← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 227

Sashe 58

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Leo ya juyar da kallonsa a kansu, ai yana ganin sune ya nufesu a natse. Champion ya fara hugging yana faÉ—in. "I missed you over my brother"......... "Miss you too our Leo". Champion ya faÉ—a cike da kauna. Shi Leo ya É—auka su Champion aminan yayansa ne kawai, bai san sun wuci nan ba.

Sake Champion ya yi ya rungumi guru dake ta faman kallon Lion, magana da ido suke yi, kun san sun kware. Bayan sun raba jiki da juna Leo ya ce. "Na ji daÉ—in ganinku brothers, dama ina son ku tayani duba mission É—in nan namu, brothers i want to to help me about this IRON FIST, na kasa samun bayanai ko kaÉ—an ne a kansu".

Kallon Lion Champion and guru suka yi, da ido suka yi magana, Lion ya ce masu su kyalesa da shi. "Let's go". Lion ya faɗa yana kallon Leo dake faman jiran amsar su Champion. "Bro ina zamu je?". Shiru Lion bai sake yin magana ba, sai dai ya wuce gaba, da sauri Leo ya rufa mashi baya, Champion and guru suka dawo wajen bed suka zauna, Champion ya jawo laptop na Leo dan su ga irin aikin da yake ƙoƙarin yi a kansu.

Shi kuwa Leo yana fitowa suka ci karo da wannan ƙosasshen heron nasu, da gudun gaske zakin ya yi kansa alamar oyoyo. Rungume juna suka yi saura kaɗan zakin ya kada shi, a hankali ya fara shafa jikinsa har izuwa gefen wuyansa kafin ya sakesa tare da yi mashi nuni da ɗakin da su guru suke yana faɗa mashi ya je can....... Da gudu zakin ya nufi wajen, shi kuma Leo ya bi bayan yayansa suka yi waje.

My people me kuke tinani wai? Akwai kallo fa. Ashe dole su Abba da su Faryan su ji shakkar Dr Aryan, member na IRON FIST wasa ne? Champion ake magana ba. Tab.

-------------------------- AZURE.

Sanye suke da sportswear ɗinsu, guntun wando zuwa cinyoyinsu da riga mai karamin hannu, Arya na rike da stick na snooker tana tsaye kusa da wajen buga snooker tasu, while Angelina na rike da basken ball ɗinsu tana kallon Manassa dake ƙoƙarin ɗaure igiyar takalmarta. V na rike da nata sandar snooker tana kallon balls ɗin, tinanin yadda zata buga ta cinye Arya take yi, while Arya na jiranta ta buga, su Manassa kuma suna buga basket ball kenan, daddy na office, sojojin dake tsaron wajen sai satar kallonsu ta ƙasar ido suke yi, yara sun fara zama ƴan'mata, 15 years suke da yanzu, matasan tula-tulansu sun ƙara girma da cika, hips ɗinsu a cike dam, musamman V da ta fita daban.

Sojojin nan tin da su ba duwatsu bane sai haÉ—iyar yawu wuke yi, bare ma idan suka ga V da Arya, sun fi sauran farin jini da shiga rai. Wata Æ´ar aikinsu ne ta shigo wajen da gudu tana faÉ—in. "Aunty V wayarki tin É—azun ake ta kira".

Da sauri V ta fasa buga balls ɗin, jikinta na rawa ta karɓi wayar tare da dubawa. Wanda take zaton ne dai ya kira, dan ga shi number US ce, dama ya ce mata idan ya je gida ita zai fara kira da numbersa na can. Jikinta har yana ɓari wajen ƙoƙarin yin picking up Arya ta kwace wayar tare da cewa. "Zo mu karisa game ɗin nan kafin ki tsaya shiriritarki".

Haba kuka ta fasawa Arya game da magiyar ta bata wayarta, Arya taki, ta ce sai sun gama. Sai da Angelina ta zo da sauri ta kwace wayar ta miƙa mata tana faɗin. "Ke kina da son saka V kuka, wai ina ruwanki da soyayyarta ne?".

