← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 227

Sashe 47

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dik ɗakin shiru ya yi babu wanda ya amsa, sai can wayoyinsu ya yi ƙara ban da na Lion, a natse suka fito da wayoyin, sms aka yi masu. Buɗewa suka yi, a tare suka ɗago suka kalli Lion dake tsakiyansu yana pressing nasa computer........ Mai da kallonsu a kan sms ɗin suka yi, hoton wani dattijo ne mai zubin kamala da dattaku, fari tas da shi mai ɗan tsawo, shi ne Lion ya tura masu saƙon a wayansu.

Cikin wata iriyar muryan da ba zaka taɓa iya shaida voice ɗinsa ba Lion ya ce. "He will arrive in the Us tonight, he will check in at the Star hotel, and have dinner by the waterfront, by the end of the night, his fate will be sealed, he will not see the next day!"...... Kallon juna Champion and Scorpion suka yi.

"Guru kai ne a kan wannan aiki". Champion ya faÉ—a yana kallon Scorpion da suka fi kira da sunan guru, abin da yasa suke ce mashi Scorpion ma shi ne, kamar kunama yake, in dai ya kalli mutum sai gabaÉ—aya gangar jikinsa ya amsa kamar yadda in kunama ta harbeka sai gabaÉ—aya gangar jikinka ta amsa. Abin da yasa suke ce mashi guru kuma shi ne namijin gaske ne wanda gabaÉ—aya baya tsoron mutuwa, rungumar mutuwa yake yi a lokacin aiki, suka ce mutuwa da kanta shakkar É—aukar guru take yi!.

"Tare zamu buga". Lion ya faÉ—a a sanyaye. Mamaki ne ya kamasu, dan sun san basu cika aikata aiki a tare ba, meyasa yau zasu yi a tare? Kaifin kwakwalwarsu da kaifinsu yasa mutum É—aya a cikinsu yana iya jagorantar aiki dik girmanta, yau ace su uku dikka a aiki É—aya? Lallai koma wanenen wannan babban kai ne!.

Shigar da hotonsa computer É—insa Champion ya yi domin ya duba waye shi? Yaki faÉ—a masu ya je wajen Seraph, ya bar abin a ransa dan yana jin kamar shi ne ke da kusanci da ita ba su ba ko in ce ya fisu kusanci da ita, dan haka a ransa ya kudurta niyar bata kulawa koda basu sani ba!....... Dik yadda aka yi shi ya kashe mata daddy ko kuma shi ne ma daddyn nata É—an banza!.

Kammala bincikensa a kan hoton Champion, bayanai suka fito mashi kamar haka. Taimur Abbas Ali, dattijo mai shekaru 55 a duniya, preministar ƙasar India, dattijo mai mulki cikin gaskiya da amana, ya tsaya tsayin daka wajen ganin ya dakatar da kisan kiyashin da ake yi wa musulman indiyawa, bashi da nuna banbanci ko kyara ga wasu addinan, akwai addinai dayawa a ƙasar, amma bai takura masu ba, ya bari suna yi kayansu, ɗan gwagwarmayar ne sosai, amma a yau so ake yi ya faɗi saboda gwagwarmayarsa kan ganin lallai sai Musulman kasar sun samu ƴanci suna rayuwa kamar kowanu Musulmi a duniya, shiyasa aka yi ca a kansa, har poisoning ɗinsa an so yi, amma ALLAH ya ketarar da shi, musulman indiyawa suna ji da shi, amma gwamnati ta basu kwangilar kashesa, kun ji kuma abin da Lion ya ce.

Jinjina kai Champion ya yi bayan gama karanta bayanai a kan dattijon, watau wanna babban aiki ne shiyasa Lion ya ce tare zasu yi, saboda akwai tsananin tsaro sosai, dole su mayar da hankali.

"Me plan ɗin?". Guru ya tambaya yana share bayanan da ya shi ma ya duba kan dattijon. Take computers dake gabansu ya yi ƙara alamar saƙo. Buɗewa suka yi a natse cike da kware, saƙo ne daga computer Lion, dik wani plan da ya shirya dan kashe mutumin ne ya basu jawabi. Natsuwa suka yi suna karantawa, plan A and B ne, basu taɓa tsara plan ya yi felling ba, amma dik da haka kullum sai sun tsara A and B saboda tsaro. Natsuwa suka yi suka karanta komai daki-daki kafin su goge saƙon, dan basu barin irin wannan shirin nasu gudun ɓacin rana.

Daga nan suka shiga gudanar da aiki. Gabaɗaya Champion ya manta da Seraph again, ya kama aikin ƙoƙarin ganin komai ya tafi daidai.

A tinaninku wani irin plan Lion ya shirya dan kashe wannan mutumi? Za su yi nasara ko a'a? Me kuke tinani a wannan ɓangare? Uhm da aiki babba a gabanmu, kwata-kwata ban taɓo dalilin kirkiran wannan labari da na yi bama, amma mun kusa isa wajen, zan so kowa ya karanta wannan ɓangare dan abu ne da zai shafi kowa da kowa musamman mata, ALLAH dai ya yi mana mai kyau!.

----------------------------🔥

AZURE.

Bayan sun ci sun ƙoshi V ta ce su je wajensu Arya. Cike da farinciki suka miƙe zasu haura sama kenan suka jiyo tsayuwar motocin GAT a harabar gidan. Ai mantawa da su V ta yi, da gudu ta nufi door tana faɗin. "Aunty I'm coming"..... Su dai kome ta yi burgesu take yi, dan haka suka bita da kallo.

