← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 227

Sashe 34

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A firgice ta tashi tana kiran sunan Mammy ɗinta. Yana ganin haka ya juya ya nufi toilet, bai yi mata magana ba bai kuma sake kallon in da take ba. Jim kaɗan ya fito, zai nufi waje ta diro ƙasa da gudu, a gabansa ta tsaya tare da riko hannunsa dake cikin terrorist hand gloves, muryanta na rawa, jikinta na kerma sosai saboda tsoronsa, dan dole kowa ya tsorata da ganinsu, bama kaga face ɗinsu complete ba, sai dara-daran idanu jajir, dik yadda aka yi suna shan wasu kwayoyi!.

"Uncle, please take me to my mammy, I am scared of this house"...... Tana gama faɗar haka ta fashe da kuka gwanin ban tausayi. Kwace hannunsa ya yi ba tare da ya yi magana ba, ya raɓa gefenta zai wuce abinsa. Da sauri ta sake binsa, ta rikesa tana rokon ya kaita wajen Mammy ɗinta.

Sau biyu yana kwace kansa tana sake rikesa, a na uku kam sai ya damko wuyanta da karfi, ya zazzare jajaye idanunsa a kan face É—inta. Da muryansa da ba zaka iya gane wace iriya bace saboda nose mask ya ce. "Your mother is dead. Calm down, we don't want nonsense here!!". Yana faÉ—ar haka ya É—agata da wuyar da ya shake mata É—in ya jefa saman gado daga in da yake tsaye...... Mutanen da kan iya harbin mutum a cikin jirgin kasa mai tsananin gudu ai saiti a kansu kuma ba'a magana.

Yana jifa da ita bai sake kallon in da take ba ya yi wucewansa abinsa. Ji ta yi duniya ya tsaya mata cak, wai Mammynta ta mutu, sai ta ji kamar almara, shiru ta yi tana jin kanta a saman iska haka. Nan kuma ta fara tunano abubuwan da suka faru a gidansu, sai yanzu komai ya dawo cikin kanta, lokaci guda wasu zafafan hawaye suka fara wanke mata fuska, da gudu ta diro kasan bed É—in, dan yanzu ta tuna komai.

Bayansa ta bi ta fito waje. Babu kowa a parlon, ta manta da zaki a gidan, yau ko kasheta zai yi sai ya faÉ—a mata me dalilinsa na zuwa gidansu har ya ja aka kashe nata mammynta? Dan a yanzu tana É—auka FT ne wannan.

Shiga da fita ta fara yi a É—akunan da ta gani kawai, dik in da zata shiga bata ganin kowa a ciki, daga karshe ta isa wajen staircase É—an siririn nan, tana goge kwallah tana jan hanci. Ya manta bai naÉ—e staircase É—in ba. Haurawa sama ta yi, a nan ta ga ashe wata duniya ce guda a saman.

ÆŠakin da ta fara cin karo da shi a parlon saman ta shiga. Nan ta ga uban computers da ba zata iya kirgasu ba, dik kuma suna kukkunne, kayayyakin aikinsu ne cike a ciki. Zazzare voilet eyes É—inta a kan komai dake ciki ta fara yi, tana rarrabe idanunta. Can ta tsayar a kan wall na É—akin dake gefe, hotuna ne kala-kala a cike a bangon. Tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki haka ta nufi wajen.

A gaban hotunan ta tsaya tana kare masu kallo, wasu hotunan an sanya jar mark a kansu, da alama an kashe mutanen kenan. Can idanunta ya tsaya a kan wani hoto wanda aka sanyawa jar mark shi ma! Da sauri ta miƙa hannu zata ciri hoto sai kuma ta gagara. A fili ta ce. "For sure my mammy tana da irin wannan hoto! Tabbas tana da hoton mutumin nan! Waye shi? Meyasa hotonsa yake gidanmu kuma yake nan da jar mark? Kenan an kashesa?".

