← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 191 OF 227

Sashe 191

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yatsa ya sanya a dimple ɗinta da ya lotsa kafin ya amsa da. "Yeah, na ci"......... Shiru ta ɗan yi game da ɗan sunkuyar da kai, sai ya ce. "Are you okay?". Ya faɗa yana sake hannunta ɗaya ya ɗago haɓarta.

"My gentle chaos, ina son tambayarka ne!". A sanyaye ta faɗa.... "Please I'm listening"......... "There was a day da ka ce mun ni kaɗai ce nike baiwa Champion na IRON FIST haƙuri kuma ya haƙura, i asked you who's Champion you didn't answer me, ka canza topic na hiran, and day before yesterday i called your phone, someone picked up, i saw his face, exactly wannan mutumin da ya kashe mun mammyna, daddy, my heart is telling me that you're hiding alot for me, who are you? Where are coming from? Who's that man i saw in your house in my fist day living there?". Babbar magana, watau har guru da ta gani a ranar farkon zamanta a gidansu bata manta da shi ba.

Yanzu Aryan ya gane babban kuskuren da ya tabka, ya manta cewa jinin IRON FIST ce ita, akwai brain, komai ƙanƙantar motsi tana lura da shi, gata dai wani lokaci shirme yai mata yawa, but ko motsi ka yi kusa da ita, zaka ga kamar bata ganka ba, amma kar take kallon komai.

Ganin ya yi shiru ne yasa ta cigaba da cewa. "Your face looks like Rimsha's face, also uncle Faryan, kana kama da shi, i try all my best dan in haÉ—aku da Rimsha, amma you're running out of her, why daddy? Are they your family?". Watau dik motsinsa a kan su Faryan ma ta tariye komai cikin kanta, ta kuma shirya titsiye shi.

Da yake yasan rauninta, sai ya ce. "Seraphina, you mean daddy yana maki karya? Don't you know that ke matata ce a yanzu? Why zan yi hiding maki some of my life privacy?"....... Shiru ta ɗan yi, tana ƙoƙarin gane me yake nufi da waɗan nan kalamai nasa.

Bai bari ta yi dogon tinani ba bare ta gano raina mata wayau yake son yi, sai ya yi gaggawar sake cewa. "Oh you mean ni mayaudari ne ko? Okey good". Ya faÉ—a tare da sake hannunta zai juya. Yasan ba zata iya juran irin waÉ—an nan kalamai nasa ba, ba zata yarda ya yi fushi ba, shiyasa ya É—aureta ta nan, ai in tasan wata bata san wata ba.

Da sauri ta tari gabansa, muryanta har yana rawa wajen cewa. "Sorry daddy, is not like what you're thinking, kawai baka fahimceni bane, what i mean here is how i called your phone someone picked up, and mutumin da ya kashe mammy na ne, so i wonder yadda aka yi wayanka ya zo hannunsa, then kai da bakinka ka ce ni kaÉ—ai nike baiwa Champion na IRON FIST hakuri kuma ya hakura, to waye Champion? Ina kuma IRON FIST? Kenan ka sansu ne?". A dame ta yi maganar, tana gudun ya ce zai yi fushi ne.

"Okey like that ake tambayar miji abu ko? Baki iya tambaya ba? Wannan zargina kike yi kai tsaye ba tambaya ba, kuma in kina zargina babu aure a tsakaninmu, dan ba'a aure da zargi". Ya faɗa game da raɓawa gefenta zai wuce irin ya yi fushin nan.

Da sauri ta sake tare gabansa, ta riko hannunsa tana faɗin. "Uhmmm uhmmm, daddy..... Daddy..... Daddy, wait mana, sorry please, ba zan sake ba"....... Tamke fuska tamau ya yi. "Go and learn how to talk to your husband sai in sake kulaki". Ya faɗa game da sake yunkurin wucewa ta gefenta..... Turo baki ta yi tare da ƙara ƙanƙame hannunsa, a shagwaɓe ta ce. "Sorry my gentle chaos, ba zan sake ba".

Nisawa ya ɗanyi game da rike hannayenta gam a cikin nasa, cike da kulawa ya ce. "I lose my phone two days back, ina ga shiyasa kika kira wani ya ɗauka, and about champion na IRON FIST, na yi maki kwatance ne da hakan dan ki san kina da kima da daraja a rayuwata, ina sonki sosai, kin san IRON FIST basa karɓar sorry ko a tarihinsu da duniya take da shi, an ce wai in suka kama mutum zasu kashesa ko da sun ce zasu yafe mashi ba ance in ya ce masu sorry suna fasa yafe mashi su kashesa ba?".... Kai ta jinjina tana ƙoƙarin gano ina ya dosa, dik ya gindayar da ita.

"To shi ne nai maki kwatance da IRON FIST É—in, then about Rimsha, ba yadda ALLAH baya halittar mutum, kin san kowa yana da masu kama da shi guda 9 a duniyar nan, kuma basu haÉ—a dangi ba, kema kina da naki masu kama dake É—in, takan iya yiwuwa ALLAH ya haliccemu muna kama da juna ne sosai da su, ni ban sansu ba, ki daina zargin mijinki, ki yarda da shi in ba haka ba aurenmu bai halatta ba".

Shiru ta É—an yi, tana jin kamar bata gamsu da sauran amsoshin ba, dik ya gindayar da ita, amma amsarsa na cewa ALLAH na halitta mutane biyu iri É—aya wannan ta yarda da shi, dan bata san addini ba, abin da bata da sani a kai aka sanar da ita karin ilmi take É—aukar hakan, sai kawai ta rungume shi tana faÉ—in. "Love you more daddy, ba zan sake abin da na yi ba, for give me?".

