← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 227

Sashe 82

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sojoji 8 ne suka rufawa Leo baya, saura suka tsaya suna kallon Noor, ba yadda za'ayi su tafi su barshi tin da shi ne assistant ɗin Leo, dole su bashi tsaro ko da su zasu mutu. Shi kuwa ya tsaya kallon V da ta ɗan turo baki tana ƙoƙarin sassauta ɗaurin da ta yi wa igiyar rucksack ɗinta, ya tamke mata ciki sosai.

Bayan ta ɗan sukurkuta ne ta ɗago kai, haɗa idanu suka yi, one side smilling ya ɗan sake mata kafin ya miƙa mata hannu. Da sauri ta miƙo mashi, kamata yai suka nufi bayansu Leo, da sauri su Angelina suka rufa masu baya, sannan sauran sojijin bar 1 ɗin suka rufa masu baya....... Su leo sun yi nisa a tafiya, sai da suka ɗaga kafa kafin suka cin masu, sun yi tafiyar good 30 mins kafin su isosu, nan ma a bakin wani ruwa suka iskosu a tsaye, ruwa ne mai ɗan yawa sosai kamar kogi, amma ba ruwan gudu sosai bane, yana tsaye haka, ga wasu dogayen bishiyoyi bakake a wajen, daga gefe akwai duwatsu da tsaunika.

Ɗan kewaye Leo ya fara yi a wajen yana dubawa, da sauri sojoji 5 suka rufa mashi baya dan bashi tsaro. Shi kuwa Noor ɗan matse hannun V a cikin nasa yai, hakan yasa ta ɗago eyes ɗinta a kansa. Can ƙasan maƙoshi ya ce. "Bani rucksack ɗinki in rike maki"...... Kamar yasan ta ɗan gaji, da sauri ta zame hannunta daga nasa.

Zuba mata idanu yai, dama ya fahimci ta gaji ne yasa ya ce ta kawo ya haÉ—a da nasa ya rike masu. Ganin tana ta faman kwancewa ne yasa ya matsa dab ita, bata ankara ba sai jin hannunsa ta yi a saman cikin nata, yana kallon cikin eyes É—inta ya fara kwance mata jakar, ai wani irin romantic mood V ta faÉ—a, while shi ya jima da faÉ—awa tin da ya riko hannunta a bakin dajin. Wani irin harara Arya ta dallah masu tare da wucewa ta fara kewaye wajen ita ma.

Kwance mata jakar ya yi, da kansa ya sauke mata shi ƙasa daga bayanta, sai ya ratayosa a hannun damansa saman shoulder ɗinsa, ya zura hannayensa a cikin aljihu yana kallon yadda ruwan kogin yake motsawa a hankali-hankali, ga dabobin daji marasa haɗari suna zuwa shan ruwa a wajen, iska na kaɗa bishiyoyin dake wajen, yanayin weather wajen akwai daɗi.

A daidai lokacin Leo ya dawo wajen, kusan a tare suka dawo da Arya, ba tare da Leo ya kalleta ba ya ce. "Ki duba mana network na wannan waje akwai karfi ne?". Ya faɗa tare da matsawa ɗan gefe ya fara kwance igiyoyin rucksack ɗinsa shi ma, ya sauƙe ƙasa, dan wajen tai mashi, yana fatan su samu network mai kyau a wajen, dan su Arya su yi aikinsu a natse, su tura drones na camera dan gano ainahin in da miyagun suke.

Sauke rucksack ɗinta Arya tai tana dallah mashi harara ta ƙasan ido, a ranta ta ce ba dan ka zo a oganmu ba da ka gane baka da wayau, amma yanzu ma nasan maganinka, da Arya kake yi, sai na wahalar da kai ta gefen aikina. Tana fito da laptop ɗinta tana tinanin kalar wahalar da Leo da zata yi a dajin nan, zata yi ta bashi wrong information sai ya ji azaba.

Kunna laptop ɗin nata ta yi ta fara duba network na drone ɗinsu. Sun kuwa yi sa'a, dubawar farko suka samu network mai karfi sosai a wajen, ɗagowa tai ta kalli Leo tare da cewa. "There is a strong network here"....... Kai kawai ya jinjina tare da ɗago da eyes ɗinsa a kan sojojin dake wajen. "Ku kafa mana tantina a nan". Daga haka bai sake magana ba, ya fara fito da important kayan da zai buƙata a yanzu. Ya miƙa masu nasa tantin, ya nuna masu in da yake buƙatar su kafa mashi, ɗan nesa dasu kenan.

Da sauri suka karɓa cikin girmamawa. Miƙewa yai ya nufi wajen tsaunikan da wani karamar ƙorama dake zubar da ruwa a wajen. Da gudu sojoji 5 suka rufa mashi baya dan bashi tsaro, saura kuma suka fara aikin kafa tantunan nasu babu kama hannun yaro. Cikin ƙasa da awa ɗaya suka gama kafa komai, tantinan mata watau na su Arya shi ne a tsakiya saboda tsaronsu, na mazan na kewaye da nasu.

