← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 227

Sashe 27

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri suka É—ago da kallonsu a kanta, Angelina ce ta fara saukowa kasan gadonta da gudu ta nufi gadon V. Tana zuwa ta haye tana faÉ—in. "Me kika samo mana........". Bata iya karasa maganar ba ta dakata cak a lokacin da idanunta suka sauka akan laptop dake gaban V. Zazzaro ido sosai tayi cike da mamaki ta ce. "V what am I seeing? Wannan ba hukumar su daddy bane? Akansu zaki fara aiki? Zaki musu kutse cikin kundinsu! Shi zaki datsa? meyasa to? Baki da hankali ko? Bari idan manyan jami'ai suka kamo ki fa kinsan hukuncin ki ko? Tin baki je koina ba kin fara datsa kundin su daddy? To me zaki yi a cikin da ki ka shiga?". Cike da tashin hankali da ruÉ—u ta faÉ—i waÉ—annan maganganu. Hakan ya sa su Arya sukai gaggawar dirowa kasa daga saman gadonsu, gadonta suka haye su ma.

Kowannensu burin shi kawai yaga me ta aikata, yarinyan akwai ƙwaƙwalwa na faɗa muku, akwai baiwa ne, dik cikinsu ita da Arya sun fi su kaifin kwakwalwar sosai, sauran ma ƴan baiwa ne, amma na Arya da V daban ne.

Zazzaro ido Angelina da Manassa suka yi, ita kuwa Arya cikin gaggawa ta kai hannu kan laptop É—in, da sauri ta rufewa bibiyar V kafin ta ce. "You're not serious at all, kin bar komai a buÉ—e, bari GI (General na sashin secret service É—in, shi ne GI, General Ibrahim) bari ya ankara da an kutsa cikin hukumarsu su bibiyeki zaki gane ne!". Ta É—an dakata tana harararta kafin kuma ta sake cewa. "Me kika shiga yi a kundinsu?".

Turo baki ta ɗan yi, wai bata ji daɗi ba an mata faɗa, kuma bata ji daɗi ba da Arya ta gyara mata, so take ace ta kware a kan komai ba sai an taimaka mata ba. A shagwaɓe sosai ta ce. "Guy ɗin ɗazun fa zan bincika, ina son sanin wanene shi? A wani sashi da wace tawaga yake? And Ina son pics ɗinsa".

Wani irin faÉ—uwar gaba Arya ta ji jin V ta ambaci Leo, Amma ta daure da cewa. "Uhm ba wani tsiya bane, for sure karan farautan daddy ne!".

V dake aikin kara kutsawa cikin kundin ne ta amsa da. "Impossible Arya, this guy doesn't looks like Daddy's boys, I think wani guru ne, but let me see"............. Zuba mata idanu dik suka yi, ta cigaba da kutse...... Silent for like 3 mins ne ya biyo baya, lokaci guda V ta fasa kara mai cike da murna tare da cewa. "Yes! I got it, I am Vanisha General Thomas, the daughter of her dad, guys clap for me".

Tafa mata É—in suka É—an yi kafin Arya ta ce. "Who's he?". Ta faÉ—a cike da matsuwar son jin wanene shi!..... Jawo laptop É—in da kyau V ta yi, a bayyane ta fara karanta masu waye shi. "NIRASH MUHAMMAD HAIZA'AN, sabbin jami'an dake kan horo, number É—auka 1". Ta É—an dakata tare da É—agowa ta kalli Arya.

Manassa da Angelina kam sun mutu a kallon pic na Leo dake gaban screen na V, dan ta fito da hotonsa da dik wasu bayanansa tana dubawa, sai suka kura mashi ido, dikkansu sai santin kyansa suke yi, musamman hajiya Arya, gabaÉ—aya zuciyarta ta susuce, tin É—azun dauriya ce kawai take yi, amma ko ido ta rufe fuskan Leo a kusa da ita take gani, musamman yadda ya É—ago idanu É—azun ya kalleta, ya ilahil alamina, ya tashi kan Æ´an'matan GAT.

"Ainahinsa ba É—an nan bane, É—an Us ne, New York City, yana da mark a sunansa, which means jami'i ne na musamman a tawagarsu! But mark É—in ma da alama jiya ko yau aka sanya mashi, in zan canka daidai daddy yana gwada shi ne saboda yana tinanin É—an baiwa ne!". A cewar V kenan, ta karisa koro masu bayanai a kansa, cike kuma da nata hasashen da kwakwalwarta ya bata.

Manassa ce ta ce. "Meyasa kika ce daddy na gwada shi?"...... V dake ƙoƙarin ciro hoton Leo ne ta amsa da. "Saboda ya je ɗaukarmu mana, kin taɓa ganin daddy ya tura wani ya je ɗaukarmu ne? For sure dad yana gwada guy ɗin nan ne".

Arya dai ta yi shiru, ita kaɗai tasan me ainahin abin dake cikin zuciyarta, amma ta ji takaicin da ya kasance Leo ba boy ɗin daddynta bane, bata so haka ba, yanzu Leo yana kan horo ne, kila ya fito da result mai girma da ba z kaskanta a gaban daddynta bama bare har ta walaƙanta shi, takan iya yiwuwa ma ya fito a sashe na musamman.

Ganin ta yi shiru ne yasa suka fara tambayarta meyake faruwa?. Kai kawai ta girgiza masu alamar babu komai. V ta ce. "Bloody I wish mu samu number guy É—in nan, da na mana kutse cikin wayansa mu sato hotunansa"...... Da sauri Angelina ta amsa da. "Let daddy comeback, zamu samu number É—insa a phone na dad".

