← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 189 OF 227

Sashe 189

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Brother yana wani irin shu'umin murmushi ya amsa da. "Kafin mu sake NEXAPOX-31 dole sai mun yi abu É—aya, idan muka tsananta ambaliyar nan, zamu samu damar sawa a rasa noma, a ruwa tsabtatacce, da matsuguni, al'umma zasu rasa wajen zama. Hanyoyin zirga-zirga na ruwa da sama su lalace, ruwan teku na karuwa, biranen gabar ruwa za su fara natsewa, a Nigeria kamar Lagos, a waje kamar Mumbai, Venice, a Avaris kamar Eldoria".

Sosai Dr James ya ji daÉ—in wannan batu, ransa ta yi fes sosai.

Brother ya ce. "Ya batun project É—inmu na Oxygen-Free Humans?"...... A natse Dr James ya ce. "Project É—in yana nan muna aiki a kansa".

Kun tina akwai ɗakin da 3D suka shiga na wasu halittu da suke kyankyasa? Na ce maku tamkar halittun mutane? To waɗan nan halittu ne Bro yake magana a kai, da su za'ayi tafiyar sabuwar addini, su mutane ne masu iya rayuwa a wurin da babu Iska, 3D sun gyara ƙwayoyin halittarsu ne dan rayuwa ba tare da buƙatar numfashi da iska ba, musamman sararin samaniya. Shi ma babban aiki ne.

Ganin sister Zinta na ɗan motsawa ne yasa Dr James cewa. "Bro goodnight, my princess tana buƙatar in kwanta ta shiga jikina sosai, nima ina buƙatar hakan, mu yi magana wani lokaci".

Wani irin kallo bro ya dallah mashi wanda ya sanya shi cewa. "Abin da ka sani ne, kuma na gama aikata komai". Daga haka ya katse kiran, ya kashe laptop É—in gabaÉ—aya tare da mayar da shi saman side sofa ya ajiye, ya É—auki wayansa tare da fito da light control na É—akin, ya kashe wutar tare kwanciya, ya jawota jikinsa sosai, yana shafa bayanta har barci ya É—aukesa, ASUBA TA GARI.

------------------------🔥

CRYSTAL PALACE.

Sai around 5 na yamma Aryan ya farka daga barci, ya yi mamakin ganin Seraphina a jikinsa tana zuba barcinta, intently ya zareta daga jikinsa, ya kwantar da ita a gefe, ya juya, dab face É—inta ya tsayar da nasa, kallon 2 mins yai mata kafin ya matsa ya manna mata sumbata a forehead É—inta.

Jikinsa babu kwari sosai, ƙasa ya sauƙo, kai tsaye ya nufi benensu yana ɗan ciza laɓɓa game da duba wayansa, nan yaga saƙon Lion, ai take ya ji kwarin jikinsa, da sauri ya ƙarisa gidansu. Bakinsa a ɗauke da sallama ya shiga room na Lion. Zazzaro idanunsa ya yi a kan Vir dake kwance saman katafaren bed ɗin Lion, ya tada kai da cinyar Lion ɗin, yana sanye da pjs, hannunsa rike da waya yana danna.

Lion ma dannar wayansa yake yi. Guru na making call, yana zaune saman side sofa, ya É—aura kafafunsa a kan throw pillow É—in dake gabansa.

"Saukar yaushe?". Aryan ya faɗa yana ƙarisowa cikin ɗakin. A kansa dik suka sauke kallonsu, take Lion ya gano yana cikin damuwa, amma ya ɗan ɗauke kansa game da cigaba da dannar wayansa. Vir ne ya amsa da. "Saukar ɗazu"........ Hayewa saman bed ɗin Aryan ya yi, zai yi magana kenan suka ji sallama again.

Da sauri suka kai kallonsu bakin door suna mamakin waye kuma zai shigo masu gida. Ɗan zazzare idanunsu dikka suka yi a kan Uncle Hussain except Lion da yai mashi kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Ciki Uncle ya shigo, da sauri Vir ya miƙe ya tarosa yana faɗin. "Welcome Uncle".

