← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 227

Sashe 124

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kifa kansa a jikin table ya yi yana sauraran hirarsu har suka shiga toilet, basu aikata komai ba, wanka kawai suka yi suka fito, dik hirarsu yana ji, har suka gama suka shirya, Rimsha tasa abayar da suka sayo a shopping, Seraphina ma ta sanya abayar da ta É—auka cikin sayayyar Rimsha. Daga nan suka dawo parlo suka hau hira da Faryan, suka bar wayoyinsu a É—aki.

Ai Aryan yana ganin su Rimsha sun tafi ya miƙe ya yi wanka, ya ɗauro alwala suka wuce masallaci, bayan sun yi sallar magrib da ishai suka fito shi sai ya wuce wajenta, guru na tsokanarsa bai tanka ba, saboda burinsa kawai ya je wajenta ya faɗa mata kada ta sake yin wanka da kowa. Zuciyarsa ta kara ninka tsanar Rimsha sosai, saboda ita ta ce su yi wanka a tare, sai ya ji yarinyar gabaɗaya ta fita ransa over.

Bai san ba laifinta bane, ko bata ce ba Seraphina zata ce, saboda wannan É—abiar Æ´an boarding ne cire kaya gaban juna da wanka a tare, basu É—aukesa a wani abu ba.

A bakin door ya tsaya yana kallon yadda ta yi balain kyau cikin abayar, tana rike da waya suna chat da Rimsha, tana faÉ—a mata uncle Faryan sai yabon kyanta yake yi, sai zuba murmushi take yi an yaba kyanta. Unexpected ta ji ya kwace wayar.

Da sauri ta ɗago kai, tana ganin shi ne ta saki ƙayataccen murmushi game da cewa. "Daddy shi ne ɗazun ka gudu ka barni ko?".......... A gefenta ya zauna tare da zuba mata ido bai ce komai ba. Gyarawa ta yi ta kwanto da kanta a saman laps ɗinta, ta juyo tana kallon kyakkyawan face ɗinsa da ya yi masifar yi mata kyau yau, yana ɗan ciza lips ɗinsa yana kallonta.

"Daddy ka yi kyau sosai yau". Ta faÉ—a tana riko hannunsa. Nisawa ya É—an yi tare da cewa.

Likes comments and share fisabilillah.

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 For more information 08161390581 Whatsapp me only.

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

STEP 1🔥

2025-12-8.🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E_____________ 42 & 43

"Daddy ka yi kyau sosai yau". Ta faÉ—a tana riko hannunsa. Nisawa ya É—an yi tare da cewa..... "Dik kyan daddy bai kai rabin baby Cherry Bloom ba, kin fini kyau ai"........ Juyawa tai, ta kifa a saman mattress É—in tare da kwantar da kanta da kyau a kan laps É—insa, tana É—an wuwwurga kafafunta ta ce. "Daddy da gaske na fika kyau?".

Shiru ya ɗan yi for almost 2 mins kafin ya ce. "Seraphina tashi mu yi magana". On a serious note yai maganar, hakan yasa ta miƙe zaune tana ɗan turo baki. Ɗan lumshe idanu ya yi saboda dafa laps ɗinsa da ta yi ta miƙe, zama ta yi suna fuskantar juna, ta natsu tsit.

Hannunta ya kama cikin nasa, a natse ya fara gwada mata haramcin shiga toilet mutane biyu, ya ce haramun ne ma kallon tsiraicin juna. Ya so ce mata ma'aurata kawai aka halattawa ganin tsiraicin juna, amma sai ya fasa saboda shirmen da tai mashi ranar, kada tasa yau ma yai suɓutar baki, maganin kada ayi kada a fara, da yanzu yasan karamin aikinta ne ta jefa mashi tambayar da zai hana shi barci.

