← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 227

Sashe 101

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai jinjina mashi su Dr Kamal suke yi suna yaba muguntarsa, suna kuma kara mashi kwarin gwiwa. Shi kuwa sai kara jin kansa na kara girma yake yi.

Cikin wani irin murya mai amo ya ce. "A yanzu duniya a tafin hannuna take! Sai yadda na yi da ita! Ni ne Devil wanda da zai yi wa mai gida Dujjal tarba ta ban girma a lokacin da zai iso! Wannan project yakamata na canza mashi suna daga PC izuwa Death is inevitable! Ko kuma a death that wipes out an entire family!!"........ Dr Mark ne ya ce. "Ka barsa a PC É—in ma ya yi".

(PC yana nufin Population Control, na ji wasunku suna cewa CRYSTAL PALACE ne PC da yake nufi, to ba haka bane, CRYSTAL PALACE fa CP ne ba PC ba kusan É—aya suke yasa kuka ruÉ—e)

Dr Mark ne ya ce. "Amma meyasa WS ta hura mana wuta kan mu saki project É—in nan yanzu? Mun yi da ita ai sai shekaru uku zuwa huÉ—u gaba, meyasa suka ce lallai mu saketa yazu?".

Nisawa ya ɗan yi kafin ya ce. "Kasan a wasu ƙasashen za'a kafa sabuwar gwamnati, ma'ana zaɓe ta ƙarato saura shekara ɗaya da ƴan watanni, sannan kasan akwai manyan ƙasashen da suka gwadawa WS taurin kai, kuma da alama ƙasashen sun tsaya da ƙafafuwansu, suna da karfin tattalin arziki da karfin faɗa aji, sannan da alama suna da power da WS take shakkarsu shiyasa suka buƙaci project ɗin nan dan su gigita kowa, a taƙaice dai gargaɗi mai karfi suke son yi wa duniya, a karkashin ƙasa kuma akwai plan na ruguje ƙasashen da suka kawo karfi suke ganin suna da murya mai karfi, sannan a gefen ƙasashen dake biyayya ga WS kuma su za'a haɗasu da wannan cuta ne domin sabuwar gwamnatin da zasu kafa, a hargitsa ƴan ƙasa ta yadda gwamnatin da ta hau sabuwa ba za'a ga laifinta a farko ba, za'a ce duniya ta shiga rikici, so ko gwamnatin ta yi shekarun mulkinta bata yi wa ƴan ƙasa komai ba za'a ce ai dama wannan balain da ta faru na wannan cuta gwamnatin ba zata iya shawo kan matsalar lokaci guda ba, so kunga a nan dik badakalar da gwamnatin zata yi babu wanda zai mai da hankali ko ya zargesu, daga nan WS zata cinwa abin da take so".

Wannan bayani nasa ya mugun gamsar da su, watau WS basa sakar cuta sai idan za'a samu sabbin gwamnatin dake masu mubaya'a, watau a kowani gwamnati sau ɗaya suke sake cuta ko da wannan gwamnatin zata sake maimaita shekarunta a mulki ba zasu saki wata cuta ba sai idan sabuwar gwamnatin ce zata hau, sannan suna yin hakan kuma dan su ruguje ƙasashen dake ƙoƙarin tasowa! Tab akwai matsala.

Dr Mark zai yi magana suka ji alamar motsi a office na Dr James, Dr Kamal ne ya ce. "Ko su Maya ne?"....... Kai Dr James girgiza kafin ya ce. "Sai dai Lazy"....... Wani irin shu'umin murmushi Dr Mark ya saki kafin ya ce. "Ce mun zaka yi mutuniyarka, James Lazy fa sonka take yi"...... Wani irin É—aure fuska ya yi kafin ya ce. "Me zan yi da tsohuwar da komanta ya kare? Kada ka manta Lazy ta haura 47 years, surgery ne da magunguna yasa take haka, da kaina in mata surgery É—in sannan in dawo in kwashi ragowa? Are you out of your sense?!".

