← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 227

Sashe 165

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Macen da ya so fiye da kansa, macen da ya sanar sirrinsa fiye da ɗan uwansa Hoosain, macen da in ta ɓata rai sai US ta tsaya na ɗan lokaci saboda fushinsa, idan ka taɓata to jini ne zai zuba, da dik wanda ya taɓata baya yafe mashi koma wanene, harta mahaifinta ya taɓa marinta a gabansa kafin su yi aure, kafin mahaifinta ya sauke hannu ya rama mata ɗaya tamkar dubu, daga mari ɗaya sai suma, kai tarihin daddyn Lion abu ne mai tarin darasi, zaku ji complete tarihin ba zan rage komai ba a gaba, dan ni wlh tarihinsa ya fi mun na kowa daɗi da ma'ana a labarin nan, ga tarin ilmantarwa.

Mom Lion ta ja shi ya shiga musulunci saboda tana son shi, sun shirya aure, uhm Muhammad Haiza'an, mamallakin HAIZA'AN AIRLINE, mutumin da ya tara dukiyan da yake iya baiwa gwamnatin Amurka da sauran manyan ƙasashe bashi a wannan lokaci, mutumin da in yai magana ko shugaban ƙasa baya ja in ja da shi, mutumin da karfin dukansa ɗaya daidai take dana mutane 20, ya rayu tamkar sarki a fada, ya nunawa mom soyayya fiye da dik mace, ya gatanta rayuwarta da dikkan ahalinta.

Family ɗinta dik suna fantamawa da dukiyansa, su je ƙasashen da suke so, ƙaninta sai a ƙasar da yake so yake cin abincin dare, kannenta ba'a magana, sun more fiye da tinani, idan zasu yi birthday su ɗauki jirgin ruwa tampatsetse, a tsakiyar teku ake party ɗinsu, a kashe kuɗi a cashe, dik daddyn Lion bai damu ba, ya sake masu komai, kamfanin jiragen sama yake da shi, kai na ce maku ku jira cikakken tarihinsa, amma daddy ya gatanta mom da ƴan uwanta.

Amma me yafaru? Da aka shirya kaisa ƙasa, ba za'a iya tinkararsa ba saboda karfin ikonsa, ko gwamnati tsoronsa take ji, karfin ikonsa ya baiwa CRYSTAL PALACE karfin iko a yau, dalilinsa yasa babu wani jami'in gwamnati da ya isa keta cikin CRYSTAL PALACE bare ya kama wani daga ciki, kuma har yau har gobe gwamnati na shakka da tsoron shiga cikin gidansa, gidan yana nan a rufe sai tarin jami'an dake gadin gidan tamkar akwai ran shugaban ƙasa a ciki, daddy ya sanya tsoro a zuƙatan azzalumai da zaman lafiya ga bayin ALLAH, ba ta yadda za'ayi a same shi bare a kashe shi, dole sai ta hanyar mutum ɗaya!

Mom Lion, ita kaɗai take da kusanci da shi fiye da yadda kowa yake da, ya rabb, ta zaɓi matsayin da gwamnati ta kwaɗaita mata fiye da wanda mijinta ya bata, ta zaɓi ta samu karfin iko fiye da wanda ya bata, ta aminta ta sa hannu kan zata fito da shi wajen da babu kowa a kama shi, ya rabb, baya fita sosai, sai dai a zo gida a samesa, amma a wannan rana da tsautsayi ta hau kansa, ta ce sai dai su fita yawo, ya ce ina take son su je, ta kwanta a jikinsa tana kirga mashi in da take son su je.

A wannan rana Lion ya zo gidan ganin jaririn ƙaninsa watau Nirash Leo, in baku manta ba Lion yana hannun Hosainin daddy ne. A wannan rana da ya zo bai samu haɗuwa da mom ba, dan tana wanka, shi kuma daddy baya son Lion ya zauna a gidansa saboda wani ɓoyayyen dalili nasa. MENENE WANNAN?.