Zamewa Arya ta yi ta koma saman bed ɗinta, ta zauna shiru, ita kanta bata san me yake yi mata daɗi ba, afkawa tai cikin tinanin da bata san na menene bane. Bata ankara ba sai ji ta yi an taɓata, da sauri ta ɗago kai, sun kewayeta suna kallonta cike da tausayawa. Manassa ce ta ɗan rungumota game da cewa. "Bloody you should stop thinking about this guy, we know he did wrong to you, amma tin da yanzu ɗaukar fansa ba zai yiwu ba ki bari mana akwai gaba ai".

Nisawa ta ɗan yi before ta ce. "Ba zaki gane bane, zuciyata tafasa take yi idan na tina yadda na yi magana ya shareni, kina ganin kowa so yake yi in kula shi, amma shi wannan har ya samu nai mashi magana, ya walaƙanta ni, okey yanzu da students suna nan ma haka zan ji kunya a gabansu?". Tamkar zata yi kuka ta faɗa, da alama tana da riko da zafin zuciya.

Hakuri suka dinga bata har ta hakura ta sauƙo, sannan suka koma kan abin da suke yi. Karfe 5 daidai suka fita zuwa mini gym ɗinsu dake ƙasa kusa da pool ɗin gidan. Sai da suka yi push-up guda 30, sannan suka fara ɗaɗɗaga ƙananan karafuna, dik sojojin dake gidan babu wanda yake ɗaga idanu ya kallesu saboda tsoron shiga matsala, amma kuma wlh dik sojan da ya yi aiki a gidan GAT sai ya so yaran nan kamar ya mutu, musamman Arya da V, suna da shegen shiga rai, sai dai soja ya yi ta dakon soyayyarsu ba samu zai yi ba.

Dik in suka fito gabaÉ—aya hankulan sojojin nan tashi yake yi, su yi ta faman satar kallonsu, kuma dik masu tsaron gidan na GAT matasa ne masu ji da lafiya da karfi, kunga kuwa dole kunamar bindigarsu ta dinga harbawa idan suka gansu.

2 hours suka ɗauka suna gym, sai karfe 7 suka ɗan yi linƙaya cikin pool saboda gumin da suka haɗa na wahalar motsa jikin, sannan suka fito, jikinsu dik ruwa suka nufi cikin gida. A zahiri idan kuka ga soldiers ɗin nan zaku zaci ƙasa suke kallo, amma dikkansu harta waɗan da suke shawagi a tsakar gidan, na bakin gate dik kowani taku nasu Arya ɗaya a kan idanunsu, su kuwa bama su san suna yi ba, sai hira suke yi cike da kaunar juna suka wuce ciki.

Zuna zuwa suka sake yin shiri cikin kaya iri ɗaya, sannan suka ɗan taɓa karatu kafin su je yin dinner.

A ɓangaren Leo kuwa, ransa gabaɗaya a ɓace, dama ga wahalar da suka ci yau, tin da ya zo GIDAN SOJA bai taɓa cin wahala irin na yau ba, kai tsaye office na GAT ya nufa. Da ya je sai da ya tsaya a waiting room, ya tura saƙonsa na son ganin GAT, sannan ya yi zaman jiran a bashi izini.

Izinin da bai samu ba kenan tsawon awa biyu, kuma GAT na zaune cikin office É—in yana kallonsa ta camerar dake waiting room É—in, so yake ya gwada hakurin Leo, dan yasan irinsu suna da zafin kai da rashin hakuri. Amma ga mamakinsa sai ya ga Leo ya jure zaman jira, in short ya gagara gane alkiblar Leo É—in ne ma, kansa ta É—aure gaskiya, sai ya ce bari sun kullah kenan, sai ya san shi ciki da waje.

Bayan awa biyu yasa aka shigo mashi da Leo É—in. A gabansa ya tsaya tare da sara mashi, jinjina kai ya yi kafin ya umarcesa da ya ajiye mashi makullin. Ba musu Leo ya ajiye. Shiru GAT ya yi yana jiran jin ko Leo zai yi mashi wani karin bayani, irin ya ce ya je ya É—aukosu ya kaisu gida, amma sai ya ji shiru bai yi magana ba, hakan ba karamin mamaki ya sake baiwa GAT ba, wai wannan wani irin mutum ne?.

Dan ya gwada shi sai ya ce. "You can go"........ Sara mashi Leo ya yi tare da juyawa ya fita. Da kallo GAT ya bisa yana mamakinsa, watau dai magana ce ba zai yi ba, to lallai yakamata a gyara mashi zama.

Kasancewar lokacin dinner ɗinsu ya wuce sai Leo ya nufi room ɗinsu kawai, bai yi dinner ba yau saboda GAT. Can ƙasan maƙoshi ya yi sallama a lokacin shigarsa ɗakin, su Zaysh suna ta faman yin waya da gida, yau suna da damar kiran kowa da rana. Vash ne ya ce yau Friday zai yi sadaka, amma da ƴan room ɗinsu zai fara, to a ƙaidar GIDAN SOJA ɗin in dai zaka zo buɗe maka account nadaga cikin list na kuɗin da zaka kashe a farko, dan haka suna da account na ƙasar amma kamar students account.

Dan haka dikkansu Vash ya basu kyautar 1k dollars, Noor ya ce ba zai karɓa ba, da Vash ya matsa sai ya ce ya baiwa Zaynash nasa, haka ya haɗawa Zaysh. Da yake Noor yana da kyawawan zuciya sai ya ce da Zaysh. "Bro ka kira Aunty Ummie mu gaisa, I really like her, Ina jin daɗin yadda kullum take ce mana mu kula da kanmu, mu ci abinci kuma mu yi barci a kan lokaci, tana da kirki sosai kuma tana sonmu sosai".
Chapter 27 · 0% Book details