Sashe 36
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai dai kuma tin daga kan manyan Generals dake kula da sashen horonsu har izuwa kan Captain da ake komai a gabansa sai da suka tsaya cak na ɗan dakiku a lokacin da suka ga abin da Leo ya yi. A lokacin da ya ɗauki bindigar da aka bashi, abu na farko da ya fara yi shi ne sai da ya fara rufe barrel na bindigar, bututun harbi kenan, sai da ya rufeta, sannan ya buɗe magazine inda ake saka alburushin ya cirota. Mamaki su Captain suke yi, domin kuwa Leo bindigar gaske suka bashi, kuma bullet ɗinta ba'ayi covering ba, sun yi ne dan su gwada shi, yana ɗaukar bindigar daga yanayin nauyinta ya gane komai real ne, shi ne ya fara rufe wajen harbinta kada ta kwace ta harbi wani, kwakwalwarsa tana da mugun gudu ne fiye da tunani, dik a ƙasa da second 20 ya yi wannan aiki!.
Hakika sun shiga mamaki, dik yadda aka yi Leo ya san bindiga matuƙar sani, basu taɓa zatan zai gane komai na gaske aka bashi ba! Shi kuwa bai kawo komai a ransa ba, ya cire bullet ɗin ya ajiye a jefe cikin kwanciyar hankali.
Captain sai da ya ɗauki ƴan mintina a ƙallah biyar kafin ya dawo daidai daga girgizan da Leo ya sanyasu. Sannan ya ce. "A ƙasa da 30 second ku mayar da bullet ɗinku, a ƙasa da second biyar ku ɗauki saitin harbi wa wancan board ɗin".
Tin bai kammala rufe baki ba suka fara, komai Leo yake yi cikin tsantsar natsuwa, a haka ya mayar da bullet É—in, sannan ya mirgina daga in da yake, cikin zafa ya É—auki saiti kamar da aka umarcesu. Ganin yadda ya yi yasa Noor ma mirginawa ya É—auki saiti.
Note, akwai abin da na mance ban faÉ—a maku ba, dik wani horon da aka yi masu ana maimaita masu shi ne har sai sun kware ya bi jikinsu, sai su fi sati suna maimata horo É—aya, kunga ni kuma ba zan tsaya mu yi ta maimaita rubutun da muka yi ba, kun gane ai?!.
Harbin tsakiyar board ɗin Captain yasa su yi, hakan yasa suka yi gagawar fara harbi, bullet ɗin kowa na da cover ne, hakan yasa ya fita salun alum ba wata ƙara sosai, shi kuwa Leo yana buga nasa sai da suka ɗan razana, dan ba cover.
Dik wajen room 1 ne basu saɓa saiti ba, suka harbi in da aka buƙata, sai su Unays ke biye masu a saiti mai kyau. Captain ne ya ce. "Yanzu ku kaddara kuna tsaka da yaki bulle ɗinku ya kare, yanzu ku ciro bullet daga waist ɗinku, ku sanyawa bindigunku a ƙasa da one minute sannan ku cigaba da musayan wuta ba tare da ɓata lokaci ba". Ya kai karshe tare da watsu masu bullet ɗaiɗai wanda zasu canza, sannan ya ce. "Minti ɗaya gareku".
Cikin zafin nama suka fara canzawa, wasu jikinsu sai rawa yake, wasu har da miƙewa tsaye, dan suna ganin a zaune buƙata ba zata biya ba. Dikkansu sun canza a ƙasa da minti ɗaya, amma room 1 sun canza ne a ƙasa da second 10 kacal saboda zafin nama da zafin jini irin nasu. Cikin zafa suka fara saita board ɗin suka yi harbi again.
Sosai Captain ya ji mugun daɗi, haka ya sanyasu suka dinga maimaitawa har sai da ya ga sun mai da shi kamar ruwan shansu, sannan ne ya ɗaukesu suka nufi wajen da za su yi hand to hand combat training. Ba kullum yaƙi da bindiga ake yi ba, akwai in da faɗar hannu yake da amfani, musamman ga waɗan da ake son kamawa ba kashewa ba, waɗan da ake son bayanai daga bakinsu, so dole su iya faɗa da hannunsu a cikin wannan sati gabaɗaya, daga yau zasu fara.
Sannan a nan aka koya musu dabarun ƙwace makami daga hannun abokin gaba. Sai da Captain ya fara koya masu yadda zasu daki abokin gaba, da yadda zasu karya hannu da kafafun mutane, shiyasa zaku ga wlh karyawa mutane hannu karamin aikin soja ne, sun kware a wannan sabga, to koya masu shi ma musamman ake yi, yadda zasu karya a take!
Sai da ya gama koya masu wannan sannan ya umarce su suyi faÉ—a da junansu, wanda ya faÉ—i sai ya sake gwabzawa da wani har sai ya iya kare kansa, sai sun kware a iya jibgar wasu amma su kada su bari a jibgesu.
Nan fa suka fara kallon juna, Leo bai zaɓi Noor ba, saboda yana tausaya mashi, yasan ma ba zai iya gwabzawa da shi ba, dan haka sai ya ce Juraiz ya zo su gwabza, dan ya gansa chocolate color, ga shi kakkarfa. Zaysh ya ɗauki Ameer, shi kuma Unays ya ce Noor ya zo su gwabza, har cikin ransa Leo bai so ba, dan ba zai iya ganin irin dukan da Unays zai yi wa Noor ba, dan yasan Unays ɗin ya fi karfin Noor, kuma yasan Unays bashi da tausayi, yanzu har cikin ransa yake jin Noor!.