Tana neman waɗan nan amsoshi tin bata samu ba idanunta suka sauƙa a kan hoton mammy ɗinta cikin kayan aikinta, shi ma hoton an zana jar mark a jiki alamar ta mutu kenan! Babbar magana! Kenan dama su ne suka shirya kasheta ko ya ake ciki ne?. Nasan izuwa yanzu jama'a kanku ta kulle, ni ma dai kaina ya kulle, me alaƙarsu da Dr? Me alaƙa hoton wannan mutumi da Seraph ta gani yanzu da Mammy ɗinta? Dik yadda aka yi Dr tasan FT ko kuma shi ya santa, in ba haka ba ya aka yi yasan ita likita ce har ya je ta cecesa?.

Kai mu É—an ji labarin Dr ko da kaÉ—an ne, kila zamu É—an samu wani haske.

Dr ta jima tana rayuwa a wannan unguwa tare da abokan zamanta watau maƙotanta, daga ita sai ƴarta a gidansu, dik wanda ya san Dr zai ce maku ita kaɗai ya sani bata da mij ko dangii, ta reni Seraph cike da kulawa, tsantsar so da kuma kauna. Ita ke kaita school ta ɗaukota, ita take mata komai, ko wajen aiki idan zata je tare da ita take tafiya in ba school, bata yarda ta barwa kowa yarta ba.

Seraph yarinya ce mai natsuwa da kwazo, ta taso cikin shaukin son shuke-suken furanni da kiwon tsuntsaye game da ƙananan kifaye a cikin ruwa. Shiyasa gidansu yake cike da shuke-shuken flowers masu ƙayatarwa, a gefe guda Dr tai mata katon glass tana kiwon ƙananan kifaye, ga tsuntsayenta a gefe suma tana kiwo. Yarinyar akwai son wasa da ruwa, dan tsab zata shige cikin ruwan kifi suna wasa tare, bata da hayaniya kuma bata zama kusa da hayaniya.

One thing Dr ba musulma ba ce! Amma ba zaka taɓa gane hakan ba sai in faɗa maka aka yi, ta yi rayuwarta ne a tsakiyan musulmai, musulman ma ƴan Nigeria masu shegen shiga rai da iya mu'amala da mutane, shiyasa babu wani abu da musulmi zai yi wanda bata iya ba, harta Alqur'ani mai girma zata iya karanta kusan rabi, addu'oin musulmai kam babu wanda bata iya ba, kuma abin mamaki dik in ta shiga damuwa addu'ar musulmmai take karantawa, sai dai ALLAH bai nufeta da karɓar shahada ba har ta koma garesa.

Haka Seraph ta taso ba musulma ba, yarinyar ta taso bata san waye mahaifinta ba, kuma bata taɓa tambayar mahaifiyarta ina daddynta ba, bata damuwa da son sanin ina yake tin da mahaifiyarta tana ɗauke mata dik wata damuwa, ta cika rayuwarta da ƙauna da kulawa.

