← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 227

Sashe 110

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin wani crazy jeans and top Maya ta shirya, kayan ya zauna ɗas a jikinta, ta gyara hair ɗinta da ya kai har tsakiyar baya, ta tara ta ɗaure a tsakiya tare da sake jelar a baya, ta yi matuƙar kyau sosai, a gefen gadonsu ta zauna tare da jawo paper ta fara dubawa. Ita ma ta yi iya dubanta bata ga wani mistake ba, sai kawai ta naɗe takardan ta mayar.

A haka Zinta ta fito ta sameta, shiryawa ita ma ta yi cikin irin kayan Maya sai dai kowa da kalar tasa, na Maya blue jeans and white top, nata kuma black jeans and milk top. Sai tashin kamshi suke yi, ta É—auki paper É—in, suka kama hannun juna suka fito.

Kai tsaye haɗaɗɗen gidan 3D suka nufa, dikkansu suna cike da tsoro da fargaba, dan sun san halinsa, yanzu yana iya hukuntasu ta hanyar kara masu ayyuka da sauransu. Abin mamaki kuma a wannan hospital ɗin ayyuka basa taɓa karewa fa, kullum Dr James yana da ayyuka bila adadi da yake sanya nurses ɗinsa.

Guards biyar ne ke gadin gate na gidan, da suka yi knocking sai sister Maya ta ɓuya a bayan Zinta, saboda ita mayyar tsoro ce, bata son haɗa ido da waɗan nan shaggun samudawan masu gadin nasu. Zinta kuwa ta yi karfin halin tsayuwa har aka buɗe masu. Su kansu guards ɗin sai da suka haɗiyi yawu na ganin kyan su Maya, yaran sun haɗu. Dik cikin hospital ɗin su ne kawai idan an gansu sai an sake juyowa an gansu.

Babu alamar annuri a kan fuskan guards É—in ya tambayi lafiya. Sister Zinta ce ta kora mashi jawabin cewa sun zo ganin Dr James ne, zasu bashi rahoto. To da yake yasansu sosai, sai ya basu hanya.

Kama hannun sister Maya dake laɓe a bayanta ta yi, ta jata suka wuce ciki, Maya jikinta sai kerma yake yi har suka karisa kofar babban parlonsu. Tsayuwa suka yi suna tinanin ya zasu yi su buɗe kofar nan yau? Dole sai da fingerprint na mamallakan gidan yake buɗewa, to ya zasu yi.

Ana haka sai ga Dr Kamal ya fito rike da waya, yana sanye da short zuwa cinya, daga sama single farare kal-kal, sumar kansa bakinkirin tana wani irin sheki a kwance luff. Wani musulmin ajiyar zuciya suka sauke kafin su tsugunna har ƙasa su ɗaga mashi gaisuwa. Amsawa ya yi tare da cewa lafiya?. Yana magana yana kallon Maya take ta faman kankame sister Zinta.

Dik sun yi ƙasa da kai, suna da kunya sosai, basu son ɗagowa su gansa a cikin wannan yanayi da yake na rashin wadataccen tufafi, dama dai dogon wando da singlet ne a jikinsa to da sauki, amma ɗan wannan shorts ɗin kai ina.

Sister Zinta ce ta ce. "Mun zo ganin master ne".......... Hanya ya basu kan su wuce shi kuma ya karisa fitowa waje. Da sauri suka miƙe suka shiga ciki suna zuba mashi godiya. Like wow, main parlon nan nasu ya matuƙar haɗuwa, ga wani sahihin kamshin dake tashi.

A tsakiyar parlon suka tsaya kallonsu a sama suna hangosa tsaye a saman bene rike da wani haɗaɗɗen cup mai ɗauke da hot green tea yana sha. Shi ma daga shi sai shorts and single irin na Dr Kamal. Ƙasa suka zube gwiwowinsu suna kallon saman, murya a sanyayye cikin girmama sister Zinta ta fara bashi hakuri tare da nuna mashi result ɗin nata.

Shiru yai masu for almost 10 mins, har sun gaji da durkuso, tamkar Maya zata yi kuka, har sun fidda ran zai amsa sai suka ji ya ce. "Get out of my house!". Yadda yai maganar ya yi balain girgizasu, jikinsu na rawa suka miƙe a zabure, kenan ya tabbata ba zai karɓi wannan aikin ba, ya soketa!.

Juyawa suka yi, idanunsu ya ciko tab da kwallah, suka nufi kofar fita. Bayansu ya bi da kallon wanda tin da suka shigo bai É—aga ido ya kallesu ba, sai da suka juya zasu fita ne slowly ya É—ago eyes É—insa a kansu. Kurawa mazaunan Zinta eyes ya yi, take ya É—an shanye har da lumshe idanu kafin ya sauke ajiyar zuciya, yadda surarta take it melt his heart.

Ji ya yi tamkar ya miƙa hannu ya jawota ya rungume, da alama da gaske yake sonta, iskanci ne kawai ya cika mashi ciki, dik wani step ɗaya idan ta taka sai ya ji zuciyansa ya amsa, yana jin tamkar yau ba zai iya barinta ba, kamar kawai ya ci amarcinsa tin da ya mallakawa kansa ita, amma bai motsa daga in da yake ba har suka isa bakin kofar parlon.

Tsayuwa cirko-cirko suka yi suna tinanin yadda ake buÉ—e kofar, basu iya ba. Slowly suka juyo da kallonsu a kansa, da sauri ya É—auke kansa daga kallonsu kamar wani mara gaskiya. Sister Zinta ce ta sake Maya tare da dawowa in da suka tsugguna É—azun ta sake tsuggun nawa. Hakuri ta hau bashi game da neman alfarman ya zo ya buÉ—e masu door.