Hannunsa ɗaya ya ɗaura a kanta, ɗaya kuma bayanta, yana shafa ash hair ɗinta da ya sha gyara sosai wajen Madam, sai sheƙi da kamshi yake yi ya ce. "Kada ki sake yin wani bincike a kaina, dik abin da baki gane ba just go straight and ask me, zan baki amsa". Yasan halinta sarai, tsab zata ce zata yi bincike a kansa da kan waɗan nan amsoshin da ya bata, shiyasa ya yi saurin taka mata burki.

"Okey daddy, but daddy yaushe zaka kaini tsakiyar teku a cikin jirgin ruwa, mu je garin da rana yake fara fitowa, ya fito a kan idona in gansa?"...... "Very soon zan kaiki, muna yin aure dai zamu tafi honeymoon a cikin tsakiyar teku, daga nan mu wuce garin da rana yake fara fitowa".

Ƙara ƙanƙamesa ta yi, shi kuma ya rage tsawonsa ya ɗauketa cak suka fito parlo, a dining hall ya direta, already an shirya mata breakfast Aisha na zaune tana jiranta, Madam ta haɗa mata wannan daddaɗar kunun alkama mai madarar, ta shirya mata a saman table. A saman chair ya zaunar da ita, da kansa ya zuba mata abincin, ya zauna kusa da ita, ya dinga feeding ɗinta a baki har sai da ya tabbatar ta ƙoshi, sannan ya bata kunun kaɗan, ya ɗauki tissue ya goge mata baki.

Time ya duba a wayansa 7:05, hannunta ya riko suka koma room ɗinta, ya ɗauka mata rucksack ɗinta game da rikota da kyau suka fita waje, Aisha ta rufa masu baya. Kai tsaye ƙasa suka sauƙa, motarsa da ya bari a gidan jiya ya ɗauko, ya juya kan motar game da cewa ta shiga su tafi, da sauri Aisha ta shiga gidan baya. Ita kuma turo baki ta ɗan yi, a shagwaɓe ta ce. "Daddy I am a Queen of your heart, tin da Queen nike ka zo ka buɗe mun door".

Wani irin kallon ƙauna ya bita da shi kafin yasa hannu ya buɗe mata motar, yana buɗewa ta shigo tana ɗan murmushi. Harararta ya ɗan yi kafin ya tada motar su wuce school. Yana parking a school ɗin ya juyo da kallonsa a kanta. "Ayi karatu sosai". Ya faɗa daidai lokacin da Aisha ta ɗauki jakarta ta fice ya basu waje.

"Okey daddy, ka dawo da wuri ka É—aukeni"........ Harararta ta yi. "Ni driver É—inki ne?"..... Damke hannun door na motar ta yi kafin ta ce. "Kai bawa nane ai daddy, my driver, ka kawoni kuma ka zo ka É—aukeni, you're my guard". Ta kai karshe game da jan hannun kofar zata fita da gudu dan kada ya damketa.

Sai dai ina, tana gama faɗa ya danna locks na motar ya rufe. Nan fa kofa taki buɗuwa. Da sauri ta juyo, hannayenta tasa ta kama kunnenta, a shagwaɓe ta ce. "Sorry daddy, wasa nike yi".

Shiru bai yi magana ba, yana dai kallon kyakkyawan face ɗinta, slowly ya matso dab da ita, har suna iya shaƙar numfashin juna. Zazzare mashi idanu ta fara yi, ya ɗan fito da tongue ɗinsa ya lashi soft lips ɗinsa kafin ya ce. "Love you forever and ever my cherry, take good care of yourself, ki yi karatu sosai".

Kai ta jinjina mashi alamar to, bata iya yin magana ba, sumbatar cheek É—inta ya yi, ta É—an rintse idanu tana sauke numfashi a hankali. Janye jikinsa baya ya yi ya koma saman kujerarsa, ya buÉ—e mata motar. Da sauri ta fita tana faÉ—in. "Love you more daddy, sai ka dawo".

Kai kawai ya jinjina mata game da miƙo mata rucksack ɗinta, ta karɓa tare da wucewa, bayanta ya bi da kallo, imagine kawai yake yi ranar da za'a ce ita matarsa ce, ya rabb, shi kaɗai yasan me yake ransa. Sai da ta ɓacewa ganinsa sannan ya tada motar ya nufi gidan Abba.

-------------------------🔥

After sometimes. Tana shiga class ta isko Rimsha ta kifa kai a saman table kamar tana kuka, da sauri ta kariso cikin class ɗin tana ambatar sunanta. Rimsha na jin muryarta ta yi gaggawar ɗago kai game da miƙewa, ta zo da sauri ta rungumeta, a lokacin babu kowa a class ɗin.

Zaunar da ita a saman chair Seraphina ta yi, ta rarrasheta sosai kafin ta tambayeta meyake faruwa, Rimsha bata ɓoye mata komai ba, ta faɗa mata an aura mata uncle ɗinta. Mamaki ne ya kama Seraphina na jin tana kuka wai dan an aura mata Uncle ɗinta, ita fa Seraphina bata san cewa ma haramun ne ka auri Uncle ɗinka na, a wautarta har mahaifinka zaka iya aura, bata da ilimi da sani ƙan ɓangaren wa yakamata ka aura, a ɗan dake ta ce. "Ke baki son shi ne?".
Chapter 191 · 0% Book details