← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 227

Sashe 138

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da okey suka amsa mashi, ya wuce gaba bayan ya miƙawa Dr Kamal wayansa, bayansa suka bi, wancan ɗakin da ake haɗa magungunar suka koma, jim kaɗan suka fito hannun Dr James rike da wata sirinjin allura da kuma ruwan maganin.

Kai tsaye SECTION D suka nufa, dik in da suka wuce sai nurses sun zube ƙasa sun kwashi gaisuwa. Basu amsa kowa ba har suka shiga cikin ɗakin da su sister Zinta suke.

Su Maya na ganinsu suka zube ƙasa dan kwasan gaisuwa. Wucewa ciki Dr James ya yi, ya fara bin yaran yana dubawa ya ga wanne yakamata ya ɗauka dan ayiwa gwajin alluran nan?.

Daidai lokacin darling dake hannun sister Maya ya fara kuka, miƙewa tsaye da shi ta yi, ta fara jijjigasa tana shafa bayansa, ta saɓashi a saman shoulder ɗinta. Ɗago kai Dr James ya yi, zubawa babyn idanu ya ɗan yi, can kuma ya nisa tare da cewa Maya. "Bani shi a nan"........ Bata kawo komai a ranta ba, ta yi sauri ta miƙa mashi shi. Karɓarsa ya yi tare da cewa Dr Mark. "Jawo mun bed ɗinsa nan". Ya faɗa tare da fitowa gaban ɗakin.

Sister Zinta dake zaune ne ta miƙe tsaye, idanunta na ɗan rawa a kan sirinjin alluran dake hannun Dr James, mamaki ya ɗan kamata.

Jawo gadon baby Dr Mark ya yi, a kansa Dr James ya kwantar da babyn, ya gyara cinyarsa zai fara yi mashi allura kenan muryan sister Zinta ya dakatar da shi. "I'm sorry sir, wannan injection É—in fa?".

Slowly ya ɗago da kallonsa a kanta, sai ya tina irin abin da yai mata last time, ba ya ce ta zo yana nemanta ba in baku manta ba, to hidiman babys yasa bata samu damar zuwa da wuri ba, shi kuma shegen zuciyar bala'i, tana zuwa ya koreta wai ta ƙara mintuna goma kan wanda ya ce, yana sonta fa, yana son faɗa mata abin dake ransa, sonta kamar ya kashesa, amma guy ɗin nan sai girman kan bala'i, haka ya koreta, tana bashi hakuri ya daka mata tsawar da ya sanyata fita da gudu tana fashewa da kuka, to tin daga wannan rana bai sake ɗaga ido ya ganta ba sai yau, tsabar iskancinsa mai lasisi ne.

"Magani ne". Ya faɗa a taƙaice.

Dik da bata da ilimi ta fannin aikin 3D, amma a nata fannin ta gano wannan ruwan ba magani bane wlh, akwai sinadarin venomous spur toxin da nematocyst stored venom a ciki, wanda kuma venomous spur toxin tasan lalata jiki yake yi, yana kone fata, shi kuma nematocyst stored venom kumburin jiki yake, ya haifar da kuraje, ko yaya za'a kwaɓa sinadarai a irin kwarewarsu ita da Maya confirm zasu iya tantance wasu irin sinadarai ne a wajen, kada ku manta dik sinadaran da ake kawo masu a SECTION C ɗinsu sai sun tacesa sun cire mai karfi daga ciki, kunga kuwa dik wanda zai san wasu sinadarai a wannan hospital ɗin to ya biyo bayansu ne!.

Bata yarda da hakan ba, jikinta na kerma, fuskarta cike da tashin hankali, dik da tsananin tsoron 3D da suke yi hakan bai hanata ce mashi. "Wannan ba magani bane,wannan ai cuta ce!". Muryanta na rawa sosai ta faɗa......... Ai a miliyan Dr Kamal ya ɗago da idanunsa yai mata kallon ƙasan ido, sai kuma ya saci kallon Dr James da ko gezau bai yi ba. A karon farko yau an samu wacce ta ce da 3D wani abu a kan aikinsu.

