Sashe 54
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Take murmushi ya ƙara bayyana a kan fuskan Seraph, har ƴan kyawawan hakwaranta suka bayyana a waje, farare kal dasu, tamkar bata taɓa cin wani abin ba, kamar audiga. Jawo school back ɗinta dake wajen drawer ta yi, nan ta fito da cardboard paper and pencil ɗinta. Ware shi ta yi, take wani kyakkyawan zane ya bayyana, zazzaro idanu a kan zanen Rimsha ta yi, cikin zolaya ta ce. "Da ace dik abin da muka zana shi zamu rayu da shi mana, da kin more over sis".
ÆŠan dariya mara sauti Seraph ta yi kafin ta ce. "Da kuwa ni kam na more ba, ke me kika zana ne ma?"......... ÆŠan turo baki ta yi kafin ta ce. "Ni waye na sani idan ba uncles É—ina ba, Uncle Faryan na zana"....... "Ban ga amfani sakamu zane ba". Star lady ta faÉ—a tare da fara nannaÉ—e nata zanen.
"Sister lady faɗa mun gaskiyar yadda aka yi kika yi wannan zane? Ban yarda dake ba, kina ga matashin da kika zana tamkar ba mutum ba!". A cewar Rimsha da ta dakatar da ita daga ƙoƙarin naɗe paper ɗin..... Ɗago ido ta yi suka kalli juna, sai ta kuma ta sauke da cewa. "Kawai zanen ne ya zo mun kaina na zana".
"Wlh ban yarda ba, ko dai saurayinki ne?"...... "Saurayi kuma?". Ta faɗa da alamar mamaki. "E mana, idan ba saurayinki ba kin manta ranar da uncle James ya ce mu yi zane a class wannan matashin kika zana, yanzu ma madam Rohisha ta sanyamu zane kin sake zana shi, dik yadda aka yi kuna da alaƙa".
Ɗan taɓe baki star lady ta yi kafin ta ce. "Ni ban san shi ba, kawai zanensa nike yi"........ Karɓar zanen Rimsha ta yi, ta zuba mashi ido na ƴan sakanni kafin ta ce. "Dik yadda aka yi yarinyar nan kin saba zana wannan zane sosai, ki duba wannan bashi da banbanci da na uncle James da ya bamu muka zana ranar"........ "Rimsha, ni fa ban iya wani zane bane sai wannan shiyasa kowani work na zane da za'a bamu shi zan zana in dai na mutane ne".
"Kenan yanzu tsakanina dake akwai ɓoye-ɓoye?". Rimsha ta tambaya cike da rashin jin daɗi abin da star lady take yi mata, tana da zurfin ciki da ɓoye abubuwa sosai, har yau taki ɗaukarta a matsayin ɗaya suke. Ganin ta ɓata rai yasa star lady ta ce. "Sorry sis, for give me, zan faɗa maki waye shi to".
Rimsha yarinya mai sanyin hali, take ta sauko ta ɗan yi murmushi game da cewa to ina jinki. Gyara zama lady ta yi tare da cewa. "Wannan shi ne kaɗai Uncle ɗin da nike da shi a duniya, brother ɗin mammyna ne, ban ma san in da yake ba, kawai na taso ne da kaunarsa a zuciyata, tin ban iya magana ba nike kallon hotunansa a ɗakin mammyna, da na fara wayau ta ce mun shi ne kaɗai kanin da take da shi, kila watarana zan haɗu da shi, lallai in san cewa shi garkuwa ne a gareta da bi bakiɗaya, ya taimaka mata a lokacin da duniya dikka suka juya mata ba, shi ya zama silar zamanta komai da ta zama a yau, shiyasa kika ga na iya zanensa sosai, hotunansa a gidanmu sun 100, mammy tana son shi sosai, amma fa ba ainahin kaninta na uwa ɗaya uba ɗaya ba, kanin daddyna ne, zamansu ya yi kyau ne yasa ta ɗaukesa tamkar kani, ko an tambayeta kaninta take cewa ba kanin daddyna ba, shiyasa nike son shi matuƙa, ba zanensa ba kome zan iya yi a kansa". Da iya gaskiyarta ta yi maganar.
