← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 227

Sashe 148

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ya wuni sukuku, ta ɗauki wannan baby ta dire ta sake ɗaukar wani, kewan darling tamkar ya kasheta, har yamma around 5 daidai 3D suka sake dawowa dan duba lafiyar yaran, kun san basa amfani da ɓargon yaron da ya raunata ko bashi da lafiya, lafiyayyun yara suke amfani da su, shiyasa kuka ga suke yawan zuwa duba lafiyarsu, sau uku a rana suke zuwa dubasu, ko ɗan zazzaɓi yaro ya yi a take zasu ɗauki mataki, basa wasa da lafiyar jariran, dan su samu sinadaran da suke so kada su yi asara.

Kewaye suka dinga yi a cikin yaran, suka auna kowanne, suka tabbatar da suna lafiya, sannan suka nufi waje. Zasu fita ne Dr Kamal ya tsaya, sai ya dawo ciki, a kusa da ita ya tsaya, can ƙasa kamar mai raɗa ya ce. "Akwai aikin da zamu yi yanzu, zuwa dare zan ganki". Ba tare da ya jira amsarta ba, ya juya ya bi bayansu Dr James.

Suna fita kai tsaye SECTION E suka nufa, zasu fara sarrafa ɓargon ƙashi da sinadaran jariran can dan yin magungunar da suke da buƙata. A tinaninku me dame suke yi da ɓargo da jinin jaririn? Magungunar me dame suke haɗawa? Wasu sinadaran suke haɗawa? Ina suke kai magungunan? Shin suna fitar da maganin ne ko kuwa ya suke yi da shi?. Alƙalamina zai warware maku komai tsab, ba zan rage komai ba, mu je zuwa.

3D na fita sai ga sister Zinta ta shigo babys safe room ɗin. BABIES SAFE ROOM (BSR) na taƙaita maku dan rage wahalar ƙira, ku ce BSR kawai.

Ta warke garau, ta sha barci a office na Dr James har ta gode ALLAH, dama jiya bata samu damar yin wani barcin kirki ba, saboda murzanta da ya dinga yi, yau dai ta more, sai yanzu da zai fita ya tada ita, ya ce ta je ta yi wanka zata wastsake. Kafin ta fito wanka ta samu haɗaɗɗen mandi rice ya ajiye mata a wajen sofar da ta tashi, ga crispy chicken da lemun abarba mai mugun sanyi, ta yi mamakin ganin irin abinci, bata taɓa cin irinsa ba, ai ce mashi ta yi zata je ta ci da sister Maya, bai hanata ba, dan bashi da matsala da ƙawancensu, sai ya ce mata ta kula da kanta, anjuma zai zo ya ɗauketa su kwana a ɗakinsa.

Tana murmushi ta ce okey. Zata É—auki kayan abinci ta ji an rungumota ta baya, ajiyar zuciya ta sauke tare da juyowa a hankali, ta faÉ—a jikinsa. Shafa lallausan gashin kanta ya fara yi izuwa gadon bayanta, ya É—an sumbaci cheek É—inta kafin ya saketa, ta É—auki kayan abincin, ta nufi kofa tana waigosa, yana tsaye ya rungumo hannaye a kirji yana kallonta, har zata fita ta sake waigosa, da alama ita ma bata son rabuwa da shi.

Kashe mata ido ɗaya ya yi, hakan yasa ta fice tana murmushi......... Sister Maya na ganinta ta miƙe ta rungumeta tana tambayar lafiyarta. Tana murmushi ta fara bata labarin abin da ya faru bayan sun zauna a gefen gado, sosai Maya ta ji daɗi, sannan ta karɓi kayan abincin ta fito da shi.

Suka zuba a plate, sauran kuma suka baiwa sauran nurses dake faman baiwa babys madarar yamma. Sosai suka ci abincin, sai santi suke yi, haƙiƙa sun yabawa girkin, basu taɓa cin abu mai daɗinsa ba, har da lashe plate sister Maya ta yi, bai isheta ba, amma already sun baiwa sauran nurses sauran abincin, da zata ƙara.