Kama kafan baby ya yi wajen cinya da nufin ya tsira mashi alluran. Ai sister Zinta bata san lokacin da ta damke hannun nasa dake rike da sirinjin ba, jikinta na tsananta kerma, idanunta cike tab da kwallah ta ce. "Ka duba da kyau, wannan cuta ce ba magani ba, ka bincika da.......". Bata iya karisa maganar ba ta haɗiye saura sakamakon ɗago da eyes ɗinsa slowly da ya yi a kanta, a razane ta sake mashi hannu tare da ja da baya, hawayen da take ƙoƙarin rikewa ne suka fara zubo mata, bata san meyasa take kukan ba, bata san meyasa hankalinta ya tashi a kan wannan allura ba, tana jin wannan baby tamkar jininta ne, meyasa bata damu da sauran jariran ba sai wannan kawai? And meyasa kuma su 3D basu sakawa kowani jariri ido ba sai wannan darling ɗin Maya ɗin?

Sun yi scanning na brain É—insa, bai ishesu ba, suka sake É—eban jininsa, dik bai ishesu ba, yanzu kuma sai sun sake yi mashi wannan alluran? For what reason? Meyasa dik suka rikice suka tashi hankalinsu a kan jaririn da satinsa 3 kawai a duniya? Meyasa? Wannan shi ne tambayar dake cikin kwakwalwar sister Zinta.
Ita kuwa Maya tambayar kanta take yi kan wai ina iyayen jariran nan dikka suke? 55 babys, kuma dikka babys É—in 3 weeks suke da shi a duniya! Which is mean dikka rana É—aya aka haifesu! Suna kama sosai, kenan uwa É—aya ce ta haifesu? How? Meyasa ake basu madara ba nonon uwa ba? Meyasa su da suke matsayin nurses su suke masu wanka ba iyayensu ba? Kai abin da rikitarwa! Babban damuwarta ma a nan shi ne yadda yaran suke kamanceceniya, sai kuga babys 5 kamanninsu É—aya kamar an tsaga kara, to ya haka? Wannan kamannin da suke da juna ya fi komai É—aure mata kai.

Jama'a idan baku manta ba a jikin kowacce mace suna cire eggs sama da goma ba? Kunga kuwa dole za'a samu kamanceceniya tsakanin babys ɗin, dan wasu uwarsu ɗaya ne! Sannan ita sister Maya ai ita kanta ce abin mamaki ko ya kuka ce? Bata taɓa mamakin yadda aka yi dikka nurses na hospital ɗin suke da 18 years a duniya ba, bata taɓa mamakin yadda suke kamanceceniya ba suma, bata taɓa tambayar ina iyayenta ba, dik bata yi wannan ba sai a kan babys ɗin nan saboda ita mayyan son yara ne ba!.

Suna ji suna gani Dr James ya danawa darling wannan allura a jefen cinyarsa. A ƙasa da second 3 wannan kwayar cuta ta yawace jinin jikin jaririn nan.

Lokaci guda wani irin jijjiga jaririn nan ya fara yi, gabaÉ—aya bakinsa ya gagara buÉ—uwa ya yi kuka, amma daga gefe-gefen kunnensa wasu hawaye ne masu É—umin gaske suke zuba, kafafu da hannayensa dik wani irin kerma suke yi tamkar yana jin sanyi.

Kallon Dr Mark Dr James ya yi kafin ya ce. "Dr yana aikin sosai, duba yadda jikin jaririn ya koma green sosai lokaci guda, lallai wannan abin zai yi yadda ake son ya yi wa duniya sosai, ban ƙara tabbatarwa ba sai yanzu dana ga zahiri, lallai na yabawa kaina ni da kaina!!". Ya faɗa yana mai da kallonsa a kan jaririn da gabaɗaya a yanzu jikinsa ta saki, ba kuma mutuwa ya yi ba, ya koma ne babu abin dake motsi a jikinsa face idanu, hawayen dake zuba daga idanunsa sun dakata cak alamar azaban ta ninku kan wanda yake ciki, na tabbata da yana da baki zai ce gara mashi mutuwa a kan wannan gwajin da suke yi a jikinsa.

