← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 227

Sashe 2

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nuna mata upstairs É—in da gun ya sake yi alamar su je, sai dai kuma bata cigaba da tafiya ba, ta tsaya tana yi mashi kallon tsab ne, lokaci guda idanunta suka sauka a kan jinin dake zuba daga yatsun hannunsa, ziiiiiirrrrrr haka jinin yake zuba kamar an buÉ—e tap a low gudu.

Da sauri ta É—an zaro dara-daran idanunta a kan face É—insa da bata iya gani. "Bawan ALLAH meyasameka? Waye kai? And me kake nema da ni?". Cikin raunin murya ta yi maganar.

Ko kaÉ—an bai yi magana ba ya cigaba da nuna mata sama da bindigar cikin yanayi na galabaita da kasawa, da alama dik sauran karfinsa ta karewa dauriya ce kawai yake yi. Ganin hakan yasa kawai ta wuce gaba ya rufa mata baya suka yi sama. Ba shi ya ce mata ba, kai tsaye ta nufi wani É—aki da aka rubuta OPERATING ROOM (O-R) a jikin door na kofar aka yi wannan rubutu.

Handle na door É—in ta murza ta tura, kofar ta buÉ—e, ciki ta shiga ya rufa mata baya. ÆŠaki ne tamkar hospital, ga gadan majinyata mai É—auke da bedsheet blue, curtains na É—akin dik blue, É—akin yana da girma sosai, ko'ina tsab yake sosai, sannan akwai katan AC dan hana ma'aikata gumi, yadda kuka san katafaren hospital dai. Daga jikin bangon dake fuskantar kofar shigowa hoton matar ce sanye da surgical gown, da alama babbar likita ce, dan tin daga kan yanayin hotunanta dake a manne a bangon zaka gane babban ce, jikin wannan bango dai dikka frames na hotunanta kala-kala ne, wani hoton tana aikin tiyata aka yi mata, wani ana bata kyautar karramawa, wani kuma tana rike da jariri sabon haihuwar da ko cibi ba'a yanke mashi ba! Gasu nan dai hotuna kala-kala. Da alama Surgeon ce.

Ai suna shiga ya cire gun ɗin daga kanta ya karisa wajen bed ɗin da kyar, yana zuwa ya faɗa saman bed ɗin ya kwanta hannunsa rike da bindigar. Ganin hakan yasa ta yi gaggawar karisowa in da yake, dik tausayinsa ya yi mugun jiƙata, da sauri ta zo ta rike hannunsa da yatsun ke zubar da jini, a nan ta fahimci jinin daga sama yake zubowa izuwa kan yatsunsa, ga kuma alamar harbi da bindiga a damatsansa. Hakan yasa ta yi gaggawar sakin hannun nasa ta nufi wasu drawers dake gefe guda.

Cikin ƙanƙanin lokacin wannan mata ta shirya cikin kayan kariya kamarsu surgical gown, gloves, face mask, face shield, surgical cap. Sannan ta kwaso kayan aikin irinsu scalpel, forceps, tissue & hemostat, retractor, suction machine, bullet extractor, irrigation syringe, suture needle da thread, surgical drapes, sterile daga cikin drawer ta kawosu saman table dake kusa da bed ɗin, jikinta har wani irin rawa yake yi mata, burinta ta yi gaggawar kammala shiryawa ta taimaki rayuwarsa, dan ta gano harbinsa da bindiga aka yi, jikin rigarsa wajen damatsan hannunsa a fashe.

Take ta hau preparation dan yin tiyata. Bayan ta gama tsab sai ta haɗa alluran kashe zafi, ta so yi mashi alluran barci ne, dan shi ne ma a ƙaida, amma sai ta ta ce bari ta yi mashi na kashe zafi, dan daga yadda zuciyarsa take bugawa out of control ta fahimci akwai abin da yake son cinmawa, yi mashi alluran barci a yanzu babban kuskure ne sosai, dan bata san waye shi ba? Bata san daga ina yake ba? Mutumin kirki ne ko na banza dik bata sani ba, bata san me zai iya zuwa ya dawo ba, so gara mata idanunsa biyu iya wuya.

