← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 226 OF 227

Sashe 226

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ai wunin wannan rana dai wanna aiki ta yisa ne kawai, amma bata san me take yi ba, har lokacin da ya zo tafiya, ya shirya ya zo sallamarta bayan sun yi connecting na drone É—in. A dake ya ce. "Zan je wani waje, wait for my call".

Kai kawai ta jinjina taki yin magana, taki ɗagowa ta kallesa. One side smile ya ɗan saki tare da riko hannayenta. "Baki mun fatan in dawo lafiya ba, ko dai kin fasa sona ne?". Cike da sonta ya faɗa...... Tana gab da fashewa da kuka, tana wani irin huci na zuciya a kusa ta ce. "Ba zan taɓa daina sonka ba, amma ai za'a rabani da kai, kawai ka je".

Tausayinta ne ya ɗan kama shi, amma ya basar da cewa. "Ba za'a rabamu ba, zan cigaba da rokan Abba ya barni in aureki, so ki kwantar da hankalinki kin ji?". Kai kawai ta jinjina tare da fashe mashi da kukan da take ƙoƙarin rikewa.

Kafin ya yi wani yunkurin rarrashi ta faɗo jikinsa, ta rungumesa tightly, tana cigaba da kuka. Ai wani irin jim ya ɗan yi, sai ya ji dik wasu sassa na jikinsa suna amsawa, wani irin yawu ya haɗiya gwad har sai da maƙogwaransa ta yi sama ta sake yin ƙasa, da kyar ya sanya hannu ya rabata da jikinsa. A gurguje ya ɗan rarrasheta, baya son ya tafi ya barta cikin kunci, da suna tare ne ya dinga janta ta tsokana, saboda yana ganinta, amma baya nan gara ya barta cikin farinciki, sai ya ce mata ai zasu shawo kan Abba zai yarda, da wannan kalaman ya yi amfani wajen shawo kanta ta hakura. Sannan yai mata sallama ya fita bayan tantin, to shi ne suka tsaya jiran Noor. To mu koma kan labarinmu.

Dikkansu Æ´an matansu sun samu damar kallonsu kafin su tafi, amma Arya bata samu daman ganin Leo ba, Noor na zuwa suka kama hanya, babu wanda yasan basa nan sai Æ´an matan nasu, suma matan basu san in da zasu je ba, sun dai san sun tafi wani waje kawai. Suna barin wajen waÉ—annan duwatsu suka kama hanya sai ga wani soja daga cikin sojojinsu ya fito daga bayan wata dutse, yana rufe da fuskansa da nose mask, ba zaka iya gane wanenen bane.

Wayan dake hannunsa ya fara daddannawa, jim kaɗan ya kara a kunnena, baka iya gane muryansa sosai saboda nose mask ɗin, ya ce. "Sir sun fita yanzu". Ba'a iya jin me ake cewa a ɗayan ɓangaren, sai kai da sojan ya jinjina game da cewa. "Okey sir". Daga haka ya katse kiran ya gudu ya koma cikin sansani.

Su kuwa suka cigaba da tafiya suna tattauna yadda zasu shawo kan wannan gagarumin aiki na gabansu a kan Æ´an ta'addar nan.

A tsakiyar dokar daji suka yi sallar magrib da ishai, while Unays ya ja sojojinsu sallar a sansani, amma ya yi mamakin ganin su Leo basu fito sallah ba, ya je room É—insu basa nan, ya kirasu basu É—auka ba. Ya tambayi Arya ta ce mashi sun je zagaye a daji ne, zasu dawo anjuma.

Ya yarda, dan haka ya jasu sallar magrib da ishai, su kuwa su Leo sun yi tafi mai mugun nisa, har wuraren 8 na safe suka samu damar isa wajen hayakin, nan suka isko wani irin wearing na wutar lantarki mai mugun ban mamaki da karfin tsaro. Amma abinku da renon AZURE cikin karkashin wasu wayoyin yantarki suka kutsa, kun tuna an koya masu horon rarrafe a cikin laka a barrack?.

To yau ga ranar amfanin wannan rarrafe, sai da suka yi wa su Arya message kan su kunna laptop ɗinsu, sannan suka kunna bluetooth ɗinsu da already sun yi connecting da laptop ɗinsu Arya a sansani, sannan suka kwanta a ƙasa cikin ciyayi, suka fara rarrafawa ta ƙasan waɗan nan wayoyi. Tsaro mai matuƙar karfin gaske ne a wajen yasa drones ɗinsu Arya suka gagara ketarawa.

Sun yi tafiyar good 30mins a rarrafe cikin ciyayi kafin su samu damar ketarawa cikin wajen, ta wannan hanya da suka shigo cike yake da ciyayi matuƙa, basa iya ganin gabansu, har suka kutsa cikin wajen ciyayi ne dogaye da bishiyoyi.

Suna samun damar ƙetarawa ciki suka saki drones dake hannayensu, sannan suka taɓa bluetooth na kunnuwansu game da tambayar su Arya shin komai ya tafi daidai?. Matan dik suka amsa masu da e komai daidai kuma suna iya kallon komai sosai.

