← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 220 OF 227

Sashe 220

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza mashi kai Lion ya ɗan yi alamar ya ake ciki?. Kashe wa Lion ido ɗaya ya yi yana ɗan ɗake kafaɗa. Hararansa Lion ya yi, babu alamar zai yi magana. Shi kam Vir da yake ya gane damuwar Aryan hankalinsa ya kwanta, sai ya fara yi matsu tsiya, sun ƙagu su ji menene yake damunsa amma Vir yana son ɓata masu lokaci.

Guru ne ya ce. "Please Vir, menene yake damunsa?". Ya faɗa cike da damuwa........ Gyara tsayuwansa Vir ya yi, cike da tsiya ya ce. "Ba wani abu mai wahala bane, mace kawai yake buƙata mu samo mashi"......... Cikin rashin fahimta Lion ya kallesa game da cewa. "Vir!!". Ya faɗa yana tamke fuska.

Tamke fuska shi ma Vir ya yi kafin ya ce. "Da gaske mace kawai yake so, sperm tai mashi yawa a mara, dole ya samu wajen juye, zan mashi alluran da zata sassauta mashi, but ko a nema mashi mata ko kuma a samu matsala, allura ba zata cigaba da rikesa ba, a nema masa mace, idan ba haka ba wlh ya ƙulla da ciwon ciki kenan har sai randa ya samu wajen juye"........ Zazzaro idanu guru ya yi, wata sabuwa in ji ɗan caca. Lion kuwa cewa ya yi. "Hakan ba zai yiwu ba, zai samu sauki ne, ba wata mace!". Ya faɗa game da juyawa ya bar room ɗin, da alamar ɓacin rai a tattare da shi.

Kallon Vir guru ya yi, can ƙasa ya ce. "Bana fatan ALLAH ya haɗa our Lion da wani kaddarar da zai sanya shi neman abu a wajen mace, yanzu dai ga shi ALLAH ya kama our champion, dole ya nemi mace in yana son zaman lafiya, a da ba wanda ya kaisa cika baki a kan cewa mace bata da amfani, bak san cewa akwai wani abin da zaka nema a duniya sai a wajen mace kawai zaka samu ba". ........ Vir dake kokarin haɗa allurar da zai yi wa Aryan ne ya ce. "A ɓangaren lafiya akwai abubuwa da dama wanda dole a wajen mace kawai namiji zai iya samunsu dan lafiyarsa ta ɗaure, shi kansa Lion ɗin zai shiga hannu ne, dan injunan jikin namiji suna cigaba da aiki da kwarinsu ne kawai idan suna samun wasu sinadarai daga jikin mace, but shaaaa, lokacin zai gyaramu ne".

Guru ya ce. "Awww ka yarda bama kan daidai sai lokacin ya gyaramu ko?"...... Yana ƙoƙarin ɗaure hannun Aryan ya nemi vein ya ce. "Muna kan daidai, amma muna yanke hukuncin da bai dace ba, ba'a hukunta wani da laifin wani, amma mu mun yi hakan". Ya faɗa game da yi wa Aryan wannan allura.

Miƙewa guru ya yi tare da cewa. "Bani da bakin magana, wannan hukuncin da muka yi shi ne daidai". Ya faɗa game da juyawa ya bar wajen. Bayansa Vir ya bi cike da tsananin tausayin guru, dan shi ma labarinsa bashi da daɗin ji, shi da Lion sun sha gubar mace ba kaɗan ba, shiyasa kome zasu ce kan mace ba mai ganin laifinsu, ko uncle baya ganin laifinsu, sai dai ya ce sun yi daidai.

Bayan ya yi wa Aryan allura sai ya rage mashi gudun AC, ya kulluɓe shi da duv kafin ya fita zuwa room na Lion. Tsaye a kan daddduma ya isko Lion yana sallah, while guru ma ya ɗauro alwala ya fito, a gefen Lion ya tsaya suka cigaba da sallah a tare.

Cikin toilet Vir ya nufa, alwala ya É—auro shi ma, ya zo ya jera kusa da su. Suka fara nafilfilinsu. Jama'a dole IRON FIST su gagari kowa a duniya, mutanen dake da kusanci da UBANGIJINSU, kun san girman sallar dare kuwa? Kai dole su fi karfin kowa.

Basu kwanta ba har asuba, suka yi raƙatainil fajir kafin su shirya zuwa masallacin, a tare suka nufi in da Aryan yake kwance. Yana ta zuba barcin wahala, ya sha azaban ciwon ciki bawan ALLAH. Guru zai tashesa Lion ya ce su barshi, haka suka kyalesa suka nufi masallaci. Yau Aryan bai yi sallar asuba ba sai around 6 na safe, da suka dawo masallaci Lion ya tashesa.

Cikin ikon ALLAH ya tashi da lafiyansa, ya yi wanka, ya É—auro alwala, sallar asuban ya biya tare da zama yana askar. Yana kammalawa around 7 ya fito, a dining room ya isko su guru zaune suna jiransa, dik suna shirye cikin tail coat É—insu iri É—aya mai mugun kyau da tsada, shi kuwa yana sanye da thobe (arabs jallabiya) fari tas.

Wani irin yunwa yake ji, saboda alluran da Vir yai mashi, cikinsa har wani murÉ—awa take yi, yana zama ya É—auki spoon, masu serving É—insu suka zuba mashi, sai kallonsa Lion yake yi, shi kuwa bai yarda sun haÉ—a ido ba, dan dik maganar da Vir ya faÉ—a daren jiya yana jinsu, dan haka bai yarda sun haÉ—a ido da kowa ba.