Hallau sai da ya yi good 10 mins shiru kafin ya yi mata alama da hannu a kan ta tafi. Da sauri ta miƙe tana zuba godiya, tana juyawa ya ɗago da eyes ɗinsa a kan mazaunanta. Zuba mata ido ya yi har ta kai bakin door ɗin. Suna tsaye sai gani suka yi kofar ta motsa ta ɗan buɗe kaɗan. Ya buɗeta ne ta wayarsa.

Handle suka kama suka ja, kofar ta buɗe, da sauri suka fita suna jan numfashi. Suna fitowa Maya ta ci karo da Dr Kamal da yake ƙoƙarin komawa ciki. Karo suka yi kanta ya bugu da kirjinsa baya ta ja kamar zata faɗi yasa hannu ɗaya ya damki wuyar rigarta, ya jata ta tsaya a kan kafafunta.

ÆŠan zuba mata ido ya yi kafin ya wuce ya basu waje. Zazzare idanu a kansa ta yi tare da sauke ajiyar zuciya na ganin ya wuce. Rikota Zinta ta yi suka wuce. Slowly ta juyo dan ta ga ko Dr Kamal ya shiga ciki, ai tana juyowa suka yi 4 eyes, dan yana tsaye a bakin kofa yana karewa albarkatun jikinta ta baya kallo.

Tana juyowa ya É—auke kallonsa tare da wucewa ciki, wucewa ita ma ta yi da sauri tana kara waigo kofar har suka fita........ Suna fito sister Zinta ta ce. "Sister Maya i wonder ooo"...... "Wonder for what?"....... Nisawa ta yi kafin ta ce. "Sister Lazy said that wancan babyn da ta fito da shi ranar is for Dr Kamal right?".

Kai Dr Maya ta gyaɗa alamar e. "But where's his wife? Ban taɓa ganin maman baby ɗin ba, and tin da muke zuwa 3D House ban taɓa ganin mace a ciki ba, su uku suke rayuwa! Kuma tin daga wancan rana da naga jaririn ban sake ganinsa ba, ko ina yake? And kin yi tinani kan irin chemicals da muke haɗawa? Ki yi tinanin irin projects da muke yi, ki tina kullum a Section C sai mun haɗa chemicals mun shiryasu a kwalabe, kullum kuma ana fita da chemicals sama da kwalba 200 daga section C, a tinaninki me ake yi da dikka waɗan nan uban chemicals ɗin?".

Nima ina son sani, dan billahil lazi ba iya cutar suke kirkira da wannan uban chemicals ɗin ba, kada ku manta project na cutar nan sun fara ne shekara uku da suka wuce, kuma sai yanzu suka iso fagen haɗa chemicals na cutar, kunga which means chemicals da ake ɗiba kullum akwai wani gagarumin abin da suke aikatawa da shi, gaskiya akwai abin da ya saɓa babba, kuma da alama gagarumin abu ne ba karami ba, dan sun ɓoye shi sosai, basu bari kowa ya sani ba, ko ita Lazy bata sani ba.

Sister Maya ta ce. "Ni kaina abin ya fara É—aure mun kai, ina suke kai chemicals da ake É—eba kullum? Kullum ana cikin shigo da sabbin chemicals, mu tacesu su shirya a kwalba, kullum da daddare sai an É—ebi chemicals É—in, ina ake kaisu? Me ake ayi da su? Ina babyn Dr Kamal da sister Lazy ta shigo da shi Section namu ranar? Ina mother É—in babyn?".

Sister Zinta ta ce. "Let me free my brain, leave it rest, kinga ki bari mu hutar da brain É—inmu na É—an lokaci, idan muka natsu sai mu tattauna a kan matsalar, dan da alama gagarumin aiki ne".

Na'am Maya ta yi da batunta, dan dama kanta kamar zai fashe saboda ciwo, ba aikin wasa suke yi ba, dan ma suna da kwarewa, tace chemicals da banbantasu ba dik kai ba, dan ma dai kullum idan zasu tashi daga aiki akwai kwayar da ake basu su sha na ɗan resting brain ne, sannan a hospital ɗin na dik karshen wata akwai wasu kwayoyin magunguna guda biyar fa ake basu suna sha, dik da suke malaman lafiya basu san kwayoyin menene wannan ake basu dik karshen watar ba, su dai suna sha kawai. Kuma idan sun sha ba karamin daɗin jikinsu suke ji ba, suna jinsu da ƙarin lafiya sosai, dik wata kasala tana barin jikinsu, suna samun karfi sosai, shiyasa tin safe suna aiki har dare basa gajiya.

Cike da wannan tinani a ransu suka koma room ɗinsu, suna tinanin yadda zasu ƙare wannan aiki su huta da bala'in 3D. Suna komawa room ɗinsu ta ajiye result ɗin suka yi kwanciyarsu a kan gado, suka fara hira cike da tsananin kaunar juna, suna yi suna farinciki game da daddaɗar murmushi dake kwantar masu da hankali idan suka ga ɗayansu ya yi!.

-----------------------🔥

CRYSTAL PALACE.

Kwance take a saman bed É—inta tana kallon saman É—akin, ta gagara ko motsawa, farkawarta daga barci alluran da ya yi mata kenan, idanunta sun kumbura sosai, har kamar zasu rufe saboda kuka. Tunawa ta fara yi da abin da ya faru tsakaninta da daddyn nata.

Lokaci guda ta ji kunyansa ya yi mugun shigarta, sai a yanzu ta fahimci ba abu bane mai kyau, sai kuma yanzu ta gane abin da kunya. Tana tsaka da tinani sai ji ta yi an turo kofar. Slowly ta kai kallonta a kan door É—in.
Chapter 110 · 0% Book details