← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 227

Sashe 178

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani haɗaɗɗen murmushi ta saki wanda ya fito da dimple ɗinta sosai, har wushiryar dake tsakanin fararen hakwaranta tas ya bayyana. "Daddy kana feeling love a kaina kamar yadda nike ji a kanka dama?"....... Kai ya jinjina mata alamar. Da sauri ta dawo kusa da shi, ta haɗe hannayenta ta kama kumatunta, cikin shagwaɓa ta ce. "Daddy, let feel our love".

"Sure?"...... Kai ta jinjina. "Let feel it daddy"....... Ɗan nisawa ya yi tare da ƙara ƙanƙame pillow ɗin a kirjinsa, kamar mai raɗa ya ce. "Give me some love words that will make my sleep more nice, idan na tashi zamu cigaba da hira, now I'm feeling sleeping, jiya ban yi barcin dare sosai ba".

Kai ta jinjina tare da matsar da face ɗinta dab shi........ "Love you more my gentle chaos, a dik lokacin da ka ji kamar kana kaɗaici, remember that you have a beautiful wife, sister, baby, Cherry, beside you, ina tare da kai to make your smile more beauty, make your heart more peaceful, make your body more........". Fasa ƙarisawa ta yi, saboda tai mashi alƙawarin ba zata sake yin maganar da bata dace ba. To

Tin da ta fara magana ya tsare ɗan bakinta da kallo, zuciyansa na ingiza shi da ya yi kissing ɗinta kawai, ya rabb, shi kaɗai yasan me yake ji a kanta, kome take yi ƙara kyau take yi, kome ta yi burge zuciyansa take yi, shirmenta abin so ne a garesa, kalamanta abin so ne a garesa, soyayyarta ya zame mashi jinin jiki.

Matsawa ta yi ta ɗan sumbaci cheek ɗinsa tana faɗin. "Sleep well, make sure that i come into your dreams as your wife, ina kwance a saman kirjinka ina......". Still kame bakinta ta yi, ta fasa ƙarisa maganar. Slowly ya lumshe idanunsa yana jin wani irin daɗi a ransa, lallai Seraphina ta fara natsuwa, sau uku kenan yanzu tana kame bakinta taki ƙarisa magana saboda ya hanata, kai lallai ya ji daɗi sosai yau.

Ganin ya lumshe idanu ne yasa ta tsaresa da kallo tana jin sabon sonsa yana shigarta. After like 5 mins slowly ya waro idanunsa kai tsaye a kan face É—inta, in a sleeping voice ya ce. "Stop looking at me Cherry".

One side smilling ta saki kafin ta ce. "Daddy ni da fuskan mijina zaka ce in daina kallonka?". Tana turo baki ta kai karshe. Hannunsa É—aya ya É—aura a kan shafaffen cikinsa dake da guraye saboda gym da yake yi, in a sleeping voice ya sake cewa. "My cherry, I'm feeling hungry sosai, ban yi breakfast ba, dinner É—in jiya ma ban ci ba". Yana magana yana lumshe idanunsa, watau sai da ya zo wajenta ya samu natsuwar iya gane ashe yana jin yunwa.

Da sauri ta ɗaura hannunta a saman cikin nasa, daidai in da hannunsa yake, sai ta ce. "Daddy tashi in yi feeding ɗinka, bari in je in haɗa maka abinci a kitchen". Ta faɗa tare da yunkurawa zata miƙe, da alamar tausaya mashi sosai a kan fuskanta. Slowly ya riko hannunta cikin nasa, ɗan jawota ya yi, sai ta tafi gabaɗaya ta faɗo kansa, fuskokinsu yana saitin na juna, in a low way sosai ya ce. "Let me sleep first, idan na farka sai ki bani abincin a baki kin ji?". Kai ta jinjina alamar to ta gagara yin magana, saboda yadda ta kalli kwayar idanunsa dab ita ya rikita zuciyarta.

