Sashe 104
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru dik suka yi, saboda sun san gaskiya yake faɗe, shegen son duniya ya mayar da kowa azzalumi mara imani. Gudun kada ta kwaɓe masu yasa suka yi shiru suka kyalesa, shi ma shirun ya yi, can kuma ya dunkule hannu ya daki glass na kofar motar sai da ta tarwatse saboda ba dukan wasa yai mata ba, gabaɗaya glass ɗin kuma ta farfasa mashi hannu sai jini jajir ta fara malala, takaici tamkar zai mutu, dik ta in da ya juya azzalumai ne masu son kai, su sha wahala su yi aiki tukuru amma tamkar basa yi saboda yadda zalunci ya cika ko'ina, dole ya fusata, dole ransa ta ɓaci, dole ya daki abin da ya fi glass.
Cikin zafa Aryan da guru suka damki hannun nasa, har suna rige-rigen damƙa. Sai dai ina, kwace hannun ya yi tare da sake dunkuleta ya daki jikin marfin motar har sai da ta girgiza, take glass ɗin suka sake natsawa cikin hannunsa, yana wani irin huci tamkar zai kama da wuta, with harsh voice ya ce. "Is better for me to die a kan irin wannan murɗaɗɗen rayuwa, kowa burinsa ya sami duniya, kowa ya manta da ALLAH da ranar tashin alkiyama, kana ƙoƙarin gyara gabas laanannun nan na kwance maka da lalata maka yamma!". Ya kai karshe tare da daddagewa ya buga kansa da jikin marfin motar ta wajen glass da ya fashe ya bar sauran guntu-guntu.
Cikin fusata ya sake ɗaga kan nasa zai buga Aryan ya rikesa da karfi yana ƙoƙarin dannansa. Dik glass ɗin ta fashe mashi goshi, abin akwai mugun cin rai da kayan takaici ne, ace jami'an da yakamata ku haɗa kai ku gyara kasar suke da alhakin wasu kaifukan? Dole ya shiga wannan mood ɗin.
Wani irin jiri ne ta fara ɗibansa a lokacin da yake ƙoƙarin kwace kansa daga damkar da Aryan ya yi mashi. Rikesa gam Aryan ɗin ya yi jini na ketowa daga gaban goshinsa in da ya buga kan izuwa kan tongue ɗinsa da ya ciza da hakwaransa tamkar zai fasa harshen nasa saboda tsananin takaici.
Guru ne ya cewa driver ɗin nasu ya taka motar da gudu sosai tin da sun kusa isa cikin airport. Basu ƙara wani tafiya sosai ba Lion ya ɗauke wuta a jikin Aryan saboda zafin da zuciyansa ta ɗauka, sumewa ya yi, ga zafin da kansa take mashi tamkar zata fashe.
Godiya suka yi wa ALLAH da ya sanya ya suma, zasu samu sauki. Shi ma Aryan É—in dauriyar ce kawai, amma ji yake tamkar yai ta buga kansa a bango kada ya dakata, wannan musifa dame tai kama.
To a haka dai suka dawo CRYSTAL PALACE, kai tsaye gida suka koma, Aryan da kansa ya yi treating Lion yadda yakamata, ya gyara mashi gaban goshinsa da hannun nasa, sannan ya bisa da alluran barci na good 5 hours dan ya samu barci, hakan zai sanya ya samu natsuwa kuma zuciyar ta sassauto.
Bayan sun tabbatar yana cikin aminci da kariyar UBANGIJI sai suka nufi room dake kusa da wanda yake a ciki, suka yi wanka, sannan suka shirya cikin pjs dan shan iska. Parlo suka dawo suka zauna, gabaÉ—aya Aryan bai nemi Seraphina ba, kuma tana ransa, dik wannan abin da yake yi tinaninta na cikin ransa, amma ya daure dan ya gwada mata yana fushi da ita har sai ta bashi hakuri.
Wayarsa ya ciro, ya kunne other sim ɗin tare da fara ƙoƙarin nemo number Faryan dan ya ji ya gida suke. Saƙonnin ne suka fara shigowa kamar ruwa, wasu tin daren jiya, sakonni sun kai 30, kuma dik na Seraphina ne. Kin buɗe saƙonta ya yi, ya nufi fita kan saƙonnin kawai unexpected idanunsa suka sauƙa kan sako da number Madam Rohisha.
Da farko kamar ba zai buɗe ba, amma da ya tina kila wani abin ne sai ya buɗe. Saƙo ne a rubuce kamar haka. "Tin da rana muke nemanka a waya a kashe, please idan ka buɗe waya ka gani ka zo gida baby taki cin abinci, taki yin magana sai kuka kawai take yi, na yi rarrashin duniyar nan amma ta ce idan baka zo ba sai dai yunwa ya kasheta".
Yana gama karanta saƙon ta duba time da ta turo saƙon 11:30 na dare. Ya ALLAH salati ya yi a fili tare da miƙewa da sauri, ya duba time yanzu karfe 10:30 na safe, ya yi daidai da lokacin da ya bar wajenta jiya. Dafe kansa ya ɗan yi, bai yi zaton abin zai kai haka ba, ya san tana da saurin kuka, to ya ɗauka idan ta yi kukan na ɗan lokaci zata mance komai ta koma walwalarta, ban san soyayyarsa ta yi matuƙar ginuwa a ranta ba, ba laifinta bane, bata san tana yi ba, laifin zuciya ce, a hankali soyayyar daddyn nata ya gama mamaye zuciyarta ba tare da saninta ba kamar yadda shi ma soyayyarta ya gama mamaye dikkan jinin jikinsa ba tare da ya sani ba.