Gyara hand gloves na hannunsa Dr James ya yi tare da kama kafan jaririn yana ganin tafin kafafunsa na yadda tsantsar jijiyoyin jininsa suka bayyana ruɗu-ruɗu saboda karɓar bakon abin da ya shigo cikin jinin da ya yi, skin ɗinsa ya koma green sosai kafin daga bisani ya fara komawa yadda yake, kana iya ganin yadda jini ke gudana a jikinsa, jijiyoyinsa suna harbawa alamar bakon abin da ya ratsa jininsa yanzu kamar ya fi karfin jinin jikin nasa.
INNALILLAHI WA INNA ILAHIR RAJIUN, KUMA WLH DA RANSA BAI MUTU BA, HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKIL! Kada ku manta fa cewa suka yi a jikin nama zasu sanya wannan cuta, wanda ya ci wannan nama zai kamu da cutar, to imagine, shi wannan jariri kai tsaye aka danƙara mashi cutar a jiki, ba a jikin wani abu ya ci ba, sinadarin zallar cutar aka zuba a jininsa, ya rab, ya rahman, ya rahim, ya malik, ya kuddus, ya salam, ya mumin, ya muaimin, ya aziz ka kawo mana ɗauki a wannan duniya da muke ciki, duniya mai cike da ruɗani da tashin hankali game da zallar rashin imani, ka rasa a ina zaka yi gwajin sai a jikin jaririn da bai ji ba bai gani ba, bai san komai ba, ya ALLAH! 3D ina zaku kai hakkin waɗan nan jariran? Dik wani jariri da kuka kyankyasa in ma kun sayar ko kun kashe ku sani hakkinsu na kanku, in kuka sayar da su aka je aka yi abin da bai dace da su ba wlh jininsu ya rataya a wuyanku ne azzaluman banza tsinannu!!!.

After kamar 5 mins da cutan ya gama yawo a cikin jinin baby sai me? Take yaron ya koma yadda yake, dama jijjigar shigar kwayar cutar jikinsa ne ta rikita shi, da ya shiga ya saje da jininsa kuma sai ya dawo daidai, cutar ta fara aiki a jininsa, sai nan da sati biyu zasu ga result, darling zai mutu ko kuwa?. Ya ALLAH.

Tin da yai mashi wannan alluran sister Zinta and sister Maya jikinsu ya hau tsuma, yana wani irin kerma, sister Maya idanu ya cika tab da kwallah, idanunta a kan yaron. Ana gama mashi alluran ta matso da sauri zata É—aukesa Dr Kamal ya rike hannunta.

Da sauri ta juyo da kallonta a kansa, tsaida video ɗin da yake ɗaukar babyn tin shigowarsu yai tare da tura wayar aljihu bayan ya yi saving. Daidai lokacin ta juyo da kallonta a kan Dr Kamal, wani irin zafafan hawaye ta ji ya fara bin ƙuncinta. Tana son zuwa ta ɗauki babyn amma ya hanata, ganin ta fashe da kuka ne yasa ya jawota jikinsa, a lokacin ta samu damar sakin wani irin marayan kukan da ba san dalili ba.

Da gudu sister Zinta ma ta yi kan baby tana son ɗaukarsa. Ajiye sirinjin hannunsa Dr James ya yi tare da cire hand gloves na hannunsa, ya miƙa hannu ya riko sister Zinta, tin da ta ga yadda babyn nan ya yi bayan an mashi wannan alluran ta kara gasgata cewa cuta aka zuba mashi. Kada ku manta dikkansu kullum suna sanye da doctors nose mask.
Chapter 138 · 0% Book details