← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 212 OF 227

Sashe 212

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya yi mamakin ganin wayarta ce, kenan tashin hankali yasa a lokacin da ta shigo ɗakin ta manta waya? Karkaɗe wayar ya yi game da ɗauka ya fita, rufo kofar ya yi ya nufi room ɗinsu na gidan, a nan ya ɗauki towel ya goge wayar, sai ya yi ƙoƙarin sakata a caji, amma babu caza, addu'a yake ALLAH yasa wayar bata mutu ta daina aiki gabaɗaya ba, ALLAH yasa ta tashi.

A aljihunsa ya sanya wayar kafin ya fita ya nufi ɗakin dad. Ko da ya je bai sanar da Lion ya ga wayan mom ba, yana son ya fara binciken komai da kansa kafin ya sanar da Lion........ In short sun yi kewaye sosai a gidan, amma basu bi diddigi ko bincike-binciken abubuwan ba, sun dai duba komai yana nan, babu abin da zasu buƙata ko da zasu dawo gidan.

Sun ɗauki a kallah 3 hours a gidan kafin su nufi gida, suna komawa kuma ɗakin aikinsu suka shiga, aikin awa ɗaya suka yi, a nan Lion ya ce akwai wasu containers da ake shirin shigo dasu cikin ƙasar daren yau, ya yi bincike ya gano ta ɓarauniyar hanya za'a shigo da su, dan haka Vir and guru su dakatar dasu, su kwace containers ɗin dan su san me aka ɗauko a ciki, sannan su kashe dikka direbonin containers ɗin, mutum ɗaya kawai zasu barshi da ransa, su mashi ɗaurin goro su dawo da shi zuwa ɗakin azabtar da mutanensu.

A kan haka suka tsai da matsaya yau, daga nan Aryan ya gudu wajen Seraphina. To mu koma kan labarin.

Wanka Seraphina ta yi, ta shirya cikin crazy jeans baki, da polo t-shirt fari tas, ta je Madam ta gyara mata gashi tana tambayarta a daren nan kwalliyar me haka?. Cike da soyayya ta ce. "Daddy ne zai zo, shi ya ce in shirya".

Madam ta ce. "To ki zo ki ci abinci kafin ya zo ɗin"......... Ta maƙe kafaɗa tare da cewa. "Kai mom daddy ya ce kada in ci komai sai ya zo"....... Madam tana murmushi ta ce. "To daddy's girl, ajira ya zo ya baki a baki ko?". Ta faɗa a lokacin da take kammala gyara mata gashin ta ɗaure suka koma kan gado. Juyowa ta yi ta rungumi Madam tana murmushi.

Daidai lokacin Suhana ta shigo cikin ɗakin, wani irin kallon rainin wayau ta yi wa Seraphina, haushin Seraph take ji dan ta fita kyau da komai. A walaƙance ta ce. "Ke tashi ki fita daga ɗakin nan zamu yi magana ya dangi".

Seraphina da bata barin ko ta kwana ta amsa da. "Ɗakinki na shiga ne?". Ta faɗa tana tamke fuska tamau, irin ba wasan nan....... "Rashin kunya zaki mun ne? Am i your mate?"........ Taɓe baki Seraphina ta yi, ta mata kallon uku goma kafin ta amsa da. "To sannu dabino sarkin shekaru".

A fusace Suhana ta ɗaga hannu zata mareta Madam ta yi gaggawar rike hannun nata, babu wasa a kan fuskanta ta ce. "Kada ki kuskura Suhana, kada ki yarda ki yi gigin ɗaura hannunki a jikinta"......…. Cike da takaici Suhana ta ce. "To kenan Aunty sai in tsaya wannan ƴar kucakar yarinyar tana faɗa mun magana?".

