← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 227

Sashe 117

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saboda ta taɓa kawo mashi maganar a lokacin da suka tafi Second Mission ɗin nan, ta ce zata so ya baiwa brother ɗinta ɗaya daga cikin quadruple ɗinsa ya aura, da buɗar bakinsa sai ya ce dikkansu ya rigada ya masu miji, tin suna jarirai akwai alkawarin wasu a kansu, kuma bil hakki da gaskiya ya faɗa, wlh ya yi wa ƴaƴan ƴan uwansa alkawarinsu Arya.

Ita kuma Aunty Lisa ta san da gaske Noor yake son V, ita ma V ɗin da gaske take son shi, dan haka a kan ƙanin nata babu abin ba zata iya ba, shiyasa ta ce ya sanya mata zobe ba tare da sanin daddynta ba, ita ta sayi zoben ma ta ajiye mashi, da ya zo yanzu ne ta bashi. Yanzu da zai zo ya kirata a waya ya ce yana son ganin V, ta ce ya zo bari ta sanar da sojojin dake gate tana da baƙo. Kun ji yadda aka yi ya shigo gidan.

So yansu a bisa ƙaidarsu V matarsa ce. E to gaskiya kam musulunci duniya ne nake faɗa maku, ALLAH ka kashemu a cikin Musulunci.

Sosai ya yi juyi da ita a cikin ɗakin kafin ya sauketa ƙasa, sannan ya kama hannun nata ya sumbaci ring ɗin. Da sauri ta zumbaci in da ya sumbatar ita ma. Wani ƙaramin kwali ya ciro daga aljihun sportswear ɗin jikinsa ya, miƙa mata ya yi yana faɗin. "Saka mun nawa dan mu kara mallakar juna da kyau".

Da sauri ta karɓa, jikinta har yana rawa ta buɗe, da sauri ta ciro zoben sai kyalli yake yi, sanya mashi ta yi tare da sumbatar hannun nasa. Shi ma sumbata ya yi kafin ya jawota jikinsa.

Lokaci guda kuma ta ɗan yi shiru, kamar mai tinanin wani abin, sai kuma ta ce. "My Romeo ya zan da daddy idan ya kalli ring ɗin?". Cike da tsoro ta faɗa, jaira time da yake sanya mata soyayya ta rufe mata ido ta manta da wani daddy, sai yanzu da ta san ta zama matarsa shi ne ta tina da daddy. Kun san idan aka ga zobe a hannunta za'a san ta yi aure, tin da kunga zoben shi ne shaidar ita ta wani ce, yanzu GAT na ganin zoben yasan me yake nufi, shiyasa, kuma bata isa cire zoben ba sai da iznin mijin nata, idan ya bata izni zata iya cirewa ta ɓoye.

Ɗan rankwafowa kanta kaɗan ya yi, kamar mai raɗa ya ce mata. "Na baki izinin ciresa ki ɓoye har sai mun bar barrack ɗin nan sai ki mayar"....... Ai wani irin daɗin da ta ji bata san lokacin da ta yi tsalle ta ɗalesa ba, tana ta murmushi, shi kuwa yana ta kallonta, daga karshe ya ɗauketa suka koma saman sofa mai zaman mutun ɗaya dake room ɗin. Zama ya yi da ita a jikinsa, ya ce a matsayinsu na masoya da suka mallaki juna yau ta bashi labarin da zai sanya shi kukan farinciki.

Ɗago kai ta yi suna fuskantar juna, tasa hannu tana shafa face ɗinsa kafin ta fara bashi labarin yadda zata kula da shi tin da ya zama nata. Ni kam na ce ba'a nan gizo ke saƙa ba, ku bari GAT ya damkeku zaku gane ALLAH da girma yake, dan wlh yai maki miji!.

----------------------------🔥

CRYSTAL PALACE.

A bakin kofa ya tsaya tare da zuba mata ido yana kallon yadda take ta faman shan golden morn ɗinta cikin kwanciyar hankali, mamaki ne ya kama shi, wai ba ce mashi ta yi ta yanke da wuƙa ba?.

Almost 5 mins yana tsaye kafin ya ɗan yi gyaran murya. Da sauri ta ɗago kai, wani irin ƙayattacen murmushi ta saki kafin ta ce. "Daddy welcome"......... Harara ya dallah mata kafin ya ce. "My cherry bloom kin mai da daddy abin wasa ko? A ina wukar ya yankeki?".

Ɗan turo baki ta yi kafin ta nuna mashi hannunta tana faɗin. "Ga wajen nan, zo ka gani"....... Gently ya tako izuwa in da take. A gefen bed ɗin ya zauna tare da cewa. "In ga wajen". Ya faɗa yana miƙa hannu zai riko hannun nata. Da sauri ta janye hannun nata tana murmushi kafin ta ce. "Kawai fa son ganinka nike, na ji ina kewarka ne shiyasa na ce ka zo!"........... Har cikin ransa ya ji daɗin da ta ce son ganinsa take yi, amma yasan ba kalamanta bane wannan, kuma tabbas ba kalaman nata bane, bayan fitarsa ta kira Rimsha ta faɗa mata ta ce tana son daddy amma daddyn ya ce baya sonta, shi ne Rimsha ta bata shawarar yadda zata gane idan yana sonta ko da gaske baya son nata, shi ne ta fara gwada shi ta gani.