Lemun abarba dake cikin botle suka ɗauko, haba daɗinsa da sanyinsa da ya ratsa masu wuya sister Maya har da rufe idanu, ta dinga santi sister Zinta na yi mata dariya, basu baiwa sauran nurses wannan lemun ba, dan ƙaramin bottle ɗaya ne daidai shan mutum ɗaya, dan haka suka shanye tas, kafin sister Maya ta tattare komai, kunsan malaman asibiti da tsabta, ta tsabtace ko'ina tsab kafin ta dawo suka zauna da sister Zinta a kan gado suna hira, sun bar crispy chicken ɗinsu, dan cikinsu kamar zai fashe saboda ƙoshi, sun sha bottle water, sai sister Maya ta ce su bar shi sai anjuma su ci, na'am da hakan suka yi.

Sister Maya ta bata labarin abin da Dr Kamal ya ce mata, sosai sister Zinta ta tayata murna, suka hau tsara yadda zasu kula da 3D har su samu soyayyarsu sosai!.

----------------------------🔥

CRYSTAL PALACE.

Da wani irin gudu ya shararo da motarsa kan titin dake cikin school É—in izuwa parking lot, tin daga nesa ya hango Seraphina, Rimsha and Faryan suna tsaye suna magana, Seraphina ta ce ita ba zata shiga motarsu ba yau, bata jin daÉ—i, ta tsani ma ai mata mata magana, shi kuwa Faryan, lover boy, sai rarrashinta yake yi, ta kafe ita da kafa zata tafi, kuma karya take yi, yarinya har ta fara koyan karya.

Uncle ne ya hure mata kunne, ya ce idan an tashi ta jira da kansa zai kaita gida, ya kasheta da kalaman kauna game da gift na chocolate har da heart design na pillow mai kyau da aka rubuta i love you blossom, ta sanya kyautar a cikin school back É—inta, shi ne yake cewa da kafa zata tafi, da karfi da ya ji tana son koyar wasu É—abi'u da ba nata ba.

Ai tin Aryan bai gama karisawa wajensu ba ya É—auko wani face ya sanya a fuskansa, face É—in da Seraphina ta fara saninsa da shi, dama suna da shi a cikin motocinsu saboda gudun ko ta kwana. Winter jacket ya É—auko, ya sanya a saman kayansa tare da kashe motar ya fito.

Gabaɗaya kishi ta rufe mashi ido, ya manta Faryan ƙaninsa ne, yana zuwa ya damke mashi da karfi, yana son tambayarsa me ya haɗa shi da ita, amma yasan in dai ya yi magana sai Faryan ya gane, dan haka ya yi shiru bai yi magana ba.

Ƙoƙarin kwace kansa Faryan ya yi, amma ya gagara, dan damkar IRON FIST ba wasa ba, abu kuma ya haɗu da kishi, ai ba'a magana. Ihu Seraphina da Rimsha suka kurma a tare, hakan ya yi silar dawowansa hayyacinsa, da sauri ya saki Faryan, idanunsa sun yi jajir, Seraphina har ta fara ruwan hawaye, muryanta na rawa ta ce. "Daddy please ka kyalesa"...... Da yake ta ganesa tin da fuskan ta fara saninsa.

Wani irin damƙa yai wa hannunta, da karfi yaja sai wajen motarsa, ya buɗe marfin ya jefata ciki, bai sake bi ta kan kowa ba ya shiga gidan gaba, yana ganin Rimsha ta zo da gudu ta rike Faryan tana bashi hakuri. Tada motarsa ya yi, da gudun gaske ya bar school ɗin.

Ni kam na ce ALLAH ya taƙaita basu haɗu da uncle bama, da abin zata fi munana!.