Daidai lokacin su Arya suka sauko da gudu, suna sanye da sleeping dress, silky short trouser and vest daga ta sama. Ai a mikiyan su Lisa suka bisu da kallo, ai sai suka rikice, a take a wajen suka rasa wacece V a cikinsu. Ba dan V kayan jikinta daban da nasu yake ba da wlh ba zasu gane ta ba, dan hankalinsu ba zai basu cewa V bata kai su tsawo ba.

GAT na shigowa parlo suka rungumesa da karfi suna mashi oyoyo, ai gyara tsayuwa su Lisa suka yi suna kallonsu, gwanin burgewa. Rirrikosu GAT ya yi yana yi masu oyoyo É—in shi ma, a haka suka kariso tsakiyar parlon. Sai a lokacin ya lura da su Lisa a tsaye, É—an sake su V ya yi, idanunsa a kan Aunty Lisa ya ce. "Welcome".

Fuskokinsu a ɗauke da murmushi suka amsa da. "Thank you daddy!"..... "Where's your dad?". Ya tambaya yana kamo V dake ƙoƙarin zamewa, so take ta gudu ɗaki dan ta ga call ɗin Noor ya shigo wayar Angelie dake hannunta. "Daddy yana cikin room". Suka bashi amsa kusan bakinsu a haɗe.

Yana satar kallon suran jikin Aunty Lisa ya ce. "I hope you're enjoying this moment and hope you take your dinner?"...... Da sauri suka amsa da. "Yes daddy, we really love this house, especially da yakasance our beautiful princess tana ciki". Lisa ta faÉ—a tana nuna mashi V da hannu.

Da yake yasan a yaran nasa V da Angelie ne masu saukin kai sai ya yi zaton ko V ta saki jiki da su ya kyautata masu ne yasa suke yabonta, and yasan ta fi sauran saurin shiga rai, ko kusa ko alama bai gane dalilinsu na kiranta beautiful princess ba. "Let me see your dad Ina zuwa". Ya faɗa tare da dawo da kallonsa a kan V da gabaɗaya ta gama ƙosawa daddy ya saketa ta gudu ɗaki, ta yi picking call na Noor, dik da tasan batun waya zai yi mata, amma ta matsu ta ji voice ɗinsa.

"My baby naga kina sauri ki gudu sama hope lafiya?". GAT ya tambayeta..... A ɗan shagwaɓe ta ce. "I want to go to toilet daddy"..... Da sauri ya saketa yana faɗin. "Run my baby"...... Kashe mata ido Angelie ta yi, dan ya ga call ɗin ita ma, da gu V ta nufi sama tana maidawa Angelie martani da ɗaga mata gera guda.

Harara Arya ta bisu da shi dan dik abin da suke yi ta gansu. Sama GAT ya nufa yana faɗin bari ya duba daddy Noor yana zuwa. Wucewa Arya da Manassa suka yi izuwa room na daddyn nasu ba tare da sun kalli in da su Lisa suke ba. Angelie ce ta ce. "Aunty Lisa ku zo mu je room ɗinku ko?". Da okey suka amsa, ta wuce gaba suk rufa mata baya. Yanzu Angelie ta gane suna da alaƙa da mutumin da V take so watau Noor, shiyasa ta matsu ta koma room ta ji bayani daga bakin V, ita kuwa V sai addu'a take yi kada su Aunty Lisa su sanar da Noor ga in da ta fito.

Tana hayewa sama ta faɗa balcony, zama ta yi saman chair dake wajen ta fara ƙoƙarin kiran numbersa kenan kiransa ta sake shigowa. Sai da ta saita natsuwarta kafin ta yi picking.

"Hello". Ta faɗa a shagwaɓe. Nisawa ya ɗan yi tare da satar kallon Leo dake kokarin sanya botiran sleeping dress ɗin jikinsa. "Barka da dare". Ya faɗa tamkar mai raɗa dan kada Leo ya jiyosa.... "Barka dai, fatan ka koma lafiya?".

"Lafiya". Ya amsa tare da ɗan yin shiru, sai kuma ya ce. "Kin manta baki karɓi wayarki ba! Ga shi gobe da sassafe zan bar barrack ɗin nan, sai ya kenan?"... Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Ba kai ka sanyani na manta komai ba".... "Like how?". Ya tambaya...... "Like the way you did mana, ka sanya na manta kaina ni wacece, na mance a wata duniya nike, ai ka yi freshing brain ɗina my heartbeat".

Ɗan waro eyes ɗinsa ya yi, shagwaɓar nan tata ta tsuma zuciyansa, ta yi melting heart ɗin nasa, in a cool way ya ce. "Me na yi maki wai?"....... "Uhm baka san a lokacin da ka matso kusa dani ka yi freshing komai ɗina ba ko?"..... Shiru yayi, lallai yarinyar nan tana son wuce dik lissafinsa, tana faman goge mashi hadda. Satar kallon Leo ya yi kafin ya ce. "Kina da zola, yanzu dai faɗa mun ya za'ayi da wayar nan?".

Turo baki ta yi tamkar tanaa gabansa, a ranta ta kuduri niyyar sanya shi sakin jiki ya yi hira da ita dolensa ko yaki ko ya so. Dan haka sai ta ce. "Da sassafe mu haÉ—u ka bani wayar kawai"..... Jinjina kai ya yi tare da cewa. "Okey goodnight".......... "Uhm komai naka daban ne, to mu haÉ—u a Whatsapp". Bata jira amsar shi ba ta katse kiran. Mamakin yarinyar ne ya rufesa, a ransa ya ce Æ´ar karama da ita sai karfin hali. A fili kuma ajiye wayar tasa ya yi irin zai shareta É—in nan.
Chapter 47 · 0% Book details