Kowannensu ya shiga nasu tantin dan shirya kayansa a ciki, irin wannan electric mattress ɗin aka basu dama, dik suka yi amfani da power bank ɗinsu masu caji da rana suka tashi mattress ɗin, suka shirya komai. Leo, Noor and Zaynish shirya masu nasu ƙananan sojoji suka yi. Shi kuma Noor ya bi bayan Leo dan duba yanayin waje, suna son tabbatar da babu muggan namun dawa a wajen ne, idan ma da akwai sai su san irin zaman da za su yi da su.

After some minutes dik suka komo cikin tantinansu harta Leo, nan fa suka fara shirin neman abin da za su sanya a cikinsu, masu kiran gida suka fara ƙoƙarin kira dan su tabbatarwa da kowa suna cikin ƙoshin lafiya. V dake zaune saman electric mattress ɗinta ne ta fara neman number daddynsu, while Arya na ta faman shirya su laptop ɗinta ta kama network na wajen da kyau, ita bata wasa da aiki ne.

Number GAT V ta kira, a lokacin da call ɗin ya shigo wayansa yana zaune a saman sofa, yau bai je office bama saboda ya baiwa Aunty Lisa lokacinsa, so yake ya kasheta da love ɗinsa. Ta shiga master room ɗinsa da nufin cewa bari ta yi wanka ta zo, shi kuma yana zaune yana ta neman numbersu Arya tin ɗazun, dik ya damu, ba dan yasan me yake yi ba, kuma yasan da su waye aka haɗasu aiki ba da ba zai yarda ba, wlh GAT jajirtaccen namiji ne, akwai taurin zuciya da jajircewa, yaransa fa har huɗu ya sadaukarwa ƙasansa, ba kowa zai iya ba sai mai juriya.

Ai yana ganin call ɗin V hannunsa har yana rawa wajen saurin yin picking. Kara wayar a kunne yai yana faɗin. "Hello my heart"....... Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta amsa da. "Daddy I missed you so much, ina jin kamar in dawo". Ta faɗa tamkar zata yi kuka. Saisaita natsuwansa yai tare da cewa. "V, kada ki manta jaruma kike ɗiyar jarumi, jinin Thomas kike, bamu san karaya ko raunin zuciya ba, ki jajirce ƴata". Haka ya dinga zuba mata kalaman kwarara gwiwa, har sai da ta ji lallai a shirye take da ta mutu a kan ƙasarta.

Daga nan ya ce ta baiwa su Arya waya, kiransu ta yi, duk suka haɗu suka sanya wayar a H-Free, banda kalaman karfafa masu gwiwa babu abin da GAT yake faɗa masu, hakiƙa ya shiga damuwa rashinsu, amma bai bari ya nuna masu cewa ya shiga damuwa ba kada zuƙatansu su raunana, sai ya dinga gwada masu ai ko ba shi zasu iya rayuwa.

Sun jima suna waya V na ta zuba mashi shagwaɓa, sun shari good 1h, suka faɗa mashi a yanayin wajen da suka kafa tantuna, da dik abin dake gudana, fatan nasara yai masu kafin su yi sallama ya katse kiran. A gefensa ya ajiye wayar bayan ya duba time 6 na magrib ta yi. Da yake parlon akwai haske wuta tamkar rana sai ba zaka gane magrib ya kawo kai ba.

Jikinsa ya bi da kallo yana tunanin yakamata ya je ya duba Lisa fa, dan da barinta parlon ma almost 1h 30mins. Miƙewa yai cike da matsuwar son ganinta, tin da ya mallaketa bai samu lokaci da ita ba, saboda shirin tafiyarsu Arya, kuma yana ɓoyewa baya son su Arya su san ya yi aure, ya ce masu hutu kawai Lisa ta zo, baya son ɓacin ran yaran nasa.

Kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa, slowly ya tura kofar tare da sanya kai. Ai sai da ya ɗan tsaya cak tare da jan wani dogon numfashi, ya shaƙi daddaɗar kamshin perfume ɗinta da ya gauraye da air freshener da ya gauraye kowacce kusurwa na ɗakin, dikka curtains a sake, ta kashe ainahin wutar ɗakin ta kunne dim light.

ÆŠan rarraba wannan tiger eyes É—in nasa irin nasu Arya ya fara yi a cikin É—akin. Can ya hangota ta baje a saman bed, tana rungume da pillow a kirji, ta tada kai da wani, ta É—aura kafafunta a kan wani. Sanye take da wasu welcome baby sleeping dress da ya fito da dikkan albarkatun jikinta.

Daga ta sama tudun breast É—inta dik a waje, rigar tana da breast cuff, ga shi siririn hannu ne da rigar, bugu da kari shara-shara ce wacce da ita da babu kusan É—aya, and a daidai tsakiyar tsala-tsalan cinyoyinta ya tsaya mata.

Gabaɗaya GAT rasa gane kansa yai, gently ya taka zuwa in da take. Ai yana isa gaban bed ɗin sai da ya haɗiye wani irin yawu gwad, kallonta ya fara yi daga sama har ƙasa, da alama ta yi nisa cikin barcin da ya kwasheta, ga wayarta rike a hannunta, da alama call ta kammala yi kafin barci ya saceta.
Chapter 82 · 0% Book details