Sashe 132
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A haka Rimsha ta fito ta samesu, hannunta ta kama tana faɗin. "Uncle zamu yi latti, ba kuna chatting ba?".... Kai ya jinnina mata alamar e, daga haka ta ja hannun Seraphina suna ɗaga mashi hannu suka wuce. Kullum tana chatting da Faryan, Aryan kuma yanzu baya zama sosai saboda yana aiki tuƙuru na son gani ya gano wanene yake yi masu wannan abin? Ina mom ɗinsu Lion take? Abin da ya ɗauke mashi hankali kenan yanzu yasa baya bibiyar chat na Seraphina.
Zuba masu idanu Faryan ya yi har suka kurewa ganinsa, nisawa ya yi tare da cewa. "Yah ALLAH ka mallaka mun wanna baiwa taka, ta tafi da zuciyata tafiyar da ba zan iya dawo da shi ba, ALLAH kada ka jarabceni da rasata ko kasako wani tseƙo a tsakani".... Ya jima tsaye yana addu'ar kafin ya shiga mota ya tafi, kuma abin mamaki har yau bai faɗawa Seraph yana sonta ba, shi dai yana ta faman ƙoƙarin su shaƙu da juna, zasu sha hira sosai kamar masoya, amma bai taɓa faɗa mata yana sonta ba.
Suna shigowa cikin school Rimsha ta ce. "Ke my star lady do you know something?"........ Kai ta girgiza alamar a'a. "Uncle Faryan sonki fa yake yi! So sosai ɗin nan ma, please ki so shi kin ji?"..…..... Da yake ita Seraphina ta ɗauka so daban kuma aure miji ma daban, a tinaninta zaka iya soyayya da wani, wani kuma zaka iya cewa mijinka ne, dan bata ma san yadda ake ɗaura aure ko yadda auren yake ba, dan haka ta ɗauka wannan kalma ta miji kamar uba yake nufi, boyfriend kuma shi ne yaren da ta fi ganewa.
San haka sai ta ce. "Ki bari ya faÉ—a mun da kansa". Ta faÉ—a tana gyara goya jakarta a baya. "To shikenan zai faÉ—a maki ai nasani, da gaske yake sonki". Jinjina kai kawai Seraphina ta yi.
Kamar daga sama Seraph ta ji an ɗan taɓa bag ɗinta ta baya. Slowly ta juya dan ta ga wanene? Sai ta ga mutum ya juya yana tafiya, yana sanye da wandon jeans daga ta ƙasa, daga sama kuma jacket fara tas, kafafunsa sanye da boot, ya sanya hukar jacket ɗin a kansa, ya zura hannayensu a cikin aljihu, dik da ya juya mata baya hakika ta gano ɗan kwalisa ne koma wanene.
Zuba mashi idanu ta yi har sai da Rimsha ta taɓata tana faɗin. "Ke me kike kallo haka?"...... Firgigit ta dawo cikin hayyacinta, zata yi magana Rimsha ta ciro wani ɗan teddy da aka manna a jikin jakar Seraphina ɗin tana faɗin. "Ya ALLAH, my star lady wannan teddy ɗin ya haɗu".
Da saurin Seraphina ta waro idanunta a kansa, lokacin guda ta saki wani ƙayataccen murmushi kafin tasa hannu ta karɓi teddyn, ɗan daidai da shi, an yisa yana haɗe da hannayensa waje guda, yana rike da wani heart da aka rubuta you're so pretty a jiki, teddyn fari tas, shi kuma rubutun baki, irin kyautar nan na masoya.
"A ina kika samu wannan haÉ—aÉ—É—en teddy É—in Nisha?". Seraphina ta tambaya..... Rimsha dake ta faman smilling ne ta amsa da. "A bayan bag É—inki na gani an manna".
Da sauri Seraphina ta sauƙo da bag ɗin nata, sai ga wani parin takarda ya faɗo, ɗauka ta yi ta buɗe. "Please bless my morning with your cool smile blossom". Shi ne abin da aka rubuta a jiki. Wani irin murmushi ne ya kubce mata wanda yasa wushiryarta ya bayyana.
"Wait for me Nisha, I'm coming".... Ta faɗa tare da juyawa da ɗan gudunta ta bi bayan mutum da ta ji ya taɓata ɗazun. Sai dai ga mamakinta ko alamarsa bata gani ba, waige-waige ta fara yi tana neman ta ina zata gansa.
A haka Rimsha ta kariso ta sameta, riko hannunta ta yi tana faɗin. "Lafiya kike kuwa?". ...... Kai ta ɗan girgiza game da cewa. "Mu je kawai"....... A tare suka juya suka cigaba da tafiya, ta ƙanƙame teddy ɗin a kirjinta, ya yi mugun yi mata kyau.
Suna barin wajen ya fito daga maɓoyansa yana sakin haɗaɗɗen murmushinsa irin na Noor ɗinmu na amana, watau familynsu Noor ba dai iya soyayya ba, yanzu zasu sace zuciya, ba'a takara dasu a fagen soyayya, dan mutum zai sha ƙasa ne. To waye ya faɗa mashi a nan school ɗin take kuma? Ga dikkan alamu ya yi bincike a kanta ne, kuma saboda ita ya nemi karantarwa a makaranta, abin da kunsan sun fi karfin hakan, amma saboda su tin ainahi sun iya bautawa soyayya shiyasa zai iya sauƙa izuwa kowani irin mataki dan ya samu soyayyarta. E KAM AKWAI BABBAN CASE! UNCLE ƊIN NOOR DA ZAFINSA YAKE TAFE. MU JE ZUWA.
