapter 77 · 0% Book details