Lion yana son Nirash sosai, ya ɗauki yaron, yai mashi wasa sosai, kafin mom ta fito ya kwantar da shi ya koma. Mom ta yi kwalliyar da tin da take bata taɓa yin isrinsa ba, sai tsokanarta daddy yake yi wai yau ta zama under 13, ta ƙara kyau, har ya ce gaskiya ba zai yarda ba, kafin su fita sai sun ɗan yi chaskale, dan ta yi kyau sosai, da yake ta san me ta shirya, ta yarda, a wannan rana ta bashi kanta na karshe, tin da yake da ita bata taɓa sake mashi jikinta irin wannan rana ba, har yake tambayarta meyasa yau bata mashi kukan yana wahalar da ita ta kame jikinta ba?.

Tana munafukin murmushi ta amsa da ai yanzu ta daina bashi wahala wajen saduwa, ta yi alkawarin yi mashi yadda yake so, ya ji matuƙar daɗi, a wajen ya ce ta faɗi me take so ya bata! Buɗar bakinta ta ce kyautar jirgin sama guda ɗaya, a wajen ya ɗauko ɗaya daga cikin takardun jiragen samansa, ya sanya hannu a kan wanda ta zaɓa, ya bata yana ƙara jawota jikinsa, dik bai san me ta shirya mashi ba..

Ta karɓa har da godiya, suka sake yin wanka, ta shirya Leo cikin haɗaɗɗun kaya, daddy ya ɗauki Leo a hannunsa yana sumbatar kumatunsa suka fito. Guards zasu rakasu ta ce yau fitar masoya ne, kada wanda ya damesu, hakan yasa daddy ya ce mutum biyu su rakasu, ta yi typing message ta sanar da mutanen can guards biyu ne kawai sukai masu rakiya, sun yi farinciki da jin hakan sosai.

Daddy da kansa ya tuƙa mota a wannan rana, motar da bai sake tuƙawa ba kenan a rayuwansa. Mom ta ce daji zasu je, dan yau soyayyarta ce sabo ta motsa, da yake ya yarda da ita fiye da kansa, bai kawo komai a ransa ba, ya ɗauketa suka shiga dajin, bakin teku dan hutawa, yana rike da Leo yana zura mashi harshe a bakin yana tsotsa, suka tsaya a bakin ruwa suna hirar soyayya, ya jawota jikinsa.

Unexpected suka ji harbi, an harbi guards ɗinsa guda biyu, da yake a lokacin akwai sa bakin gwamnatin wannan lokaci, sai abin ya tafi cikin tsari, yana bin gwamnatin bashin kuɗi billions of dollars, shi ne kan su biya gara su haɗa baki a kashesa, dalilin kenan da yasa suka yaudari mom da ta haɗa harda yaranta ta kashe dan a rasa magada kuɗin Haiza'an gwamnati ta ci bulus, ita kuma mom da yake kanta dusa ce a ciki, sai ta aminta da su, ta shayar da jaririnta guba, Lion ya gudu, saboda a lokacin da suka kusa kama daddyn Lion ɗin ya yi wa Hoosaininsa message kan ya ɓoye mashi Lion!.

A wannan lokaci sun gagara kama daddyn Lion, ya rike mom sun gudu cikin daji, abu ɗaya yasa ya tsaya aka kama shi, watau da ya ga mom ta sanya mashi bindiga a kansa ta ce ya miƙa wuya, ya rabb, gigitar wannan al'amari yasa ya tsaya ya gagara motsawa, macen da yake ƙoƙarin bada ransa ya ceceta ita da ɗansa, amma ita ce ta sanya mashi bindiga a kai take cewa ya miƙa wuya ga miyagu?!

Sumar tsaye ya yi, ya dinga kallonta babu kyaftawa, a wannan lokaci WS-HOSPITAL guards suka kewayesa, WS-HOSPITAL su brain É—insa suke so, while gwamnati kuma suna son a kashesa dan kada su biya kuÉ—insa da suka ci.

