← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 227

Sashe 152

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gently ya taƙo ya ƙariso, dik ɗakin natsuwa tsit suka yi, Manassa da Angelina suka zubawa Leo idanu, V na kife saman mattress ɗin har yanzu tana kuka. Hakiƙa Manassa ta ce Leo yana yi mata yanayi da Vash, musamman idan zai yi magana, sai ka zaci Vash ne yake motsa baki yake magana a wajen, dimple ɗinsu iri ɗaya, sharpe na eyes ɗinsu iri ɗaya, dan dai idanun Leo jade ne, kuma kamar sleeping eyes haka suke, na Vash kuma a waje suke gulu-gulu, amma shape ɗin ɗaya.

Saitin in da Arya take ya tsaya, slowly ya ɗan sunkuyo kanta kaɗan, zubawa dajin idanu ya yi for 2 mins, sai kuma ya ce. "Wannan ai hayaki ne". Ɗagowa da kallonta a kansa ta yi, sai taga ba ita yake kallo ba, shiru ya ɗan sake yi, can kuma ya kai hannunsa saman mouse ɗinta, ya ɗan yi ƙoƙarin yin gaba da drone ɗin, amma sai abin ya ci tura, ya yi iya yinsa abin yaki yiwa.

Slowly ya dawo da kallonsa a kan, while ta tsaye ƙashin wuyan nan nasa da ya fito sosai da kallo, kunga ya sunkuyo kanta ne, so tana iya kallon wuyansa sosai. Ganin ya dawo da kallonsa a kan face ɗinta wani irin rass gabanta ya faɗi, gagara kallon cikin idanunsa ta yi, cikin zafa ta yi ƙasa da idanunta.

"Meyasa drone É—in yaki yin gaba?". Ya faÉ—a in a cool way. Sai da ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, ta saita natsuwarta kafin ta ce. "Nima ban san meyasa ba, amma na fi tinanin akwai gagarumin abin da dake bayan dogayen bishiyun da hayakin ke fitowa daga wajen ne". Tana magana muryanta na É—an rawa, dan gabaÉ—aya ganinsa a dab ita ya rikitata, har take jin kamar numfashinta zai É—auke.

Daidai lokacin Zaynish ya shigo hannunsa rike da bindigarsa, yana sanye da army waterproof jacket, ya yi kyau matuƙa, a kusa da Leo ya ƙariso ya tsaya, zuba mashi idanu su Angelina suka yi, a dake ya sarawa Leo kafin ya rage tsawonsa, ta ɗan sunkuyo yana kallon wajen.

A daidai lokacin Noor ma ya shigo, dan jin Leo shiru. Yana shigowa V ta miƙe zaune tana kallonsa, shi kuwa tamkar bai san da zamanta a wajen ba, a ɗayan gefen Leo ya tsaya, ya zamana Arya da Leo suna Tsakiya. Zubawa hayakin wajen idanu suka yi. Hayaki ke bakinkirin yake tashi a tsakiyar dokar daji, gaba daji baya daji, waje mai sunkuru da cikowar itatuwa, waje ne da ba zaka taɓa yarda halittar ɗan adam tana rayuwa a wajen ba, akwai alamar ban tsoro a wajen, ga wasu manyan tsaunuka da koguna a wajen.

Noor ne ya ce. "Idan muka yi duba da tsuntsayen dake shawagi a sararin samaniyar kewayen hakan na nufin akwai tabkeken teku a wajen! Idan kuwa haka ne lallai ba shakka wannan teku dake kusa damu ta ratsa ta wajen"..

Jinjina kai Leo ya yi alamar haka ne, in a cool way sosai ya ce. "Idan kuwa akwai taku a wajen to tabbas akwai wutar lantarki a waje, dik yadda aka yi akwai igiyoyin wuta sosai a wajen wanda su ne suka haka drone ɗin nan wucewa, lallai muna buƙatar sanin menene a wajen cikin gaggawa, dan ga dikkan alamu gagarumin abu ne a wajen"....... Jinjina kai Zaynish da Noor suka yi, su kuwa matan gabansu ne ya yi mummunar faɗuwa jin batun da mazan ke tattaunawa.