Leo ya ce da Arya. "Start moving the drone zuwa wasu wurare ki duba mana hanya, ki duba mana tsaronsu, su waye a kan hanyarmu kuma me suke tare da shi, wasu irin makamai ne a hannunsu da sauran bayanai na aiki da kika sani".

Da okey sir ta amsa, da yake bata samu damar ganin fitansa ba sai ta juyo da drone ɗin ta samu damar kallon kyakkyawan fuskansa cikin helmet ɗinsu ma soji kafin ta juya kan drone ɗin ta fara ƙoƙarin nema masu hanya kenan sai ta ji Leo ya ce. "Oh s***".

Jin haka yasa ta juyo da drone ɗinta, me zata gani? Gabaɗaya su Leo kewaye suke, an masu zobe, wasu riƙaƙun mutane da baka iya ganin komai na daga jikinsu ne suka kewayesu da manyan bindigun da suka fi na su Leo ɗin, da alama already sun san da zuwan su Leo wajen, dan ta ko'ina sun kewayesu, sun ɗaura masu bindugu a kai, zasu kai mutum 15 haka, ashe sun ɓuya a cikin ciyayin ne suna jiran shigowarsu, sun yi kwantan ɓauna.

Ya rabb, ya sojojin AZURE zasu yi? Captain ya yi gaskiya, a cikin soja akwai maciya amana, dik yadda aka yi akwai sa hannun wasu manya a kamasu, wani soja ne daga sansaninsu ya ci amanarsu? Waye ya bashi aikin? Ya zasu yi kenan? Suna tsaka mai wuya! Ace cikin abokan aikinka ma maciya amana, cikin manyanku maciya amana, ina ake son su sanya ransu? The game is over but over masu waye? AZURES SOLDIERS OR THE GANGSTER'S?. Let's meet in part 2 to see what's going to happen!.

-----------------------🔥

WS-HOSPITAL.

Tsaye Dr Kamal and Dr James suke a É—akin da darling yake kwance, Dr Mark bai dawo ba. Dr James ya zubawa darling idanu yana ta kallonsa, mamaki yasa sun gagara kwakwarar motsi.

Darling ɗan tahalikin da bai san komai ba, kwance yake a cikin glass ɗin da suka sanya shi, ya ɗage kafafunsa sama yana ta wasa sosai, alamar kyakkyawar lafiya da kuzari sun wanzu a jikinsa, fatar jikinsa ta canza ta koma ta ainahinta, sai dai kurajen nan ne da suka fito mashi ne suka ke nan, amma lafiya kam ya sameta matuƙa, ƙurajen ma sun fara raguwa, ruwan cikinsu na bushewa.

Lamarin da ya gigita 3D kenan, ya rabb, ta ya aka yi darling ya samu lafiya? Dr James ya yi iya dube-dubensa bai samu wani dalili ba, sai dai yana zargin kamar akwai wanda yai mashi alluran maganin cutar NEXAPOX-31 ɗin nan, domin da ya binciki jinin darling ta na'ura ya gano akwai sinadarin da ta keta cikin jininsa kwanaki biyu baya! Dik yadda aka yi akwai abin da ya saɓa.

To waye yai mashi alluran maganin? Waye ya kirkiri maganin bayan shi kansa wanda ya kirkiri cutar bai gama haɗa maganinta ba, yanzu ake ƙoƙarin haɗata, wani mai basirar ne ya rigasa haɗa maganinta?.

Jama'a waye kuke tinanin ya ceci ran darling? Waye yai mashi alluran maganin cutar nan? How? Ta yaya? Yaushe? Waye kuma a ina? Ni kaina na kiɗime da ganin wannan abin, akwai dai abin da ya saɓa! Ko dai a cikin 3D ɗin ne ɗaya imani ta shigesa ya ga ba zai iya barin darling a cikin wannan cuta ba sai ya bashi maganin? Wani bawan ALLAH ne yai wannan aiki?

Ga project na kwarin nan da suka jima suna yi IRON FIST sun kama container, ga kuma darling ya samu sauki, kuna tinanin zasu yi shiru ne?.

Jama'a su waye WORLD SYSTEM dake ɗaukar nauyin 3D suna shuka fasadinsu a bayan ƙasa? Su waye ainahin IRON FIST dake ƙoƙarin cetan duniya daga musifun WS, shin WS mutane ne ko kuma dai na'urorin ne dake juya duniya? Idan mutane ne a ina suke? Su waye su? Me makomar DOL? Zasu kwaci kansu ko za'a kashesu? Ga Lazy ga IRON FIST! Shin IRON FIST zasu bayyana wa duniya? Idan suka bayyana me makomarsu? Seraphina, Aryan, Rimsha, ya zata kaya? Me a cikin containers da IRON FIST suka kama? Me ake yi da ɓargon jariran nan? Mun ji abin da ake yi da jininsu, me ake yi da ɓargo da ƙashinsu? Wasu irin magunguna ake mana gaurayensu? Menene maganin cutar NEXAPOX-31? Nasan zaku so ganin yadda 3D zasu haɗa maganin ko dan ku ajiye saboda tsaro.Tambayoyin suna da mugun yawa, amma alƙalamina zai amsa maku komai.

Jama'a labarin yanzu zai fara, STEP 1 dik sharar fage ce, yanzu zamu shiga ainayin labarin.
Chapter 226 · 0% Book details