← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 227

Sashe 40

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sake matsawa zuwa mutum na biyar ya yi, watau Unays, sanya mashi ya yi shi ma aka harba two bullets a sama. Ya matsa na huÉ—u Vash, yaro ya zama shirgegen soja mai rai da lafiya. Sanya mashi kambunsa ya yi, ya sake matsala ya sanyawa Zaysh dake na uku kafin ya matsa ya sanyawa Noor dake matsayin na biyu, watau Leo ya tsaya tsayin daka sai da ya mayar da Noor dakakken namiji, dik in da ya sanya kafa Noor sai ya sanya, bai mashi ta daÉ—i ba amma a karshe yasa ya yi nasara!.

Lokacin da Captain ya zo sanyawa Noor wannan kambu shi da kansa yasan Noor namiji ne a yanzu, sai da ya kare mashi kallo kafin ya sanya mashi kambun, sannan sai da ya sanya hannu ya buga shoulder ɗinsa da karfi alamar jajircewa kafin ya wuce wajen oga Leo dake tsaye tamkar wanda aka sassaƙa! Ya kafe kallonsa a waje guda, wanda da na juya dan ganin wa yake kallo sai da na firgita.

Ya ilahi ya lillahi, wani bawan ALLAH yake kallah wanda dik da yana sanye da Dr nose mask hakan ba zai hana ka san cewa ALLAH ya yi halitta a wannan waje ba, kamanninsa da Leo tamkar an tsaga kara ne, still shi ma kitso ce a kansa na kalba, kitson ma zara-zara kuwa, zanensu ya fito sosai, ya tara kitson a tsakiyan kai ya É—aure, hannunsa rike da p-cap da ya cire daga kansa. Dik da yana zaune kai daga ganinsa kasan mazajene a wajen, eyes É—insa kalar sanyi, irin jade eyes É—in nan, in kuka gansa zaku zaci yana jin barci, ga idanun very sharp, har sun fi na Leo rikitarwa, dan shi zaku zaci yasa kwalli a idon ne, kuma haka halittarsu yake, kunga É—an round mouth lips É—insa kuwa? Gasu pink color kamar na mata, maza da ja aka sansu, su kuma nasu pink color ne sosai. ALLAH ya yi halitta a wannan waje jama'a!.

Slowly ya mayar da p-cap dake kansa, gabaɗaya ya kafe Leo da kallo shi ma. Zayra'an Muhammad Haizaan kenan, Big Bro na Leo, the same father the same mother, su biyu ne rak wajen iyayensu, Zayra'an zai kai kimanin 32 years a yanzu, tsayayyen namiji ne wanda ya samu horo a AZURE shekarun baya da suka wuce, zakaran da a lokacinsa babu wanda ya iya bugesa, yaki yarda aiki a AZURE shiyasa ya koma Us military, mutumin da yadda kuka ga Leo haka yake, har ma ya fi Leo wasu dabi'u masu gindayar da mutane, zaka iya zaman shekara da shi bai ce maka kala ba, in ma kai ka mashi magana ba lallai ya amsa ba, kaifi ɗaya ne, wlh in ya ce e to fa e ɗin nan ne babu wanda ya isa ya sanya shi canzawa, idan kuma ya ce a'a fa ita ma ta zauna, yana da nuna iko da isa a waje, a cewarsa dik in da ya je shi ne sarki, dole kowa ya yi ƙasa da kai dan girmanawa a garesa. A lokacin da ya karɓi horo a hannun GAT ne, lokacin GAT yana matsayin Commander kafin ya samu karin girma.

Dik wata izza da isa a barwa Zayra'an kayansa, bakinsa bata buɗewa ta yi magana sai dai ido ya cika aiki. Idan ya zuba maka ido sai ka tsargu ka yi abin da ba shikenan ba, idan ya zare maka ido da alamar tuhuma in baka yi saa ba sai ka saki fitsari a wando, idan ya yi maka magana cikin tausasawa sai ka rikice saboda daɗin muryansa, idan kuma ya daka maka tsawa in har baka da kwarin zuciya kana iya sumewa! Kyansa yana haukata dayawa, yana rikita maza da mata, shiyasa baya shiga taro, baya zuwa ko'ina saboda idanun jama'a, kada ku manta sun fito ne daga ƙabilun da suka fi kowani ƙabilu kyau a duniya! Kunga kuwa batun kyau ma sai dai ayi shiru, amma suna rikita kwakwalen mata da maza, ko namiji ya gansu sai ya sake juyawa ya gansu bare mace.

Sanya mashi kambun Captain ya yi tare da buga shoulder ɗinsa alamar kwararawa. Daga nan Captain ya karɓo kambun karmawa mataki na biyu, a nan aka sanyawa Ameer da sauran matansan room ɗin nasu dana room 3.

Daga nan ne GAT ya tashi tsaye, cikin takun jarunta ya isa gaban mic da aka tanada dan jawabinsa. Take dik wani soja dake wajen ya ƙara kamewa da alamar girmamawa.

Da kaifaffar harshe ya ce. "Ina yi wa sojojin da suka yi nasara murnar tsallake wannan babban aiki, hakika sun cancanci jinjina ta musamman, jaruman gaske ne, kuma dikkansu sun fito da sakamako mai kyau, sai dai a bisa doka wannan horon bar two da aka basu lallai ba za su karɓi sakamakon horonsu ba har sai sun ƙaddamar da Mission guda biyar, bayan sun kammala shi sun dawo, a nan ne zasu samu sakamakonsu na farko da na biyu, misali idan ace yanzu sun fita da muƙamin lieutenant, idan suka gama wannan Mission ɗin, suka yi shi da kyau, kuma suka yi nasara, suna iya fita da muƙamin General, Major General, har izuwa muƙamina, dan wannan Mission da zasu yi shi zai tabbatar da jarumta da kwarewarsu a aiki, dan haka yau ba rana ce ta yaye ɗaliban soja ba, yau rana ce ta shiga sabon babi, za'a basu hutun sati biyu, zasu je gida suga dangi da iyaye, dik abin da zasu yi zasu yi shi ne a cikin wannan sati biyun, daga nan za su dawo bakin aiki dan shiryawa wannan mission ɗin!". Ya dakata yana kallon iyayen sojojin.

