← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 227

Sashe 11

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kakkausar murya ya ce. "Zaku rarrafa cikin ruwan nan ne a kasa da minti biyu ku fita ta gefen can, kada wanda ya bari kansa ya taɓa igoyiyin nan, idan kanka ya taɓasu tabbas zaka sako ne daga farko, kuma kada wanda ya bari kansa ya taɓa ruwan!!". TOH FAH!

Ai dukkansu bin ruwan da kallo suka yi, yana da tsawon taku 30, sannan suka ga igiyoyin da aka ce kada kansu ya taɓa, lallai aiki ne babba. UHM BASU SAN AIKI BABBA MA YANA GABA BA, AI YANZU MATAKIN PRIMARY SUKE, SAI GABA.

Wasu kuma takaici suke yi na fararen t-shirt dake jikinsu, yanzu shikenan rigarsu ya tashi a aiki kenan? Ga shi basu ga alamar fuska a wajen Captain ba bare su ce ya yi hakuri ya bari sai gobe zasu shiga kada kayansu ya ɓaci, gobe sai su sako bakaken kaya, ba hali, dole suka ɗaura ɗamara, sun fi su 100 a wajen, amma mutane uku ne suka fara faɗawa cikin ruwan kai tsaye, ciki harda NIRASH wanda shi ne farkon faɗawa bayan ya ajiye littafin da yake karantawa ɗazun da watch dake ɗaure a hannunsa a gefe kusa da Captain, ya faɗa cikin ruwa ya fara rarrrafawa da gwiwowinsa.

Zaysh ya rufa mashi baya, sai wani kyakkyawan chocolate guy dake tsaye a kusa da su shi ma ya faÉ—a.

Shi kansa VASH a wannan karon tsayawa ya yi yana kallon Noor cike da tashin hankali, dan wlh bai kawo a ransa zasu shiga ruwa ba, ga balain sanyi da ake yi.

Muryar Captain ce ta karaɗe kunnuwansu da cewa. "Mintuna biyu gareku, dik wanda minti biyu ta gota bai fito ba sai ya sake farowa, zai yi ta farowa har sai ya fito a mintuna biyu ko ƙasa da hakan"...... Ai tin kafin ya rufe baki mutasa sun kai 30 suka faffaɗa, still dai Noor and VASH suna tsaye, saboda sun gaji.

ÆŠaya bayan É—aya matasan nan kaf suka faÉ—a saura su biyu, suka ci minti É—aya a tsaye a wajen, sai da sukaga babu wani sarki sai ALLAH sannan suka faÉ—a cikin ruwan suna aikin haÉ—e rai. Sai dai ko tsakiya basu kai ba mintuna biyu suka cika, Captain ya yi wa waÉ—an da suka fito kafin mintuna biyu alama da su ja baya, su sun tsira.

Waɗan da basu fito ba har mintuna biyu ya cika suna fitowa aka ce su sake farawa, tamkar zasu yi kuka haka suka sake komawa, a karo na biyu ma Noor and VASH basu fito a mintina biyun ba, kun ga rarrafe ba kamar tafiya a ƙafa bane.
Hakan yasa aka sake mayar da su, da dai VASH yaga babu mai iya kwatarsa a wannan gida, Mama no dey baba no dey fa sai ya zage a karo na uku ya fito a ƙasa da mintina biyu. Shi kuma Noor tin yana da sauran karfi har ya gaza, amma bai iya fita a kasa da mintuna biyu ba.

A tinaninsa taimaka mashi za'ayi idan ya gaza, ina ai sai ya ga akasin haka, dan a horon soja ba'a taimako, shiyasa zaku ga suna tashi a marasa tausayi, to ba'a gwada masu tausayi da imani ba a yayin horo, ubansu suke ci har zuƙatansu su bushe ba kaɗan ba.

Ai Noor bai tashi sanin a GIDAN SOJA GIDAN WUTA yake ba sai da ya ji saukar wannan uwar kwandorom ɗin takalman Captain a tsakiyar bayansa, ya takashi da karfi a cikin ruwan yana daka mashi tsawan ya yi sauri, dan kowa ya fita saura shi kaɗai, yana ɓata masu lokaci.
Dole tasa Noor ya cije, yana zafafan hawaye ya fara iyo a cikin ruwan nan, da kyar da suÉ—in goshi, ya maimaita sama da sau biyar, sannan ya iya fitowa a mintuna biyu daidai.

Da ya fito a tinaninsa barinsa zasu yi ya huta, sai fa ya ga akasin haka, domin kuwa sake zangon tafiya suka fara yi dan komawa ainahin cikin Barrack in da suka fito kenan, a lokacin karfe 7 daidai ta buga, sun É—auki awa É—aya da rabi a wannan waje kenan suna horo.

Da kyar Noor ya iya kai labari, ya ja kafafunsa suka karisa wajen, suna zuwa suka tsaitsaya a wannan katan fili da suka tsaya bayan fitowarsu daga É—akunansu, a nan ne Captain ya ce. "Mintuna 30 gareku na yin wanka da canza kaya, 7:30 daidai zaku fara breakfast, zuwa 8 dole kun gama, 30 mins na É—an hutawa dan kuna sabbin zuwa, 8:30 zaku fara gwada horon hannun zuwa 11 zaku shiga class! Lokacinku ya fara daga yanzu!". With harsh voice ya faÉ—a.

