← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 198 OF 227

Sashe 198

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai ya ɗan jinjina alamar haka ne, shiru ya biyo baya for like 2 mins, Aryan ne ya katse masu shirun da cewa. "Our Lion ina neman wata alfamar"....... Zazzaro jade eyes ɗinsa Lion ya yi, bai taɓa jin Aryan ya nemi alfarma a wajensa ba, abin da yasani shi dai komai nasu na juna ne, komai nasu ɗaya ne, amma yau Aryan yake batun alfarma? Menene wannan da girma haka?.

Shiru Lion bai tankar mashi ba, da yake suna fahimtar shirunsa sai Aryan ya gane yana saurarensa kenan, wlh shi kansa Aryan É—in zuciyansa a razane yake da kalaman dake shirin fitowa daga bakinsa, amma bashi da wata mafita ne, sai ya daure da cewa. "Alfarmar da nike nema shi ne ina son É—auko sister É—inta in kawota nan ta É—an zauna for some days".

Tamkar fuska tamau Lion ya yi har sai da Aryan ya ji kishi ta kama shi..... "Reason?". Lion ya faɗa a dake..... "Kada ka tambayi reason please, zan faɗa maka gaba, yanzu dai please bro, ba zata jima sosai ba"...... Shiru Lion bai sake yin magana ba, sai ma miƙewa da ya yi zai bar wajen, saboda baya son abin da zai ɓatawa Aryan rai, kuma shima baya son ransa ta ɓaci a wannan lokaci.

Binsa da kallo Aryan ya yi yana tinanin yadda zai ɗauko Rimsha, har Lion zai fita Aryan ya ce. "Our Lion yarinya ce ƙarama, zata........". Maganar tasa ta dakata ne sakamakon juyowa cikin zafa da Lion ya yi, wani irin kallo ya wurga mashi kafin ya ce. "Mace ko jaririya ce zafin cizonta ya fi dafin kunama! Ko yau aka haifeta kada ka kuskura ka jawota cikin rayuwarka!!". Ai Lion an shaka ka warke, kome zaka ce mu mata ba zamu ga laifinka ba, sister Lazy ai sai shiru.

Maganar da ya yi ne yasa su Vir shigowa cikin room ɗin da saurin dan ganin menene yake faruwa, a fusace Lion ya juya ya fice da sauri. Miƙewa Aryan ya yi, ya kwanta a gado cike da tinanin yadda zai yi ya dawo da Rimsha gidan, ya yi rantsuwa da ALLAH sai ya dawo da ita.

Saman bed É—in su Vir suka hau suna tambayansa menene yakefaruwa tsakaninsa da Lion? Banza da su ya yi, suka tambaya har suka gaji bai yi magana ba, daga karshe ma rufe idanunsa ya yi tamkar mai barci. Dole suka kyalesa suma.

------------------------🔥

KHAIZA'AN'S HOUSE.

Su Abba sun ɗauko Aunty Luna lafiya sun dawo da ita gidan, a lokacin da Rimsha ta dawo daga school sai ya isko Aunty Luna a gidan, ɗan baya-baya da ita ta fara yi tana rakuɓewa.

Aunty Luna watayyar mace, kuma da kallo É—aya ta ji Rimsha ta shiga ranta, sai ta jata a jikinta, tin bata cire uniform ba ta rikota game da cewa su je ta cire mata uniform ta yi wanka. A lokacin su Abba dik basa nan, ya ce Harleen ya kashi shopping dake saman nan da kansa ya sayawa surukarsa kyauta ta ban girma na maraba da shigowa Khaiza'ans family.

To shi ne suka tafi, Ammie na É—akinta, Faryan yana shigo da Rimsha suka gaisa da Aunty Luna ya wuce room É—insu. Kama hannun Rimsha Aunty Luna ta yi suka nufi É—akin Rimshar tana tambayarta meyafaru idanunta suka kumbura sosai har haka.

Ai tamkar Rimsha jira take a tambayeta, fashewa da kuka mai tsuma zuciya ta yi, sai kawai ta juya ta rungumi Aunty Luna tana cigaba da kuka, anki a fahimta, anki a gane damuwarta, kowa yana ganin kamar zasu yi zaman lafiya da Aryan, ina zaman lafiya tsakanin wuta da audiga fisabillillahi?.

Rungumeta Aunty Luna ta yi suka karisa cikin ɗakinta, a gefen gado ya zaunar da ita game da ɗago haɓarta tana goge mata hawaye tana faɗin. "Sorry my sister, yo shiru ki faɗa mun menene yake damunki? Waye ya taɓaki?".

Ai gagara yin shiru Rimsha ta yi, tana wani irin shessheƙa tamkar zata shiɗe, gwanin ban tausayi.

*Jama'ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faÉ—akarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaÉ—antarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba'ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account É—ina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581. Mutanen Niger ku mun magana ta numberta sai in baku Nita É—in da zaku yi payment É—inku a ciki, idan kuma kati ce ku mun magana dai zan faÉ—a maku komai.*

Likes comments and share fisabilillah.

QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥

🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

For more information 08161390581 Whatsapp me only.

STEP 1🔥

2025-12-26.🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E_____________ 67 & 68

CRYSTAL PALACE.

Ai gagara yin shiru Rimsha ta yi, tana wani irin shessheƙa tamkar zata shiɗe, gwanin ban tausayi. Jawota jikinta Aunty Luna ta yi, ta hau rarrashinta.