Wani irin harara Arya ta dallah mata kafin ta ce. "Ki daina shiga hurumina Angelina, idan ina yanke hukunci kina mun katsalandan watarana ba zaki ji ta daÉ—i ba". ....... "Dukana zaki yi ne?". Angelina ta faÉ—a tana harararta ita ma. "Kina tinanin ba zan iya dukan naki bane?". Cikin fushi Arya ta faÉ—a.

Angelina zata yi magana Manassa ƴar ba ruwana ta ce. "Har yanzu ba zaku daina faɗa ba"...... Harara su biyun suka dallah mata kafin Angelina ta ce. "Ke ina ruwanki?". ......... Wai kun san da cewa suna faɗa kuwa? Dik yadda suke kaunar junan nan idan ta kwaɓe masu ba karamin gwabza faɗa suke yi ba, kamar zasu kashe juna, musamman Arya da Angelina, kuma abin da baku sani ba dikkansu Manassa aka fara haifa, amma Arya ta zage da cewa ita ce babba, sai suka bar mata girman, amma ban da haka Manassa ce farkon faɗowa duniya, sai Angelina, Arya ce ta uku sannan V.

"Babu ruwana ku cigaba da yi". Manassa ta basu amsa. Tsaki Arya ta ja tare da jefar da stick ɗin hannunta, ta nufi side na pool ɗinsu dan ta ɗan yi linƙata saboda ta haɗa zufa a wannan game da suka buga. Ita kuwa V Angelina na bata wayarta ta bar wajen da gudu tana murmushi, garden na gidan ta shiga ta zauna saman kujera tare da fara ƙoƙarin kiran number, dan call ɗin ta katse.

Sau uku tana gwadawa call ɗin yaki shiga, daga karshe ta kunna data ta shiga Whatsapp. A nan ta ga saƙonsa na cewa sun sauƙa lafiya. Murmushi ne ya bayyana a kan face ɗinta ga kuma guntun hawayen kukan da Arya ta sanyaya, kan contact ɗin ta shiga tare da rubuta mashi call me. Tana turawa ba'afi 1 min ba sai ga kiransa ya biyo baya ta direct call. Jikinta har yana rawa wajen yin picking.

"Hello". Ta faɗa cike da matsuwar son jin voice ɗinsa, yana daga kwance saman katafaren bed ɗinsa, ya tada kai da cinyar daddynsa dake mashi tausa, wai kun san yadda daddy yake ji da Noor kuwa? Ɗah namiji ɗaya kamar rai, magajin dik waɗan na kadarori ai kun san dole a ji da shi sosai. Sai wani shagwaɓasa daddy yake yi yana matsa mashi damatsan hannu, wai sun sha tafiya ya gaji. Kawai dai daddy ji dashi yake yi, ba wani gajiya, baya son ko ƙuda ya taɓa mashi ɗan lelensa.

Noor wasa-wasa soyayya na son koya mashi wasu É—abi'u, yana jin kunyar daddy ya jisa yana hira da mace, amma ba zai iya hakura bai kirata ba tin da ta ce ya kirata, shi ne ya ce wa daddy wai abokiyar aikinsa ne, shi kuwa daddy ya ce okey, ya kasa kunne yana jinsu.

"Where did you drop your phone na dinga kira baki ɗaga ba?"......... Ɗan shagwaɓe murya ta yi tare da cewa. "Sorry, na barsa a ɗaki ne ni kuma ina waje muna buga snooker"....... Satar kallon daddy ya yi, sai yaga baya kallonsa, ƙasa sosai da murya ya yi kafin ya ce. "You look so beautiful this morning, you melted my heart, since da na shiga plane, I've been thinking about your beauty, your smile, they way you hug my dad, I felt like.......". Kasa karisawa ya yi saboda ɗago ido da ya yi suka haɗa ido da daddy dake kallon ɗan bakinsa, yana magana ne yadda daddy ba zai jisa ba, shi ne daddyn yake karantar ɗan bakin nasa.