Siririn murmushi Rimsha ta saki tare da cewa. "Ko dai ko dai"...... "Ko dai me?". Ta faÉ—a tana harararta. "Ko dai son shi ya kamaki?". ........ "Brother É—in daddyna ne fa, the same Father the same mother, aikin ga babu soyayya a tsakaninmu, da aka ce akwai damar yin soyayya to idan na girma zan yi aure shi kawai zan aura".
Yara da su sai manyance da iyayi ga shegen wayon tsiya.
Note sunan Seraph ni na yanke sunan, ainahin sunan Seraphina ne, saboda saukin kira yasa nike sauƙaƙa maku ta hanyar yanke sunan.
Murmushi Rimsha ta saki tare da kara ware zanen da kyau tana kallon kyakkyawan fuskansa, uhm batun haɗuwansa ba'a magana. Cikin zolaya Rimsha ta ce. "Har na ji zuciyata ta buga a kansa, ya haɗu sosai, shiyasa dik in kika yi zanensa sai kin cinye marking kin barmu a baya, dole in koyi zana shi ni ma ko dan samun marking, kuma ba karya ya haɗu, zan rinƙa zanensa in manna a bangon ɗakina a gida".
Harararta Seraph ta yi tare da kwace zanenta, a natse ta ce. "Uncle É—ina bai yi arha har haka ba, mutum ne mai tsada da darajar da ta fi lu'ulu'u, ba zan bari ki koyi zana mun shi ba, dan nasan har cikin toilet sai kin yi zanensa, yanzu fa shi ne uban da kawai nike da shi a duniya, ina fatan in haÉ—u da shi a nan kurkusa"...... Tana rufe baki sai ga Aana ta shigo room É—in, gadonta ta nufa tana faÉ—in. "Seraphina daddy É—inki ya zo, wai ki je".
Wani irin faÉ—uwar gaba ta ji, jikinta take ya yi sanyi saboda har yau tsoronsu take ji, dik da wancan zuwansa ya tausasa mata, ya kalleta da kulawa har da runguma, amma murÉ—aÉ—É—un mutane irin wannan ba'a gane in da suka dosa. NaÉ—e zanenta ta yi tare da maida shi cikin jaka, tana hararar Rimsha ta ce. "Mu je ki rakani".
Zazzaro ido Rimsha ta yi kafin ta ce. "Uncle ɗinki na jikin hoton nan ne?"... Kai ta girgiza alamar a'a tare da cewa. "Wannan wani ne, zan baki labari, mu je"......... Sauƙowa ƙasan bed ɗin ta yi, ta wuce gaba Rimsha ta rufa mata baya, kai tsaye suka nufi parking lot, dan yau ko office na director bai je ba, yana cikin mota a zaune.
Excuse ta yi mashi tare da buɗe front side, ta shiga tana ƙoƙarin matsawa Rimsha ta shiga ya rufe kofar da kansa. Lokaci guda ta ji babu daɗi, dan ita tasa Rimsha ta rakota, wannan kamar cin fuska ne ai, sam bata ji daɗi ba. Baya Rimsha ta koma ita ma, cikin rashin jin daɗi ta juya ta koma hostel ɗinsu, da kallo Seraph ta bita har ta kurewa ganinta, da yake akwaita da saurin kuka sai idanunta suka cika tab da kwallah, take violet ɗin suka ciza sosai.
Ƙasa-ƙasa ta ce. "Good afternoon daddy". Ta faɗa a daidai lokacin da hawayen da ya cika mata ido ya hau zuba. Sai da ya ɗauki good 2 mins kafin ya amsa da. "How's your day?". Ya faɗa tare da juyo da kallonsa gabaɗaya a kanta. Shiru ta gagara amsawa.