Kallon uku saura kwata Seraphina ta yi mata, bata sake tanka mata ba, dan kuwa tasan in dai batun duka ne to mutum ɗaya ne kawai zai daketa ta haɗiye ta yi shiru, shi ne kuma daddy Champion, bayan shi wlh ko Madam ta daketa ba tare da kwakkwarar dalili ba sai ta rama, dan ba'a haifota dan wani ya taɓa lafiyarta ba! Tana ji da kanta da kuma jikinta, she respected herself! So dariya ma Suhana ta bata wai zata dage.

Miƙewa ta yi ta sauƙo ƙasan gadon Madam, sumbata ta mannawa Madam a cheek game da cewa. "Than you mom, ina ga daddy ya dawo bari in je". Ta faɗa game da baiwa banza ajiyar Suhana. Madam ta saki hannun Suhana tana ta faman murmushi suka yi sallama.

Seraphina na fita Madam ta ce. "Baki da hankali ne zaki ce zaki ɗaura hannunki a jikinta? Me ta yi maki? Baki duba yanayin jikinta bane? Kina ɗaura hannunki a jikinta wlh sai kin yi nadama, dan kuwa ko taɓata kika yi jikinta na nuna alamar hakan, bare mari, tsab yatsunki zasu bayyana a kan fuskanta, kin san waye daddyn da take kiran nan kuwa? Kin san a kanta zai iya komai ko baki sani ba? Zai iya ɗaure dikka zuri'armu, dan haka ki bi a hankali, na kawo ku gidan nan ne dan cikar burinmu ba dan faɗa da su ba, in kin san ba zaki iya jura ba gara ki koma". Babu wasa a tattare da ita ta faɗa.

Zama gefen gadon Suhana ta yi, tana turo baki na rashin kunya ta ce. "Sorry Aunty, it can't happen again"...... "Ya dai fi maki". Madam ta faɗa tana miƙewa.

Ita kuwa Seraphina ɗakinta ta koma, ta hau feshe jikinta da perfumes da ya saya mata masu daɗin kamshi, ta haɗu matuƙa sosai. Zama ta yi a gefen bed tana laluɓo wayarta zata kirasa, sai kuma ta fasa, ajiye wayar ta yi a gefen gadon ta miƙe da sauri ta nufi wajen curtains dake wajen door, a bayan labulayen ta ɓuya tana ɗan leƙowa.

After like 5mins da tsayuwarta a wajen ya shigo bakinsa a ɗauke da sallama. Tsayawa ya ɗan yi a tsakiyar ɗakin yana kalle-kalle game da shaƙar kamshinta da ta fesa yanzu, a cikin ransa ya ce. "Awwa yau ɓuyan mun aka yi kenan". Ya faɗa game da sake saurarawa, abinku da jami'an kwarai, tuni ya gano tana ɗakin ta hanya biyu, na farko sautin nunfashi wanda shi ko me yaya baya ɓuya a waje, muddin ka saurara sai ka jisa, na biyu kamshin perfume da ta fesa yanzu, ya nuna alamar yanzu-yanzun nan mutum yana cikin wannan ɗakin, dan kamshin bai ko gauraye da airfreshner dake ɗakin bama.

Juyo da kallonsa a kan curtains na wajen door ya yi, a nan ya ji karfin fitar numfashinta ya fi yawaita, kun san su a horon da ake basu ana mugun koya masu amfani da nunfashin mutum, ta haka ne suke iya zaƙulo abubuwa dayawa.

Ya gane nufinta yanzu, wai tsoratar dashi take son yi, juyawa ya yi kamar bai ganta ba, sai ta buɗe labulen ta leƙo, ganin yana ƙoƙarin wucewa zuwa bakin gado ne yasa ta yi murna bai gane tana wajen ba, a hankali ta fito, ta ɗan yi taku step uku kafin ta daka tsalle ta mashi kukan kare a kunne......... Da gangan ya nuna alamar ya razana, har da faɗawa saman gadonta.

