Sashe 216
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A daidai wannan lokaci karfe 12 na dare AZURE ta yi kiran meeting na gaggawa kan lamarin MISSION NA DOL. BGA ya tura takarda office na GAT, ai GAT yana ganin takardan ya yi kiran meeting na gaggawa, a lokacin har ya tashi a aiki da yamma, amma da yaga BGA ya turo takarda kan DOL sai ya fasa tashi, ya bada lokacin around 12 na dare zasu yi zaman, ya gagara hakura sai gobe, dama tin tini yake jiran wani motsi daga wajensu.
(Ni kam na ce ai ko dan su Angelina team DOL zaku rinƙa samu umarni da wuri daga GAT!)
A wannan meeting room da suke zama dik end of the week su yi meeting kan tsaro aka shirya zaman. An tsara komai, kafin 12 ta cika dik wasu jiga-jigan generals sojoji sun hallara a wajen. Kamar kullum, GAT ne ya fara miƙewa, ya kunna mic na gabansa, a dake ya yi wa kowa barka da zuwa, kafin ya baiwa BGA damar gabatar da abin da ya tarasu.
Dik kowa ya natsu tsit, BGA ya miƙe cikin mutunta kai, ya zaro farar takarda daga file na gabansa kan table, sai da ya fara yi wa kowa barka da zuwa kafin ya sanar dasu abin da Leo ya sanar da shi a waya. Bayan ya kammala bayani ne ya koma ya zauna sai MGR ya miƙe tsaye, cike da girmamawa ya ce. "A ina wannan waje yake? A ina su Nirash suke dama?".
Cike da É—an mamaki Captain ya kalli MGR, cikin ransa ya ce. "Ko ina ruwansa da in da suke tin da ba a karkashin office É—insa suka tafi Mission ba?". A fili kuma binsu da ido kawai ya yi yana mamakin halin wasu jami'an ba tare da ya yi magana ba.
BGA ya rike mic ɗinsa game da cewa. "Bani da sanin takamamman in da suke, saboda bai faɗa mun ba, amma dai koma ina ne ina jin babban waje ne, kuma sun zaɓi waje mai kyau suka kafa sansaninsu".
MGR ya ce. "Wai dama su nawa ne a sansanin nasu? Da wasu sojoji suka tafi?"........ General Ibrahim IB ne ya ce. "Ina ganin dik wannan ba shi ne ya tara mu a nan ba, umarni suke nema dan zuwa duba menene a wajen, so yakamata ne mu duba mu ga idan ya dace a basu izini sai a basu, a basu izinin su je su duba a sirrance, in sun ga me a wajen sai ayi zama kan abin da ya dace, either a basu umarni kan su tashi wajen in abin da bai dace ba ake yi a wajen, ko kuma a basu umarnin kama masu aiki a wajen, in kuma abin da ya dace ake yi a wajen ba shikenan ba". Ya yi maganar yana kallon MGR. Tin da ya fara magana manyan generals suke jinjina kai alamar tabbas zancen General Ibrahim haka ne.
Bayan ya kai karshen maganar ya juyo da kallonsa a kan GAT da ya yi shiru yana sauraren shawarinsu. General Ibrahim IB a dake ya ce. "Sir, ni a tinanina yakamata a basu izinin zuwa su duba menene a wannan waje, saboda mu san matakin da yakamata mu É—auka".
MGR ne ya ce. "Amma kafin a basu izini yana da kyau mu fara sanin in da suke, saboda ko mun ji shiru a kai masu ɗauki"....... Uhm kai Captain ya jinjina, a cikin ransa ya ce. "Ko kuma a faɗa maka in da suke dan ka ji ko kana da alaƙa da wajen hayaƙin ba"........ Shi dai GAT bai ce komai ba, shiru yana cigaba da saurarensu dan ya ji shawaran kowa.
General Ibrahim IB ya ce. "No need MGR, ba sai mun san takamaiman daidai in da suke ba, umarni kawai za'a basu su kaddamar da aiki, mun basu makamai wadatattu masu lafiya, mun basu dik abin da zasu buƙata! To me na neman sanin ina suka kafa sansani? Dan kai masu agaji? Agajin me bayan wanda suke tattare da shi?"........ MGR ya ce. "Kar ka manta rayuka ne suma, and bamu san wani irin hayaki ne a wajen ba, kada yazamana abin ya fi karfinsu yafi karfin makaman da suka tafi da shi azo a far masu, gara mu san in da suke ta yadda ko an fi karfinsu zamu tura masu wani agaji na gaggawa".
Kai General IB ya girgiza. "MGR wai me naka na son sanin in da suke? A ƙarƙashin office ɗinka suka tafi Mission ne? Ko dai kana da wani plan a ƙasa ne?". Ib ya faɗa yana tsare MGR da ido.... Take MGR ya haɗa malaman jikinsa, ya ɗan yi shiru kafin ya ce. "No sir, ba wani plan, kawai na damu da rayukansu ne duba da yadda muke rasa sojojinmu a arewacin kasar nan, so ina tsoron rasasu ne".
