← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 227

Sashe 24

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Suna isa rooms É—insu suka wuce, dan lokacin sallah saura Æ´an mintuna. A gurguje suka yi wanka, ga shi ba ruwan zafin gasa jiki, wlh dik wanda ya gansu yasan a tsananin gajiye suke. Noor dai ko wanka bai yi ba, gado ya haye, ya kwanta abinsa, tin da bani horo a gaba ai sai barcin huce gajiya.

Su kuma suka shirya suka tafi masallaci, Leo ya shirya cikin wasu tsadaddun ripped jeans blue mai bala'in kyau, daga sama ya sanya polo shirt fari tas, still ya sanya army p-cap, amma ya juya p-cap É—in dan ya iya yin sallah. Ya tara kitson kansa ya É—aure a baya, ya tura jelar cikin p-cap É—in, sai tashin daddaÉ—ar kamshi perfume na kamfaninsu Noor yake yi. Watau yau Leo ya fito a ainahin É—an duniyarsa, ripped jeans É—in nan ta kara mai da shi irin shahararrun Æ´an iskan nan ne, irin jeans É—in nan ne masu zubin crazy, but ripped ba'a yayyage take skint a waje ba, tana yayyagen amma daga ciki an sanya wani tadin jeans É—in, yagi-yagin ya zama kamar kwalliya ce kawai.

Dadduma ya ɗauka ya fita zuwa masallacin, su kansu Zaysh da suke maza sai da suka kallesa suka kara, daga karshe ma zuba mashi idanu suka yi har ya fita. Sannan suka karisa nasu shirin, Zaysh kayanmu na hausawa ya sanya, kyakkyawar jumpa milk color da ta sha guga sosai. Vash ya sanya three-pieces suit. Ya yi matuƙar kyau, amma sai santin kayan Zaysh yake yi, wai shadda tai mashi kyau, Zaysh ya ce su je masallaci su dawo zai bashi kyautar kala biyu, ya zaɓi wanda yake so, sai murna yake yi.

------------------- After 40 mins.

Bayan sun yi sallah sun fito, za su nufi dining hall, a kan hanyarsu na zuwa suka ci karo da GAT da ya fito daga office É—insa, sai sauri yake yi, ai take kowa ya kame suka hau sara mashi. Har ya wucesu kuma sai ya dawo, a gaban Leo ya tsaya, dama tin É—asun da ya kalli yadda suka yi suka dawo gida yake ta faman kallon Leo a video É—in, dan yaga shi yai masu jagora.

Key ɗin hannunsa ya miƙawa Leo, a natse ya ce. "Ka je sashin horar da jami'ai na musamman ka ɗauko mun yarana ka kaisu gida". Yana gama faɗar haka ya wuce bai kara wata magana ba. Mamaki ne ya kama Leo, to shi a yaushe ya san yaransa fisabilillahi? Bai san hakan ma dik gwada shi yake son yi dan ya tabbatar da cewa da gaske da ƙwaƙwalwa Leo yake aiki ne ko kuwa! Watau ya gano yaran da kansa, ya yi tinani da brain ɗinsa.

Ya ɗan jima a tsaye kafin ya juya ya nufi harabar office na Seniors ɗin nasu. A hanya ya haɗu da Captain, sara mashi ya yi, har zai wuce Captain ya miƙa mashi hannu kan su gaisa, ya ɗan yi mamaki. Katse mashi mamakin Captain ya yi da cewa. "A lokacin da ba lokacin horo ba ka ɗaukeni matsayin brother"....... Watau a lokacin horo kuma ba sani ba sabo.

Jinjina kai ya yi tare da bashi hannu suka gaisa........ "Ina zaka je?". Captain ya sake faɗa...... Sai da ya ɗan yi shiru na ƴan sakani kafin ya ce. "GAT sent me to pick up his children from school and take them home"....... Jinjina kai Captain ya yi, shi ma zuciyarsa cike da mamakin yadda aka yi su Leo suka dawo, a tarihin AZURE team biyu ne suka taɓa haye waɗan nan gwaji dik da akwai wasu masu zafi a gaba, amma tin a farko babu wata wahala sun fara wucewa, gaskiya su ɗin ƴan baiwa ne.

Wucewa Leo ya yi ya nufi wajen motocin. Duba key dake hannunsa ya yi, ta Pagani huayra lmola ce, yasan mota sosai shiyasa ya gane key ɗin wacce ce. Kai tsaye ya nufi motar, bai ɓata lokaci wajen shiga ba, ya ajiye daddymarsa a saman seat na motar, a natse ya tada ta ya nufi barin wajen.

Sai da ya tafi kaɗai ya fara tinanin ina nema school ɗin kwararrun jami'an yake? Kwararru ma ta wani ɓangare ne? Dan kwarewar ai kala-kala ce. Hakan yasa ya tsaya tare da tambayar wasu zaratan sojoji dake ta faman sarawa motar a tinaninsu GAT ne a ciki. Sauke glasa ya yi tare da sara masu, sannan ya yi masu sallama. A mutunce suka amsa, a natse ya tambayi ina ne school na yaran GAT.