Da yake tana son shi sosai, sai ta ce. "Ka yi hakuri daddy, ba zan sake ba, dama a school ne muke yi tare har da su sister Aana idan muka yi lattin zuwa class, amma ba zan sake ba"...... Ajiyar zuciya ya sauke tare da sake hannayen nata kafin ya ce. "To kada ku sake".

FaÉ—owa jikinsa ta yi tare da cewa. "Daddy baka zo kun gaisa da Rimsha bafa, ta zo har gidan nan"........ ÆŠan É—auke wuta ya yi na É—an sekonnin jinta a jikinsa kafin ya ja dogon numfashi tare da saukewa a hankali, tsintar kansa yai a wani irin yanayi, É—an gyaran murya ya yi kafin ya ce. "Cherry ba kin ce kina son daddy ya aureki ba?".

Da sauri ta gyaÉ—a mashi kai alamar e......... "To tashi in faÉ—a maki wani abin". Da sauri ta raba jikinta da nasa, tana kallon kyakkyawan fuskansa........ "Cherry, idan har kina son daddy ya aureki to ki daina hawa jikina".

Cike da mamaki ta ce. "But daddy why? Are you not my daddy?"........ Ɗauke kallonsa daga kanta ya yi, on a serious note ya ce. "Idan kina hawa jikina yanzu to aure zai haramta ne a tsakaninmu, ki bari sai mun yi auren tukun nan, ko oyoyo daga yau na hana, and in kina son in aureki ki dinga sanya ɗan kwali, ki kuma koyi sirri, kada ki sake faɗawa Rimsha abin dake tsakaninmu, dan babu kyau ki dinga faɗawa wata wani abu a kan mijinki". Ya so ce mata idan tana kwanciya a jikinsa tana jefasa cikin wani yanayi, amma ya yi saurin kama bakinsa gudun ta jefesa da wata tambayar da ba zai iya amsawa ba, dan Seraphina kam hankalin da sauƙi.

Hannu ta sanya ta toshe baki, tana É—an murmushi ta ce. "Daddy waye ya faÉ—a maka ina faÉ—awa Rimsha maganarka?"......... Wani irin kallo mai wuyar fassaruwa ya watsa mata kafin ya ce. "Kina faÉ—a mata ko baki faÉ—a?"..... ÆŠan turo baki ta yi. "Ai kaÉ—an nike faÉ—a mata ba dayawa ba"....... "Awwe ashe dai kina faÉ—ar"....... Murmshi ta É—an yi ta sanya tafukanta ta rufe fuska. Wani irin kallon kauna ya wurga mata da waÉ—an nan dara-daran eyes É—in nasa.

"Dubeta a wajen". Ya faɗa yana ɗan ciza harshe......... "Kai daddy kai daddy ka bari mana". Ta faɗa tana kai mashi dukar wasa a kirji. Wani irin yanayi mai mugun daɗi ya tsinci kansa a ciki, sai kuma ya miƙe ya koma saman sofa, ya zauna yana cigaba da kallonta, ALLAH ne kaɗai yasan irin son da yakewa babyn Cherry ɗin nan nasa, kome take yi kyau take ƙara mashi, yarinyar ga shiga rai.

Haka suka kasance, har around 10 na dare, yai mata sallama ya fito, tamkar zata yi kuka, bata son rabuwa da shi, to amma ya zata yi? Dole ta hakura.

Yana fita ta kira Rimsha, Rimsha na É—agawa ta ce. "My Nisha kin san me?". Rimsha dake kwance a room na Faryan ta tada kai da laps É—insa suna kallo a laptop É—insa ce ta amsa da. "Ina zan sani tin da baki faÉ—a mun ba, meyafaru?".