Tana kuka jikinta na kerma, wani irin gigitaccen tsawa ya daka mata, da karfi ya ce. "Will you shut up! I'm coming for you, bari mu koma gida, sai kin faÉ—a mun wanda ya baki izinin kula Faryan!".

Cak ta tsaya da kukan, ta tsai da idanunta a kansa, mamaki ne yakamata na yadda aka yi yasan sunan uncle Faryan É—in Rimsha, to ai ita bata faÉ—a mashi ba, hasalima tin da ta haÉ—u da Faryan basu zauna sun yi hira ba, ko a ina ya san sunansa? Ta jefi kanta da tambayar da babu mai amsa mata, ya ALLAH watau jinin IRON FIST akwai barain, har ta gano ya kira sunan Faryan dik da damuwar da take ciki.

Ai yana parking a garage ɗinsu ta ɓalle door na motar, da gudu ta fita, kafin ya fito ta haye elevator zuwa hawansu, dole ya tsaya jiran elevator ɗin ya dawo ya ɗaukesa. Tana shiga parlonsu ta gudu bayan Madam ta ɓuya, tana kuka ta ce. "Mom kada ki bar daddy ya dakeni, na shiga ukuna".

Madam na ƙoƙarin yin magana sai ga shi ya shigo, har lokacin huci yake yi tamkar zai kama da wuta. A tsakiyar parlon ya tsaya, babu wasa tattare da kan fuskansa ya ce. "Come here!".

Jikinta na kerma sosai, hawaye sun gama wanke fuskarta, ta ƙanƙame Madam tana faɗin. "Mom please help me, don't let him go in with me"...... Madam ta gagara yin magana, dan ita kanta tsoron Aryan take ji, yana cikin kwanciyar hankali ma tsoro yake bata bare ace yana cikin fushi.

Daidai lokacin Aunty Safiyya da Suhana suka fito jin hayaniya a parlon. Ganin abin dake faruwa yasa suka yi saurin ƙarisowa........ Ran Aryan ya ƙara ɓaci, a fusace ya tako ya nufosu tamkar wani mayunwacin zaki. Ai yana ganin ya nufosu kuma Madam bata ce komai ba, sai ta saki Madam, da gudu ta diro ƙasa, tana ƙoƙarin watsawa da gudu ya damƙo gashin kan nan nata.

Sama ya ɗagata sai saman shoulder ɗinsa, su Aunty Safiyya sai kallonsu suke yi. Bai direta a ko'ina ba sai cikin room ɗinta, a tsakiya ya direta tare da fara ƙoƙarin yi mata magana.

Haba ganin bata da mafita ne, babu mai iya kwatarta a hannunsa ne yasa ta tuna abin da ta karanta a littafan can, yadda ake controlling fushin namiji, dan haka dole ta yi amfani da wannan dabara, dan wlh tana balain tsoron dukan Aryan, ta ji kamshin lahira ranar, bata son ko a mafarki ta ƙara jin even one slap from him.

Da sauri ta datse idanu, ta faɗo jikinsa, hot hug ta bashi game da saka mashi kukan shagwaɓa, tana goggoga kanta a saman lion chest ɗinsa..... Jimmmmm haka ya ji duniya ta tsaya mashi, omg, this kukan shagwaɓa melted his heart over, ga goga kanta a kirjinsa da take yi, ga shi she hugged him tightly, ai ɗauke wuta ya yi, zuciyansa na wani irin spark na shauƙin ƙaunarta....... 👀

Cikin kukan shagwaɓa ta ce. "I'm so so sorryyyyyyyyyy daddy, ba zan sake ba, for give me my gentle chaos"...... Oh God, this gal ta gama da daddy yau, wannan suna da ta kirasa my gentle chaos ya gama narka mashi fushin da ya ɗebo, fushin ya narke ya koma so da kaunarta sabo!. Bai san time da ya rungumeta tightly ba, wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke, fushi ta gudu.
Chapter 148 · 0% Book details