Intently ya miƙa hannunsa ya ɗago haɓarta, ya yi mamakin ganin tana kuka, kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya kasa, dan ba zai iya shareta ba a yanzu da ya gane wacece ita, sake haɓarta ya yi ya kama hannayenta dikka biyu da hannunsa ɗaya, jawota jikinsa gabaɗaya ya yi, ya ɗagata cak ya ɗaura a saman laps ɗinsa tare da ciro hankey daga aljihunsa. Hawayen ya fara goge mata a natse kafin ya ce.
"Why are you crying Seraphina?"...... Kai ta shiga girgiza mashi alamar babu wani dalili. Hannu yasa ya kwantar da kanta a saman faffaɗar kirjin nan nasa, ya ɗan yi shiru tamkar mai tinanin wani abu, ita ma shiru ta yi tana shaƙar daddaɗar kamshinsa. Almost 5 mins suna a haka kafin ya ce. "Ya school?"........ "Lafiya". Ta amsa.
"Akwai abin da kike so ne?". Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ce. "Please daddy idan an yi hutu kada ka kaini wancan gidan da kake kaini ni kaɗai ɗin, babu daɗin zama"........ "Nima yanzu bana son in kaiki in da zaki yi nisa dani, zaki zauna a gida tare dani"....... Dik da tana balain tsoron gidansu, amma sau dubu gara shi a kan gidan da yake kaita ta zauna ita kaɗai, ko ba komai a gidansu zata ji motsin mutane. Dan haka sosai ta ji daɗi tare da ɗan rungumesa kafin ta ce. "Thank you daddy". Yarinta fa kenan, har ta mance da ta taɓa jin tsanansa a ranta, kuma fa lokaci guda ita ma ta jisa a ranta, dik yadda aka yi suna da alaƙa ta jini mai karfi, irin wannan abu jini ne ke fusgarsu.
Sun jima suna tattaunawa, dik da bashi da yawan magana, amma ya daure ɗaya biyu suka ɗan yi hira, sannan ya ɗauko cartoon-cartoon na su chocolate, biscuits, har da su sweet sosai ya bata. A ɗan shagwaɓe ta ce. "Daddy Madam ta hana mu cin kayan zaƙi fa, wai cikinmu zai yi ciwo"........ Ɗan zuba mata ido ya yi, lokaci guda kwakwalwarsa ta fara tariyo mashi lokacin da take jaririya cikin towel a kwance, a ransa ya ce. "Ba zan taɓa manta lokacin da aka haifa mana ke ba, da hannunsa Lion ya ɗaukeki ya yi maki huɗuba da sunan da Seraphina ba, bayan tafiyansa Mammynki ta dage sai Seraphina take son a kiraki".
Katse mashi tinanin ta yi da cewa. "Daddy zaka koma da su sweet É—in ko?"........ Kai ya É—an girgiza tare da cewa. "Ki je da su, babu wani ciwon da cikinki zai yi, ai baki girma ba"...... Shiru ta yi, a ranta ta ce to zancen waye zata É—auka? Na Madam ko na daddyn nata?
Ganin ta yi shiru ne yasa ya ce. "Ki ce wa Madam daddynki ne ya ce ki zo da sweets ɗin"........ Da okey ta amsa tare da kwasan kayan ta fito. Bayanta ya bi da kallo har ta kurewa ganinsa, ajiyar zuciya ya sauƙe sannan ya tada mota ya wuce, ita kuma tana shiga room ɗinsu kai tsaye wajen Rimsha ta nufa. A gefen bed ɗinta ta zauna tare da cewa. "Sorry sis".
Miƙewa zaune Rimsha ta yi tana faɗin. "Nevermind my lovely star lady, daddyn nan naki akwai zafin rai da faɗa, amma ba komai"....... One side smiling ta ɗan saki kafin ta ce. "Wannen kikeso a cikinsu, zaɓa zan baiwa su Aana saura".