← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 227

Sashe 53

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Minister na karɓar wannan cokali da aka fitar mashi daga kwali ya fara cin abinci kenan gubar ta ratsa jininsa, dan gubar tana da karfin gudu ne fiye da yadda kuke zato, cikin ƙanƙanin lokaci ta kewaye jininsa gabaɗaya har ya fasa ɓargon ƙashi, spoon biyu ya ci bai kai na uku ba ya fara aman jini. To kun ji yadda aka yi, shi kansa jami'in da ya yi serving abincin ya mutu, saboda ya tattaɓa sassar jikinsa da hannun, musamman fuska, ya shafi fuskansa, a take gubar ta huda jikinsa shi ma.

------------------------------

Kwanciyar 5 mins Champion ya yi sai ga guru ya dawo. Miƙewa Champion ɗin ya yi, ya dawo cikin toilet ɗin, a natse ya mayar da fankar ya ɗaure, suka wanke hannayensu a toilet ɗin tare da shiryawa suka fito waje. Reception suka nufa, card ɗin suka miƙa masu tare da cewa akwai sayayyar da zasu je su yi, zasu dawo nan da 30 mins.

Manager ya amsa da to tare da karɓar card ɗin. Daga nan suka wuce suka fita. Basu zame ko'ina ba sai gida, dan sun gama aikin da zasu yi a wannan waje, wasu manyan mutum suka shirya aiki a kansu. Kun san manyan mutane idan zasu yi meeting suna samun wajen da ba za'a taɓa zaton suna wajen bane, koda ace mutanen kirki ne mutanen, suna ɓadda kama dan meeting, yanzu kunga ai babu wanda zai zargi mutumin kwarai zuwa gidan karuwai! Kunga zasu samu damar yin meeting ɗinsu a natse.

Wasu manya ne su uku suke zaman tattaunawa kan yadda za'a kawo karshe IRON FIST, manyan ɗaya daga ciki ma babban soja ne, sai Minister na tsaro da wakilin shugaban ƙasa. Shi ne fa suka shiga ta cilling ɗin nan, a tab fankarsu na toilet ɗin ɗakin da suke meeting ɗin guru ya zuba acid a cikin wannan chemical ɗin, take hayaki kaɗan-kaɗan ya fara fita, shi ne ya dawo suka tafi, wannan hayaki nan da mintuna goma zata kewaye ɗakin nasu, kafin su farga ta kewayesu, in kuma suka shaƙa ko sau ɗaya ne zasu fara aman jini, daga nan minti uku ya yi yawa su wuce lahira.

Su guru suna kula da dik motsin gwamnati a kansu fiye da yadda gwamnatin ke nemansu, dik wani take-taken jami'ai a tafin hannunsu suke, dik wata ƙullah-ƙullah da shirya yadda za'a yakesu da ake yi suna sane, wannan meeting ɗin sun san da za'ayi shiyasa suka fito da shirin gamawa da su, wai a hakan gwamnatin ta yi dabara, sun zo gidan karuwai meeting, a tinaninsu ai babu wanda zai zaci suna wajen, har da ɓadda kama na sanya fuskan boge dik dan kada a ganesu, basu san a tafin hannun su Lion suke ba.

Shiyasa hankulansu a kwance da suka haÉ—a komai suka fita, nan da 10 mins dai gidan karuwan ma zai rikice.

A yayin da dik wannan yake faruwa ƙasa na can ta rikice, dik wani babba ana kiransa da ya koma gidansa yanzu, saboda IRIN FIST sun fita aiki. Suna ɗaukar lokaci kafin su fita aiki, idan kuma suka fita fa to a tashi ɗaya suke zubar da mutane 10 zuwa 15, in sun gama suka lafa zasu ɗauki lokaci basu yi wani aikin ba.

Kwance a gida suka isko Lion, ya yi wanka yana shirye cikin sleeping dress, dogon wando da riga mai dogon hannu saboda sanyi, yana kwance saman katafaren bed ɗinsh mai girman gaske wanda suke kwana su uku ɗin. Hannunsa rike da waya yana latsawa, while makeken TV dake manne a bangon room ɗin nasu na magana, labarai ne na yadda ƙasa ta rikice a ƙasa da mintina 10, an rasa babban IG na ƙasa, anrasa babban baƙonsu daga India, ga babban soja da minister ɗin tsaro da aka rasa, uwa uba wakilin shugaban ƙasa, kunga kuwa dole ƙasa ta rikice, dare ya zama tamkar rana, hankula sun tashi.

Abin da zai baku mamaki kuma dik wani Camera dake babban hanya su Lion suna da shi a computers ɗinsu, sun datsi camerorin gwamnati ba tare da sun sani ba, yanzu haka manyan ambulance sai gudun cetan rai suke yi a birnin, kuma suna ganin dik abin da yake faruwa, su kaɗai sun girgiza ƙasa bakiɗaya, suna nan cikin kwanciyar hankali su kuma. Kai su Lion fa basu fito ba sai da suka shirya!.

Suna shigowa guru ya nufi toilet dan yin wanka, Champion kuma ya nufo in da Lion yake kwance. Yana zuwa ya kwanta kusa da shi tare da ciro wayansa, a sanyaye ya ce. "Yanzu nike samun wannan sako ta email".

Ya faÉ—a yana nuna mashi hoton da ya gigitani, hoton daddyn Noor dake tsaye a bakin ruwa shi yake nunawa Lion.

