← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 227

Sashe 159

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wannan karon a hankali sosai ya fara zura karfen, dan in ya yi garaje yana iya huda cikin jikinta ya shiga wani waje tin da ba ruwan dake taimaka masu karfen ta wuce salun alum. Ya É—an yi tafiya kaÉ—an sai kuma ya sake zaro karfen da sauri saboda haÉ—ewar da jikinta ya fara yi, hanyar dake can ciki ya matse, kun san in mutum ya mutu haka jikinsa a hankali zai fara haÉ—ewa har ka takure waje guda, so a wannan lokaci babu wani abin da zai iya shiga jikin mutun ta private part É—insa, to gawa idan ta yi minti talatin zuwa awa É—aya ma babu abin da zai sake amfani a jininsa, in macece gabanta ba zai sake buÉ—ewa ba bare baya, kamar yadda zaku ga hakwaranta ke datsewa ba zasu buÉ—u ba haka ne, shiyasa dole ya saka mai dan taimaka mashi.

Oil ɗin ya ɗauko, ya shafe karfen da shi, ba zai dai hakura ba, a haka ya sake tura karfen a gabanta. Kai tsaye cikin cikin yarinyar ya nufa. Ya fara tafiya ya sake tsayawa yana kallon wajen mararta a cikin computer dake jinin gadon. Sai da ya ɗauki 3 mins yana kallon yanayin marar tata yana ɗan junjuya naurar dake kan cikin nata yana duba lungu da saƙo wajen kafin nan ya saki na'urar kan cikin nata, ya sa hannu ya ƙara gyara kafafunta, ya buɗesu sosai dan ya buɗe jikin nata da kyau, da alama dik da mai da ya zuba ɗin da wahalar wucewa, kuma yarinyar bata fi 15 mins da mutuwa ba, da ta kai 30 mins ma dik bala'insa bai isa ya shigeta ba, sai dai ya hakura.

Cigaba da zura karfen a hankali ya yi idanunsa a kan computer dake gabansa, yana kallon hanyar da yake bi sosai ne, da kyar ya samu ya isa kofar ovaries nata, komai na ta ƙara tsukewa.

Kofar follicle É—inta ya buÉ—e tare da zura needle suction tube É—in ciki, tsotse ruwan dake cikin follicle É—in nata ya fara yi dik da yaga ba yawa sosai. Da kyar ya samu damar tsotse ruwan, sai da ya kwashe tas, sannan ya fara zaro bututun, da kyar yake jansa, saboda jikinta nata faman kama bututun, haka ya zaro shi ba imani ba tausayi.

A cikin wani karamin kwalba ya zuba kwayayyen haihuwar da ruwan tata tare da sanya hannu ya ɗauko audiga bayan ya rufe kwalbar, a gaban nata ya cusa audigar can ciki, ya bar mata shi a ciki. Sai dai abin da ya yi mugun bashi madarar mamaki shi ne ganin alamar eggs sama da 50 a cikin wannan ruwa da ya yi, ya ga alamarsu sosai, bayan yasan dik alluran da suke masu basu taɓa samun mace mai eggs sama da 15 ba, to how comes yau sama da 50?.

Ni kam na ce hmmm, ruwa rabin cokali ya ishi mai hankali wanka, amma kai ba zaka gane cewa wata aya bace hakan, kila zaka É—auka nasara ce da samun cigaba, ai UBANGIJI ya iya yi wa kafurai irinku É—aurin talala!

Daga haka ya ɗan haɗe mata kafafunta waje guda kafin ya matsa zuwa gado na gaba cike da al'ajabin wannan eggs guda 50 ɗin. Haka suka bi yaran gabaɗaya suka kwashi eggs ɗinsu, a cikinsu sun samu yara biyar sun mutu, yara biyar ɗin nan kuma dikkansu sun samu eggs sama da 50 a jikinsu saɓanin a baya da suke samun 10.