A gaggauce ta ajiye alluran a gefe bayan ta yi mashi, sannan ta ɗauko almakashi ta fara yanka hannun jacket ɗin tasa daga wajen yatsunsa har zuwa damatsan hannunsa, ta cire hannun rigar gabaɗaya, a gefe ta ajiya game da mayar da almakashin cikin try na kayan aikinta. Sai ta ɗauko antiseptic dan ta tsaftace in da bullet ɗin ke ciki. Ta yi matuƙar tausaya mashi baiwar ALLAH, ta ga ya rasa jini sosai, kuma still zubar da jini yake yi, tamkar bullet ɗin ta gota hanya, ta nufi kusa da kashi ko jijiya haka.

Da sauri ta É—auko X-ray machine, na'urar ce da ake amfani da ita kafin cire bullet dan gano wurin da bullet É—in ya tsaya sosai. Idanunta ta kura a kan na'urar tana kallon yadda bullet É—in ta fasa namar damatsan hannunsa ta shiga ciki. Sosai tausayinsa ya kara kamata, ganin ta gano in da bullet É—in yake ne yasa ta ajiye machine É—in a gefe ta É—auko scalpel, wukar duba ta asibiti, ana amfani da ita dan buÉ—e fata ko nama a inda bullet É—in ya shiga. Ganin tsokar nama ta yi yawa a damatsan nasa ne yasa ta É—auko x-c dan reÉ—e namar ta rage. A natse take aikin cikin tsari da tausasawa, amma cikin zafin jini babu kasala a tattare da ita.

Dik abin da take yi mashi yana ganinta, idanunsa biyu amma bai motsa ba, da yake ma ta yi mashi alluran kashe zafi!.

Bayan ta reɗe namar wajen ta ajiye a gefe ne sai taga jini ya tsananta zuba sosai, hakan yasa ta ɗauko suction machine, na'urar da ake amfani da ita dan tsotse jinin, bayan ta rage mashi jinin wajen sai ta ɗauko antiseptic solution, magani ne irin chlorhexidine da ake amfani da shi dan tsabtace wurin harbin, a natse ta tsabtace wajen tsab kafin ta ɗauko retractors, wannan da ake amfani da shi ne dan riƙe nama da buɗe wajen aikin dan ganin bullet ɗin sosai.

Yanzu ta samu ganin bullet ɗin yadda yakamata, dan haka sai ta rike retractor ɗin da hannu ɗaya, ta sa ɗayan hannunta kuma ta ɗauko forceps, wannan abin ne mai kama da almakashi, ana amfani da shi dan kama bullet ɗin cikin sauƙi. A hankali ta riko bullet ɗin ta cirosa, kai tsaye ta jefasa cikin ruwa mai sanyi sosai dake cikin bowl da ta ɗauko before.

Wani irin jini jajir ne ya fallatsa ya biyo bayan wannan bullet da ta cire, hakan yasa ta yi saurin ajiye su retractor ɗin ta ɗauko sterile gauze pads, da shi ta yi amfani dan tsotse jini dake ɓulɓula a wajen!. Sannan ta ɗauko irrigation syringe, sirinji mai girma da ake amfani da shi dan wanke wurin da ruwa mai tsabta ko maganin kashe kwayoyin cuta, so ita ma da maganin ta wanke mashi wajen.

Bayan ta kammala ta É—auko sutures, Igiyoyin likitoci da ake amfani da su dan É—inki wurin da aka yi aikin. A natse cikin tausayawa sosai ta É—inke wajen tsab sakamakon yanka naman wajen da ta yi da kara buÉ—a wajen harbin, sannan ta sanya sterile gauze pads da bandage ta rufe tsab, dan kare wurin kada wata cuta ta samu hanyar shiga.

