← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 227

Sashe 67

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lion ne ya ce. "Sune a next mission namu"........ Shiru room É—in ya yi, dukkansu suna tinani daban-daban, lallai kuwa sun É—auko dala ha gammo, mission kan WORLD SYSTEM, na yarda da gaske su Lion sun sayar da ransu, basu tsoron mutuwa, sun shirya mata a koda yaushe. Yanzu wasan zai fara, su Noor zasu yi mission a kan IRON FIST, su kuma IRIN FIST zasu yi mission a kan WORLD SYSTEM, kungiyar da suka fi haÉ—arin ma haÉ—ari.

Ni dai na shirya tsab dan bin kowani team a wannan tafiya, dik wacce ta shirya ta haÉ—o kayanta mu wuce, batu ake na gaskiya da gaskiya, reality amma a novel, get ready my people, wannan karon bamu zo da wasa ba!.

Sun jima suna tattaunawa a kan wannan matsalar, har zuwa 12 na dare, sannan suka miƙe suka nufi dining room. Dinner suka ti sama-sama saboda dare ya yi, shi Lion ma green tea kawai ya sha, Champion ya sha Amercano, guru ya ɗan sha coffee, daga haka suka nufi room na Leo.

Sun sha madarar mamakin ganin idanunsa biyu, ya dukufa a kan laptop dole-dole sai ya ɗan samu wata makama a kan IRON FIST, aiki tukuru yake yi, dik wasu kisan da IRON FIST suka yi sai da ya bankaɗo bayanai, amma babu wata makama ko alamar da za'a iya gane su. Dik kisan da zasu yi sun subarwa da mutum jini, bugu da kari sun fi yin kisa da poison ko Chemical, kansa ya ɗauki zafi sosai, ruwa roba biyar ya shanye amma bai iya gano komai ba, idan ya binciko wani kisa nasu sai ya miƙe ya fara kewaye a cikin ɗakin yana tinanin yadda aka tsaya komai, ya kewaye room ɗinsa ya fi sau hamsin, amma dai babu wata haske, tin yana aiki a kan gado har ya sauƙo ƙasa.

Brothers ɗin nasa suna shigo ya ɗago ido a kansu, da sauri ya miƙe ya koma saman bed yana kallonsu. Ɗan kallon juna suka yi kafin su karisa in da yake, cike da damuwa ya ce. "My love please come and help, my brain is about to tarwatsewa wlh".

Champion zai yi magana Lion ya rigasa da cewa. "Babu wanda zai taimaka maka, da kanka zaka yi komai". Daga nan ya kafawa su Champion dokar kada su kuskura ko da sunan wasa su taimakawa su Leo a kan wannan mission da zasu tafi, su je su yi faÉ—a da kansu su yi nasara, idan har zamu taimaka masu kenan babu amfanin su kaisu AZURE ai, su kam waye ya taimaka masu a lokacin nasu mission É—in? Ba su suka kwaci kansu ba? Dan haka su Leo su kwaci kansu suma.

Kuma Lion yana da gaskiya, kunga abin da ake jiran su goge su maye gurbinsu kenan wayau IRON FIST, idan suka fara tayasu aiki ta ya za'ayi su jajirce su zama mazan gaske? Ai kunga gara a barsu su ci ƙwaƙwa su tsira da kansu. Lion ya ce ko mutuwa suke yi babu wanda zai taimaka masu, bama zai bibiyu mission ɗin nasu ba, su je su fafata su zama mazan gaske, kuma da gaske yake yi wlh, dan ya gana su Champion ma bibiyar Mission ɗin nasu Leo, ya ce su fafata da kansu, suma su shiga tsananin rayuwa ko mutuwa, daga nan ne dik wata sauran tausayi zai bar ransu, zasu zama mutane in ji Lion.

Da haka suka yi wa Leo goodnight bayan sun karfafa mashi gwiwa, suka wuce izuwa room É—insu. Hankalinsu a kwance suka kwanta, Lion ya ce ya basu nan da kwanaki biyu su yi tinani a kan WORLD SYSTEM, shi ma zai yi nashi tinani, after two days zasu sake yin zama a kansu dan yanke hukunci kafin su fara ainahin bincike a kansu!.

Suna kwanciya ba jimawa Lion da guru suka yi barci, shi kuma Champion ya É—auki wayansa ya duba layin Seraphina ko tana online, sai ya ga bata nan, ya kirata sau É—aya da bata É—auka ba ya fahimci ta yi barci, hakan yasa ya kashe wayarsa shi ma ya yi barci, ya so ne ya jita, dan kukan da ta yi É—azun abin ya tsaya mashi a rai, ta faÉ—awa Rimsha ita kaÉ—ai ce a gidan kuma tana tsoro.

Kai inna biyewa rubuta komai fa zamu jima ba'a kai in da muke so ba, dan haka After some days.

A ƴan kwanakin nan da suka wuce abubuwan da suka faru sun haɗa da Aryan ya ɗauko madam Rohisha da ƴar marainiyarta ya dawo da su wajen Seraphina, ya kuma nema masu school da suka gama dan komawa su yi senior set a can, ya kuma nema masu izinin dawowa gida su dinga kwana ba boarding ba, ya yi sa'a aka bashi, ya yi matuƙar murna sosai, dan baya son kwananta a school, gara mashi a C-P ɗin nan, dik time da ya tashi ya shigo ya duba lafiyarta.