Cike da farincini ta ce. "Daddy ya ce idan ina son ya aureni wai in daina faɗa maki tsakanina da shi, kuma wai in daina hugging ɗinsa, mu daina wanka tare". Sai murmushi take yi ta faɗa, tamkar ba yanzu ya gama ce mata kada ta sake faɗa ba........ Miƙewa zaune Rimsha ta yi tare da cewa. "To amma waye ya faɗa mashi kina faɗa mun?"........ "Ni ma ban sani ba, kawai ya ce in daina faɗa maki ne"........ Dariya Rimsha ta yi tare da cewa. "Daddyn nan naki daga gani rigimamme ne, to ba zaki daina faɗa mun ɗin ba, mu ba aminai bane? Mun zama one blood ma yanzu".

Tana murmushi ita ma ta ce. "Ai na ce mashi to ba zan sake faɗa maki ba, amma ba zan daina ba, kuma ba zai san na faɗa maki ba, yanzu ki bani shawarar yadda zan sa ya so ni sosai kin ji?"...... Satar kallon Faryan dake kallonsa ta yi kafin ta ce. "Ina room ɗin uncle Faryan, ki bari anjuma idan na koma ɗaki"........ Hararar wasa Faryan ya dallah mata kafin ya ce. "Me kuke ɓoyewa?"....... Da sauri ta ce. "Uncle wannan da muka je gidansu ɗazun ɗin ne fa! Star ladyta! Ka tina?".

Da sauri ya ce. "Yauwa bani ita mu gaisa". Bata kawo komai a ranta ba ta miƙa mashi wayar, karɓa ya yi suka gaisa, bayan sun gaisa ya dinga yabon kyanta, sai murmushi take yi, daga bisani ya ce. Bai so daina kallonta ba, dole ce kawai tasa, amma please ta turo mashi pics ɗinta dayawa bari ya dinga gani.

Cike da murna ta ce mashi to zata turowa Rimsha ta turo mashi, daga haka suka yi sallama, ya katse kiran tare da dawo da kallonsa a kan Rimsha da ta tsaresa da ido. "Kai Nisha wannan kawar taki akwai kyau, kina ga eyes É—inta, i wish in sameta matsayin mata, kai Nisha ina ganin ina sonta fa".

Hannu bibbiyu Rimsha tasa ta toshe baki tana murmushi kafin ta ce. "Uncle yau da kanka kake son mace?". Gerarsa irin na Aryan É—in nan ya É—aga mata, cikin salon son Seraphina dake ratsa zuciyansa ya ce. "Wlh wani irin sonta ne ya shigeni tin da na fara kallonta, please Nisha help your uncle kin ji? Kinga kawarki ce, zaki iya koya mata sona".

Aikuwa cike da farinciki ta ce. "Uncle ko dan yadda ka kasance kai É—aya ne mai sanyani farinciki a gidan nan dole in tayata samo zuciyar Seraphina, nima ina kaunarta sosai, zan so ta shigo zuriarmu kuma gidanka, ba zata yi wahalar samu ba, tana sona, tana da saukin kai, zata so dik abin da nike so, and zan baka numberta, kai ma ka dinga kiranta"....... Ya ji daÉ—in wannan kalamai, bai san time É—in da ya bawa cheek É—inta haÉ—aÉ—É—en sumbata ba, cike da farinciki ya ce. "In dai kika tayani shawo kanta nai maki alkawarin sabuwar waya da sabowar mota and laptop".

Wani irin tsalle ta daka ta rumgumesa tana murna, shi ma rungumeta ya yi yana murmushi.

A yayin da haka yake faruwa, shi kuma Aryan yana master room na Abba suna magana da Abba a kan Rimsha, bai samu damar sauraren voice na wayar da su Rimsha suka yi yanzu ba.

Yana zaune a gefen gadon Abba, while Abba yana kwance saman bed. Dik abin dake faruwa Aryan ya zayyanewa Abba game da Rimsha, abin da ya gani da idanunsa na abin da aka koya masu a school. Daga karshe ya ce. "Abba aurar da ita zan yi, zan haÉ—ata aure da Vash in the next 2 months masu zuwa!". Babu wasa a kan fuskansa.
Chapter 124 · 0% Book details