Ai da gudu suka fara watsewa, ji kake dam! Dam! Dam! Suna taka kasa, dik suka watse ya rage Noor da baya iya tafiya da kafafunsa sosai. Da gudu VASH ya dawo baya ya zo ya taimaka mashi suka koma room É—insu.

Da yake suna girmama lokacin, dayawansu cikin kasa da mintuna 15 suka kammala shiri except Noor da suna shiga É—aki ma bajewa ya yi a kasa yana jan doguwar numfashi game da saukewa a hankali-hankali, har su VASH suka gama wanka, dik suka shirya cikin wandunan jeans and t-shirts masu balain kyau shi yana zaune.

Vash ne ya ce. "Noor 30 mins garemu fa, kasan dokoki da tsare-tsaren gidan nan, ba'a kauce lokaci!".... Yana kwaɓe fuska ya ce. "Ni babu in da zan sake zuwa!"........ "Noor baka son lafiyar jikinka na lura, gara maka fa ka tashi, dan wlh in muka gama breakfast ko baka yi ba lokacin horo dole Captain ya fito da kai da duka".

Noor zai sake yin magana, Leo ya riga shi da cewa. "Make sure you clean this floor before I come back". Maganansa ta farko a garesu keman. A natse ya yi magana, yana da murya mai sanyi da kaifi ga balain daÉ—in saurara, yana gama faÉ—a bai jira amsarsu ba, infact bai É—aga ido ya kalli in da suke ba ya sa kai ya wuce da sauri abinsa, dan ya kammala shirinsa cikin wasu zafafan kayan dake nuna shi É—an royal family ne, kansa sanye da army p-cap........ Yana yawan sanya p-cap ne saboda baya son kallo, in dai zai bar gashin kansa a buÉ—e sai an dinga kallonsa ko ina ya juya, shiyasa yake yawan rufewa, bugu da kari p-cap É—in na É—an hana ganin face É—insa sosai, ya huta da idanun jama'a a kansa, ga kuma kitso a kansa da ya yi, ai dole ayi ta kallonsa, kyan gashi kyan kitso da kyan halitta. Say Masha ALLAH.

Bayansa suka bi da kallo. ZAYSH ne ya ce. "This guy acting like he's our parents, ji yadda yake bamu umarni". ......... VASH ne ya ce. "I don't know why I like his character".......... "Same to me bro, and I like his sharp voice, ji yadda ya yi magana yanzu fa, like wow". Noor ya faɗa yana cigaba da kwaɓe fuska.

"Yeah, yana da tsari mai kyau for his life, but why baya mana magana bayan we're together in the same room?". Cewar ZAYSH da abin ke bawa haushi..... "That's why a like his style, he don't want to talk, and hakan girmama kai ne, amma dai yakamata ace yana yi mana magana like friends tinda we're the same now, and kuma ba wani finmu shekaru ya yi ba fa". Cewar VASH.

"We lost 5 mins again, ba lokacin wasa bane yanzu, let's go guys". Zaysh ne ya faɗa. Da sauri Vash ya ce. "Noor I don't want to see you in this situation, please tashi ka yi wanka, kaga dattin jikinka ya ɓata mana floor har wannan mai fuska irin na gangsters ɗin yana baka command na ka gyara masa waje ko?".

"Ai ba zan gyara ba, da wani nuna isa da iyayin nan nasa". Noor ya faɗa yana ɗaure fuska kafin ya daure ya miƙe, da kyar yana tangaɗi ya afka cikin toilet.

"Bari in taimaka mashi in gyara wajen". Cewar Vash yaro mai saukin kai, kuma iyayensa manyan kai ne, amma yana da sauki sosai. Da sauri Zaysh ya ce. "Don't do that, ku bar wajen haka in ga uban me wancan É—an rainin hankalin zai yi idan ya dawo, ba ya wani ce mu gyara mashi waje ba? To ku bari mu ga me zai iya".

ÆŠan zazzaro idanu Vash ya yi. "But not for him kawai ai, cleaning the place is for our healthy all"........ "I know that, but for now ka bari mu ga gudun ruwan shi, me zai iya yi mana, kasan fa idan bamu gwada mashi muma guraye bane ba zamu zauna lafiya da shi ba, yana wani É—aga mana kai like ya fimu ne, idan ya yi wasa ma muka gama horon nan result ya fito a karkashinmu zai yi aiki".

Noor da ya fito yanzu ɗaure da towel ne ya jingina da jikin bangon wajen toilet ɗin tare da cewa. "Da kuwa ya gane kuransa, ni dan in bashi wahala har takalmata zai rinƙa wankewa".

"Zaysh, Noor kuna da matsala, idan aka biye ta ku zamu ɓata breakfast time ɗinmu a nan". Vash ya faɗa....... Karisowa ciki Noor ya yi, da sauri ya hau shiryawa yana tinanin yadda zai rinƙa gujewa horon nan. Waje Zaynash ya nufa yana jin haushin Leo a ransa, saboda yadda yake nuna masu shariya.

Hall na cin abincinsu ya nufa, yadda tsarin hall ɗin yake wajen cin abinci ne da kowani table yake ɗauƙe da four chairs, kuma kowani table da number ɗakin mutane a jiki, kamar su Leo da ɗakinsu yake room number 1, to haka table ɗinsu ma yake da number 1 a jiki, su huɗu ne a ɗakin kazalika chairs huɗu ne a wajen.
Chapter 11 · 0% Book details