← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 227

Sashe 156

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin muryan kuka ta ce. "Ni ka turo mun sister Maya, ita kaɗai nike son gani".... Nisawa ya ɗan yi, ya sunbaci goshinta kafin ya ce. "Yanzu zan turota, amma ki mun murmushi"...... Din da tana cikin ciwo hakan bai hanata murmurawa kaɗan ba, kara sumbatar goshinta ya yi tare da miƙewa, yai mata sallama ya fito.

Tsaye ya isko Dr Kamal da Maya a tsakiyar parlon, yana faÉ—a mata ta je ta yi wanka ta fita wajen aiki, sai dare zai sake zuwa ya É—auketa, shi kuma Dr Mark da ba ruwansa da soyayya tini ya yi gaba abinsa.

A dake Dr James ya ce. "Maya ki je sama ɗakina sister ɗinki na kiranki". Daga haka bai sake magana ba, ya sauƙo ya nufi waje. Jawota jikinsa Dr Kamal ya yi, ya rungumeta tare da bata sumbata a goshi. Ya saketa yana mata bye-bye. Sama ta haye tana mashi bye-bye ita ma, sai murmushi take yi.

Sai da ya ga hayewarta sannan ya wuce ya bi bayan Dr James suka nufi cikin hospital É—in.

--------------------------

CRYSTAL PALACE.🔥

Abba khaiza'an's House.

A yau Abba ya shirya sadaki na alfarma, da misalin karfe 8 na dare, ya shirya cikin shiga ta alfarma, ya sanya thobe and bisht, ya naÉ—a rawani tamkar wani balarabe, amma haskensa kowa ya gani yasan ba balarabe bane.

Kai tsaye ya tasa Faryan da Harleen a gaba, dan dole ya ce su rakasa ya je ya kai wannan sadaki, yana son jibi jumma a É—aura wannan aure, ba fa fashi ko za'a mutu. Kai Abba namu na amana.

Ga Abba ga grandpa, me kuke tinani a kan wannan kai sadaki?

Likes comments and share fisabilillah.

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️

QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

For more information 08161390581 Whatsapp me only.

STEP 1🔥

2025-12-17.🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E_____________ 53 & 54

Kai tsaye benen su Noor suka nufa, ta hanyar sama ma suka bi. Already Abba ya sanar da daddyn Noor zasu zo, dan haka ya shirya tarba na musamman a garesu.

Suna knocking ɗaya aka buɗe masu kofar, uncle ɗan kwalisan mu ne ya fara tarbansu, fuska ɗauke da wannan lallausan murmushin nasu na gado mai kwantar da hankali, yai masu sannu da zuwa, har da riko hannun Harleen yana ƙara masu sannu da zuwa.

Ciki suka shigo, a saman sofa suka zauna, ga kayan cima kala-kala an jibga masu dan girmamawa a garesu. Sama Uncle ya haura. Jim kaÉ—an sai ga shi ya dawo da dikka family, Aunty Luna, Aunty Lusi da daddy.

Aunty Lusi akwai izza jama'a, a family É—in su Noor dik ta fi kowa izza, bata da yawan magana, sai kallo da ido, bata shiga sabgar kowa, kuma ta tsani a shiga nata, amma dik da wannan izza nata tana kallon Abba sai da ta ji faÉ—uwar gaba, ta gagara haÉ—a ido kai tsaye da shi.

Dik suna sanye da pjs ne a jikinsu, da yake basu jima da tashi daga barci ba. Abba yana daga zauna daddy Noor ya ƙariso ya zauna a kusa da shi, sannan ya miƙa mashi hannu kan su gaisa, Abba bai bashi hannu ba, sai dai ya ce mashi salamu alaikum kawai, daddy Noor bai sa me ya ce ba, ita kanta musabahar ba wai ya saba yi bane, dan ya mutunta baƙin nasa ne yasa ya yi.

