← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 227

Sashe 42

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dafe kirji V ta yi, ganin ya tare yasa ta sauke ajiyar zuciya. Tamkar ball haka ya yi jifa sama da wayar sai ya capke da hannunsa, akwaisu da saiti ne sosai. Dawo da kallonsa a kanta ya yi, a dake ya ce. "Answer me, a yaushe na sanki? Meyasa zaki yi wa Auntys ɗina karya har kina ƙoƙarin sanyasu ɓata rai dan na ce ban sanki ba? Wacece ke? A ina kika sanni?".

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

https://www.facebook.com/share/g/1EUXbqsDjP

STEP 1________🔥

11-11-2025.🔥

FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥

E_____________10

Bamar zata yi kuka ta amsa da. "To ai ni na sanka in kai baka sanni ba, kuma dama kai na zo gani"....... Ɗan waro eyes ɗinsa kaɗan ya yi, sai kuma ya yi saurin ɗauke kallonsa daga kanta. Ita kuma kara ja da baya ta yi tana turo baki............. "Your lion voice is so sweet that touch and melting my heart!". Ta faɗa cikin sigar tsantsar so! Tana magana kuma tana kara ja da baya wai dan ma kada ta ɓata mashi rai ya damketa.

Shiru bai yi magana ba, yana dai satar kallonta ta ƙasan ido........ "Baka son ka yi magana dani ne? Aunty ta ce in kula da kai fa"....... Still dai bai yi magana ba kuma bai ɗago ya sake kallonta ba. A daidai lokacin Angelina ta iso wajen tana faɗin. "V ki yi sauri, daddy yana jiranmu a motar zai mayar damu gida". A ruɗe take maganar, dan idan GAT ya gane V bata wajen sun shiga uku, kun san kuma doka ce ya kafa masu cewa babu ruwansu da sojojin barrack ɗinnan, and bugu da kari manyan sojoji basa aurar da ƴaƴansu ga sojiji ƴan uwansu sai in ALLAH ya tsaga da rabo, amma basa taɓa yarda, shiyasa zakuga ga mata kyawawa a cikin barrack amma sojiji zasu fita waje neman aure, kowa baya son ƴarsa ta yi takaba, sojoji a kowani lokaci suna iya rasa ransu ko da sabbin aure ne!

Angelina na zuwa ta ja hannunta, da sauri suka wuce tana waigosa hankalinsu a tashe. Da sauri Noor ya É—ago yana kallonsu, ya yi mamakin ganin tsananin kamannin dake tsakanin yaran, zuba masu idanu ya yi har suka kurewa ganinsa. Ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa zai bar wajen, a nan ya lura da wayarta dake hannunsa.

Da sauri ya bi bayansu, sai dai ko da ya je bai gansu ba, daddynsu ya É—aukesu. Zubawa wayar ido na É—an lokaci ya yi kafin ya kunna light É—in screen, hotonta ne a gaban screen É—in, ga wayar babu password, dan haka sai ya É—an shiga cikinta. Videos na soyayya kawai ya fara cin karo da shi, fita ya yi ya kashe wutar screen É—in, cike da tinanin ina zai sake ganinta ya bata wayarta ya nufi wajensu Leo.

A É—ayan side na hall É—in ya isko Leo tsaye da Big Bro É—insa suna magana, Leo ya ce yayan nasa ya bari sai gobe su wuce Us, shi kuma yayan nasa ya so su wuce yau ne, amma Leo yaki fir, wai akwai aikin da bai kammala ba, akwai sauran shirye-shirye da yake yi.

Baki a ɗauke da excuse Noor ya iso wajen. Zayra'an yana tsaye tsayuwar jarumai Noor ya ɗaga mashi gaisuwa cikin girmamawa. Shiru tamkar ba zai amsa ba, sai kuma can har sun fidda rana zai yi magana ya amsa a kalma ɗaya watau lafiya. Daga haka ya wuce ya nufi gidan da ya kasance yanzu mallakin su Leo. Bayan passing out ɗinsu sun baro yankin barrack kai tsaye, an basu gida cikin layin gidajen senior staff, gida mai shegen kyau, bene ne, mai ɗauke da ɗakuna 6, uku a ƙasa da parlo sai uku a sama shi ma da parlo, kitchen ɗaya da harabar gida, toilet a kowani room, tsarin ginin ya yi kyau matuƙa, dikka jami'ai 12 da zasu tafi mission ɗin nan a wannan gida zasu zauna kafin tafiyar tasu! Su 12 ɗakuna 6, kowani ɗaki mutane biyu kenan, saɓanin mutane 4 a lokacin da suke horo bar one!.

Kallon tsab Leo ya yi wa Noor kafin in a cool way ya ce. "Wannan wayar fa?". Kallon wayar Noor ya yi kan ya amsa da. "Na wata ce da ban santa ba, yanzu ma nemanta nike yi in bata"........ Wani irin kallon tuhuma Leo ya jefa mashi wanda bai san lokacin da ya ce. "Bro da gaske ban santa ba, kawai ina tsaye ta zo ta sameni, ka yarda dani".

Zura hannayensa a cikin aljuhu Leo ya yi, ya É—an taka baya step biyu gaba kafin ya ce. "Ya da saurin tsarguwa boy? Ko ka ji na ce wani abin ne?"....... "Naga kana bina da kallon tuhuma ne". Ya faÉ—a yana tura wayar a aljihunsa!. "Uhm". Leo ya faÉ—a tare da juyawa zai bar wajen.