Haka suka kama shi mom na tsaye, suka ɗaɗɗauresa da igiya, wlh daddy yana tsaye yana kallon cikin idon mom bai motsa ba, ta rigada ta kashesa da ransa, wannan wani irin cin amana ne mai tsananin zafi?. Taya kuke tinanin Lion zai yafe mata? Ko shaiɗan bashi da kalaman da zai sanya zuciyar Lion ya yarda da mace, wlh babu mahaluƙin da ya isa ya sanya shi ya yarda mace tana da kirki, ya taso yana ganin yadda mom da dad ɗinsa suke soyayya sosai tamkar zasu haɗiye juna, amma daga karshe ku duba fa?.

Da yake mom tasan daddy na mutuwar son yaransa, sai ta ce a tsayar da shi, kafin a wuce da shi bari ta baiwa Nirash guba a gabansa, so take ta kashesa da heart attack ne kawai....... Azzaluman suka tsaya, ta karɓi guba a hannun ɗaya daga cikin guards na WS-H, ta buɗe kwalbar, tin da uwar daddy sarauniyar Ring Of Power ta haifesa bai taɓa zubar da kwallah ba sai a wannan rana, yana gani ta tsiyaya gubar a marfin kwalbar, ta ɗigawa Nirash dake ta faman wasa a baki, take ya fara lashe baki abinsa.

Ya rabb, sai ga hawaye masu tsananin zafi sun fara zuba daga idanun daddy da suka rikiɗe suka yi jajir tamkar wuta, ya ALLAH, ko motsi ya gagara yi, waɗan nan hawaye da suna magana, da sun faɗawa duniya kalamai daga zuciyar daddy wanda zasu firgita duniya! Haka guards na WS-H suka wuce da shi, mom kuma aka dawo da ita gida da nufin gwamnati zata bata muƙami na musamman a gwamnatance.

Tana dawowa gida ta kwantar da Nirash a kan gado, ta shirya kayanta, ta É—auki takardan jirgin da ya mallaka mata, ta fita da gudu ta bar Leo a kan gado, daga nan ta nufi gidan gwamnati, dan tasan Hoosainin daddy ba zai kyaleta ba, in duniya dik gatanta ne sai ya ga karshenta a irin wanan bakar zuciyar tasu.

Tana barin gidan sai ga Lion ya shigo, dan a lokacin ya samu labarin dik abin dake faruwa daga bakin Hoosainin daddynsa. Cikin zafa ya hau benensu, yana neman mom É—insa, a lokacin bai san da sa hannunta ba, dan lokaci daddy bai faÉ—a masu ba, sai daga baya ne ya kirasu a waya yake sanar da su har Aryan ya É—auki kiran.

Yana shiga ɗaki ya isko Leo kwance kumfa na fita daga bakinsa, yaron yana fafutukan rai ko mutuwa, ai tuni Lion ya mance da abin da ya kawosa, ya rungumi ƙaninsa da gudu ya fita. Jama'a tarihin daddy akwai taɓa zuciya sosai, ya sha gwagwarmayar rayuwa bawan ALLAHN nan, amma zaku ji komai dallah-dallah a gaba, yanzu tsakure ne, tarihinsa shi ne the most best part a littafin nan!.

Kunga a yanzu ko shaiɗan bashi da kalaman da zai zuga Lion ya yarda da mace har ma ya sota, irin wannan zazzafar cin amana mai ƙona zuciya, hmmmm, dan haka kome Lion ya ce da mata ƴan mata ayi hakuri, ba laifinsa bane, muɗin ne muka dinga bashi darasin rayuwa mai tafarfasa bama mai zafi ba, ga Dr ma ta ƙara mashi nata ta hanyar kashe mashi yaya, ai shi Lion hmmmm na dai yi shiru, amma yaga rayuwa!.

-------------------------🔥
Chapter 165 · 0% Book details