Dariya ta fara yi tana karawa, zuba mata idanun ya yi yana ganin tsantsar kyan da ta ƙara. Sai da ta yi mai isarta sannan ta ce. "Daddy kai ba jarumi bane, ka cika tsoro, na fika jarumta, da nice ba zan tsorata ba, ka zo in koya maka jarumtata!". Tana murmushi ta faɗa. Shi kam kallonta kawai yake yi, yana jin tamkar ya jawota ya rungume, ta yi wani irin musulmin kyau tamkar amarya.

Ganin sai kallonta yake yi ne yasa ta natsu tare da komawa kusa da shi, cike da kisisina yarinyar nan har da tsugunnawa a gabansa, sai ka rasa daga ina take koyo kisisina da kirsa yarinyar nan.

"Sannu da dawowa daddy, am...... In..... Ka yi hakuri tsorataka da na yi, dik saboda soyayyarka ce". Tana turo baki ta faÉ—a. Shi kam izuwa yanzu dik wasu kalaman da zasu fito daga bakinta ya daina mamaki, yarinya kamar wata uwar mata, sai kirsa da kisisina.

Uhm rasa abin faɗe ya yi, sai kawai ya bita da ido. Kwanto da kanta a saman laps ɗinsa ta yi, ta riko hannunsa cikin nata, tana turo baki, a shagwaɓe sosai ta ce. "My gentle chaos talk to me mana".

Uhm miƙewa ya yi game da kama hannunta, ya miƙar da ita, ya jata suka nufi waje ba tare da ya yi magana ba. Shopping na sama suka nufa, sai faman kallonsa take yi, taga ya yi tsantsar kyau yau, wannan suit ɗin ta kara fito da kyansa.

Kai tsaye wajen abayas ya wuce da ita, da kansa ya zaɓo mata wani haɗaɗɗen after dress mai balain kyau fari tas da veil ɗinsa. Dress room na shopping ɗin suka shiga, da kansa ya ware rigar ya sanya mata a jiki, ya ce. "Haɗe maɓallan mu gani". Ya faɗa yana mata kallon ƙasa-ƙasan ido.

Turo baki ta yi. "Ni daddy ban iya sakawa ba, yadda ka fara haka zaka kammala"...... Ɗago eyes ɗinsa a kan face ɗinta ya yi, da sauri ta ce. "Da gaske ban iya ba, ai kaga ban taɓa sanya irin wannan kaya ba"....... Wani irin musulmin hararar kauna ya dallah mata kafin ya kai hannu saitin kirjinta ya kama maɓallan.

Zubawa hannunsa ido ta yi, sai taga yatsunsa suna ɗan rawa, baya son taɓa jikinta. Da sauri ya haɗe mata maɓallai ukun, zuwa flat tummy ɗinta maɓallan suke, sauran gaban rigar a buɗe, rigar ta haɗu sosai. Hannu yasa ya ware veil ɗin rigar, ya yafa mata a kai, sai ya ce. "Ki yi rolling ɗinsa mu je".

ÆŠan turo baki ta yi. "Ni daddy ban iya rolling ba"....... "Wannan kam nima ban iya ba, amma bari in kira ma'aikaciyar wajen ta zo ta maki". Ya faÉ—a game da juyawa da nufin ya fita....... Da sauri ta riko hannunsa. "Ni daddy ba sai ka kira wata ba, kada ma ta ji muryanka".

"To ba na sanya nose mask ba sarkin kishi? Ai ba wanda zai ga fuskata"....... Make kafaÉ—a ta yi. "Ni dai dik da haka daddy ban yarda ba". Ta kai karshe game da kama veil É—in, ta fara rolling tana cewa. "Na iya fa".......Zuba mata idanu kawai ya yi, awww ashe ta iya tsiyace dama.

Rolling ta yi mai kyau kamar yadda Rimsha take yi, ta ce. "Daddy na yi kyau?"....... Kawai tsintar kansa ya yi d kashe mata ido É—aya yana sauke ajiyar zuciya. Waro idanunta ta yi. "Daddy, dama ka iya kashe ido É—aya?"...... Siririn harara ya dallah mata, bai yi magana ba ya riko hannunta suka fito.
Chapter 212 · 0% Book details