Ba ɓata lokaci suka sanar da shi ai suna ɓangaren computer ne, su kwararrun jami'ai ne ta ɓangaren computer. Godiya ya yi masu tare da jan motar ya wuce, da kallo suka bisa suna manakin irin tsantsar kyan da yake da shi, basu taɓa kallonsa a barrack ɗin ba sai yau.

Kai tsaye gate na school É—in ya nufa, ya yi mamakin ganin babu students. Yau jummaa tin 1 suka tashi, yanzu kuma 2:30 ta yi, students dik sun watse, GAT ya shiga meeting ne ya makara zuwa É—aukar yaran nasa, ga shi kuma bai basu driver ba saboda tsananin son da yake yi masu, komai da ya shafesu da kansa yake zuwa ya yi, dan in yasa ayi masu sai ya ga ba'ayi masu yadda ya dace.

Rarraba idanunsa ya fara yi tin da ya shiga school É—in, makarantar tana da girma sosai, zaka ce ba'a cikin barrack É—in ma take ba saboda girma. Yawo ya fara yi a ciki yana neman ta ina zai gansu ne wai. Can ya hango wata studens sanye da uniform É—insu, tana duke a kusa da filin wasanninsu, jan motar ya yi ya karisa wajen. Jin motsin mota yasa ta É—ago kai slowly.

Ya subhanallah, ALLAH ya yi halitta a wannan waje, Æ´ar yarinya ce da bata wuci 13 years ba, tana sanya da mini sket zuwa santala-santala cinyoyinta, black color ne sket É—in, sai top daga sama white color, haka uniform É—in nasu, tana da gashi mai tsananin kyau, bakinkirin, ta É—aure shi kashi biyu, ta zubo jekar ta gaba gar kasan kirjinsa, ga jekar gashin an É—aure da ribon kalar uniform É—in, kafafunta sanye da boot fari tas, tana goye da jaka black color.

Ganin motar yasa ta ɗaure fuska sosai, tamkar bata taɓa sanin menene dariya ba, da ta haɗe ran ma ta fi kyau. Da sauri ta bar wajen ta shiga wajen wasannin. Kallo ɗaya yai mata ya ɗauke kansa, kuma ya gane ita ce ƴar GAT, dan ga kama nan a kan fuskansu. Jan motar ya yi ya bi bayanta har zuwa wajen wasanin cike da mamakin meyasa ta ga motar gidansu kuma bata tsaya ba? Bai san yaran nan sun fi ubansu murɗaɗɗen hali ba.

A ɗan nesa da su ya faka motar tare da fitowa, ya jingina da jikin motar a ransa yana jin ba zai iya juwa ya yi masu magana ba, ɗan ɗagowa ya yi ya kalli yarinyar, sai ya ga ashe su biyu ne a wajen, ɗaya tana ƙoƙarin ɗaure igiyar boot dake kafafunta, ɗayar kuma hannunta rike da basket ball.

Da sauri ya ɗauke kallonsa a kansu, amma ya sha mamakin ganin kamar kamanninsu ɗaya su biyun. Dan ya tabbatar kallon gefen ido ya sake binsu da shi, nan fa ya kara shiga mamaki ganin da gaske ne a kan fuskokinsu babu wani banbanci, sun yi mugun kama na wuce misali. Like seriously! Wow, abin da mamaki. Jingina sosai yai da jikin motar yana mai da kallonsa ƙasa, babu alamar zai yi masu magana.

Wasu Æ´an'mata guda biyu ne da suka shigo wajen basket ball É—in a yanzu suka sanya yai gaggawar É—an raba jikinsa da jikin motar, dan ta witsiyar ido ya gansu, sai yaga tamkar almara ce ko inuwarsu Arya ya gani.

Nan fa ya ji kamar kwakwalwansa ta ɗan juya, a cikin ransa ya ce kenan ƴaƴan GAT Quadruple ne? Kuma dikka mata masu tsananin kama da juna? Kai bai taɓa ganin haka a zahiri ba. Amma sai ya fiske tare da mai da kallonsa ƙasa.

Wacce ke rike da basketball É—in ce ta ce. "Arya time is going let's finish this game before that ya kariso". Kalamanta ya nuna basu san da Leo a tsaye a wajen ba. Arya dake faman É—aure igiyar boot na kafafunta ne ta É—ago da kai. "Angelina dad can't come now, because he has a meeting, so we have a lot of time da zamu buga game É—in nan slowly".

Uhm Angelie, Arya, Manassa and Vanisha, ƴaƴa ne ga GAT namu, ƴaƴan da kenan ya mallaka a rayuwansa, ƴan huɗu ne watau quadruples, sun taso ne cikin tsananin kula da soyayyar mahaifi, bai taɓa bari sun yi kuka ko sau ɗaya na rashin wani abu ba a rayuwarsu, yana sonsu fiye da yadda yake son kansa, basu da mahaifiya, daga su sai uban masu aiki dake kula da su, ma'aikatan gidan GAT sun haura 15, kuma dik saboda farincikin su Arya ya zuba su. Sun taso sangartattun yara waɗan da basa ji kuma basa ragawa kowa, ranon soja ne su ɗin, basu ɗaukar rainin hankali, musamman Arya, asalin sunanta DINEARIS, suna ce mata Arya ne kawai saboda wani dalili na daddynsu da yasa ya ɓoye ainahin sunansa.
Chapter 24 · 0% Book details