← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 196 OF 227

Sashe 196

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga nan suka cigaba da tattaunawa kan aikinsu, kowannensu yana kawo hasashensa da zurfin tinaninsa kan menene a wajen wannan hayaki. Suna tsaka da hirar ne sai ga team 2 sun zo wajen, su Unays kenan. Da ido Leo ya cewa ƴan room ɗinsu su yi shiru kan wannan case ɗin, yanzu Leo ya ƙara hankalta da mutane tin da suka kama sojojin ruwan nan, da Captain ya daka mashi warning kan aminta da mutane ma sai ya kara kame kansa, dama can su basa yarda da mutane ai kun sai.

Da su Unays suka zauna sai Noor ya É—auko masu wani hira daban kan aiki, ya fara neman jin hasashensu kan wannan mission É—in....... A haka suka cigaba da hira har dare, lokacin sallah ne kawai yake tada su.

After some hours.

Gari ya yi sanyi, sojojin dake sansanin gabaɗaya suna wajen wuta suna shan ɗimi, matan ma suna tare da su except Arya dake cikin ɗaki tare da wannan yarinyar nan, ta baiwa yarinyar abincin darenta sun ci tare, ta ƙara yi mata wanka, yanzu haka tana zaune a tsakiyar tantinsu rike da laptop tana ta ƙoƙarin tabbatar da abin da take zargi a kan wannan waje da aka harbe drone na V.

Yarinyar kuma ta kwanta a ƙasa kusa da ita, sai Arya ta ɗago kanta ta ɗaura a kan cinyarta, ta rasa meyasa take son yarinyar sosai take kuma tausayinta. Yarinya har ta fara murmurewa kyanta na kara bayyana.

A wannan lokacin ne sojojin team 1 suka fita da waÉ—an nan Navy É—in ta bayan tantunansu ba tare da kowa ya sani ba, dikkansu suka É—auki mutum É—aiÉ—ai suka wuce. Kai tsaye bakin ruwa suka nufa. Suna tafiya cike da jarumta, dik sauran sojojin ba wanda yasan meke wakana, suka isa cikin ruwa ta baki kaÉ—an. Leo yasa pistol É—insa ya harbesu ba tare da sun farfaÉ—o daga alluran barcin da aka yi masu ba, suka jefa gawarwakinsu a cikin ruwa, suka tsaya sai da suka tabbatar gawarwakin sun bi ruwa, sannan suka juya suka koma sansani.

Cikin tantunansu suka shiga, suka canza kaya zuwa marasa nauyi na barci, sannan Vash, Zaynish and Noor suka fito zuwa wajen wutar nan. Leo kuma sai can ya fito game da zuwa bakin wutar.

Dik suka mimmiƙe suka sara mashi, bai yi magana ba ya kira V ta hanyar yi mata alama da hannu, da sauri ta nufesa. A gefe ya tsaya ta bisa, cikin wannan natsuwa tasu ya faɗa mata abin da suka shirya da Noor. A daidai lokacin Noor ya iso wajen. Leo baya son Noor ya fara aikata ba daidai ba daga shigansa musulunci shiyasa yake son ɗaura wannan aure, dan yasan Noor ba zai hakura da daina taɓa V ba tin da sun saba.

Noor na zuwa wajen ta rungumo shi game da faÉ—a mashi ita dik hukuncin da ya yanke ta yarda da shi. Ya ji daÉ—in hakan, ya É—auko sadakin diamond chain É—insa ya bata, ya kira daddynsa a waya ya haÉ—a shi da Leo. Kun san daddy farincikin yaransa kawai yake so, dan haka ya aminta da wannan haÉ—i, sai dai fa ya É—an tirge da farko, ya ce meyasa Noor zai shiga wata addinin ba tare da ya nemi shawarinsa ba?.

Hakuri Noor ya dinga bashi, daga nan komai ya wuce. In taƙaice maku a wannan dare aka ɗaura masu aure irin na addinin musulunci ba tare da sanin GAT ba, sai dai sanin Aunty Lisa da ita dama kun san ai tana bayan Noor koma me zai je ya zo, tana nan dai tana cin amarcinta abinta, ta ƙara kyau, yanzu da GAT yaga su Arya sun yi dogon zango ya fito da batun auren nasa, yanzu haka ana ta shirye-shiryen dinner partyn da za'ayi a cikin barikin.

V bata musulunta ba, Noor bai ce ta musulunta ba, Leo ya ce ya kyaleta da kanta zata ce zata musulunta, kuma wannan musulunci shi ne daidai, ba wanda za'a cewa mutum ya yi ba, a cewar Leo in dai tana zaune da musulmai tana ganin kyawawan halayensu tsab zata musulunta.

Bayan sun É—aura auren ne, Noor da V suka koma wajen wutar, Vash and Zaynish suka rufa masu baya, shi kuma Leo ya koma cikin tantinsa dan aikin dake gabansa, bashi da lokacin zama a bakin wuta dan jin É—imi shi, yasan me yake gabansu. Arya ma dai irinsa ce, bata da wannan lokacin, aiki ya fi mata komai muhimmanci.

A wannan lokaci Manassa ta ɗauko rucksack ɗinta, ta zo ta da nufin ta gyarawa Zaynish hannunsa ta sake wanke mashi. Da sauri Angelina ta bita, a kusa da shi suka zauna, ya ware masu tafin hannun nasa, ya sunkuyar da kansa ƙasa yana kallon farin yashin dake wajen.

Kwance bandejin dake hannunsa Manassa ta yi, ta wanke mashi hannun game da zuba mashi magani, ta sanya sabon cotton kafin ta mayar da bandeji ta rufe mashi. Sai sorry Angelina take ce mashi, shi kuma ko kaÉ—an bai É—ago ya kalleta ba.