Slowly ya saketa game da lumshe idanunsa, kafin wani É—an lokaci ya yi barcin gaske mai daÉ—in da ya jima bai yi irinsa ba. Shiru ta zauna tana ta faman kallonsa, bata son matsawa daga kusa da shi ko kaÉ—an, tana ganin kamar rabasu za'ayi idan ta matsa, har da kwanciyar ruf da ciki, ta É—aura kanta a saman kirjinsa, tana kallon face É—insa, a hankali barci ya É—auketa ita ma.

CRYSTAL PALACE, idan na kira sunan CRYSTAL PALACE a yayin da muke cikin CRYSTAL PALACE ɗin muna labari to ina nufin zuciyar CRYSTAL PALACE gabaɗaya ne, watau gidan MUHAMMAD HAIZA'AN, gidansa ne zuciyar CRYSTAL PALACE, gidan da ya fita daban a tsarin ginin cikin CRYSTAL PALACE ɗin, gidan da aka ware a waje daban, yana gefe can, wani shinfiɗaɗɗen titi da aka shinfiɗa wanda ya miƙe har cikin gidan kawai abin kallo ne, kun san dukiya tai kuka ba kaɗan ba, ya rabb, tin daga farkon titin nan jiga-jigan jami'an SSO ne suke shawagi, ko tsuntsuwa basa bari ta gifta ta sararin samaniyar gidan Haiza'an, lallai na shaida dik wani karfin iko ya kare a wannan waje.

Zaku rantse da ALLAH dik jami'an dake US aka zuba a wannan gidan, wasu irin guards waɗan da ko fuskansu baka iya gani face idanunsu dake rikitar da zuciyar bawa su ke gadin gidan, ya kuke tinanin san da yake raye kenan? Wai a haka ya rasu ne wannan karfin ikon! Ya ALLAH. To mu yi tattaki zuwa cikin gidan dan mu ga meke going a ciki, ya tsarin gidan yake tin da na ce ya fita daban da tsarin sauran gine-ginen dake cikin CRYSTAL PALACE ɗin. Jama'a ban taɓa tinanin za'a samu gidan da zai fi Black Tiger empire haɗuwa ba, sai ga CRYSTAL PALACE da kanta, ga kuma uwa uba zuciyar CRYSTAL PALACE watau gidan Haiza'an, ya ALLAH kai mana arziki mai albarka kawai.

Siffar ginin gidan ya kasance irin ginin mediterranean ɗin nan ne ta gefe-gefe, daga ta gaban gidan kuwa zallar glass ne, girman gidan ya fi fili flot 20, saɓanin benayen CRYSTAL PALACE shi wannan gida yana da gate, an kewayesa ne, sai kun wuci gate uku manya-manyan masu cike da tsaro na ban mamaki kafin ku ƙarisa cikin gidan, sannan shi wannan hawa uku ne kawai.

A gefe guda harabar gidan ga tampatsetsen lambu mai ɗauke da ƙananan arche, ƙananan ƙoramu ne da aka yi su dan ƙawata lambun, ga wasu irin fitillu da aka ƙawata lambun wanda ko dare ne zaku zaci rana ne saboda haskensu da ƙawarsu, uwa uba lambun da glass wall aka kewayesa, daga waje kana iya hango haɗuwarsa ta ciki, ya ALLAH, ga wasu kifaye orange and red da aka zuba cikin tampatsetsen glass suna ta yawo cikin ruwa, shi ma ya ƙara ƙawata lambun matuƙa, ga wasu flowers masu mugun kyau da ɗaukar hankali, a bakin kofar lambun daga gefe an yi wasu flower da aka shukasu aka yi siffar sunan HAIZA'AN'S GARDEN da su, jama'a wlh lambun nan ya haɗu fiye da yadda kuke hasashensa a ranku, kuɗin da aka narƙa a wannan waje, kai kuɗin mahaikatan dake gyran lambum nan kawai jarin wani ɗan siyasa ne a Avaris!.

A budget ake cire kuÉ—in masu aikin gyaran gidan Haiza'an, a shekara ake lissafi a cire kuÉ—in masu gyaran gidan, akwai mata akwai maza, kowa da aikinsa, kullum na ALLAH sai sun share ko'ina sun gyara tamkar yana raye............ Jama'a baku tunanin bayan mutuwar daddy Haiza'an akwai abin da ya faru kuwa?.