Jin ya yi salati ne yasa guru tambayarsa lafiya! Ai ina, bai bi ta kan guru ba ya nufi waje da sauri tamkar zai tashi sama. Kai tsaye benensu ya nufa. Yana shigowa ya shiga cikin É—akinta kai tsaye.
A bakin door ya tsaya ya zuba mata ido, tana zaune a tsakiyar gado, ta rungumo katuwar teddy É—in fari tas da girmansu kusan É—aya da ita, sai yazamana tamkar ita da kawarta Rimsha ne suka rungumi juna, tana manne da waya a kunne, tana kuka tana faÉ—awa Rimsha daddynta yana fushi da ita, tin jiya da ya fita cikin fushi bai dawo ba kuma bai kirata ba, da ta kirasa yaki É—auka, da ta matsa ya kashe wayarsa, Rimsha ta taimaka mata ba zata iya jurewa ba.
Ya so ace ya ji amsar da Rimsha ɗin ta bata, amma ya cigaba da zuba mata ido yana kallon yadda take kuka tana turo baki, idanunta sun kumbura sosai, sun yi jajir, while ƙasan idanunta ya yi jajir, tsinin hancinta ma jajir, sai shessheƙa take yi. Har cikin ransa ya ji zafin ganin yadda ta sha kukan, amma ya daure yana jiran ta gama wayar, ta ɗan kifa kanta a jikin Teddy ɗin.
Ba yadda Rimsha bata yi da ita kan ta faÉ—a mata meyasa daddyn nata ya yi fushi ba amma taki faÉ—e, me ta yi mashi sai ta ce babu, ta É—aukarwa kanta alkawari ne kan ba zata sake gigin maganar hotonsa da kowa ba, shiyasa taki faÉ—awa Rimsha a kan hoto ne. Daga karshe dai rarrashinta Rimsha ta yi, ta ce tin da Monday zasu haÉ—u a school ai kada ta damu zasu san yadda zasu yi da daddyn nan.
Da haka dai ta lallaɓata har ta samu ta yi shiru. Daga haka suka yi sallama, tana ajiye wayar ta ɗago kai tana jan hanci. Unexpected idanunta suka sauƙa a kansa, ya yi holding hands ɗinsa a saman chest ɗinsa, kallonta kawai yake yi. Ai wani irin zabura ta yi, da gudu ta diro kasan gadon tare da sakin Teddy ɗin nata.
Sake hannayensa ya yi tare da buɗe mata, ta zo da gudu ta faɗa jikinsa tare da fashewa da sabon kukan da muryanta sam baya fita. Rungume sosai ya yi tare da ɗagata sama suka koma cikin room ɗin, a gefen bed ya sauketa, ya zaunar da ita tare da tsuggunnawa a gabanta, tana cigaba da kuka sosai mai taɓa zuciya.
Hannu yasa ya ɗago haɓarta, suna fuskantar juna, ɗan shanyewa ya yi ganin yadda face ɗinta ya yi jaga-jaga da hawaye ga kumburi ido. Can ƙasan maƙoshinsa ya ce. "For give me my Cherry Bloom". Ya faɗa tare da kamo hannunta yana ɗan rarraba ƴan yatsunta kuma yana ɗan mammatsatsu, idanunsa a kan face ɗinta.
Cikin kuka tana shessheƙa ta ce. "Daddy for give me, na san na yi maka ba daidai ba, amma baka bani damar in baka hakuri ba, dana kiraka ma kashe wayarka ka yi"....... Manna ɗan hannun nata a kumatunsa ya yi, yana kallon cikin idanunta ya ce. "Ba saboda ke na kashe waya ba, kuma daddy ba zai taɓa yin fushi da Cherry Bloom ɗinsa ba, na yi tafiya ne zuwa........ ". Kome ya tina sai kuma ya fasa faɗa, da ya so ce mata ya je Washington ne sai ya fasa.
ÆŠayan hannunta ta É—aura a saman kyakkyawan madaidaicin sajensa dake kwance a gefen da gefen kyakkyawan face É—insa, É—an shafawa ta yi izuwa lallausan kumatunsa kafin ta ce. "To daddy for give me, I promised you that ba zan sake kwatanta abin da na yi ba"....... "Daddy ya yafe maki, yanzu faÉ—a mun burikanki guda uku daga cikin burukanki da kike son cikawa a duniya!". So yake ya sanyata farinciki, ya faÉ—a yana matsa Æ´an yatsunta dake saman kumatunsa.
"Ina da buri huɗu dama". Ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya. Zuba mata idanu ya yi ba tare da ya yi magana ba alamar yana saurarenta kenan......... A shagwaɓe ta ce. "Daddy ina son zuwa in da rana yake fitowa, ina sun zuwa garin, ina son ganin rana ya fito a kan idona, ina son yawo a tsakiyar teku cikin jirgin ruwa ina ganin manyan shark suna yawo, ina da wannan buri, kuma shi ne babban burina a duniya bayan son ganin Annabi Muhammad ko da a mafarki ne! Ka ji buri biyu! Na farko son ganin Annabi, na biyu zuwa in da rana yake fitowa, da yawo cikin tsakiyar katon teku, na uku ganin daddyna da uncle ɗina, ina son in gansu, in rungumi daddyna in ji ɗumin jikinsa, in faɗa mashi wani mugu ya shigo gidanmu ya kashe mammyna dan ya ɗauka mana fansa, daddyna fa soja ne daddy, yana da karfi kuma yana da bindiga, mammyna ta ce babban jami'i ne, shiyasa nake son in gansa sai in faɗa mashi ya ɗauka mana fansa, burina na huɗu ganin fuskan SSO jarumaina kenan a duniya".