Turo baki ya ɗan yi tare da cewa. "Daddy stop it nooow, stop looking at me". Ya faɗa yana miƙewa zaune tare da hararan daddyn nasa. Gefe daddy ya koma yana faɗin. "Dole na bar kallonka tin da an samu wacce take melting heart ɗinka"........ Pillow ya ɗauka ya fara kaiwa daddy dukan wasa yana faɗin shi a kyalesa.

"Wai ni na kulaka ne? Na kyaleka ai". Daddy ya faÉ—a. Kwanciya ya koma ya yi tare da É—aura pillow É—aya a wajen bakinsa wai dan ma kada daddy ya karanci lips É—insa....... Shi dai daddy gefe ya koma yana jiran a gama wayar yau dole a faÉ—a mashi budurwa ce ko abokiyar aiki?.

"My heartbeat daddy kake wa haka ko?". V da gabaÉ—aya kalamansa na É—azun suka gama tsumata ne ta faÉ—i hakan, ta ji daÉ—in yadda ya ce ta yi kyau yau da safen nan, abin ya yi mugun sanya zuciyarta ya yi fari. Shiru ya É—an yi kafin ya ce. "Daddy ne yake tsokanana dai".

Nisawa ta É—an yi kafin ta ce. "Daddy yana sonka sosai". Tarar numfashinta ya yi da cewa. "Over to over ma kuwa, fiye da kansa"....... Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa. "Mu yi video call?"...... Wurga dara-daran eyes É—insa a kan daddy ya yi kafin ya amsa da. "Later after daddy ya fita".

"Okey where's my Auntys?". Shiru ya É—an yi kafin ya ce. "They escort Aunty Luna, tana da meeting a ofishin jam'iyyar da suka tsai da ita takara"..... Sosai V ta yi mamakin jin cewa Luna Æ´ar siyasa ce, da sauri ta ce. "Dama Aunty Luna babba ce?"...... Tambayar ta so bashi dariya, amma sai ya fiske da cewa. "She's 35 years old, Aunty Lusi 30 years old, then my two sisters da suka mutu, sannan Aunty Lisa 25 years, sai ni". Ya kai karshen maganar tare da kin faÉ—a mata shekarunsa.

Gaskiya ne, Aunty Luna gogagiyar ƴar siyasa ce, daddynta ya bata goyon baya ɗari bisa ɗari, kujerar Gwamna take nema, sannan macece mai son jama'a, saukin kai da tausayawa talakawa, ga kyauta kamar me, har shi daddynsu yana da tsananin kyauta wanda daga garesa suka koya, dik Sunday sai sun bi gidan marayu da gajiyayyu sun raba masu kayan abinci da tsabar kuɗi. Ita kuma Auntu Lusi CEO ce ta SLBANK, babban banki ne sosai. Ita kuwa Aunty Lisa yanzu take degreenta na biyu a fannin lafiya. Kun san shi kuma Noor ina ALLAH ya jefasa ai, so dik yaran daddy Noor suna da abin yi, zakaru ne da ƙasa ke alfahari da su, basu tsaya cewa su mata ne kawai babu abin da zasu iya ba, sun tsaya tsayin daka, sun yi aiki tukuru dan gina gobensu dana iyalansu, sun samu uba wanda ya jajirce a kansu dik da babu uwa!.

"To kai shekarunka nawa?". V ta tambaya cikin zolaya. "Kamar naki suke". Ya bata amsa yana mai da kallonsa a kan daddy. Kukan shagwaɓa ta sanya mashi kan lallai ya faɗa mata shekarunsa, to yaro yana cikin shauƙin sabuwar soyayya ina zai so ɓacin ranta, sai kawai ya amsa mata da. "23 nike da shi".
Chapter 58 · 0% Book details