Zaynish ya ce. "Idan muka yi duba da hayakin dake tashi ba hayaki ne na yau da kullum ba, lallai wannan hayaki gagarumin abu ne ake ƙonawa, ku yi duba da yadda yake tashi sama, a maimakon ya yi sama gabaɗaya, sai yana watsewa a cikin dajin, alamar abin da ake ƙonawa yana ɗauke da guba".

Kai suka jinjina alamar haka, ba shakka a zancen Zaynish..... Jama'a ku tafawa renon AZURE, sun san aiki!.

Leo ne ya ce. "Zaynish, Noor, ku kira Vash ina da magana daku a ɗaki"...... Da okey sir suka amsa, dawo da kallonsa a kan Arya ya yi. "Keep watching the place carefully, komai ƙanƙantar motsi ki sanar dani". Yana kai karshe ya miƙe daga kanta, cikin zafa ya nufi waje.

Bayansa ta bi da kallo, bata iya zare idanunta ba har sai da Zaynish ya zo wucewa, sannan ta É—auke kai. Sunkuyowa kanta Noor ya yi, cikin zola ya ce. "Brother É—ina yai maki kyau ne?".

Ɗago da kallonta a kansa ta yi, zata mashi tsiwa sai taga yai mata mugun kwarjini, haɗiye maganarta ta yi, ta ɗan yi ƙasa da ido. Ɗagowa yai zai nufi waje raunatacciyar muryar V ta katse shi da cewa. "My Romeo". Ai ƙara ɗaure fuska ya yi, ya fice da sauri ba tare da ya kalli in da take ba.

Yana fita V ta fashe da sabon kuka tare da kwantowa jikin Angelina tana ɗan shessheƙa, yau Romeo ya yi fushi mai zafi da ita. Ita kuwa Arya ta cigaba da kallon aikinta, Manassa da Angelina suka zauna yin gulmar Leo da Zaynish, ba su yi gulmar Noor ba saboda kada V ta sauke haushi a kansu. A yayin da a waje kuma ruwan sama na zuba tamkar da bakin kwarya, while sojojinsu guda 34 ciff suna tsaye cikin ruwan kewaye da tantunansu dan bada tsaro, sun sanya army waterproof jacket.

To mu leƙa sashen jigon labarinmu, mu ɗan duba su sister Maya sai mu sake dawowa, watakila kafin mu dawo sun gano wani motsi, su kuma lovers Romeo and Juliet kila zasu shirya.

-------------------------🔥

WS-HOSPITAL.🔥

Sister Maya ta bata labarin abin da Dr Kamal ya ce mata, sosai sister Zinta ta tayata murna, suka hau tsara yadda zasu kula da 3D har su samu soyayyarsu sosai!.... Bayan sun kammala hiran, sai suka tashi, suka shiga baiwa jariran madara wanda nurses suke haÉ—a masu suna ajiyewa kowani baby a jikin bed É—insa.

Suna baiwa yaran suna murmushi suna cigaba da baiwa junansu shawarin yadda zasu kara sace zuciyoyin 3D.

A ɗayan ɓangaren kuma, 3D tsaye a cikin SECTION E, a ɗakin Drugs factory ɗinsu. Dr James tsaye gaban wasu injuna, yana sanye da kayan ƙariya, yau nose mask dake face ɗinsu irin manyan nan ne masu ɗauke da oxygen, hakan zai sanya ba zasu shaƙi numfashin Drugs factory ɗin ba, wannan oxygen ya wadatar da su.

Dr Kamal ne ya ɗauko wannan jini dake bokiti, wanda suka sanya a freezer ta daskarar masu da shi, tin ɗazun dama suka ajiyesa a waje mai ɗumi, ya narke, a cikin wani tangameme faranti mai zurfi ya zuba jinin, wani karfe dake tsakiyar farantin ya fara jujjuyawa yana kwaɓa jinin, engine ne wajen.