Sun yi matuƙar murnar ganin sun samu eggs guda 50-50 a jikin matattun yaran nan, kunga a take sun samun 250 eggs kenan, haba sai farinciki suke yi, suka sanya aka kwashi yaran aka mayar da su in da suke killacesu, aka ɗauki gawarwakin waɗan da suka mutun kuma, haka suka haƙa rami suka binnesu kamar yadda ake binne kare.

Suka tattari eggs ɗin suka kaisu cikin wannan freezers room ɗin nasu, sun yi matuƙar farinciki yau, sun samu eggs almost 400 a jikin yaran, sun fara jin cewa burins na kyankyasan 2000 babys a wannan shekara zai cika, saura kaɗan.

Bayan sun kammala suka fito suka nufi SECTION E. Suna kan tafiya ne Dr Kamal ya ce. "Jammy ina ganin mu bar yaran nan su huta na watanni 3 ko huɗu kafin su cigaba da karɓar alluran nan, naga gabaɗaya jikinsu ya canza, alamar alluran ya fi karfin garkuwar jikinsu, ya yi masu yawa, kaga har mutane biyar sun mutu, alluran yai masu overdose, kuma dikkanmu mun san cewa yaran nan tin shekarunsu bai kai karɓar wannan alluran ba muke danƙara masu shi, tin suna 13 years, jikinsu bai yi wani kwari ba, a wata allurai kala uku masu karfi muke yi masu, wanda haka kuskure ne a fannin lafiya, ka sani na sani!".

A taƙaice Dr James ya ce. "Ko mu dakatar ko bamu dakatar ba dikkansu mutuwa zasu yi, already alluran ya kashe garkuwar jikinsu, dan haka ba zamu dakatar ba, gara kawai a cigaba har zuwa lokacin da zasu mutu, kuma ai idan suka zo mutuwa sun fi bada eggs dayawa, baka ga 50 eggs kowacce daga cikin matattun suka bayar ba?".

Dr Mark ya ce. "Yanzu ma ai sun fara mutuwa, one by one haka dikka zasu ƙare, yau biyar, wani watan ma biyar ko sama da haka zasu mutu, a haka zasu ƙare, dan haka ba wani zancen mu dakatar da yi masu allura, already su tasu ta ƙare". ........ Ya rabb, ku ji yadda suke magana tamkar ba ran ɗan adam bane suke mutuwa.

Shiru Dr Kamal ya ɗan yi, dik da cewa yana son aikin nan nasu, suna samun maƙudan kuɗaɗe, amma a yau yaran nan sun ɗan bashi tausayi, dan ya ga jikinsu ya fara lalacewa sosai da sosai, alluran ya gama kashe.

A haka suka shiga SECTION E. Sai suka shiga cikin wani ɗaki mai tarin glasai dayawa. Wajen tamkar lap ne haka, ga wasu halittu na ban mamaki dayawa a cikin glasses dake ɗakin, an yi glasses ɗin dogaye tamkar show glass haka, to a ciki ne waɗan nan halittu suke, tamkar suka ƙoƙarin yin wasu halittun ne.

Tin daga kan yanayin matakan tsaron da suka zubawa wannan ɗaki zaku san ba waje ne na wasa ba, zaku san wane ne mai bala'in haɗari. Gaban wani tangamemen glass mai girman gaske suka tsaya. Wani irin jibgegen halitta ne a ciki mai kama da dabba mai kuma kama da mutum, yana da wasu irin ƙulu manya-manya a tamolon kansa, idanunsa tamkar ball saboda girma, gwanin tsoro.

Wannan halitta ba komai bane face ɗaya daga cikin fitintinun da suke kirkirowa duniya, Dr James ya ja ragamar wannan project ɗin, shi ya harhaɗi kwayoyin halitta, su DNA ɗin nau'ikan dabbobi da mutane daban-daban, suka tacesu a lap, sannan ya fara kyankyasan wannan halitta, tin shekaru 8 baya yake yin wannan project ɗin, halittace mai matuƙar haɗari, yana daga cikin plan na WS dan hana duniya zaman lafiya, a wannan asibitin ba jarirai kawai ake kyankyasa ba, ba kuma magani kawai ake haɗawa ba, kazalika ba iya cututtuka kawai suke kyankyashewa ba, suna kyankyasar hadda dabobi, kai dik yadda kuke zaton asibitin nan ya zarce tinaninku, ku dai sai mun natsa cikin labarin.

