← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 227

Sashe 22

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A maimakon Leo ya ɗauka, sai ya barta a wajen, suka hau gwabzawa da hannu, while su Noor ma suna fafatawa. Cikin ƙasa da minti biyar room 1 suka lallasa room 2 suka yi laushi. Dik sun kai abokan faɗar nasu ƙasa saura Noor da suke ta fafatawa, shi gaskiya bashi da karfi, amma ya dage don ya zo na farko, ai ya ɗanɗani daɗin zuwa na farko yanzu baya wasa.

Tsaitsayawa su Leo suka yi suna mayar da numfashi, while su Unays suna baje a ƙasa suna nishi sama-sama. Captain ne ya ce. "Nan fagen yaki ne, kuna iya taimakawa ɗan room naku, dan ko a daji ne zaku taimaka mashi daga abokan gaba".

Ai tin bai gama rufe maki ba Zaynash da Vash suka yi kan su Noor, take suka kai guy ɗin ƙasa. Hannu suka dunkule suka bugi na juna, amma ban da Leo dake tsaye a gefe yana rike da waist ɗinsa, tafawa suka sake yi cike da murnan sun yi nasara. Shi ma Captain murna ya yi sosai, dan bai san meyasa team nasu Leo suke mugun burgesa ba, musamman Leo and Noor, yana jinsu har cikin ransa.

Hutawa ya basu dama su yi na kamar mintuna biyar, aka basu ruwan sha kafin su wuce su koma dan yin lunch and sallah, dan time ya yi.

Kai tsaye masallaci musulman cikinsu suka wuce. Bayan sun yi sallah suka haɗu a dining hall ɗinsu. Kamar yadda suka saba cin abinci suka ci, suka ƙoshi nak, sannan aka basu hutun 30 mins, a nan suka yi zaman hira, shi kuma Leo ya fito da wannan book ɗin ya fara karantawa. A kusa da shi Noor ya zauna, yanzu ya daina zama kusa da su Zaysh.

Dik abin da Leo yake yi yana kallonsa, so yake ya dinga kwaikwayonsa saboda rayuwar Leo É—in tana burgesa, amma bai yi magana ba har 30 mins ta cika, a nan aka kwashesu zuwa wajen gwajin makamai. A yau handling heavy weapons aka sanyasu, manyan bindigu aka basu su rike, aka É—eba masu lokaci, nasan dayawanku baku san cewa bindiga tana da nauyi ba ko? To nau yi gareta, musamman idan akwai bullets a cikinta, shegen nauyi ne da ita, ai ko da iya rike bindigunsu aka barku ba karamin aiki bane, amma haka suke wuni dakon kayansu bayin ALLAH.

A yanzu good 30 mins suka ɗauka wajen rike bindigun nan, daga nan aka ware 30 mins again aka koya masu magana da idanu ga junansu, idan sun shiga wata matsala ga dabarun da zasu isarwa da juna saƙo ba sai sun yi magana kowa ya jisu ba, Captain ya basu kalaman sirri ga junansu, wanda dik in da suke idan suka ambaci wannan kalma an san so ne, sannan kowani room ya basu kalaman sirrin gane juna ko a cikin duhu ne.

Yau sai da suka yi sallar al'asar sannan suka bufi class É—insu. Shi ma yau sabbin makamai za'a koya masu, sun natsu tsit suna rike da notebook and pen. Cike da tsantsar jarunta Captain ya shigo É—auke da katuwar littafin makaman nasu.

A saman table ya ajiye littafin kafin ya juya ya kallesu da kyau. Sai ya juya ya fara rubutu a board ɗin, yau ya koya masu yadda bindigun suke, wajen bullet, yadda ake goge bindigar da dik wata sirrin bindiga. Wannan ɓangaren ba zan rubuta maku shi dallah-dallah ba, dan ban san iya ina rubutuna zai tsaya ba, akwai ɓata gari, ba ta yadda za'ayi in fitar da sirrin komai! Hakan na kamar cin amanar ƙasa ne! Dan haka ita bindiga sirri ce, kawai dai yau Captain ya yi masu darasi kan dik wata sirri na bindiga, ya bage masu komai!.

Awa uku tsu suka ɗauka suna karatu, dan yau babban aiki ne, kuma kasancewar sun yi wannan dogon karatun yasa karfe biyar yau suka tashi daga horo, Captain ya ce wannan abin da aka koya masu yau yana buƙatar dogon nazari da natsuwa dan ya shiga kansu, saboda a wannan gaɓa ne idan suka yi kuskure kaɗan bindigar kan iya ja masu matsala har ta yi kisan kai, dan haka su kula sosai.

Dan haka karfe 5 suka koma rooms É—insu, basu sake fita ba sai lokacin sallah musulman cikinsu suka fito suka nufi masallaci, basu dawo É—aki ba sai da suka yi sallar isha'i, suka ci abinci, sannan suka dawo. Wanka suka yi, kowannensu ya yi shirin kwanciya, sannan suka ciro wayoyinsu suka hau kiran gida, yau har da Zaynash, ya fito da wayansa a gabansu bai ji kunya ba, ya kira Ummie ya haÉ—ata da su Noor suka gaisa. Still dai Leo bai yi masu magana ba, suma basu yi gigin kai mashi waya ba.

Noor ya dinga murna yana faɗawa daddynsa yau ya yi kokari ya zo na ɗaya, shi ma daddy murna ya dinga yi. Sosai suka sha hira, daga nan ya kira Aunty's ɗinsa mata su uku, Luna, Lusi, Lisa, hira suka dinga yi, ya dinga yi masu kukan ya yi kewarsu, ashe dama su suka kara shagwaɓa shi suka mai da shi na mata, suma kukan kewansa suka dinga yi, wai baya nan yanzu ba wanda suke yi wa tausa. Shagwaɓa ya dinga zuba masu suna biye mashi.