Bayan ta kammala komai ta tattare tsab, ta gyare wajen ta kuma goggoge jininsa da ya zuba har saman mattress na bed ɗin. Ko'ina ya zama tsab-tsab tamkar ba'ayi aikin komai ba, sai dai bata lura da uban jinin da ya malala ta kasan bed ɗin ba, dan a lokacin da ya kwanta ya saki hannun nasa jini ya zuba sosai har ya malala, hankalinta ya tafi wajen ƙoƙarin ceto ransa yasa bata kula da jinin ba.

Kurawa wajen da ta yi mashi aikin idanu ta yi na ƴan mintoci kafin ta dawo da kallonta a kan fuskarsa. A ranta ta ce. "Yana buƙatar magunguna irinsu antibiotics dan hana kamuwa da cuta, e.g. ceftriaxone, da kuma painkillers dan rage zafi, da e.g. paracetamol, tramadol, sai anti-inflammatory drugs, dan hana kumburi wajen da kumburin jiki, da tetanus injection, lastly sai wound dressing set, dan canza bandage akai-akai, ga shi bani da su a gidan nan".
A saman wani sofa set mai zaman mutum biyu dake cikin ɗakin ta zauna tana mayar da numfashi, ta yi aiki matuƙa, dan har 4 na asuba ta yi.

-------------------------🔥

4:30AM. Daidai agogon jikin bangon ɗakin ya buga. Barci ɓarawo ya ɗan fara ɗaukarta, tamkar a mafarki a hankali ta fara jiyo sautin alamar tafiyan mutane a cikin gidan wanda hakan ya yi mugun ɗaga mata hankali yasa ta farka a firgice, ji ta yi tamkar buɗe parlo door ake ƙoƙarin yi. A zabure ta kai kallonta kan patience ɗinta dake kwance saman gado, taga dai ko alamar motsi bai yi ba.

Miƙewa tsaye ta yi tana dafe saitin zuciyarta. Da sauri ta nufi kofar fita har kamar zata kifa, a ranta take faɗin yau kuma wace iriyar kaddara ce wannan? A fili kuma ta ce. "Hasbiyallahu wani'imal wakil".

Kamar É—azun a guje ta nufi É—akin Æ´arta, still dai yarinyar tana ta zuba barcinta cikin kwanciyar hankali. Addu'a ta yi ta tofa mata kafin ta nufi waje, ta jawo door ta rufe mata sannan ta nufi down da gudun gaske. ÆŠai-É—ai bibbiyu take tsallake steps É—in nan.

Tana isa tsakiyar parlo sai gani ta yi an banko door ɗin an shigo. Gabanta ne ya buga da karfi ganin kartin maza majiya karfi kuma madaka katti har guda biyar sun afko cikin parlon. Gabaɗayansu sanye suke da bakaken kaya tamkar waɗan da zasu tafi taron ƴan wuta, ga wata uwar rigan sanyi mai zubin puffer jacket da ta kai masu har kasa sosai, sun sanya hular rigar a kansu wanda ya sanya fuskokinsu bata fita ba, ga nose mask daga ta ciki da suka gargame fuska da shi. Irin waterproof boot ɗin nan ne a kafansu, ga wasu maka-makan hand gloves a hannayensu, a takaice dai baka iya ganin komai nasu, iya jajayen idanunsu ne kawai a waje shi ma idan ba ka leƙa cikin hular rigar sanyin nan ba baka iya ganinsu.

Salati ta fara yi jikinta na tsananta kerma. Cikin harshen turanci ta fara tambayarsu. "Who........are...... You". Da kyar ta iya faÉ—in hakan.

Dik cikinsu babu wanda ya yi magana, suka nufo cikin parlon, suka jero har in da take tsaye. Kasancewar su biyarne yazamana É—aya yana tsakiyarsu kenan, hakan yasa na tsakiyar ya É—aga hannu sama ya kyasta yatsunsa, take suka yi wa matar zobe, ko bata ga fuskokinsu ba tasan waÉ—an nan babu alamar imani a tattare da su.
Chapter 2 · 0% Book details