Abba ne ya ce Harleen ya kawo trollyn da suka zo da shi. Jawo shi ya yi gaban Abba, sai satar kallon Aunty Luna malam Harleen yake ta faman yi, yana wani É—aure fuska, kaman wanda aka sanya dole...... A mutunce aka gaggaisa, Aunty Luna and Aunty Lusi suka É—aga wa su Abba gaisuwa. Aunty Luna sai satar kallon Harleen take yi ita ma, hakika ya yi kyau cikin tail coat É—in nan, kyansa ya sake fitowa sosai da sosai!.

A dake Abba ya ce. "A addininmu muna yin sadaki, ba zobe ba, dan haka wannan shi ne sadakin, idan yai masu kaÉ—an suna iya furta adadin abin da suke so sai a kawo masu, nan da jibi nike son a É—aura wannan aure". Babu wasa a tattare da shi yai magana, ga izza kamar shi ne ubansu har daddyn Noor É—in!.

Zuba mashi idanu suka yi. Abba ya kalli Aunty Luna a lokacin da ya buɗe akwatin kuɗin. "Ƴata idan kuɗin bai maki ba zaki iya faɗar nawa kike so" . Ya kai karshe daidai lokacin da yake zuge zip ɗin akwatin.

Dollars ne zallah, sai ɗanyen gold guda biyu a ciki...... Ai dikka family babu wanda bai waro idanunsa waje ba ganin maƙudan kuɗin da Abba ya buɗe a cikin akwatin nan, ba su taɓa zatan Khaiza'an's family suna da wannan kuɗin ba, suna kallon Abba matsayin bai wuci ɗan majalisa a kuɗi ba, ba su kaisa matsayin gwamna bama, basu san ko shugaban ƙasa ba za gwada mashi kuɗi ba.

Hakikanin gaskiya ba su kawai ba, har su Faryan sun girgiza da ganin kuɗin nan da Abba ya buɗe, ya ilahi, Harleen da Faryan kallon juna suka yi, a cikin zuciyoyinsu suna tambayar kansu a ina Abbansu ya samu waɗan nan maƙudan kuɗaɗɗe? Ga gold, wannan kuɗi ai zai iya saya masu bene guda a CRYSTAL PALACE in da za'a sayar, sai dai a CRYSTAL PALACE ba'a sayar da gida sai dai ka kama haya!.

To dik wannan kuɗin Aryan ne ya baiwa Abba, kun tina dama ya ce zai turo kuɗi, to shi ne ya turo a akwati, kuma wannan gold ɗin Aryan fa cewa Abba ya yi sadakin Rimsha ne ya biyawa Vash ɗan lele, amma kunga Abba da ƙoƙari gold ɗaya ya cire ya bari a gida wai na Rimsha, ya tattaro sauran dik ya kawowa su Aunty Luna dan baya son harkar raini, kada a rainasa! Yana son nuna masu muhimmanci ƴaƴansu, yana so su san ba wai kawai za'a auri ƴaƴansu bane, za'a kula da su ne sosai.

"Abba babu komai, ni ba sai ka bani komai ba". Cewar Aunty Luna, tana magana ta É—ago slowly zata saci kallon Harleen kenan suka haÉ—a ido da shi, dan shi ma ya É—ago zai saci kallonta. Kashe mashi ido É—aya ta yi game da binsa da lallausan murmushi.

Ai sai ga Harleen ya fara tari, yana neman ruwa. Da sauri uncle ya ɗauko ruwa a bottle, ya buɗe ya zuba mashi a cup ya miƙa mashi. Karɓa ya yi, ya fara sha, sai da ya sha rabi, sannan ya ɗago ya saci kallonta, still shi take kallo tana murmushi. Harara ya watsa mata, ita kuma ta ɗan turo mashi baki kafin ta sake kashe mashi ido ɗaya.

