← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 227

Sashe 116

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga nan ya tanbayi ina sauran Angels ɗin nasa, ta faɗa mashi suna waje suna aikin cetan ran Jami'in, a ɗan dake ya ce. "Awww wai ba mutuwa ya yi ba dama kike wannan kukan daughter?"...... Da e ta amsa tare da faɗa mashi yadda komai ya wakana. Girgiza kai ya yi, a cikin ransa ya ce mata koma yaya ba zasu taɓa rabuwa da raunin zuciya ba, shi ai ya ɗauka ma an kashe sojan ne a gabanta yasa ta birkice, shiyasa yai mata uzuri dan bata taɓa kallon mutuwa a gabanta ba, to ashe ma ba haka bane.

Ƙara karfafa mata ya yi kafin su yi sallama ya ajiye wayar, ya kara jawo Aunty Lisa jikinsa, sai da suka zubawa juna soyayya sosai, ya yi kissing ɗinta sosai sannan ya saketa game da kama hannunta suka nufi parlo. A nan suka yi sallama ya nufi waje ita kuma ta zauna a saman sofa.

A ɓangarensu Arya kuma, in ƙara takaice maku labari a washegarin ma sai can yamma su Leo suka bar sansanin ƴan ta'addan nan, sai da suka yi kwanaki biyu a hanya kuma kafin su dawo sansaninsu. Suna dawowa suka kira barrack kan azo a ɗaukesu MISSION IS DONE!. Take suka hau shirin komawa. A ranar da suka dawo Manassa ta yi treating hannun Zaynish da ya sha yankar wuƙa.

A wannan rana daɗi kamar Arya ba zata mutu ba, sai satar kallon Leo da bai san tana yi ba take ta faman yi. Noor da V kuwa a tare suka kwana manne da juna wajen da suke hura wuta dan jin ɗumi, suka ɗaure ƴan ta'addan da suka zo da su a jikin bishiyar dake kusa da su. In ƙara taƙaitawa kwanansu ɗaya da dawowa jirgin da ta kawosu ta dawo ta ɗaukesu, amma a wannan karon sai da suka yi tafiya cikin daji kafin su samu wajen da yakamata jirgin ta sauƙa, suka naɗe tantunansu, suka tattara komai suka koma barrack.

Ko da suka koma hutun satin biyu aka basu dan su sake shirin shiga Mission na biyu, ba'a faÉ—a masu me result na mission na farko ba, so ake yi sai an haÉ—a Mission É—in guda biyar dikka.

Mission ɗinsu a kudancin ƙasar bashi ne the most important ba, mission ɗinsu a arewacin ƙasar shi ne ma dalilin wannan missions ɗin a labarin nan, dan haka zan yi skipping ɗayan mission ɗinsu na Kudancin nan mu je arewaci, saboda in na biyewa rubuta komai zamu ja lokaci, gara mu rubuta the most important ɗin.

Kamar yadda suka yi mission na farko haka suka saka yi mission na biyu, sun kuwa yi lafiya sun dawo lafiya babu wanda ya rasa ransa. Daga nan ne aka sake shigar dasu ɗakin horo na musamman, saboda zasu tafi mission a kan Arewacin ƙasar dake cike da jiga-jigan ƴan ta'addan masu haɗari, sai aka ware watanni biyar za'a sake horar dasu tamkar ba gobe kafin su tafi mission ɗin.

Tin da suka shiga wannan É—akin horo ba waya, ba komai har sai da suka horu na watanni biyar É—in nan, aka sabonta masu komai, suka sake fitowa a sabbin yayewa sabbin jini, a lokacin jinin nasu na tafasa.

Sai ana saura sati biyu su tafi Mission É—in aka fito dasu daga É—akin horo. A tsawon watanni biyar É—in nan sun sake canzawa sosai, jikinsu ya sake ginuwa tamkar na Æ´an wrestling, sun zama zakwakuram jami'ai.

Tin da suka dawo mission na biyu bai haÉ—u da V ba har aka shigar dasu horo, shiyasa ranar da suka fito ita ya fara marmarin ya gani, ana maido masu da wayoyinsu numbeerta ya fara kira, a lokacin dab da mangrib ne, a maimakon y fara kiran daddynsa sai ya tafi ga Juliet É—insa, daddy bai san sun fito horo ba, ya dai san a week É—in nan zasu fita.

Yana kiranta ta sanya mashi kuka bayan ta yi picking. To abinku da renon mata a farko, shi ma kukan ya sanya mata na shagwaɓa yana faɗin. "Ni dik yadda za'ayi yau sai na ganki". Wlh Noor ya kware a duniyanci, idan kun gansa a ɗakin horo ba zaku taɓa cewa ya san wani abu wai soyayya ba bare shagwaɓa, babu wasa no nonsense, amma idan yana waya da V, ya ilahi, kunga Leo, V, Aunty's ɗinsa and daddynsa, idan yana waya da waɗan nan gabaɗaya shashasha yake zama, ba zaku taɓa zatan zai iya rike bindiga ba idan kuka gansa a yanayin soyayya, sai in kunga murɗewar jikin ne zai nuna maku alamar da jarumi kuke tare.

Jin ya sanya mata kuka yasa ta hakura da nata ta hau cewa. "To ka yi shiru ya isa haka"...... Make kafaɗa ya yi tamkar yana a gabanta, a shagwaɓe ya ce. "Ni in kina son in yi shiru kawai in ganki"...... Cikin zolaya ta ce. "To ka zo gidanmu yanzu".