Yana binta da wani irin kallo kafin ya ce. "Waye ya koya maki karya kuma?"....... "Ni daddy ba wanda ya koya mun, kawai ni na tuna da kaina"...... Wayarsa ya ciro daga aljihu, ya shiga cikin record na wayarta dan ya duba, sai ya ga bayan fitarsa ai ta kira Rimsha, a ransa ya ayyana cewa Rimsha ce ta koya mata, sai ya ji yana son jin me suka tattauna, ga shi bai É—auko bluetooth ba, dan haka sai ya hakura da jin hirar tasu sai ya koma gida, ya haske hasken screen na wayar ya mai da ita cikin aljuhu kawai ya zuba mata idanu tana shan golden morn É—inta tana É—an turo baki.

After 2 days.

Zaune yake a saman sofar parlonta rike da waya yana dannawa, yau ya tsara gayu cikin wasu tsadaddun three-pieces suit masu shegen kyau ash color, ya yi kyau matuƙa, sai tashin kamshin yake yi. Ya yi nisa cikin abin da yake yi unexpected ya ce an ce. "Hi, well-done sir"......... Da yake kansa na sunkuye ne yana taɓa waya sai ya ɗan ɗago eyes ɗinsa ya kalli yatsun kafafunta, a tinaninsa dama Aisha ce ƴar wajen Madam, amma daga yatsunta ya gane ba ita bace, dan Aisha fara ce sosai ta fi Suhana.

Kuna ganin Aryan kamar baya kallon abubuwa ko? To har yatsun kafafun Madam sai ya faɗa maku yadda suke, dik abin dake tare da Seraphina yana sane da shi, kuma yana kula da sanya idanu a kan komai sosai, su ne suke kallon kamar ba ruwansa da su, dan kunga idan ya shigo gidan room na Seraphina kawai yake wucewa, idan ya tashi kuma ya fice abinsa. To ba haka bane, wani lokaci yana shigowa gidan har ya fita babu wanda yake sani har ita Seraphina ɗin, wani lokaci karfe 1 dare suna barci yake shigowa ya sake fita, dan haka ya san komai, tin ma kafin su Aunty Safiyya su zo gidan yasan zasu zo, kuma yana sane da cewa ita Safiyya tana da dalilin zuwanta gidan, watau dan ta fitar da Seraphina daga CP, dama ya yi shirin canzawa Seraphina ɗin school izuwa wanda yake cikin CP dan kada ma ta sake fita CP ɗin, sai kuma sara ta zo a kan gaɓa ya sameta da waɗan can littafan.

Kai kafin ya É—auki Madam aiki ma sai da ya san wacece ita in and out, ba kawai ya É—auketa bane! Dan haka dik wani motsinsu a tafin hannunsa suke, kawai yana son su kama kansu da kansu ne.

Su suke ganin kamar sun mashi wayau bai sani ba, basu san cewa da IRON FIST suke tare ba, kasar da ba kasarsu bama suna iya sanin halin da take ciki in and out, suke aikin sirri a kan wasu abubuwa ma bare a kan family ɗinsu, family ɗin ma wacce Champion ɗinmu yake matuƙar kauna, ai ganinsu kawai yake yi.

Ganin bai É—ago ba kuma babu alamar zai amsata ne yasa Suhana ta sake matsawa dab shi, cikin yanga irin nasu na Æ´an mata ta sake ce mashi hii. Shiru tamkar babu shi a wajen. Daidai lokacin Seraphina ta fito shirye cikin wani dogon wandon jeans ash color da riga top fari tas, ta yi bala'in kyau. Sai ma da ta gyara ash hair É—in nan nata yana wani irin sheki, Madam ta É—aure mata hair É—in a tsakiya sai ta saki jelar a baya har saman mazaunanta, ga wasu guntu-guntu gashi da suka kwanto ta gaban goshinta.

Hannunta rike da wayarta da kuma Æ´ar siririyar fashion bag É—an karamin da ko wayarta ba zai iya shiga ba, sai tashin kamshi ita ma take yi. Ganin Suhana a tsaye a gabansa yasa ta É—an tsaya daga nesa tana faÉ—in. "Daddy I done".

Sai a lokacin ya ɗago eyes ɗinsa a kanta, wani irin cool ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa tsaye. "Super my Cherry bloom". Ya faɗa yana nufota. Da sauri Suhana ta bashi hanya, saboda da ya miƙe kwarjini da cika idonsa ya kara ninkuwa....... Murmushi Seraphina ta yi tare da cewa. "Daddy my birthday date ya kusa zuwa, mammyna bata nan, na kai 2 years bana celebrating, yakamata this year in yi ko?".

A gabanta ya tsaya tare da cewa. "Zamu yi celebration mai lasisi this year". Ya faɗa tare da riko hannunta, har wani ɗan lumshe idanu ya yi da ya taɓata, kamshin perfume ɗinta yana mugun tafiya da shi. A cikin ransa yana faɗin a ranar birthday ɗin nan zan mallakeki kowa ma ya huta, aurenmu zai zama special, a fili kuma cewa ya yi su je.

Binsa ta yi tana É—an waigo Suhana dake tsaye, ita ma juyawa ta yi ta bisu da kallo har suka wuce kafin ta juya cike da takaici ta koma cikin É—akin Madam, tin da ta kalli Aryan a ranar farko ta ji ya kwanta a ranta, tana son ganin full face É—insa, amma ta rasa dama, dan su face mask ya zame masu jiki, ko a gidansu su ukun nan ne zaku gansu da shi a fuska, yanzu ta zo ne da yanganrta dan ya É—an kulata ko da gaisuwa ce su yi, amma ya shareta, abin ya kona mata rai.
Chapter 117 · 0% Book details