Bayan sun kammala Manassa ta miƙe ta nufi tantinsu ta mayar da rucksack ɗinta, sannan ta dawo ya zauna a kusa da Vash tana satar kallonsa ta ƙasan ido, while tana chatting da shi matsayin aljana, ya ce mashi taga ya kula mace yau, kuma sai ta hukunta yarinyar.

Shi kuwa ya ce mata. "Wannan yarinyar rayuwata ce, in kika kasheta ni kika kashe, dan haka kin rasani kema". Wani irin musulmin daɗi ta ji, yadda ya ce wannan yarinyar rayuwansa ne, ya rabb, sai ta ji tamkar ta miƙe ta je ta rungumesa, sai murmushi take yi, tama gagara amsar da zata bashi.

Ita kuwa Angelina tana zaune kusa da Zaynish tana aikin satar kallonsa, Unays kuma yana satar kallonta, yana ta ALLAH ALLAH Zaynish ya tashi ya dawo kusa da ita ya zauna.

----------------------------🔥

CRYSTAL PALACE.

Ko da aka fita breakfast Seraphina ta yi rarrashin duniyar nan Rimsha taki kulata, daga karshe ma miƙewa Rimsha ta yi ya fice waje, zuciyanta baya jin rarrashi ko kaɗan, ita kaɗai tasan waye Aryan.

Tana fita Uncle ya dawo kusa da Seraphina ya zauna, yana kallon kyakkyawan face É—inta ya ce. "Baki yi kewata bane?". ÆŠan turo baki ta yi. "Na yi amma kaÉ—an".

Haɗaɗɗen murmushi ya sakar mata kafin ya ajiye mata chocolate ɗin hannunsa a saman table ɗinta, chocolate mai heart design, ya yi mugun burgeta chocolate ɗin, ta ɗan zaro idanu a kan face ɗinsa kafin ta ce. "Is so nice, thank you". Ta faɗa game da miƙa hannu ta ɗauki chocolate ɗin.

Zuba mata idanu ya yi, yana binta da wani irin kallon ƙauna mai narka zuciya, yana jinsa a wani irin duniya na musamman. Ita kuwa ɓare chocolate ɗin ta yi, sai taga mai zalar madara ce a tsakiya, ɗan turo baki ta yi. "Daddy ya hanani sha milk". A dame ta ya maganar tamkar zata yi kuka.

Kai wannan shagwaɓar tata yana mugun tafiya da imaninsa fa, ɗan nisawa ya yi game da cewa. "Meyasa ya hanaki shan milk?"......... Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ce. "There was a time da na yi ciwon ciki a school, sai muka je hospital, a nan ne aka ce in daina shan milk".

Hannu ya kai kan eyes ɗinta, ya ɗan janye fatar ƙasa na idanun kafin ya ce. "E kam dole daddy ya hanaki shan milk, anyway ki sha wannan ba dayawa bane ai, ba zai maki wani illah ba". Ya faɗa game da cire hannun nasa daga kan fuskarta.

Ai tana jin hakan ta ɗauki chocolate ɗin ta fara ci, sanyawa a bakinta ta yi zata gutsira ta cire saura kenan uncle ya yi saurin ɗago haɓarta, sai yasa bakinsa ya ɗan gutsira yana kallon cikin kwayar idanunta. Ai bata san lokacin da ta saki chocolate ɗin ya faɗi ƙasa ba, ta fasa sha, ta kuma zazzare violet eyes ɗinta a kansa sosai.

Ganin ta jefar da chocolate ɗin ne yasa uncle ya ɗan miƙe yana ƙoƙarin haɗe bakinsu ya tura mata na bakinsa da ya gutsira. A zabure ta miƙe tana ja da baya. Cike da mamaki ya fara binta da kallo, dan su wannan ai ba wani abin bane a wajensu, meyasa take gudu to?.

"Beb, are you okey?". Ya faɗa yana miƙewa tsaye da kyau. Tana ƙara zazzare mashi idanu ta ce. "Dad ya hana in bar wani namiji ya taɓani, and i promised him that ba zan yi hakan ba, then mom also, ta mun warning a kan irin haka, please sir kada ka sake gigi yi mun irin wannan abin, kada ka sake gigin haɗa bakinmu, i can't tolerate this". Da iya gaskiyarta take magana, babu wasa a kan fuskanta.

Ganin hakan ne yasa ya ja da baya yana ce mata sorry, ya ce ba zai kara ba ta yi hakuri........ "Just go kawai!". Ta faɗa cikin tsiwa tana nuna mashi hanyar wajen chair ɗinsa, bata son dik wani abun da zai ɓatawa daddy Champion namu rai.

Uncle na juyawa zai koma wajensa ta yi gaggawar wucewa ta fito, ta nufi wajen Rimsha, ta yi ta ƙoƙarin dannarta har aka dawo class, yau ko abinci basu ci ba. Haka suka wuni a school babu daɗi, Rimsha taki sakewa su yi hira, har aka tashi school.

Farya ya riga Aryan zuwa, sai ya ce da Seraphina ta zo su mai da ita gida. Tana ɗan murmushi ta ce. "No uncle, ka bari daddy zai zo, ya hanani hawa motar kowa"........... Faryan bai matsa mata ba, ya ɗauki Rimsha kawai, da yake Rimsha jikin babu daɗi ba wani sallamar kirki suka yi da Seraphina ba, baiwar ALLAH jikinta ya yi mugun zafin zazzaɓi sosai, wani irin azababben ciwo kanta ke yi mata, duk ta fita hayyacinta, ta shiga fron seat kawai ta zauna shiru, ƙara bata hakuri Seraphina ta yi game da yi masu bye-bye.
Chapter 196 · 0% Book details