Wani irin dariyar mugunta Dr Kamal ya yi kafin ya ce. "Zakuwa ku dace, tana sonka sosai fa, kada ka manta ta yi maka abubuwa da dama a rayuwa, ita ta taimaka maka wajen kawo ƙarshen Muhammad Haiza'an, kada ka manta idan ba da sa hannunta ba baka isa shiga CRYSTAL PALACE har ka sace Muhammad mu yi nasarar cire ƙwaƙwalwansa ba, dan haka Lazy bata cancanci ka ki ta ba". Ya kai karshe yana dariyar shakiyanci da iskanci.

Kara ɗaure fuska Dr James ya yi tare da cewa. "Stop it! Dik abin da Lazy ta yi she did it because of money, na biyata hakkinta sai kuma ta ce zata yi aiki tare damu, tana sha'awar kasancewa tare da mu, na mata adalci na ɗauketa aiki, sai kuma me? Ta ce tana son ai mata surgery a canza mata kamanni kada ƴaƴanta su gane fuskanta zasu kasheta, haka nai mata surgery na canza mata kamanni, daga karshe ma ta gudu ta baro Washington ta dawo nan da zama, dik na karɓeta saboda girman aikin da ta yi mana, kunsan kwakwalwar Muhammad ba wasa ba, na bata aiki a ƙarƙashin office ɗina dik dan in yabawa ƙoƙarinta, dik ban mata adalci ba?".

Hararansa Dr Mark ya yi kafin ya ce. "Ka dai faɗi gaskiya, ba wani dan kayi mata adalci yasa ka ajiyeta a ƙarƙashin office ɗinka, kawai ka ɗauketa ne saboda nufinka a kan ƴaƴa Muhammad, kana son sperm and brain ɗinsu, kuma kasan ita kaɗai zata iya wannan aiki, saboda ita kaɗai tasan ainahin jininsu!".

Hararansu shi ma ya yi kafin ya ce. "Dik da haka dai na yi mata adalci"..... "Kai ku bar tuna mana baya, bamu taɓa aiki mai tsananin wahaka ba irin waɗan nan ayyuka guda biyu". Cewar Dr Kamal.

"Wani aiki kenan?". Dr James ya tambaya. Dr Kamal ya ce. "Aikin ƙwaƙwalwar Muhammad da kuma aikin ƙwaƙwalwa Namjoon, mun wahala a kan ayyuka biyun nan"....... Kai kawai Dr James ya girgiza alamar wahalar ta zarce ayi magana.

WAYE NAMJOON? WANI IRIN AIKIN ƘWAƘWALWA AKA YI MASHI? NASAN KUN GANE WAYE MUHAMMAD KAM AI! WATAU MAHAIFIN SU LION! KENAN A WANNAN HOSPITAL ƊIN AKA CIRE ƘWAƘWALWARSA? LALLAI AKWAI GAGARUMIN MATSALA NA KIN ƘARAWA KUWA!.

Kamar yadda suke zaune suke wannan hira cikin nishaɗi da tsokanar juna haka suma su Maya suke zaune suke hira. Bayin ALLAH kansu ya shiga ruɗani ne, sun shiga tsananin tashin hankali na ganin irin aikin da aka sanyasu, wannan document da aka basu su karanta, jerin sunayen chemicals da ake son su zaƙulo su haɗe masu ne, wani chemical ɗin idan sun haɗa shi da wani sai an barsa ya yi sati biyu ya gama tsumuwa sai a sake suba wani.

Da farko da suka fara aiki ba su damu sosai ba, sai yanzu da aikin ya yi nisa, suna isa kan manya-manyan chemicals masu haÉ—ari kuma masu tsanani a guba shi ne fa hankulansu ya tashi, sun san idan aka haÉ—a kaza da kaza ga abin da zai haifar, nan fa suka yi mugun gigita, dik sun sha jinin jikinsi.

