← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 227

Sashe 79

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da gudu ta diro ta zo ta rungumi Madam tana faɗin. "Mom ki zo mu yi murna, ana hira da Admiral, my hero, jarumin da babu biyunsa a duniya, kinga hira da shi ake yi a kan IRON FIST ɗin nan da suka addabi al'umma, an miƙa masu case ɗin ne su kamosu, mom admiral basu taɓa karɓar aiki kuma su faɗi ba, yanzu karshen IRON FIST zai zo, zasu daina ta'addanci da kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba". Dik a kiɗime take magana tana haɗe words, daɗi yasa bata san ma me take faɗe ba.

Kun san waye wannan da Seraphina ta ruɗe a kansa? Gaskiya bai taɓa karɓar aiki kuma ya faɗi ba, kwararre ne, jami'in SEAL U.S Special Operations ne, idan ana maganar Seal a waje to ba'a kiran dik wani jami'i, Seal yana nufin SE Sea ruwa kenan, A Air sama kenan L Land kasa kenan, a takaice SEAL na nufin Sea, Air, and Land. Su ɗin sojoji ne da ke iya yaƙi a ruwa, sama, da ƙasa, Su ne ƙwararrun sojojin U.S Special Operations da aka basu horo mai tsanani sosai da babu biyunsu, su zasu iya aiki a kowanne irin muhalli, teku, kogin, bene, cikin ruwa, kan ƙasa, da kuma ayyukan da ake tsallaka cikin jirage ruwa da sama, ba kamar sauran sojoji suke ba, a sauran sojoji zaku ga na ruwa daban, na ƙasa daban, Air Force ma daban, kuma kowannensu da irin horon da ake bashi, to su haɗe masu horon dikka ake yi a masu, imagine!

Baa ɗaukar mutum horon Seal sai idan ya karɓi horon aikin soja, dan haka kawai ba zai iya karɓar horon seal ba, ba kowa yake iya haye horon ba ko da ya karɓi horon soja, za'a ɗauki mutane 50 amma da kyar 5 suke iya hayewa basu mutu ba, a horon suke mutuwa, manyan tekuna ake jefasu a masu horon sojojin ruwa, sanna a masu horon sojojin sama, azo a masu horon sojojin ƙasa, ga training na sirri da ake basu kan kwarewa a ɓangaren fasaha da sarrafa computer, wlh dik US su ne jami'an da babu biyunsu, kuma basu da yawa saboda ba kowa yake iya tsallake horonsu ba.

To shi wannan guy da Seraphina take haukar cewa yana burgeta shi ne O-9 Vice Admiral na Seal Special Operations, mutum ne da babu wanda yasan fuskansa, kullum suna sanye da covering nose mask, kuma idan ba babban aiki irin kama IRON FIST ba ba zaku gansu a hira da wasu ba, basa shiga jama'a saboda suna ɓangaren jami'an sirrinsu ne, shiyasa basu bari an san face ɗinsa ba.

Su uku ne mafiya kwazo a hukumar Seal, wanda matsayinsu yake tafe a jere. Da O-10 Admiral mai matsayi kaman ace GAT a hukumar sojan ƙasa, sai O-9 Vice Admiral mai magana a wannan hira ta yanzu da Seraphina take gani, sai kuma O-8 Rear Admiral upper half, su ukun nan daban suke, kuma ba'a taɓa kallon complete face ɗinsu ba, tin Seraphina bata yi wayau sosai ba take kaunarsu a jami'an Seal, dan time to time tana bibiyarsu a wayar mom ɗinta, tana mugun son jarumai ne yarinyar.

Amma kun san wani abin mamaki? Wannan da ake live da shi ɗin fa ba kowa bane face Aryan, a idanun duniya su ne seal, a bayan duniya sune IRON FIST, yanzu gwamnati ta gagara kama IRON FIST shi ne aka damƙa masu case ɗin, dan an san dik US babu jami'ai masu aiki da cikawa biyun, to my people ya kuke ganin wannan wasa zata kaya? Zasu gagara kama IRON FIST ne su zamana karo na farko a rayuwansu sun faɗi a mission? Ko kuma zasu kama kansu ne a matsayinsu na IRON FIST? Ga shi dai sun karɓi mission ɗin, sun kuma rattaɓa hannu! Me kuke tinanin zai faru? Zasu yi aiki da basira a wannan ɓangaren ne ko kuwa dai ya zasu yi?.

IRON FIST a bayan fage, US SEAL SPECIAL OPERATIONS a idanun duniya, jami'an da duniya ke girgiza da jin sunansu, gaskiya su Lion akwai ƴan rainin wayau, to yanzu ya zasu gudanar da wannan mission fisabilillahi? Gasu can a AVARIS suna gudanar da bincikensu a kan aikinsu na IRON FIST, sun hau live sun sanar da sun karɓi aikin kama IRON FIST, kai ana wani iya shege a littafin FIVE LIONS, nima zan so ganin ta yadda zasu kama kansu kam!.

Da yake dik wanda ya kwana a Us ya tashi yasan su waye Seal Special Operations (SSO) bari in taƙaita masu sunan, kowa yasan su waye jami'an SSO, hakan yasa Madam ta ce. "Kai Alhamdllh, lokacin kawo karshen waɗan nan IRON FIST ɗin ya yi babyn daddynta".