A tsakiyar tampatsetsen harabar gidan akwai wani waterfall wall, architecture design of gunking zaki ne dake faman fesa ruwa daga bakinsa, ya wage baki sosai ruwa na zuba ta bakin nasa, a ƙasa an yi mashi round tamkar rijiya ruwan da yake zubarwa tana taruwa a wajen, daga can ƙasa akwai hanyar da ruwan yake sake komawa bakin zakin, ba karamin ƙara gyara gidan wannan design ɗin ya yi ba. Ga wasu shuke-shuken flowers a gefe guda da suka ƙarawa gidan haɗuwa.

A gefen dama akwai guest suite, ɗakunan baki guda biyu tare da toilet da kayan more rayuwa a ciki. A gefen lambu akwai tangamemen garage na parkin motocin wanda tsab zai iya ɗauke motoci 30 ciff, gate na shiga garage ɗin automatic ne, da kansa yake buɗewa da rufewa, har yau akwai jiga-jigan motocin daddy guda biyar ciff a fake, tsadaddun motoci ne da suka haɗa da Maserati Levante Trofeo, Rolls-Royce Cullinan, Bugatti Chiron Super Sport, Mercedes-AMG G 63 sai wata mota mai tuƙa ƙanta, motocin dik an rufesu da car cover.

Sannan akwai katafaren swimming pool a ta gefen ginin ba harabar gidan ba, a ɗan gefe aka ƙawata shi, yana ɗauke da sky blue ruwa mai balain kyau da ɗaukar hankali. A gefen pool akwai glass wall na tennis, basketball, filin wasanni na tennis da basketball har ma da football.

A gaban zakin wani tampatsetsen baranda ne a wajen wanda babban parlo door yake kansa. Kai mu haura ground floor dan wlh ƙawartuwar harabar gidan nan ya zarce in iya faɗa maku shi lokaci guda, sai a hankali.

Mu lula grand entrance hall, babban kofar shiga ground floor, kofar ya haɗu, ga kakkafar tsaro da idan ba mamallakan ginin ba babu wanda ya isa ƙetarawa izuwa ciki, ya fi kofofin CRYSTAL PALACE tsaro da amfani da kimiyar zamani.

Kana shiga kofar akwai wani dogon corridor mai kyau wanda yake ɗauke da fitilar chandeliers a tsakiyar corridor ɗin daga sama, duk tsawon corridor din nan sai da chandeliers ɗin nan ya kusa kai ƙasa saboda tsawo da haɗuwarsa.

Idan ka wuce corridor ɗin sai haɗaɗen automatic door, kana buɗesa da wani katafaren living room zaka fara cin karo, haɗuwar parlon nan ba zai faɗu ba, kusan za'a ce five in one ne parlon, dan haɗaɗɗun luntsuma-luntsumar sofa set kala biyar ne a cikin parlon, kowani set ya haɗu matuƙa.

A cikin parlon akwai door da zai sadaku da tamgamemen mediterranean kitchen, kitchen ne mai siffa ra gargajiya, amma su gas na zamani ne a cikinsa, da alama daddy yana son gargajiya, dan a waje harahar gidan cikin wannan lambu akwai hut da aka ƙawata har guda uku, sai dai bukkar ba'a kewayesu da komai ba face glass, samansu kuma exactly bukar da ake yi a ƙauye, cikin bukkokin kuma haɗaɗu kujeru ne na zama dan shaƙatawa, to da alama yana ɗan son gargajiya.

Iya wannan kitchen ɗin ne a ground floor, sai wani haɗaɗɗen butterfly stair case da ya yi sama izuwa first floor, nan ma akwai babban parlo two in one, sai master suite, katafaren ɗaki mai ɗauke da babban balcony da ke kallon wajen harabar gidan da sauran cikin CRYSTAL PALACE ɗin. Sai katafaren toilet mai ƙunshe da jacuzzi da shower mai ban sha'awa.
Chapter 178 · 0% Book details