Hannun Vir ya rike yana faɗin. "My son South Korea ta karɓeka fa, ka ƙara kyau matuƙa"..... Dik da fuskan IRON FIST basu san me murmushi ba, Vir ya nuna alamar ya ji daɗin ganin Uncle, dik da bai murmusa ba, ya ɗan saki fuska yana kara riko Uncle ɗin.

Guru dake zaune saman side sofa ne ya miƙe tsaye yana faɗin. "Uncle yau kai ne a gidanmu?"......... "Hunaish ba dole in zo ba, tin da kun mun ya ji". Ya faɗa daidai lokacin da yake zama saman bed.

Dik hayewa gadon suka yi dan jin dame uncle ya zo masu ne. Zuba masu idanu sosai Uncle ya yi na, kallon 2 mins yai masu, dik sun zuba mashi idanu suna except Lion da tin da ya É—auke kai bai sake É—agowa ba, ya cigaba da dannar waya.

Ganin kallon ya yi yawa kuma Uncle ya yi shiru ne yasa guru ya ce. "Uncle talk now"........ Nisawa ya É—an yi game da cewa. "Nazo ne da maganar komawarku gidan Haiza'an"....... Slowly Lion ya É—an É—ago da kallonsa kaÉ—an, sai kuma ya sake sauke idanunsa. Vir ne ya ce. "Uncle komawarmu gidan dad ba zai yiwu ba, kasan in muka koma can dole za'a san bayan dad na raye, dole kuma É—ayan biyu zai faru, ko dai duniya ta san mu ne IRON FIST, ko kuma mu ajiye aikin SSO".

A dake Uncle ya ce. "Dama dole zaku shaidawa duniya kune IRON FIST, lokaci ya yi da zaku maye gurbin Haiza'an a idanun duniya! Ku yi fito na fito da kowa, ku sanya tsoro da gaggarwa a zuƙatan mugaye".......... Guru ne ya ce. "Uncle a yadda muka tsara komai ai kaga da sauran aiki a gabanmu ko? Ka bari mu ƙarisa sai mu koma gidan dad ɗin".

Vir ya ce. "Ga aikin shirin dakatar da ambaliyar da ake ƙoƙarin sakewa, ga aikin........". Hannu Uncle ya ɗaga mashi wanda yasa ya yi shiru, a dake cikin izzar sarautarsu Uncle ya ce. "Bar dik wannan zance, so nike kawai ku koma gidan Haiza'an, lokacin ɗaukar fansa ya yi, bana son in mutu baku cika mun burina ba". Ya kai karshen maganar yana kallon Lion da ko sau ɗaya bai ɗago ya gansu ba tin da suka fara magana, kuma babu alamar zai sanya baki a maganar tasu.

Guru ya ce. "To amma Uncle tare da kai zamu koma ko?"........ "Tukun nan dai".......... Vir ya ce. "In dai zamu koma can to dole mu ajiye aikin SSO, dan IRON FIST fito na fito zata yi ba da iya gwamnati ba, da duniya bakiɗaya ne"......... A taƙaice Uncle ya ce. "SSO da IRON FIST wanne ya fi amfani ga al'umma?".

Aryan da tin da suka fara magana bai tanka bane ya amsa da. "IRON FIST suna sama da kowa da komai"....... "To daga yau IRON FIST kuke ba SSO ba! Dole ku ajiye aikin SSO, ku fito fili ku ceci duniya! Lokacin ya yi da zaku haÉ—e family dik waje guda, dik ku koma gidan Haiza'an da zama, ku haÉ—a kanku, ku natsu ku cika mun burina"...... Tashin sense, e lallai kam Uncle ya zo da babbar magana fa.

Tsit ɗakin ya yi, ganin haka yasa uncle ya ce. "Zayra'an baka ce komai ba". Dik suka mayar da kallonsu a kan Lion da yake faman pressing phone. Shiru Lion bai yi magana, almost 3 mins, har sun fidda ran zai tanka, can ƙasa cike da izza ya ce. "Ba ka yanke decision ɗinka na?". Ya faɗa tare da miƙewa, ya nufi balcony.

