← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 227

Sashe 44

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin ya É—an yi one side smelling ne yasa ta ji wani irin Musulmin daÉ—i, da alama kalamanta suna huda zuciyansa, yarinyar ta iya soyayya sosai. "Baka ce komai ba! Ina auntys É—ina? Ka kira mun su mu gaisa zan faÉ—a masu kaki bani damar in kula da kai kamar yadda suka ce in yi".

Kafeta da ido ya yi, yana ta faman kallon É—an bakinta, a ransa ya ce ba zaka ga baki ba sai iya magana, a fili kuma ya gagara cewa komai. Ganin yadda yake kallon É—an bakinta ne yasa ta turo shi gaba kaÉ—an kafin ta ce. "Ba zaka yi magana dani bane?"....... Still dai bai motsa ba, babu ma alamar zai yi magana. Juyawa ta yi tare da taka step biyu tana faÉ—in. "Shikenan tin da baka son yin magana dani, bari in tafi kawai".

Sai a lokacin ya ɗan yi gyaran murya tare da ɗauke kallonsa daga kanta, ya zura hannayensa cikin aljihu, da wayar tata gabaɗaya tare da taka step uku ya dawo ta gabanta, ya zamana suna fuskantar juna. Muryansa can ƙasa ya ce. "A ina kika sanni? Wacece ke? Meyasa kike ƙoƙarin shiga rayuwata?".

Wani irin faÉ—uwar gaba ta ji na ganinsa a kurkusa da ita haka, da kyar ta haÉ—iyi yawu gwad. Muryarta ne ya fara rawa wajen cewa. "Am....... In.... Nima..... A mafarkina na sanka......". Gagara cigaba da magana ta yi.
Ganin haka yasa ya ɗan yi step ɗaya baya, dan ya lura ta tsorata da ganinsa a kusa da ita haka ne. Wani irin ajiyar zuciya ta sauke ganin ya ja baya, har da ɗan dafe kirji. Intently ya ɗago da kallonsa sosai a kanta, sai haki take yi tamkar wacce ta ci gudu ya ƙoshi. Ita ma ɗago ido ta yi suka kalli juna ido cikin ido, at the same time suka ji wani irin yanayi ya ziyarci zuƙatansu.

A daidai lokacin jerin gwanon motocin BGA suka danno kai kan titin zasu wuce gida. Da sauri ta mannu da jikin bishiyar. Takawa ya yi step biyu ya tsaya dab da ita dan ya kare mata motocin kada su haska su ganta a wajen, dan in suka ganta ita za'afi hukuntawa, dik da bai san wacece ita ba, amma yasan dokar AZURE, koda bakuwa ce a nan sai an ji dalilinta na biyo wani jami'i, sai an hukuntata. Shiyasa ya tare mata.

Slowly ya dawo da kallonsa a kan face É—inta, while ita ma shi take kallo, kurawa juna idanu sosai suka yi, gagara rike kanta ta yi har sai da ta kwantar da kanta a saman massive chest É—insa, ya matsa kusa da ita ne sosai, ga kamshinsa dake ratsa hancinta, ga shi kuma abin da zuciya ta jima take begen gani ne......... ÆŠan motsa eyes É—insa ya yi ya bi gashin kanta da kallo, wani irin yanayi ya ji na jinta a jikinsa, sai ya ji kamar komai ya tsaya mashi cak. Ita kuma wani irin daÉ—in da ta ji har bata san time da ta sanya hannunta dikka biyu ta rikosa ta baya ba!.

A daidai lokacin motocin suka gama wucewa, ɗan ja da baya ya yi kamar yana tsoronta haka. Da sauri ta ɗago kai suka haɗa ido, sai ta tsinci kanta da jin kunyansa, hakan yasa ta juya da gudu ta bar wajen. Bayanta ya bi da kallo yadda yake gudu har ta kurewa ganinsa, tana sane sarai da bata karɓi wayarta ba, dan dama na ce maku tarko ta ɗana mashi da wayar, ta yi alƙawarin sai sun yi ta haɗuwa da sunan karɓar wayar nan, in sun zo rabuwa ta tafi ta bar mashi wayar, a haka har ya fara sonta.

Da yake ya zura wayar a aljihu ɗazun ne sai ya mance da ita, dan haka yana gani har ta gudu bai tina ya bata ba. Juyawa ya yi ya koma side ɗinsu. Sai da ya koma room ɗinsa, zai hau bed kenan ya ji wayar a aljihunsa, da sauri ya cirota, mamaki ne yakama shi na yadda aka yi ya shagala ya mance bai bata wayarta ba, to me ya shagalantar da shi? Ya tambayi kansa......Ni kam na amsa mashi da kyan V da iya maganarta, ga daɗin murya da shagwaɓa, shi ya mantar da kai me ka je yi wajenta!.

Kurawa wayar idanu ya yi yana ta mamaki, a daidai lokacin Leo ya shigo room ɗin bakinsa a ɗauke da sallama ƙasa-ƙasa. Ajiye wayar a gefen bed ya yi tare da kwanciya yana yi wa Leo barka da dawowa! Toilet Leo ya wuce ba tare da ya amsa shi ba!.

Ita kuwa kai tsaye gate na gidansu ta nufa. Tana zuwa ta hau knocking ba wani tsoro, dan dama fitar ce mai wahala, shiga kam tasan maganin jami'an, ita ma ai jami'a ce, dik wata makirci ta iya.