"Kuna tinanin zaku sayemu da kuɗi ne kenan?". A cewar Aunty Lusi, ta yi maganar a dake, bata ɗaukar raini na ce maku. Ɗago idanu a kanta Abba ya yi, take ta ji dik wani kwarin gwiwa ɗinta ya gudu saboda kwarjinin Abba, ƙawar da kanta gefe ta yi, kirjinta na bugawa da karfi, amma ta daure game da sauke ajiyar zuciya.

A dake Abba ya ce. "Idan hakan muka so ma zamu iya, amma yanzu dai ba sayan naku muka zo yi ba, sadaki muka kawo!". Cike da izza babu wasa a tattare da shi yai maganar, ya bata amsa ne dan yaga tana fa ilmi....... Uncle ne ya ce. "Lusi be patient please"...... Miƙewa Aunty Lusi ta yi zata bar wajen, a cewarta ba zata iya tsayawa ba, kun san tana ji da mulki tin da ƴar siyasa ce, gwamna take nema.

"Koma ki zauna ayi komai a gabanki!". Abba ne ya faÉ—a on a serious note. ÆŠago da kallonta a kansa ta yi, sai ta ji ba zata iya ja in da shi ba, ta rasa kwarin gwiwa, dole ta koma ta zauna tana sauke ajiyar zuciya.

Daddyn Noor bawan ALLAH shi dai da ido kawai yake bin Abba, to aka ce faɗar da ya fi karfinka sai ka mayar da shi wasa. Su Harleen kam sun san waye Abba, sun san wlh da ya yi niyya sai dai yana zaune a gida yasa a ɗauko mashi family ɗinsu Noor gabaɗaya a kai mashi, har ita mai taƙama da tana neman gwamna ɗin, dik zai sanya a ɗaukesu a kaisu gida, ba zai zo da kansa ba, amma ya daure ya zo da kansa, ai sun samu martabawa sosai.

Miƙewa Abba ya yi tare da cewa. "Wannan shi ne sadakin, mu a addininmu ba zobe bane, addininmu ya baiwa kowa ƴancinsa, ya fitarwa kowa haƙinsa". Ya faɗa yana kallon daddy. Daddyn Noor mutum ne da baya son hayaniya, wlh kamar Noor yake, sai kawai ya bi Abba da ido, shi bashi da damuwa in har yaran nasa suna so ko yau a ɗaura auren.

Daidai lokacin grandpa ya sauƙo, ai yana ganin Abba ya ƙara sauri yana dogara sandarsa, tin bai gama sauƙowa ƙasa ba yana faɗin. "Me ya kawoku gidan nan?". Ai ko kallon in da yake Abba bai yi ba, sai gyara bisht ɗin jikinsa ya yi, ya juya yana faɗin. "Harleen mu je".

Cikin faɗa grandpa ya ce. "Ba zan barku ba, sai hukuma ta shiga tsakaninmu, ba zan hakura ba"......... Ko kallon in da yake Abba bai yi ba, ya wuce gaba, su Harleen ma babu wanda ya kulasa, suka wuce suka fice, sai bala'i yake yi, daddy Noor ya jawosa yana ƙoƙarin rarrashinsa.

Abba kam ko a jikinsa, ba dai abin da ya kawo shi ya yi ba? Ai shikenan, bashi da lokacin su grandpa. Suna komawa gida suka isko Ammie da Rimsha suna ta shan hira. Rimsha na ganinsa ta nufesa da gudu tana oyoyo Abba.

Da buɗar bakinsa sai ya ce. "Amarya yau kin ƙara kyau fa, ko dai fuskar taki tasan ke amarya ce?"....... Ɗan zazzare mashi idanu ta yi. "Abba amarya kuma?". Kai Abba ya jinjina mata, ya riko hannunta suka wuce izuwa cikin parlo, a saman sofa ya zauna, Rimsha ta haye jikinsa.
Chapter 156 · 0% Book details