Almost 10 mins, wannan inji yana juya jinin jaririn, sai Dr James ya ɗauko wani ainahin sinadari a cikin kwalba wanda ake cewa collagen peptides ya zuba a cikin jinin jaririn. Collagen peptides sinadari ne dake ƙarfafa fata, hana wrinkles, da inganta laushin fata.

Ya barshi kamar 10 mins injin na mixing É—insa, sannan ya sake É—auko ainahin sinadarin retinoic acid ya zuba a ciki, manyan kwalabe ne sosai fa yake É—aukowa, sinadarin retinoic acid yana sabunta fatar jiki, rage wrinkles, da hana tsufa.

Bayan ya zuba injin ta yi mixing like 10 mins sai ya sake ɗauko, hyaluronic acid shi ma ya zuba a ciki. Hyaluronic acid ainadarin ne dake hana bushewar fata, yana sa fata ta yi taushi da ƙyalli tamkar glass, bayan ya zuba dakamar 10 mins shima sai ya sake ɗauko kwalbar nicotinamide mononucleotide ya zuba a ciki.

nicotinamide mononucleotide sinadari ne dake sabunta kwayoyin halitta, watau cells da kuma kashe alamun tsufa. After 10 mins inji na mixing, suka haÉ—e da juna da jinin jaririn, sai ya sake É—auko resveratrol ya zuba a ciki.

resveratrol ana samun shi ne a cikin inabi, yana da tasiri wajen hana tsufa da kuma kare fata daga lalacewa, yana da matuƙar amfani a aikin 3D. Baya ga shi sai ya ɗauko coenzyme ya sake juyewa a ciki.

coenzyme yana da matukar amfani wajen inganta kuzari a cikin jiki da kuma hana lalacewar fata, bayan shi ya ɗauko kwalbar epidermal growth factor ya zuba a ciki. Epidermal growth factor sinadarin ne dake sabunta fata a gaggauce cikin ƙanƙanin lokaci ya warkar da raunuka da dik wani tabo, ki koma tamkar ƴar tsana, babu tabo ko kaɗan a jikinki.

Ya sake ɗauko stem cells watau ƙwayoyin halitta na asali ya zuba a ciki, in jin dai tana nan kunne tana mixing komai ta haɗesu su zame abu guda.

stem cells yana sabunta fata da gyaran jiki gabaÉ—aya, daga shi sai ya É—auko alpha lipoic acid ya sake zubawa, tsabar yadda injin ke mixing har wani hayaki-hayaki ne yake tashi daga cikin farantin, ga sinadaran da ake ta daddalawa a ciki. To alpha lipoic acid shi ma sinadarin ne dake rage kumburin fata da hana tsufa.

Daga shi sai ya ɗauko babbansu kuma na ƙarshensu watau glutathione ya zuba. Wannan sinadarin yana sa fata tayi haske sosai, yana cire wrinkles, komai yawan tamu-tamun tsufarki zai yi fata-fata da shi ya mai da skin ɗinki very smooth tamkar yarinyar ƴar 13 years, yana da karfi sosai, a take yake cire tamu-tamun, sannan ya fi sauran dik sabonta fata da hana shi tsufa sosai.

Yauwa kafin mu wuce gaba, dama na ce maku zan yi maku bayanin kan sinadaran dake cikin jinin jariri dan ku samu ƙarin ilmi kuma ku fahimta da kyau, dan haka kafin mu ce zuwa gaba ku ji me 3D zasu aikata, bari in baku wannan bayani.

A jinin jariri akwai sinadarin hematopoietic stem cells kamar da na faɗa a haba, to hematopoietic stem cells sinadarai ne dake samar da sabbin ƙwayoyin jini red & white blood cells. Ana amfani da su wajen warkar da cututtuka kamar ciwon sankara, sannan suna wanke tsoffin jini.

Na biyu a baya na ce a jinin jariri akwai sinadarin mesenchymal stem cells su kuma waɗannan ƙwayoyin halitta suna taimakawa wajen sabunta fata, ƙashi, da sauran sassan jiki, dik tsufarka zaka zama sabon matashi mai ji da karfi da lafiya tamkar ɗan yaro under age.
Chapter 152 · 0% Book details