A haka suke rayuwarsu a wannan gida, Dr tana aiki ta rikesu da albashinta, ta shagwaɓa Seraph sosai. A takaice yadda suka rayu kenan, ainahin su waye su zai zo a gaba!...... My people na fara wani tinani! Ina daddyn Seraph? Meyasa kowa bai san shi ba? Dik daɗewar da ka yi da sanin Dr ba zaka taɓa sanin ina mahaifin yarinyar yake ba, wasu ma a gabansu Dr ta haifi yarinyar amma basu taɓa ganin ubant ba, sai suka ɗauka cikin shige ne kawai, kun san su ba wata matsala bace dan ka haifi ɗan shege, shi ne basu damu ba, amma wani lokaci suna tambayar kansu ya aka yi Dr take da kuɗi sosai fiye da kowa a unguwar? Albashinta bai yi kaɗan ya riketa ba kuwa?. To na fara wani tunani, anya kuwa FT ba shi ne mahaifin Seraph ba kuwa? Ku duba labarin da kyau! Ba'a taɓa ganin mahaifinta ba! Kila sai tsakan dare yake zuwa wajen Dr ko? Kuma ya ceci Seraph, sannan ya ce ayi mata komai da take so amma kada a bari ta sake kallonsa a duniya! Ku tina ya shiga gidan Dr kai tsaye, ya nuna mata sama kaman yasan nan ne ɗakin duba majinyatarta yake, ya fito da Seraph ta view, waye ya faɗa mashi akwai hanya ta wajen idan ba ya yi wa gidan farin sani ba?! A lokacin da ya je gidan ya nunawa Dr bindiga, ko kaɗan bata ji tsoron bindigar ba, hakan na nufin tasan bindiga sosai har bata tsoronsa! Wacece ita?! Kai ni ma da kaina kaina ya kulle, wannan hasashena ne na yi, kowa yana da damar yin nasa, alkalamina kawai shi yasan gaskiyar wannan sarkakiya!.

To a takaice kun ji labarin Seraph, mu je kan labarinmu.......... Ta jima sosai a tsaye a wajen tana karewa hotunan kallon ba tare da tasan kowa a ciki ba face hoton mamanta da wannan mutumi, can ta ga hoton wani dattijo a waje. Zazzaro voilet eyes ɗinta a kan hoton da kyau ta yi, lokaci guda ta ɗan ja baya, shiru ta yi tana ƙoƙarin tunano a ina tasan wannan mutumi?.

Daga bayanta ta ji alamar motsi tamkar ana zuwa, hakan yasa ta bazama da gudu ta nemo wajen ɓuya, bata son su ganta. A bayan wasu drawers na tarin documents ta ɓuya, tana leƙosu a gefe. Champion and Scorpion ne suka shigo.

A tsakiyar ɗakin suka tsaya, lokaci guda suka fara rarraba jajayen idanunsu a ɗakin, can ƙasa Champion ya ce. "Akwai wanda ya shigo room ɗin nan". Da turanci ya yi magana, hakan yasa Seraph yin gaggawar sanya hannu ta toshe ɗan bakinta tana mamakin yadda aka yi suka gane an shigo masu!.
Wucewa gaba Scorpion ya yi yana amsawa da. "I think so". A gaban wata computer ya tsaya tare da cewa. "Maybe wancan yarinyar ce, the reason why na ce zamanta a nan zai haifar mana da matsala kenan! Let Lion back zai É—auketa ne gaskiya ya kaita wani wajen ko boarding school".

Karisowa gaban nasa desktop computer Champion ya yi, suka shiga aikin da suka saba ba tare da ya sake yin magana ba, tamkar kurame a waje haka suke gudanar da rayuwansu, abin ma gwanin ban mamaki. Seraph na kallonsu suna ta fiffito da hotunan mutane a cikin computer suna sanya masu jar mark, wasu green, da alama list ɗin waɗan da zasu baƙunci lahira ake yi, aiki suke yi da jini a jika, kuma cikin zafa. Ai baki ta saki tana kallon Ikon God.

Bata ankara ba sai gani ta yi sun miƙe kusan a tare alamar sun gama abin da suke yi, suka nufi fita, Champion ne ya datse door ɗin har da key ta waje, wai dan kada ta sake shigo masu ɗaki, bai san da ita ma a ciki ya gargame ba. Suna fita ta fito ta nufi kofa da gudu, sai kuma me? Ji ta yi a rufe, hankalinta ne ya yi mummunar tashi, ta hau buga kofar da karfi, sai dai ina, soundproof ce door ɗin, harta bangon ɗakin, in dai mutum yana ta waje ba zai taɓa jin abin da na ciki yake faɗe ba, ko da zai yi ta ihu ne.
Chapter 34 · 0% Book details