Ai idanu su Zaysh suka zuba suna kallonsa cike da mamaki, wai kato da shi yana abu kamar mata, sai ma da yake magana da su Aunty Luna, wlh zaku É—auka macece take magana, har murya, ya canza voice ya koma sak su, cike da yanga. Dik abin da suke yi Leo yana jinsu amma bai tanka ba.

Wai waye NOOR. Mu ɗan ji waye shi kaɗan. Ya fito ne daga babban family, sune mamallakan STARS BODY LUSH, Companyn da ya fito na farko a duniya, mahaifinsa yana da wasu mahaukatan kuramen kuɗi, su shidda ne a family ɗinsu sai, daddynsu, Lisa, Luna, Lusi, sai Uncle ɗinsu ƙanin daddynsu wanda shi ma babban mutum ne, Noor bashi da mahaifiya, ta rasu a lokacin da take nakudansa, daga karshe aiki aka yi aka cirosa, bai sha nonon uwa ba sai madara, yana ɗaya daga cikin abin da ya kara mai da shi haka, ga cutar tsoron dake damunsa.

Akwai abin da ya faru da mahaifiyarsa a lokacin da take da cikinsa ne, wanda wannan firgici yasa nakuda ya tashin mata, tashin hankalin yasa zuciyarta ta buga bata haihu ba ta mutu, shi ne abin ya taɓa Noor. Su Lusi su suka renesa har ya girma, mahaifinsa yana mutuwar son ya haifi ɗa namiji wanda zai gajesa, ko bayan ransa zai tsaya ya kula da ƴan uwansa da kuma dukiyansu, amma sai ALLAH ya bashi ƴaƴa mata, a karshe ya samu namiji, ya yi matuƙar murna na samun Noor, sun renesa cikin gata da kulawar da ko kuda basu bari ya taɓa shi in suna nan!. Magajin billions of dollars ne nan.

Sai dai a lokacin da ya fara girma suka fahimci yana da tsananin tsoro, dan ko irin wasan nan da suke yi na razana mutum in suka yi mashi suma yake yi, daddynsa ya shiga tsananin tashin hankali, daga nan ya fara yawo da shi kasashe dan neman mashi lafiya, Amma ina sauki taki samuwa, daga karshe uncle É—insa ya bada shawarar a shigar da shi hukumar soja, idan ya kasance cikin maza zai samu jarumta.

Da farko daddynsa yaki, ya ce shi ba zai iya ganin É—ansa a wahala ba, sai daga baya da suka ga yana girma abin yana kara karuwa sosai, harta maganarsa ta koma ta mata, shi da ake son ya zana tsayayyen namiji da zai kula da dukiya, shi ne ya kare a mata maza ai kunga ba zaman lafiya, nan fa daddynsa ya aminta da a kaisa gidan soja mafi horon wahala.

Uncle ɗinsa ya nemo, a nan ya zaƙulo AZURE, take aka yi applying. Cikin ikon ALLAH, da yake kuma suna da abin hannu, ya samu. Ko da za'a kawosa nan ya sha kukan rabuwa da ƴan uwansa mata, suka dinga cewa babu mai yi masu parkin gashin kansu ya kitsa masu jelar, dan shi yake yi masu dama, na ce maku dik wani abin da ya shafi mata ya iya.

A takaice Noor maraya ne, babu uwa, bai sha nonon uwa ba, ga ciwon tsoro, ga shi cikin mata ya girma, ai ko daga nan zaku san Noor ya yi namijin kokari ma, rana tsaka ya tsinci kansa a wannan wahala! Ya jure gaskiya. Labarinsa a taƙaice kenan, saura bayani zaku ji a gaba. Me yasami mahaifiyarsa har ta firgita nakuda ya tashin mata unexpected? Wani irin tashin hankali ne yasa zuciyarta bugawa kafin ta haihu?.

--------------------🔥

Sun jima suna waya da Auntys É—insa kafin su yi sallama, ya ajiye wayar ya kwanta shiru yana tinani, da yanzu a gida yake yana kwance tsakaninsu, suna mammatsa mashi jiki cike da so da kauna.

Zuciyansa cike da wannan tinani barci ta yi awon gaba da shi. Shiru room ɗin ya yi alamar dik sun yi barci, sai Leo da ya miƙe ya nufi toilet. Alwala ya ɗauro ya dawo kan dadduma, nafilfili ya zo ya yi tare da addu'oi, sai around 1 sannan ya kwanta.

Washegari kamar kullum haka ta kasance masu. In takaice maku sai da suka jera kwanaki biyar suna sake maimaicin horo, suka sake karanta sirrin bindigar nan da kyau, tin ranar Monday suna abu É—aya har zuwa ranar Friday. Yau gajeran lokaci ne, karfe 2 suke tashi a horo su je su huta.

A yau kuma Captain ya ce zasu motsa zuwa matakin horo na gaba, dan haka sai suka farka da wuri, karfe 5:30 ta yi masu a hall da suke haɗuwa kafin su fara training. Izuwa yanzu dik wata wahala ta bi jikinsu, basa gajiya sosai, kuma basa wani nauyin barci, harta Noor yanzu jikinsa dan dole ta fara karɓar horo, musamman da yana kasancewa kusa da Leo, yana samun kwarin gwiwa.

A saman stage Captain ya tsaya, ya sanyasu rera taken gidan soja, bayan sun kammala ne ya kwashesu zuwa gym na barrack É—in. Da yake yau ce ranarsu ta farko, sai ya ce.
Chapter 22 · 0% Book details