Aikuwa bai sake yin magana ba ya katse kiran ƙid, ita ta zaci ma network ne ko katinsa ne ya kare. Miƙewa ta yi tare da ajiye wayar, ta shiga toilet. Ruwa ta watsa ta fito, nan ta isko su Arya a zazaune kowacce a kan gadonga. Dik suna rike da wayoyinsu, Angelina na kallon fina-finan batsa da ra saba, Manassa na yi wa Vash tsiya, dan ta yi kutse cikin kundin jami'an nasu, a nan ta sato number Vash, ta shigar wayarta tana mashi tsiya, bata faɗa mashi ita bace, ta ce mashi ai ita ba mutum bace, aljana ce, amma a cikin aljanun ma ita ma soja ce. Da farko ya ɗauka wasa take yi, sai ya yi iya yinsa ta faɗa mashi wacece ita amma taki.

Yanzu haka diramar da suke yi kenan, ta ce mashi ya yi kokari da ya iya shiga horon watanni biyar ɗin nan tin ciwon kafarsa bata gama warkewa ba. To da yake sau ɗaya kunga suna haɗu da ita a mission ɗinsu na farko, a ranar kuma kunga ta nuna mashi ita ba sa'ar yinsa bace, ƴar GAT take dole ya bata girma, shiyasa bai taɓa kawowa ransa cewa ita ɗin bace, yasan ma bata da numbersa.

Ya yi mamakin yadda tasan komai a kansa, ƴar banzar yarinya kuma a cikin kundinsa na form da ya cika lokacin shigarsa aiki ta sato bayanansa, amma take ta wana bawan ALLAH, yanzu tasa ya fara yarda aljanar gaske ce, dan tana faɗa mashi abubuwa na mamaki a kansa, dik abin da yake yi a cikin barrack ɗin sai ta faɗa mashi, kuma wani lokaci drone nasu Arya take turawa ta duba me yake yi, wani lokaci t fake da zuwa office na daddy ya leƙasa, shi kuwa yanzu ya gama saddakarwa da aljana ya yi gamo.

Yaran GAT akwai tsiya, ita kuma Angelina tana can tana iskancewarta ga can Unays yana ƙoƙarin macewa da tinaninta. Ita dai Arya hoton Leo take ta faman kallo a wayarta, a ranar da suka dawo sansaninsu ne ta dinga snapping ɗinsa ba tare da ya sani ba,wani lokaci yana zaune a bakin ruwa zata ɗaukesa bai sani ba, shi ne idan bata aikin komai sai ta zauna ta dinga kallo.

A kusa da Angelina V ta zauna tana faɗin. "Angelina my Romeo sun fito horo yau da yamma fa". Ta faɗa tana leƙo cikin wayar tata. Nan ta ga abin da take kallo, ai take ta kara matsawa suka fara kallo a tare, kan kace me V ta fara tsuma tana shiga yanayi, ita Angelina dama ta jima da shiga yanayin.

A haka Aunty Lisa ta shigo ta samesu, suna ganinta Angelina ta kashe wutar screen ɗin tare da miƙewa zaune tana wani yauƙi. V ce ta ce. "Aunty kayan nan sun maki kyau"..... Irin short jean and crop top ɗin nan ne take sanye da su, sun yi mata kyau ɗin kuwa sosai, sai ma da ta saki coily hairn nan nata irin na Noor, ta haɗu gaskiya iya haɗuwa.

Arya dai kallo É—aya ta yi mata ta É—auke kai tare da cigaba da abin da take yi. "V come". Aunty Lisa ta faÉ—a tana kallon Arya. Tana son taga yaran GAT dik sun rungumeta kamar tadda Angelina da Manassa suka yi, amma Arya da Manassa ta gagara samun wannan damar daga garesu, idan ta yi masu magana zasu amsa, baya ga haka basa karawa, idan sun fito bata yi masu magana ba kuma suma basa yi mata, haka suke.

Miƙewa V ta yi ta nufeta tana faɗin. "Aunty delirious zaki bani ne?". Hannunta kawai Aunty Lisa ta ja suka fita, kai tsaye main parko suka sauƙo, tana zuwa wajen dining ta ɗauki wani plate dake rufe ta bata. Karɓa V ta yi tana mamakin me a ciki, zata buɗe Aunty ta ce. "No, jeki kaiwa baƙon dake bq".

Bata kawo komai a ranta ba, da bathrobe a jikinta ta fito ta nufi bq. Tin a bakin kofa ta ji kirjinta na ɗan bugawa, a ranta ta ce. "Anya ba my Romeo bane wannan baƙo?". Tana tinanin tana shiga ciki. Excuse ta yi a parlon, babu kowa, sai ta nufi cikin room. Nan ma excuse ta yi, ba'ayin magana ba, tura kofar ta yi ta shiga. Tana shiga daga bayanta ta ji an rungumota, sumbata ya mannawa cheek ɗinta kafin ya ce. "Sai da kika sakani zuwa ko?".

Ai da sauri ta ajiye plate ɗin a ƙasa ta juyo garesa, da karfi ta rungumesa tare da cewa. "Missed you over my Romeo". Hannunta da ta ɗaura a saman kirjinsa ya kama, wani kyakkyawan diamond ring dake karamin yatsansa ya cire ya sanya mata a babban yatsanta na tsakiya.

Ai wani irin kara ta saki tare da kara daka tsalle ta rungumesa. Matseta a jikinsa ya yi, sai ya É—auketa cak yana juyi da ita a cikin É—akin, tana murmushi tamkar bakinta ba zai rufu ba. Kun san su idan namiji ya sanyawa mace zobe shikenan tazama matarsa, haka al'adarsu take, shiyasa take murnar tazama tasa, dama ya ce ba zasu tafi next Mission ba sai ya sanya mata zobe, Aunty Lisa ce ma ta bashi wannan shawara saboda tana ganin GAT ba zai yarda Noor ya auri V ba.
Chapter 116 · 0% Book details