A gefe guda kuma su Noor soyayya ta kara kulluwa a tsakaninsa da V, yanzu sai shirin komawa barrack yake yi, nan da kwanaki uku zasu koma, kuma har yau basu haÉ—u da Leo ba, Leo É—in ne ya ce bashi da lokaci, saboda yana nema kashe kansa a kan bincike, ba dare ba rana yana aiki É—aya, har rama guyen nan ya yi, Zayra'an na ganinsa amma bai ce ko uppan ba, shi daÉ—i ma ya ji na ganin yadda kanin nasa ya dukufa kan aiki babu wasa babu kama hannun yaro, ko abincin kirki Leo baya ci, idan ya zauna a gaban computer sai ya samu wani É—an haske yake matsawa, kansa tamkar zai fashe saboda ciwo, amma ya dage.

Shi ma Noor ya dage da aiki babu kama hannun yaro, hakan yasa jiya suka yi faɗa da V, ta ce ya daina sonta, baya bata ishasshen lokaci, sati ɗaya baya da suka fara soyayya wuni suke yi manne da waya suna hira da juna, yanzu kuma idan ya yi mata message da safe sai ya shiga aiki, baya sake bi ya kanta sai can yamma, wayarsa ma kashewa yake yi, yana kara hora kansa da motsa jijiyoyinsa, a taƙaice dai basa waya sai dare, daren ma daga karfe 8 zuwa 10 suke waya sai ya ce mata goodnight, ko ta so ko bata so ba zai kashe wayar ya shiga aiki ne abinsa.

Ba wai dan baya sonta ba, sai dan aikin dake gabansu yanzu ya zarce wasa, dole ya mayar da hankali idan ba haka bama Leo zai rabasu da ita ne, ita kuma bata gane ba, sai fushi take yi da shi, ya yi mata bayani amma bata gane ba, ita dai kawai lokacinsa take so, shi kuwa ya ce ta yi hakuri ba zata samu lokacinsa yanzu ba.

To shi ne tun jiya ta yi fushi da shi, ya yi rokon duniyar nan a Whatsapp ta sauraresa taki yarda, daga karshe ma ta rufe wayarta, yanzu haka tin jiya bai ji voice É—inta ba, dik ya kiÉ—ime ya fita hayyacinsa, ga aikin da ta sha gabansa. Ya kira number Angelina da yake da shi, yasa ta bata waya amma ta ce ace mashi ya manta da ita, kada ya sake nemanta, Noor bai tashi sanin a sati É—aya da Æ´an kwanaki da suka yi suna soyayyar nan mugun sonta ya shigesa ba sai yau.

GabaÉ—aya yau ya gagara yin aikin ma, wlh sai kai komo yake yi tsakanin É—aki da waje, ya rasa me yake yi mashi daÉ—i, jikinsa dik a mace, ita kawai yake tinani yake son jin muryarta, daga karshe ya yanke shawarar komawa AZURE gobe mai maimakon jibi, ya ce tin gobe zai koma dan ya samu ganinta ko hankalinsa zai kwanta.

Jama'a kunga irin abin da Lion yake gudunwa IRON FIST kenan, shiyasa suka haramtawa kansu soyayya, da gaske ne idan kana soyayya wasu abubuwan ba zaka mai da hankali a kansu ba, kuma su a yadda suke ɗin nan dik yarinya da suka so ma sun cutar da ita ne, saboda sun san a kowani lokaci mutuwa zasu yi, bare yanzu da suke ƙoƙarin ɗauko mission ɗin da duniya dik ta gagara, abin dake ɓoye a cikin duhu suke shirin bangaɗowa duniya shi, kuma kun san gagarumin haɗari zasu jefa kansu, ga dai Noor, soyayya na neman hanasa abin dake da muhimmanci a kansa, ta yi fushi da shi ta jefa zuciyansa a cikin wahala da tinani, tasa ya gagara yin aikin dake gabansa, har yana tunanin zuwa wajenta gobe.

A gefe guda kuwa Aunty Lisa na can tana abin da ta ga dama da zuciyar our daddy GAT É—inmu, tasa bawan ALLAH ya zama yaro É—an 20 years, sai juya shi take yi yarinyar nan, shi kuwa sai biye mata yake yi, ya zauna ya gama zuba mata sexy and romantic words yarinyar nan sai ta ce mashi. "Daddy all this fa westing of time ne". Kuma Æ´ar kaniya har kwana mafarkinsa da kalaman nasa take yi, amma take cigaba da mashi abin da take so.

Yau dai da ta kawo shi har wuya, ya yi ya yi su yi video call taki yarda, sai ya katse kiran tare da miƙewa ya koma gida, a take ya nemi bizar zuwa US, ga shi two days ago su Arya suka yi passing out ɗinsu, dama ya ce idan suka fita kafin su fara aiki zai kai su yawo, dan haka sai ya shirya masu tafiya gabaɗayansu.

Da yamma jirginsu ya É—aga sai US, bai sanar da su Arya ga in da zasu je kai tsaye ba, kazalika bai sanar da Aunty Lisa yana zuwa ba, while Noor bai san V na hanya ba, ya bari sai da suka yi dirar mikiya a airport sannan ya kira daddy Noor ya faÉ—a mashi suna US yanzu.

Ai da sauri daddy ya umarci ƙaninsa uncle ɗin su Noor da ya ɗauki motoci da guards aje a ɗauko mashi bakinsa a airport. Noor bawan ALLAH yana ɗaki yana ta faman shirye-shirye kan cewa gobe zai wuce AZURE ya je ya ganta, ya gama shirya rucksack ɗinsa, yana kwance a saman bed rike da waya yana ta faman neman numberta.
Chapter 67 · 0% Book details