Sister Maya ta fi tausayi da saurin karaya, cike da tashin hankali ta ce. "Sister Zinta kina ganin me nike gani kuwa? Me kike tinanin zasu yi da wannan abin?"...... Sister Zinta da ta gama shan jinin jikinta ne ta amsa da. "Sister Maya na fara fita a hayyacina ne ko kuwa dai mafarki nike yi? An taɓa haɗa waɗan nan sinadaran waje ɗaya ne? Kisan kai zasu yi ne?".

Dogon numfashi sister Maya ta ja kafin ta ce. "Babban tashin hankalina shi ne waɗan nan sinadaran da muƙa haɗa waje guda, kamar Dimethylmercury CHH, kin sani, sinadari ne dake shiga jiki a hankali ba tare da nuna alamu ba, sai daga baya ya haifar da matsalolin fata, kumburi, da raunuka masu wari, kuraje masu fashewa su fitar da jini, amfani da shi yana da matuƙar hatsari!"

Ta ja numfashi kafin ta cigaba da cewa. "Ga kuma sinadarin cantharidin CHO, sinadarin da ake samu daga wasu kwari masu haÉ—ari, yana sa kuraje su kumbura su fashe su fitar da ruwa wani lokaci kuma har jini suna yi. Ga kuma sinadarin ricin CHNO, sinadarin dake haddasa kumburi da kuraje masu zafi sosai. Hallau ga arsenic trioxide AsO, sinadarin dake sa mutum jin daÉ—i rayuwa a farko, amma daga baya yana haddasa cututtuka na fata, kumburi, da kuraje masu wari. Dik da wanna suka sake cewa mu zuba thallium sulfate TlSO a ciki, mugun sinadarin dake haddasa matsalolin fata da kumburi ba tare da an yi saurin gano shi ba". Ta kai karshe tamkar zata yi kuka, dik da basu san me za'ayi da waÉ—an nan sinadaran ba tabbas sun gigita da haÉ—awa, suna jin kuma tamkar ba zasu iya cigaba da haÉ—awa ba.

Na ce kun tuna cewa da Dr James yana gabar da project ɗinsa, a abubuwan da ya kirga cutar take haifarwa har da kuraje masu fashewa su yi jini? Nasan yanzu kun gane daga wani sinadari aka samu wannan, sannan ya ce ciwon yana shiga ne a hankali, yana ɓuya na sati biyu kafin ya bayyana a jiki, kenan kunga irin sinadaran da aka zuba mashi yasa zai ɓuya a jiki na tsawon sati biyu, lallai akwai matsala, mu leƙa CRYSTAL PALACE mu dawo.

CRYSTAL PALACE.

Shirye suke cikin tsadaddun tail coat masu bala'in kyau launin dark blue watau navy da ya yi masifar fito da tsantsar kyansu, ku hasko fararen fata a cikin navy blue ya zasu kasance?.

Musamman Aryan and Lion da suka cire face mask É—in fuskansu a yau suna karisa shiryawa, barema Lion da ya fito daga Pamira blood, hasken irin pure white É—in nan ne mai balain kyau.

Ya ilahi, tamkar ka samu waje ka zauna ne ka yi ta faman kallonsu kawai kada ka ɗauke idanu, idan kuka kalli lips ɗin Lion oooooo, ya ALLAH, zaku zaci ya sanya pink janbaki ne, ya ciza kala sosai yana wani irin kyalli, hakama lips na Aryan, bakin Lion irin round lips ɗin na ne mai masifar kyau, ga shi ɗan karami, lipa ɗinsa suna da ɗan cika daidai masha ALLAH. This two guy complete face ɗinsu ya haɗu, ga sexy gorgeous body, a gaskiya Lion yana kama da Leo sosai, kamar an tsaga kara, hatta hair ɗinsu golden white dake ta faman sheƙi kamar gold idan ya ji gyara, ya ALLAH, na sake cewa ya ALLAH.
Chapter 101 · 0% Book details