Baki É—auke da sallama Ammie ta shigo ta samesu, dama a jikinta ta ji Rimsha na kuka shiyasa ta zo rarrashinta. Karisowa ciki ta yi, suka haÉ—u da Aunty Luna suka rarasheta sosai, sai da ta yi shiru, sannan Aunty Luna ta ce Ammie su je waje su yi magana.

Kwance suka baro Rimsha suka fito, a parlo suka zauna Aunty Luna ta tambayi Ammie me ya sa Rimsha take kuka haka? Dan ita wlh Rimsha ta kwanta mata a rai matuƙa, tana jinta tamkar sister ɗinta na jini watau sister Lisa.

Ba ɓoye-ɓoye Ammie ta sanar da Aunty Luna gaskiyar abin dake faruwa. Cike da mamaki Aunty ta ce. "Kan wannan abin ne take irin wannan kuka? Waye shi Aryan ɗin? Ba namiji bane?".

Ammie da tasan waye Aryan ne ta amsa da. "Yayan Harleen ne wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya"...... Shiru Aunty Luna ta ɗan yi, sai kuma ta ce. "Shikenan ina zuwa". Ta miƙe ta fita, ɗakin Rimsha ta koma, nan ta iskota tana waya da Seraphina, ta ce dan ALLAH Seraphina ta zo gidansu yanzu tana son ganinta.

Aikuwa Seraphina kafa sarkin son yawo, sai cewa ta yi gata nan zuwa, amma bata san gidan nasu ba ai. Rimsha ta ce. "Benen dake É—auke da number 2 shi ne benenmu"....... A lokacin Aryan ya fita, Seraphina É—in ta yi wanka tana shafa mai.

Aikuwa kafa sarkin yawo, a gurguje ta karisa shirinta ta fito, ta danya wani crazy jeans fari tas, daga sama top baki, sai ta É—aura winter jacket a saman kayan wanda ya zo mata har gwiwa saboda sanyin da ake zubabawa, kafafunta sanye cikin socks, ta sanya ankel boot a kafafunta.

Kai ba É—ankwali, ta nufi wajen Madam tana faÉ—in. "Mom É—aure mun gashina zan je gidansu Rimsha". Cike da mamaki Madam ta ce. "Kin faÉ—awa daddy ne?". ÆŠan zazzare violet eyes É—inta ta yi, sai kuma ta ce. "Zan kirasa a wata mom, yanzu dai É—aure mun".

Ba musu Madam ta gyara mata gashin, ta cufke mata a tsakiya game da sake jilar a baya, waɗan nan guntaye na gaban goshin kuma ta ƙara gyara mata su, ta kwantar mata da su da kyau kafin ta feshe gashin da turarukan gashinta.

Tana murmushi ta amsa da ta gode, fitowa ta yi ta kira number Aryan, a lokacin ya gama wannan rikici da Lion kan dawo da Rimsha gidan, yana kwance saman sofa, ya tada kai da cinyar guru suna ta yi mashi magana ya yi banza da su.

Kiran na shigowa ya ciro wayar, ganin my Cherry yasa ya katse kiran ya kirata. Bugu ɗaya ta ɗauka, cike da zumuɗi ta ce. "Daddy zan je gidansu Rimsha tana kirana". ....... Ai sai da ya ji wani irin rass, da sauri ya miƙe zaune. Sai kuma ya ɗan nisa tare da cewa. "To ki je, amma kada ki jima". Ya faɗa mata hakan ne kawai dan kada ta sake zargan wani abu, yanzu idan ya hanata tana iya cewa sai ya bata dalili, dama ga shi ta ce taga yana kama da Faryan, kunga kuwa tsab zata gasgata zarginta.

"Love you daddy, shiyasa nike sonka sosai"........ Ƙasa ya yi da murya sosai, tamkar mai raɗa yana satar kallon Vir da ya tsare shi da ido kafin ya ce. "Love you more Cherry"...... Dik abin da ya faɗa guru na jinsa, amma kamar bai ji ba, shi kuwa Vir baya jinsa amma ya karanci bakinsa tsab, ya gano me ya ce.

Dan haka yana katse kiran sai ya ce. "You love who?"...... Hararansa Aryan ya yi game da miƙewa zai bar wajen ba tare da ya yi magana ba. Damko hannunsa Vir ya yi, ya jawosa da karfi har sai da ya faɗo jikinsa, ya damki arabs hair ɗinsa da karfi kafin ya ce. "Kaima sarautar zaka gwada mana ne?".

Ai cikin zafa Aryan ya miƙe ya damko korean hair ɗin Vir, da karfi ya ja yana faɗin. "Dama kwana biyu da ka tafi na huta da sa ido, ka dawo kenan yanzu, zamu fara raba hali"..... Dik cikinsu ba wanda ya kai Vir sa ido kam, ko baya jin me ka faɗa in dai yana ganin bakinsa sai ya san me kace.

Kafa É—aya kan É—aya guru ya É—aura yana ganinsu, dan in da sabo sun saba wannan faÉ—a...... Damke gashin Aryan É—in shi ma Vir ya sake yi yana faÉ—in. "Sai ka faÉ—a mun waye kake cewa I love you, na dai san ba Abba bane, kuma ba su Faryan bane".

Kwace kansa Aryan ya yi yana faɗin. "Ba zan faɗa ba". Ya wuce ya nufi cikin ɗaki. Miƙewa suka yi a tare suka rufa mashi baya guru ka zolayarsu.
Chapter 198 · 0% Book details