Yanzu ba zaku gane me zasu yi wa duniya da wannan halitta ba, amma gaba zaku gane, yanzu haka renon halitta suke yi yana ƙara girma, a wannan ɗakin akwai nau'ikan halittu daban-daban, kowanne kuma da amfaninsa da dalilin yinsa.

Bayan sun duba halittar yana nan lafiya yana barci, sai suka ƙara gaba zuwa wajen wasu glasses ɗin, nan kuma wasu irin ƙananun halittu ne masu kamar ƙudaje a cike a cikin glasses ɗin, a gaban wajen suka tsaye, Dr James ya ce. "Waɗan nan halittu sun kusa barin wannan waje, a cikin week ɗin nan WS zasu karɓesu".

A tinaninku me za'ayi da su kuma?.

Jinjina kai Dr Kamal suka yi, suna ƙara yabawa kansu a wannan project ɗin, dan sun sha baƙar wahala. Sun yi yawo a cikin wannan ɗaki sosai, sun duba halittu daban-daban dayawa kafin su fito su nufi office ɗinsu. A office ba Dr James suka zauna, a tare suka yi breakfast around 11 na safe, sannan suka ɗan taɓa aiki zuwa 1 kafin Dr James ya ce bari ya duba Zinta a gida.

Fitowa ya yi ya bar su Dr Kamal a office ɗin, ya nufi gida. Tin da ya sako kafafunsa a cikin parlon nan wani irin musulmin kamshi ta bugi hancinsa, shaƙa ya yi ya lumshe idanu tare da ƙarisawa ciki. A cikin ransa yake cewa a ina suka samu wannan kamshi mai daɗin haka? Ko'ina tsab-tsab, watau batu na gaskiya 3D akwai mugun tsabta sosai, basa shiri da ƙazanta ko datti waje, komai nasu tsab da yake likitoci ne.

Shi da kansa a yau ya shaida lallai yau mata na cikin wannan gida nasu, sama ya haye yana ta baza hanci yana shaƙar kamshi. A parlon sama ya isko Maya zaune tana karata wani littafi na lafiya da ta ɗauko daga room na Dr Kamal.

Tana ganinsa ta zube ƙasa tana ɗaga mashi gaisuwa. A dake ya amsa tare da cewa. "Ina madan ɗin take?"..... Tana ɗan sunkuyar da kai ta amsa da. "Tana cikin room"........ "Kun yi breakfast ne?".

Kai sister Maya ta gyaɗa mashi. "Mun sha tea"....... "Iya shi kawai?". Kai ta sake gyaɗawa. Ciki ya wuce yana tinanin ɗure zai yi wa Zinta yanzu, ga komai suna da shi, kitchen ɗinsu shaƙe da kayan abinci fa, ace tea kawai zasu sha, bai yarda ba.

Kofar room ɗinsa ya tura, wani kamshin na daban ne ta kai mashi karo a hanci, shaƙa ya yi tare da ɗan lumshe idanunsa kafin ya shigo, sister Maya ce fa ta zaɓo turarukan gida daga cikin turarukan dake ɗakin Dr Kamal, ta gansu kala-kala kwali-kwali, dan 3D akwai son kamshi da tsabta na faɗa maku, to wasu turarukan ma basu taɓa amfani dasu ba, basu san ya yake ba, ita kuwa tana zuwa ta dinga bincikawa tana taɓawa sai da ta ji wanda kamshin yai mata, sannan ne ta fito da shi, ta bi lungu da saƙo na gidan ta fesa, sannan ta ɗako wani daban ta fesa a ɗakuna.
Chapter 159 · 0% Book details