Da sauri Noor ya bisa yana faɗin. "Bro, believe me, I don't know this girl shaaa". Cigaba da tafiya Leo ya yi, har suka kusa shiga cikin gidan nasu kafin can ƙasa a natse ya ce. "Ita ce ta mafarkin da aka damemu da yinsa tsawon shekaru biyu kenan ko?"........ Da sauri ya girgiza kai tare da tare gaban Leo, yana ɗan shagwaɓe fuska ya amsa da. "Bro, ka bari mana, ni fa na faɗa maka wacce nake mafarki ban taɓa ganin face ɗinta ba, sai dai kyakkyawan surar jikinta".

"Uhm". Leo ya sake faɗa tare da sa kai zai raɓa gefensa. Sake tare gabansa Noor ya yi. "Baka yarda dani bane bro?"...... Tsayawa ya yi, suka kalli juna ido cikin ido kafin ya amsa da. "Asalin yarda kuwa, sai dai ina mamaki ne, anyway ka dai mai hankalinka a kan aiki, idan ka ce zaka biyewa mace zata shashantar da kai ne, ba zaka cinwa abin da kake so ba!". A dake da iya gaskiyansa ya faɗa, dan shi yana ganin in dai ka haɗa hanya da mace to zaka zama ragon namiji ne, wai ba zata barka ka yi abin da yakamata ba, sai ta sa ka zama mai rauni.

"For sure bro, zan yi ƙoƙarin ganin ban kauce hanya ba, kuma zan yi ƙoƙarin ganin na jajirce. But bro she's so cutie, pretty and.......". Sai kuma ya yi shiru.......... "Ta mafarkin ko ta zahirin?". Leo ya faɗa a taƙaice. Shiru ya ɗan yi kafin ya amsa da. "Both, amma ta zahirin karshe ce"......... "Uhm". Leo ya sake faɗe tare da sa kai ya wuce, ya shige cikin gida, da sauri Noor ya bi bayansa, sun zo daidai tsakiyar gidan Leo ya ce. "Ba zan hanaka kula mata ba, saboda ni da kai akwai banbanci, but in ka bari ta fara ɗauke maka hankali fiye da tinani zan katse dik wata alaƙarku ne".

A ɗan shagwaɓe ya ce. "Ba za ayi haka bama, aiki shi ne gaba da komai, ba zan bari ta shafi aikina ba"...... Jinjina kai Leo ya yi, a daidai lokacin suka fara tattaka staircase zasu haura sama izuwa room ɗinsu........ "Wacece ita kuma ƴar waye?". Leo ya faɗa can ƙasa, tamkar mai raɗa dan yana gudun yayansa ya ji suna maganar mata ya ce dama ba aiki ne a gabansu ba, yasan yayan nasa na gidan tin da ya ce bari ya zo nan ya ɗauki wayansa da agogonsa ya koma hotel da ya dauƙa.

"Dik ban san waɗan nan amsoshi ba, yau na fara ganinta, amma ka bani two days zan samo maka dikkan amshoshin da kake son ji". Cikin ɗan shagwaɓa ya faɗa.......... "Hallau dai shagwaɓar". Leo ya faɗa a lokacin da yake tura door na room ɗinsu.

"Naka ne kai kaɗai ai, wa kai kawai nike yi wa, ko daddy banai wa shagwaɓa yanzu". Ya faɗa yana nufar wajen bed. Leo kuma juyawa ya yi ya fita ganin yayansa baya ɗakin, kenan sun barosa a waje, yana son su yi sallama kafin ya tafi hotel da ya sauƙa. Shi kuwa Noor kwanciya a saman bed ya yi tare da ciro wayar V ya ajiye a gefe, sannan ya ciro tasa wayar. Lokaci guda tinaninta ya faɗo mashi a rai, yadda ta ce. "Your Lion voice is so sweet that touch and melting my heart". Yadda ta yi maganar a shagwaɓe hakika ta taɓa zuciyansa, sai ya ji tamkar ta cigaba da yi kada ta dakata.

Kawar da tinanin ya yi tare da jawo wayarta dan ya ga ko akwai wata hanya da zai bi wajen samun damar mayar mata da wayar. (Anya Noor ba neman damar sake ganinta kake yi ba kuwa? In ba haka ba me na wani damuwa da son a mayar da wayar? Naga ai zata fika buƙata, sai ta nemo kayanta!.)

Yana kunna light na screen ɗinta sai ga kira ya shigo. "My life partner". Shi ne sunan dake yawo a kan screen ɗin nata. Wani irin amsawa ya ji kirjinsa ta yi, sai ya fara tinanin kamar ya ɗauka kamar kuma ya bari. Can kuma ya tina ai gara ya ɗauka ya sanar masu ta bar wayar a wajensa su zo su karɓa mata. Da wannan tinani yasa wayar na gab da katsewa ya ɗaga tare da sanyata a H-free.

Daga ɗayar ɓangaren aka ce. "Hello". Ko ba'a faɗa mashi ba yasan ita ce, saboda kwarewarsu a aiki sau ɗaya suke jin sautin abu su haddace, tabbas wannan muryanta ne, kuma hakance, ita ce ta kira number tata da wayar Angelina.

Dama da gangan ta bar wayar a hannunsa, dik tarko ta ɗana mashi na yadda zata samu damar yin magana da shi kenan, kunga idan wayanta na hannunsa zasu sake haɗuwa, kuma zata samu damar sake yin magana da shi, har da cewa sai bayan sati zata yarda ta karɓi wayan, wai kullum zata dinga kiran number da layin Angelina tana gaisawa da shi, sai ta ce mashi bata gari, sai sun saba ta waya sannan ta karɓo wayar, a cewarta in suka saba da kansa zai ɗauki numberta. Kai kun ji yarinya mai wayau ta kafawa Noor ɗinmu tarko! Kai yaran GAT they're very Smart wlh.
Chapter 42 · 0% Book details