Binsa da kallo suka yi suna mamakin yadda Lion yake sak daddynsa, banbancinsu kawai daddy yana da jumurin juran abu, shi kuwa Lion ina.

Nisawa suka yi game da dawo da kallonsu a kan Uncle da ya ɗan sha jinin jikinsa, dan ya gane nufin Lion, kuma dama yasan halin kayansa, wannan nuna iko da isar tasu a waje gado ce, watau Uncle ya nuna mashi iko tin da bai nemi shawararsa ba ya yanke cewa zasu koma gidan dad, shi ne Lion ya yi banza da su, kuma ba zai koma ɗin ba, in kuna son shiri da Lion har ya yi abu to ku nuna mashi cewa shi ne sarki a wajen, akasin haka to wlh ba zai yi abin da kuke so ba, Uncle yasan da hakan, ba'a tilasta jinin Haiza'an a kan abu, lallaɓasu ake yi, ka nuna masu power zasu baka mamaki ne, ba power kakansu Lion ya nunawa daddyn Lion ya ce lallai ya bashi hakuri bane yasa ya bar mashi masarautar? To su haka suke, in suna waje sune kawai masu power, komai ikonka dole ka durkusa masu.

Miƙewa Uncle ya yi, ya bi bayan Lion ɗin, yana tsaye a balcony, ya zura hannaye a aljihu yana kallon yanayin cikin palace ɗin. A gefensa ya tsaya cikin sanyin murya ya ce. "My decision is it not yours?"....... Shiru babu alamar Lion zai tanka, ya gano Uncle ya zo da kalaman yaudara ne, ba zasu fahimci shi bane, akwai dalilin da yasa baya son komawa gidan dad ɗinsa.

"Zayra'an talk to me now"...... Shiru babu alamar Lion zai tanka, dik yadda uncle ya so shawo kansa abin ya ci tura, Lion ko kaÉ—an bai tanka ba, babu ma alamar zai yi magana, rarrashin duniyar nan Uncle ya yi, amma Lion ko É—agowa ya kallesa bai yi ba, da alama sarautar ce yau ta motsa mashi. Da Uncle ya gaji sai ya dawo cikin É—aki, ya nufi waje yana faÉ—in. "Aryan ku shawo mun kan murÉ—aÉ—É—en É—an uwan nan naku, yau ya koma Haiza'an É—in sak". Ya kai karshe game da ficewa.

A tare Aryan da Vir suka yo ƙasa kafin guru ya rufa masu baya, suka isa in da Lion yake tsaye, idanunsa a kan cikin CRYSTAL PALACE ɗin. A gefe-gefensa suka tsaitsaya game da zubawa PALACE ɗin idanu suna kallonta, Aryan ya ce. "Our Lion me ya ɓata maka rai?". Sun fahimci ransa a ɓace.

Shiru dai babu alamar zai yi magana. Vir ne ya ce. "Uncle ne ko mu?". Still bai motsa ba. Guru ya ce. "Baka son mu koma gidan dad ne?"....... Still dai babu alamar zai kulasu. Suka yi iya yinsu Lion bai motsa daga in da yake ba, yadda kuka san sassaƙa bawan ALLAHN nan aka yi, wasa-wasa har mangrib suna tsaye a wajen Lion bai ko kalli in da suke ba.

Sai da aka kira sallah ya juya ya nufi cikin ɗakin, Vir zai rikosa Aryan ya dakatar da shi ta hanyar kama hannunsa...... "Kyalesa yana kan dokin zuciya ne, sai ta sauƙa, Uncle ya nuna mashi kamar ya isa da mu ne, ya ce zamu koma gidan dad"..... Vir ne ya ce. "Ba dan ma uncle ne ya nuna mashi wannan isa da mu ɗin ba ai da yau mutum ya ji a jikinsa, amma kasan Uncle dole mu yi hakuri da shi".
Chapter 189 · 0% Book details