Irinsu Ummie da basu san me Mission yake nufi ba sai daɗi take ji, ita dai ƙaninta ya zama soja tin da ta gansa da kaki. Sauran iyaye kowa fuskarsa ta sauya, musamman daddyn Noor dake da mallakin ɗa namiji ɗaya tilo a duniya, kunga kuwa ba zai so a tura shi wani Mission da manyan ƴan ta'adda a duniya ba. Basu gama dawowa daga tinanin da suke yi ba suka ji GAT na kirga irin mission da zasu yi, ciki har da kirgo kungiyar IRON FIRST wanda jiga-jigan jami'an Amurka sun ƙasa damkesu, amma wai ake kiransu matsayin mission na biyar da su Ko za su yi. BABBAR MAGANA, DA MATSALA KUWA!

Kai wasa ma ake yi. A cewar daddyn Noor, domin shi bai yarda IRON FIRST mutane bane, yadda duniya take maganarsu, an gagara kamasu ɗin ne za'a ce wai su Noor zasu yi mission a kansu, very funny thing. Amma fa a cewar daddyn Noor, dan yana ɗauka Noor da ya sani ne, kunsan sanin da ka yi wa mutum a farko ko me zai zama a haka zaka dinga kallonsa, shi daddy kawai yana kallon Noor a ɗan shagwaɓa rago mai kukan da ya sani yake yi!.

GAT ya kammala jawabinsa da kiran sunayen manyan Æ´an ta'adda da zasu yi mission a kansu, daga nan ya ce Leo shi ne shugaban da zai jagoranci wannan runduna tasu, su 12 ne kenan a tawagar, from room 1 to room 3, kunga mutane 4 ne a kowani É—aki, su 12 kenan. GAT ya naÉ—a Leo a matsayin Commander wannan runduna, dole su yi mashi biyayya da karrama shi, Noor assistant, daga nan ya umarci da a kawo stars É—insu, kowa iyayensa su sanya mashi star É—insa a gaban riga.

Yana gama magana aka saki bindigu uku sama da karfi. Sannan Captain ya É—auko stars É—in a cikin box, iyaye one after the other aka fara kiransu suna zuwa dan sanyawa yaransu. A room 1 iyayen Vash aka fara kira. Wani kyakkyawan matashi ne ya taso ya kariso wajen, dik in da ake neman namiji wannan ya kai. Dr Aryan Muhammad Khaiza'an kenan, babba likita kuma natsastsen matashi mai jini a jika. (Ku lura, sunan mahaifin Vash da mahaifin Leo kusan iri É—aya ne, amma ba É—aya ba, na Leo Haiza'an, na su Vash Khaiza'an)

A gabansa ya tsaya tare da karɓar star ɗin, ya sanyawa Vash a gaban riga, da karfi Vash ya sara mashi kafin su rungumi juna cike da kauna da kewar juna. Daga nan Vash ya bisa suna sauƙa ƙasa dan kara ganin juna.

Iyayen Zaysh aka kira a mataki na gaba da su zo. A natse Ummie ta tashi ta nufi wajen, jikinta sai rawa yake yi, dan har ga ALLAH a tsananin tsorace take da sojojin dake wajen, kun san su ko kakinsu mugun kwarjini ne da shi. Tana zuwa ta karɓi star ɗin, da kyar ta iya jurewa, Captain ya nuna mata in da zata sanya mashi! Sakawa ta yi tana ta kallon fuskansa, gabaɗaya yanzu tsoronsa take ji, kwarjininsa ya firgitata, dik ya canza kamar bashi ba. Sara mata ya yi kafin su rungumi juna kirjinta kamar zai fashe saboda tsoro da faɗuwar gaba, take ta fara ruwan hawayen tsantsan farinciki, yau ALLAH ya cika masu burinsu ya zama soja. Daga nan ya bita suka sauƙa ƙasa dan su gana da kyau.

Sai daddyn Noor da aka kira, cike da farinciki da alfahari ya taso, wasu jiga-jigan guards suka take mashi baya har zuwa in da Noor yake a tsaye, aka bashi star ya sanya mashi, sannan suka rungumi juna, sai da daddy ya girgiza jin jikin Noor a jikinsa, ya ji namijin gaske, ai a take ya ji zuciyansa ta wastsake, ya ji lallai Noor zai iya wannan Mission É—in!. Da sauri daddy ya ja shi suka nufi wajensu Aunty Lisa da tin shigowarsu GAT yake ta kallonta, ya ga Æ´ar kyakkyawa, da alama su Arya zasu samu second mother idan da rabo!

Lokacin da aka kira family ɗin Leo Big Bro ɗinsa ya miƙe ya fito sai da kowa ya kallesa ya sake kallah, dan ma dai yana sanye da winter jacket mai ɗan tsawo zuwa gwiwa da ta rufe kakkarfa kuma kyakkyawan surar jikinsa, amma dik da haka an kafesa da idanu. A gaban Leo ya tsaya a dake tare da karɓar star ɗin ya sanya mashi sannan suka rungumi juna. Dik wanda ɗan uwansa ya sanyawa star ɗin nan sai an buga bindiga sama alamar girmamawa!.
Chapter 40 · 0% Book details