"Dik sojan da ya fito daga nan AZURE na sani kun sani ba dai wani ɗan ta'adda ya fi karfinsa ba, kun san irin horon da muke basu, manyan ƙasashen duniya nan suke kawo sojojinsu dan mu horasu saboda ingancin horarwarmu, to me naka na jin tsoron rasasu? Baka yarda da kanka bane?". General IB ya faɗa, babu wasa a tattare da shi.
BGA ya ce. "Shi nima na gani, no need mu damu da abin da muka san mun fi karfinsa, koma menene sojojin AZURE suna iya tinkararsa ba tare da tsoro ko shakka ba, ko kai da kanka baka yarda da horon barrack É—in namu bane?".
MGR ya girgiza kai game da cewa. "Sorry sir, ni dama saboda damuwar rasasu ne, amma ba komai, nima ina bada goyon bayan a basu izini su je zubasu"..... Shiru ne ya ɗan biyo baya a room ɗin, kafin General IB babban General na AZURE, sojan da baya ɗaukar wasa kuma baya wasa, jami'in da gaskiya da aikinsa suka kawo shi kujeran da yake kamar dai Captain Onbish, jami'in da baya karɓar cin hanci, baya bin bayan rashin gaskiya, ko ɗan uwansa na jin yakama da laifi sai ya hukuntasa daidai da hukuncin da ake yi wa kowa!.
A dake ya ce. "Sir ni a nawa shawarar a basu izinin a sirrance su je su gano menene a wajen, in suka bamu information na abin dake wajen sai mu san matakin dayakamata mu É—auka". Ya faÉ—a yana kallon GAT dake ta binsu da ido.
Jawo paper neman umarnin GAT ya yi. Ya buɗe ya ɗan duba rahoton da BGA ya rubuta kan DOL ɗin. Pen ya ɗauko, cike da kwarewa ya rattaɓa hannu kan ya bada izinin su je su duba. Daga nan ya miƙawa General IB paper. Karɓa IB ya yi, ya ɗauki pen ɗinsa shi ma ya rattaɓa sign ɗinsa. Daga nan ya miƙawa Lieutenant General shi ma ya sanya hannu, sai aka miƙawa Major General shi ma ya sanya hannu, sai Brigadier General watau BGA shi ma ya sanya hannu, sannan aka baiwa Colonel ya rattaɓa nasa hannun, sai Lieutenant Colonel, sai Major, daga nan aka baiwa Captain, yana sanya hannu aka baiwa First Lieutenant, bayan ya sanya hannu sai Second Lieutenant, yana sanya hannu suka maidawa BGA takardan.
Karɓa ya yi, dikkansu suka haɗa maki wajen yi wa team DOL fatan alkhairi da fatan nasara, daga nan GAT ya ce a rufe masu taro da addu'a, kasancewar General IB musulmi ne sai ya riga kowa miƙewa ya fara kwararo masu addu'a har da na fatan ALLAH yasa GAT ya musulunta, dan mutumin kirki ne sosai, ga kaunar kasa da ƴan kasa, yasan aikinsa matuƙa.
Daga nan aka tashi wannan zama around 1:30 na dare, GAT ne ya fara fita kafin su General suka rufa mashi baya. Yana komawa gida ya isko Aunty Lisa tsaye a parlo sanye da sleeping dress tana ta faman jiransa, ta É—an kiba sosai, da alamar tana da ciki.
Yana shigowa ta tafi ta rungumesa tana mashi welcome, shafa kanta ya yi game da cewa. "Ya shirye-shirye?"...... "Welcome my oga sir". Ta faɗa kafin ta bashi amsar tambayarsa na ya shirye-shirye da cewa. "Komai yana tafiya daidai a nawa ɓangaren kai fa?".
Rage tsawonsa ya yi ya É—auketa cak yana amsa mata da. "Komai daidai, amma party biyu kawai za'ayi sai soldiers day shi ma É—aya". Ya faÉ—a a lokacin da suke shigewa room É—insu.
Watau jama'a shirye-shirye bikin GAT da Aunty Lisa ake yi, ana shirin party, yanzu ya fitarwa da duniya cewa zai yi aure, shi ne ake shirye-shirye, ga alamar kuma Aunty Lisa na da ciki, har ma ya É—an fara girma. Akwai shagali, su Arya sai dai su dawo su samu Aunty É—insu da baby, dan cikin Aunty Lisa zai iya kai 3 month ma. Gaskiya daddy GAT yana sha'aninsa, ya tura yara mission shi kuma yana buga nasa mission É—in a gida, bari dai in yi shiru kada ace na ce, to ban ce ba!.
D------O-----L.
Tin Arya tana iya jurewa ta taka da kafafunta har ta gagara, abin yai mata yawa, ga barci ga gajiya. Wani irin jirin gajiya da ya ɗebeta bata san lokacin da ta tafi gabaɗaya ta faɗi ƙasa ba.
Intently Leo dake gabanta ya juyo, ganin ta faɗi ƙasa yasa ya juya ya kalli hanya, sun kusa isa sansaninsu, duba time ya yi a wayansa 3:30 ya yi....... Matsawa dab ita ya yi, a cikin ransa yana faɗin dole ya bata ainahin horo ba horon kare kai ba, in dai zai yi aiki da ita dole ta iya jurar dik wani wahala, dole ta zama kaman shi, dan haka daga gobe dole ya fara horar da ita.