ÆŠaya daga cikin sojojin wajen ne ya buÉ—e mata gate É—in. Mamakin ganinta ne ya kamasu. ÆŠaure fuska ta yi tare da sanya kai zata wuce ciki, da sauri sojan da ya buÉ—e mata ya bata hanya ta shigo. ÆŠaya daga cikin sojojin ne ya ce. "From where at this time? Kuma a yaushe kika fita gidan nan?".

Harara ta dallah mashi kafin ta ce. "Kana da business dani ne? Dik wanda ya sake mun magana a cikinku ya yi wa kansa, dan zama zan yi a nan har daddy ya dawo yasan na fita! Kun san sauran kuma idan yasan na fita, dan baku iya aikinku ba tin da zaku bari in fita ba tare da izininsa ba, ku rai nawa ne a wajen nan da har ni zan fita baku sani ba?". A dake ta faÉ—a.

Shiru suka yi, dan kuwa ta ɗauresu da magana, sun kuwa san idan GAT yasan ta fita sun shiga uku, ace sojoji sama da goma ke gadin gidan har V ta fita babu wanda ya sani? Ai suka yi sake GAT ya ji wannan magana sun shiga tara ne ma, dan haka suna ji suna gani ta wuce cikin gida tana hararansu, babu wanda ya sake ce mata ko ƙala. Tana shiga parlo ta daka tsalle tana faɗin. "Smart girl, wai ni ko yaushe na koyi waɗan nan wayo ne ma?".

Tana cikin surutan nata ne ta É—ago kai sai a kan su Aunty Lisa dake zaune a dining room suna dinner, da yake glass wall ne wajen dining room É—in sai suna iya ganinta. Da gudu Angelina ta taso ta nufota, muryarta har yana rawa wajen tambayarta ya aka yi? Ta samu ganin Noor?. Bata fuskanci wata matsala ba ko?.

Zazzare idanunta a kan su Aunty Lisa ta yi, cike da mamaki ta ce. "Aunty". Suma sai kallonta suke yi, sai a yanzu suka gane gaskiya Angelina take faÉ—a masu na cewa ba ita ce suka haÉ—u da ita É—azun ba. Kun san me yafaru ne? A lokacin da suka shigo gidan Angelina kawai suka samu a parlo, su Arya sun yi sama. Nan fa suka fara rungumar Angelie suna tambayarta dama nan ne gidansu? Ita kuma bata ganesu ba sai ta fara tambayar su waye su, nan suka zayyane mata komai, ta ce ba ita bace sai dai ko in sister É—inta V, kuma bata nan sai ta dawo, suka kafe lallai ita ce, Aunty Lisa har da cewa ga ash hair É—in nan nata, komai sak na wacce suka haÉ—u, su basu yarda ba, lallai ita ce. Ita kuwa ta kafe ba ita bace, ta ce sai dai su jira V ta dawo dan su tabbatar.

Shi ne fa suka yi shiru suna ta mamaki, masu aiki suka yi masu iso kamar yadda GAT ya basu umarni, sannan suka kaisu ɗakunan da ya ce su kaisu, wanka suka yi suka shirya, sannan suka sauƙo dan yin dinner, har yansu basu ga su Arya ba, dan kun san Arya ta tsani shiga cikin mutane, bata son hayaniya, kuma idan ba dole ba bata sauƙowa ƙasa sai in daddynta ya dawo ta zo ta yi mashi oyoyo. Angelie ita ta zauna da su Lisa har yanzu da V ta dawo, Daddyn Noor kuwa yana room da aka bashi, yana jiran GAT ya dawo su ci abinci a tare.

A natse V ta kariso wajensu, cikin girmamawa ta gaisa da su kafin ta zauna a kusa da aunty Lisa, nan fa suka fara nuna mata kauna tare da tambayar dama su identical twins ne bata faɗa masu ba tasa sun ruɗe! Tana murmushi ta ce a'a su identical quadruple ne ma ba twins ba! Mamaki yasa su Aunty Lisa rikicewa, suka fara lallai a nuna masu sauran, V ta ce su gama dinner zata kaisu wajensu Arya, dan tasan wlh Arya ba zata sauƙo ƙasa dan su gaisa ba, sai dai ita aje a sameta. Shiru room ɗin ya yi suka cigaba da cin abincinsu a natse, V tamkar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha saboda tsananin daɗi, yau ta kwanta a kirjin love ɗinta!.

----------------------------🔥

CRYSTAL PALACE.

Mu koma baya mu gani. Tin tana kuka kaɗan-kaɗan har sautinta ya daina fita, take ta ji nunfashinta ya fara sama-sama yana ƙoƙarin ɗaukewa, a zabure ta miƙe tsaye tana ta ƙoƙarin jawo numfashin, amma ina, babu iskan da zata iya ja ta shaƙa. Laluɓe ta fara yi tana ƙoƙarin kama bango ta jingina, amma ta gagara, tangaɗi ta fara yi tana kai hannu ta rike wuyanta ta fara ɓarin abubuwa, dan ji take yi tamkar an shaƙeta ne, take ta fara tari tana zazzaro idanu waje.

Kafin wani ɗan lokaci ta sulale ƙasa babu numfashi a jikinta!........ A can cikin gida kuwa, bayan sun kulle ɗakin kai tsaye suka sauƙo ƙasa, wanka Champion ya shiga room ɗinsa ya yi, ya shirya cikin tail coat mai bala'in kyau launin ash color, still dai fuskan sanye da nose mask, ya fito ya isko scorpion a parlo. Miƙewa ya yi suka nufi hanyar fita, da alama barin gidan za su yi.
Chapter 44 · 0% Book details