Matsawa Seraphina ta yi, ta shige jikin Madam tana gwada mata yadda SSO suke magana a live, live ɗin da ya tara manyan jami'ai daga sassar duniya, manyan shugabanni, kowa kawai burinsa yai magana da su, su kuma da Aryan ne da guru a wajen suke magana, Lion yana barci, bai ma san ana yi ba, kuma shi ne admiral ɗin da ya rattaɓa hannu a kan misson na kawo karshen IRON FIST a duniya, amma kunga ɗan duniyan barcinsa yake hankali a kwance, sun je yawo ne suka dawo, yanzu ba jimawa dawowarsu daga Arewacin ƙasar Avaris, sun je binciken da suke yi ta bayan fage, dik a gajiye ya dawo shiyasa yake barci.

Idanu Madam ta zuba tana ganin yadda manya ke magana, idan Aryan zai yi magana sai kowa ya haÉ—a natsuwansa, gasu Æ´an gayu ne Æ´an kwalisa, akwai shegen iya É—aukar wanka su ukun nan, kuma kaya iri É—aya suke sanyawa, komai É—insu iri É—aya, zo ku ga yadda ake magana cike da jarumta ga sharp voice, sannan ga class da tsantsar natsuwa sai IRON FIST.

Da sauri Seraphina ta ce. "Mom ki bani wayarki in kira daddyna in faÉ—a mashi ya kunna world live ya ga SSO suna magana, bana son kiransa da wayana dan kada live É—in ya katse, ina son in faÉ—a mashi kuma ina kallon live".

Da yake na faÉ—a maku dikkansu fuskokinsu a rufe sai bata gane Aryan ba, kuma iya face É—insu ne a Camera, sannan suna sanye da p-cap daga shi har gurun. Ita ma Madam bata gane Aryan bane, da yake ita dama bata san ainahin face É—insa ba, Seraphina kawai ya nunawa, idan zai shigo gidan kuma shi yasan hanyar da yake shigo kai tsaye sai room na Seraph kaman wani aljani.

Da sauri Madam ta bata wayar, shigar da number Aryan da ya bata ta yi, jikinta har yana rawa wajen shigarwa, sai ta ga ashe Madam tana ma da number, danna mashi kira ta yi. Suna tsaka da live ɗin sai ta ga vice admiral ya miƙe tare da barin wajen, turo baki ta yi tare da cewa. "Mom ina vice zai je?".

"Kai babyn daddynta akwaiki da rigima, to gama wayar mana sai ki fara neman jin ina zai je". Madam ta bata amsa cike da mamakin halin Seraphina da shegen son jaruman mutane...... Tin É—azun Aryan ya yi picking call É—in yana jinta tana zubawa Madam shiriritarta, da ya ga alamar ta mance da ta kirasa sai ya ce. "Baby what's going on?".

Murmushi ta yi tare da ƙara manna wayar a kunne da kyau, cike da farinciki ta ce. "Daddy ka kunne wayarka ka duba Us military world live yau my hero's suna live"...... Mamaki ne ya kama shi, shiru ya ɗan yi kafin a ransa ya de. "Blood is thicker than water, watau Seraphina bata sansu bama sonsu take yi, bata taɓa ganin Lion and Guru ba, amma suna cikin ranta sosai, bare shi da ta san face ɗinsa, tana tsananin son shi sosai, ALLAH mai iko.

Sayayyar voice ɗinta ne ta katse shi da cewa. "Daddy baka jina ne? Please ka je ka gansu, jarumai ne, zasu kawo mana karshen IRON FIST masu kashe mutane fa"...... Face ɗinsa ne ta ɗan canza, a sanyayye ya ce. "Baby baki son IRON FIST ne?"........ Da sauri ta gyaɗa mashi kai tare da cewa. "I hate them daddy, mugaye ne, suna kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba, daddy su fa suka kashe mom and daddyna, don sune terrorists na ƙasar nan, nasan for sure su suka kashe mammyna!". Ta kai karshen maganar idanunta na cikowa da kwallah.

"Is okay baby, Don't cry, I agree that you don't like IRON FIST, but don't cry over them, I'm going to hang up now, I'll call you back later, I'm doing something right now". Ya kai karshen maganar da alamar damuwa a tattare da shi, bai ji daÉ—i ba yadda kowa yake masu kallon manyan Æ´an ta'adda.

"Daddy make sure you watch the live ka ji?"....... Da sauri ya amsa da okey tare da katse kiran. Nisawa yai tare da É—an jingina da jikin sofar parlon É—akin da suka kama, yai shiru yana tunanin kukan Seraphina, da yanzu yana CP babu abin da zai hana shi zuwa gareta ya rarrasheta, yasan sai ta yi kuka tin da tai maganar iyayenta, shiyasa yai saurin katse kiran dan kada ya ji kukanta, yasan Madam zata rarrasheta shiyasa bai damu sosai ba. A fili ya ce. "Zayra'an baka yi wa Seraphina adalci ba ko kaÉ—an, me laifinta zaka ce baka sonta a kusa da kai? Ka manta hakkinta dake kanka? Ka manta ita É—in amana ce a kanka da ALLAH zai tambayeka ka rike amanar? Ya ka yi da ita? Gaskiya baka kyauta ba!.....".

Jin motsin fitowa ne yasa yai shiru tare da É—ago kai ya kalli kofar shigowa, guru ne ya fito yana zura hannayensa a cikin aljihun pj's É—in jikinsa. A kusa da Aryan ya zauna, cikin natsuwa da sanyin murya ya ce. "What are you thinking bro?".
Chapter 79 · 0% Book details