A ɓangaren Aryan kuwa, yana barin school ɗin gidan Abba ya nufa bayan ya ajiye motarsa a gidan Lion. A wannan lokacin kuma Abba ya dawo daga gidansu Noor ransa a matuƙar ɓace. Ya je su sake ganawa da familyn Noor, in baku manta ba ai da ya je na farko daddyn Noor baya nan ko? To shi ne yaga yakamata ya koma ya gana da shi.
Sai dai yana koma ya isko kakan Noor na wajen uba, wani masifaffen dattijo, shi daddyn Noor kun san bashi da matsala, da Abba ya faɗa mashi buƙatarsa sai daddy ya ce ai wannan ba wata matsala bane, in dai su Aunty Luna suna so shi bashi da wata damuwa dan basu addini guda. Abba ya ji daɗin hakan sosai.
Sai kuma me? Wannan dattijon ya ce idan sama zata haɗu da ƙasa ba zai haɗa jini da wani addini ba idan ba mutane marasa addini irinsa ba!. Daddyn Noor ya yi ƙoƙarin faɗa mashi cewa ai hakan ba wani matsala bane, amma wannan dattijo ya ce daddyn Noor yai mashi shiru, har da karawa da cewa daddyn Noor bai san ciwon kansa ba, shi komai yana da sauki a kai, to shi ba zai ɗauki wannan iskancin ba.
Na faÉ—a maku daman cewa Abba yana da mugun zafi, da zuciya, aikuwa sai ya ce da dattijon. "Da a cikin lumana babu cin mutuncina ko cin mutuncin addinina ka ce ba zaka bani aure ba, da zan hakura, amma tin da iko da karfi zaka gwada mun, ka zagi addinina, wlh, narantse da sarkin da ya busan rai sai mun haÉ—a jini daku, waÉ—an nan yara sai mun auresu, zan gwada maka mun fika ji da kai da izza, ba'a haifi wanda zai kalli Muhammad Khaiza'an ido cikin ido ya gaggaya mun magana ba!!".
Aikuwa dattijo ya hau shi ma, ya fara surfa balai, wai ko ya mutu idan daddyn Noor ya haɗa jini da su Abba bai yafe mashi ba, Uncle da daddyn Noor sun yi ƙoƙarin tausan dattijon, amma ina, yaki hakura, daga karshe dai suka yi baram-baram da Abba, har marinsa Abba ya kusa yi Uncle ya rikesa yana bashi hakuri.
Daddy Noor ya ja Abba waje, ya dinga bashi hakuri, ya ce mashi. "Kasan yanayin tsufa, amma ka bari zan shawo kansa a hankali"...... Cikin fushi Abba ya ce. "Ka shawo kansa ko kada ka shawo kansa dik ya rage naku! Aure ne a wannan gida sai mun yi, ko kuso ko ma ku ku ƙi!!". Babban magana!..... Daddy Noor ya ga ikon ALLAH, kai Abba akwai zuciya da saurin fushi, baya ɗaukar nonsense....... To daddy Noor, a matsayinka na uba ko ka bada auren ko kada ka bada Abba namu na gargajiya sai ya ɗaura wannan aure, yau ake yinta a CRYSTAL PALACE.
A fusace Abba ya baro benen yana wani irin huci, zuciyarta ta É—auki zafi, tin da ya shigo gida bai yi wa kowa magana ba, su Harleen sun kewaye shi suna tambayar lafiya? Amma ina, bai amsa kowa ba. A daidai wannan lokaci Aryan ya shigo parlon cikin fushi shi ma.
Domin kuwa yana gab da shigowa gidan ya haɗu da daddyn Noor, bayan sun gaisa daddy yake ce mashi. "Na zo kara baiwa Muhammad Khaiza'an hakuri ne a kan abin da ya faru, idan ba damuwa ka mun sallama da shi"...... Cike da mamaki Aryan ya tambayi abin dake faruwa, daddy ya zayyane mashi komai, ransa idan ya yi dubu ya ɓaci, shi ne Aryan ya ce daddy ya bar masu kofar gida tin kafin yai ball da shi. Dole ya juya da koma.
Shi kuma ya shigo cikin gida da fushi. Yana zuwa ya tsaya a tsakiyar parlo, kowa sai da ya sha jinin jikinsa da suka gansa a wannan yanayi. Cikin kunar rai ya ce. "Abba na faɗa maka bana son auren ana dole ne? Ba ga shi yanzu ka je ka ja an taɓa mana ƙimarka ba! A kan wata mace zaka ja wasu banzaye su faɗa maka magana! Ko so kake mu kashesu ne? Kasan zuciyarmu ba zata iya ɗaukar wani ya gaya maka magana ba meyasa zaka kai kanka wajen ƙasƙantattun mutane?!".
A fusace Abba ya ce. "Aryan sai ka auri wannan yarinya, dan sai na gwada masu ba'a ja dani!". Cikin dokin zuciya ya faÉ—a....... "No Abba! Ba zan auri kowa ba". Cikin fushi ya faÉ—a....... Da karfi Abba ya ce. "Zaka aureta Aryan!!"........ A fusace shi ma Aryan ya ce. "Ba zan aureta ba na ce maka, wai Abba rayuwata ce ko naka? Kai zaka zauna da ita idan ka aura mun ita ne? Ko zan mutu idan ban yi aure a wancan gidan ba sai dai in mutu, amma aure ba zan yi ba!!"..
A fusace Abba ya miƙe tsaye, jikinsa har yana wani irin kerma, ya nuna Aryan da sandar hannunsa, cikin tsawa ya ce. "Ko kaki ko ka so sai ka aureta, sai na gwada masu ba kowa ake taɓawa b!!".