Dikkansu sai kallonsa suke yi, aikuwa ya mai da kansa kan abinci. Ana zuba mashi mandi rice ya sanya spoon ya É—ebo, zai kai bakinsa sai ya fasa ya nufi bakin guru É—an autan IRON FIST da abinci. Ba tare da ya É—ago ya kalli guru ido cikin ido ba kawai ta danna mashi abincin a baki, ya zare spoon É—insa, ya É—ebo wani ya kai bakinsa.

A natse ya fara ci yana wani kara yin ƙasa da kai kamar wani maras gaskiya. Kallon Lion da guru Vir ya yi, sun haɗe hannu sun yi folding a kirjinsu suna kallon Champion. Ko sau ɗaya bai ɗago ya gansu ba har ya ci ya ƙoshi, ya ci abinci da mugun yawa yau, dan plate shake tab ya cinye, ya sha ruwa roba ɗaya full, sannan ya ɗauki tissue ya goge bakinsa, yana gamawa ya miƙe, ya dai ki kallonsu ya wuce da sauri ya fice daga room ɗin.

Yana fita ya je ya sanya kaya irin nasu sak, bai sake bi ta kansu ba ya nufi waje, kai tsaye Khaiza'ans House ya nufa. Su kuwa yana fita suka kalli juna, sai kuma suka É—auki spoons a tare, ba wanda ya ce da É—an uwansa kala, suka fara cin abinci a natse.

Bakinsa a É—auke da sallama ya shiga gidan Abba, ya wani uban tamke fuska babu alamar wasa a tattare da shi.

GabaÉ—aya family suna dining room suna breakfas, daga in da yake tsaye a parlon yana hangosu a cikin dining room É—in. Zamansa ya yi a kan sofa yana jiran su kammala, ya fito da wayansa kenan sai ga kiran Seraphina ya shigo wayan.

Picking ya yi game da karawa a kunne. Kukan shagwaɓa ta sanya mashi kafin ta ce. "Daddy what about school? In tafi da kafa ne?"........ Duba time ya yi. 7:30 ta yi, a dake ya ce. "Baki iya sallama and gaisuwa bane?"......... "Sorry, na manta ne, ina sauri batun school, good morning my husband".

Nisawa ya ɗan yi. "Za'a zo a kaiki, akwai in da zan je yau". Yana gama faɗa ya katse kiran, ɗaya daga cikin guards ɗinsu na benen SSO ya kira. Dama ya taɓa kaita school, dan haka Aryan ya ce mashi. "Jeka kai Cherry School yanzu".. bai jira amsarsa ba ya katse kiran.

A daidai lokacin su Faryan suka fito daga dining room É—in, wajensa suka nufo, cikin girmamawa suka É—aga mashi gaisuwa. Harleen ango sai wani kyalli face É—insa take yi. Dikkansu amsa É—aya Aryan ya basu, daga nan bai sake yin magana ba.

Miƙewa suka yi, Hareen ya nufi sama ɗakinsa, shi kuma Faryan ya tsaya a wajen door yana faɗin. "Rimsha ki yi sauri kada ki yi latti"...... Ita kuwa ganin Aryan a parlo yasa ta gagara barin dining room ɗin ta fito, tana shirye cikin uniform, tana tsoron ko numfashinsa ta ji.

Miƙewa Abba da Ammie suka yi suka fito, while ita kuma Auntu Luna tana room ɗinta kwance tana barci, bata farka ba, dama in baku manta ba yar daddyn Noor basa tashi barci safe da wuri, fatan kun tina Noor a AZURE BARRACK a lokacin da Captain ke tashinsa da ruwan sanyi.

Abba yana É—an dogara scepter É—insa ya kariso saman sofa, ya zauna game da mai da kallonsa a kan Aryan. Cikin girmamawa Aryan ya É—aga mashi gaisuwa. Amsawa ya yi fuska ba yabo ba fallasa. Gaisuwa ya É—agawa Ammie ma, tana murmushi ta amsa.

Shiru ne ya ɗan biyo baya, Abba na jiran jin me Aryan zai ce mashi, dan wannan zaman da ya yi da biyu, while Faryan na jiran Rimsha dake zaune a dining room ta gagara fitowa, ta yi ƙasa da kai, ko kallon in da Aryan yake bata iya ɗago ido ta yi ba, ɗan kwarin gwiwar da Seraphina ta bata jiya har take jin zata iya ganin Aryan tai mashi magana ma ya gudu, tana ganinsa yanzun nan ta ji komai ya gudu, tsoronsa ya ninku a ranta.

"Abba na zo ɗaukar yarinyar nan ne in koma da ita gidana". Aryan ya faɗa a dake....... "To Alhamdllh, abin da nike fatan ji kenan, ai gata ta shirya zuwa school yanzu, ka yi dropping ɗinta a school, idan an tashi sai ka ɗauketa ku wuce gidan naka ko?"...... Kai kawai ya jinjina, miƙewa tsaye ya yi tare da wucewa ya nufi kofa kafin ya ce. "Ta sameni a mota yanzu".

Rimsha dake jinsu ne idanunta suka cicciko da kwallah, gani take yi shikenan rayuwarta ta zo karshe idan ta je gidansa. Ƙoƙarin danne hawayen nata ta yi, ta mike ta fito wajensu Abba. Cike da farinciki Abba ya ce. "Mamana jeki mijinki na jiranki a mota, ALLAH yai maki albarka kin ji? Ki yi hakuri da halinsa watarana komai zai wuce".
Chapter 220 · 0% Book details