Kallo ɗaya Lion ya yi wa hoton ya ɗauke kansa ba tare da ya yi magana ba. A dake Champion ya ce. "ARM company ne suka buƙaci da a kashe masu wannan mutumi, amma ni ina ganin wannan matsala ce tasu ta cikin gida, kasan kayan kamfanin BODY LUSH ta samu karɓuwa matuƙa a duniya, ta buge kowani product, shiyasa hankulan sauran Company ya tashi suke son a kawar masu da shi!"....... Kai daddyn Noor ɗin namu ake farauta fa! Ko da yake dama yadda kayan kamfaninsa ta yi suna dole ya samu makiya ta ko'ina bawan ALLAH.

Shiru wajen ya ɗan yi for almost 2 mins, in a cool way Lion ya ce. "Ba zamu yi wani aiki yanzu ba, sai nan da 2 years, sai duniya ta ɗan yi shiru an manta da labarinmu, dan haka ka mayar masu da aikinsu"........ Sanin cewa basa magana biyu yasa Champion ya yi cancel wannan aiki, ya mayar da saƙon cewa ba su da lokaci yanzu, daga nan ya toshe wannan email ɗin nasu, dik da cewa su ba'a isa a bibiyi email ɗinsu ba saboda mayun computer ne su, amma suna toshewa time to time saboda tsaro.

Shiru suka kwanta kowa yana latsa wayansa, gabaɗaya hankalin Champion ya koma kan tinanin Seraph, ya fara kewanta, ya kwana biyu bai je ba. While shi kuma Lion ba zaka taɓa sanin a wani hali ma yake ciki ba, ga shi dai yana ta latsa waya.

A haka guru ya fito sanye da bathrobe fara tas a jikinsa, a tsakiyar room ɗin ya tsaya yana ƙoƙarin goge gashin kansa da karamar towel fara dake hannunsa. Miƙewa Champion ya yi ya sauƙo ƙasa, toilet ɗin ya shige dan yin wanka shi ma.

Ganin Lion ya kura mashi idanu yasa guru cewa. "Ya dai my guy? Na maka kyau ne yau kuma?"...... Hararansa Lion ya yi ba tare da ya yi magana ba, kuma bai É—auke kallonsa ba. "Wai ka kyasa ne ka biya sadaki?". Guru ya faÉ—a cike da iskanci da tsiya a maganar tasa.

Wani irin mugun kallo Lion ya dallah mashi bai dai ce komai ba, kuma babu alamar zai yi magana....... Towel dake hannunsa ya jefawa Lion a kan fuska, ya nufi gaban closet É—insu yana faÉ—in. "Idan ranka ya biya ka faÉ—a mun".

Intently Lion ya same towel É—in daga face É—insa tare da cigaba da kallon guru ta glass wall da ya raba room É—in nasu da wajen closet É—insu, babu dai alamar zai yi magana.

Shiru É—akin ya yi, jim kaÉ—an guru ya fito sanye da sleeping dress irin na jikin Lion É—in, sai tashin kamshi yake yi, kai tsaye ya nufo bed ya zo ya kwanta tare da jawo wayarsa dake gefen Lion É—in. Sai a lokacin Lion ya É—auke kallonsa daga kan guru ya mayar kan Champion da ya fito yanzu, shi ma yana sanye da bathrobe fari tas, hannunsa rike da towel yana goge gashin kansa.

Wai kun san wani abin mamaki da su Lion ne? Tsananin son juna suke yi, ba zasu iya juran rasa mutum É—aya daga cikinsu ba, amma kuma su sun iya raba mutane da Æ´an uwansu, a lokacin da Lion bashi da lafiya hauka ne kawai guru da Champion basu yi ba, basa iya juran ko ciwo É—ayansu ya ji, kuma abokai ne fa kawai, sai dai abotarsu ta zarce kawai! Sun zama tamkar jinin jikin juna.

(Su waye suka ga trailer ɗin labarin nan da na saki kafin fara posting ɗinsa? Kun tuna na ce maku abokai da ba'a taɓa ganin irin abotarsu ba?)

Champion bai lura da Lion na kallonsa ba, ya wuce ya shirya cikin irin kayan jikinsu, sannan ya dawo in da suke. Yana isowa wajen ya ɗauki remote ya kashe Tv dake magana. A tare guru da Lion suka miƙe. Ƙasa suka sauƙo, jerawa suka yi izuwa parlo dan yin dinner. Tamkar ba kisa suka yi ba fa, suka ci abincinsu a natse, babu mai magana a cikinsu kamar kurame. Bayan sun kammala suka miƙe sai ɗakin da zakinsu yake a kwance.

Sai da suka duba lafiyansa sannan suka wuce zuwa room nasu, suka yi amfani da light control suka kashe wutar gidan, sannan suka kwanta. Asuba ta gari.

------------------------🔥

STAR LADY

Kwance take a saman bed a room É—insu, yanzu ba jimawa suka dawo daga class, da yake suna exams ne sai suke tashi da wuri. Ta afka duniyar tinani da damuwar sun kusa yin hutu, shikenan zata rabu da Rimsha, za kuma ta koma wannan kuntataccen gida da Champion yake kaita ita kaÉ—ai tana rayuwa kamar mayya, ta tsani a yi hutu wlh.

Shafa fuskanta Rimsha da ta shigo yanzu ta yi, a ɗan firgice ta miƙe zaune, ganin Rimsha yasa ta saki ƙayataccen murmushin da ya kara fito da tsantsar kyanta, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Sis ina kika je?"........ Rimsha dake zama a gefenta ne ta amsa da. "Tinanin me kike yi ke kuma?"....... "Tinanin ankusa hutu zamu rabu".

Ajiyar zuciya Rimsha ta sauƙe, idan akwai wacce bata so a yi hutu to tana ganin a biyo bayanta, ta tsani komawa gidansu wajen waɗan nan mugayen Uncles ɗin nata. Shiru ne ya ɗan biyo baya kafin Rimsha ta katse masu shirun da cewa. "Ina zanenki yake?".
Chapter 53 · 0% Book details