Captain na cewa start suka fara gwabzawa tamkar wasu mayunwatan zakuna, duka suka fara kaiwa junansu babu tausayi babu tausayawa, kowa ya iya allonsa ya wanke ne. Wani irin naushi da Unays ya kaiwa Noor a baki sai da bakin nasa ta fashe, take jini ta fara zuba, sosai Leo ya ji zafin haka, sai ya ji tamkar jikinsa aka nausa, a ransa ya ce bashi Unays ya ci, dik duka ɗaya da ya yi wa Noor sai ya biya shi. Amma shi kuma ga shi ya yi wa Juraiz mugun duka har ya baje a ƙasa yana numfashi sama-sama, kuma yake cewa zai ramawa Noor.
Zaysh babu tausayi ya yi wa Ameer mugun duka shi ma, har ya fasa mashi baki, daga karshe ƙasa Ameer ya zube yana numfashi sama-sama. Ba karya Noor ya daku a hannu Unays duka mummuna ma kuwa, har sai da Captain ya shiga tsakaninsu, dan yaga Unays kamar ya mayar da abin gaske ne over, kun san dama yana jin haushin ƴan room 1, shi ne ya fara sauƙewa a kan Noor.
Ba Leo kawai ba, hatta su Zaysh sun ji takaicin dukan da Unays ya yi wa Noor, jikinsu har tsuma yake yi na ganin yadda bakin Noor yake jini har ya kumbura!.
Shi kansa Captain bai ji daÉ—in dukan ba, amma ya za'ayi? Dik cikin horo ne. Haka suna ji suna gani aka sake haÉ—a Noor da wani saboda doka ce in aka kada kai sai ka sake da wani. A nan ma Noor duka ya ci ba karya. Aka sake haÉ—a shi da wani, da team 1 suka ga fa za'ayi mashi mummunar illah sai Leo ya ce a haÉ—a shi da shi. Da sauri Captain ya aminta, saboda shi ma tausayin Noor ya gama cika shi.
Da aka haÉ—asu sake jiki Leo ya yi Noor ya yi nasara a kansa, sannan shi aka haÉ—a shi da wani, dik dai abin da suke yi manyansu na kallonsu. A wannan horo dai ba'a tashi ta daÉ—i ba, dan bakin Noor a kumbure dam suka nufi wajen breakfast.
Da kyar Noor ya iya cin abinci saboda yadda bakinsa take yi mashi zafi ga kumburi, sai da Leo ya mashi kalaman jarumta, sannan ne ya ci. Bayan sun gama karyawa aka ɗaukesu zuwa wajen da zasu yi guerrilla warfare training. A nan aka koyar da su yadda ake amfani da muhalli dan samun nasara a yaƙi.
Kowa ya shiga cikin maɓoya, dan dole ne su ɓuya kuma su yi tafiya a kwance ba tare da an gan su ba, kamar kwantan ɓauna kenan. Sannan aka koya masu yadda zasu ɓuya su saje da ciyayi dan kare kai, da yadda in sun ɓuya zasu fito da bindigunsu su yi harbi. Dan dole suyi hari ba tare da sun bayyana kansu ba, shi ake cewa yakin sunkuru.
Sai da suka yi awa guda a wannan horo sannan aka ɗaukesu zuwa wani tapkeken ruwa da aka yi shi musamman dan yin river crossing under attack training. A nan Captain ya koya musu yadda za su tsallake ruwa cikin gaggawa a yayin farmakin makiya, su tsallaka ana harbinsu da bindiga ta baya, dole su koyi kaucewa bullet a cikin ruwan. Kuma dole su iya yin iyo a cikin ruwa mai gudu, ana koya musu yadda ake ratsa ruwa ba tare da abokan gaba sun gan su ba, dole su natse cikin ruwa su rike numfashinsu suna tafiya har su haye. AIKIN SOJA BA NA RAGWAYE BANE MY PEOPLE'S, BA DIK KAI BA WLH! WAI DAN MA BAKU GANIN AZABAN A ZAHIRI, A RUBUTU BA ZAKU FAHIMCI AZABAR SOSAI BA, SAI KUN GANSU SUNA NISHI SAMA-SAMA TAMKAR RAI ZAI YI HALINSU A KAN IDONKU TUKUN NAN, A NAN NE ZAKU JI ZUƘATANKU SUN KARAYA, KUN TAUSAYA MASU.
Duk wanda bai iya tsallake ruwan a cikin lokaci ba sakowa zai yi. Haka suka dinga fama, waÉ—an da akwai pool a gidansu sun yi kokari, amma an sha ruwa kam, an kuma ci azaba, sai numfashi sama-sama suke yi tamkar ba zasu kai labari ba, amma a haka suka jure.
Bayan dikka wannan wahala sai aka kaisu in da zasu yi attack simulation, waje ne da aka shirya masu tamkar farmakin gaske, su kwaci kansu, unexpected suka fara jin farmakin.
Cikin zafin nama suka fara fito da kwarewarsu a fili, abu na farko da suka fara yi shi ne rarraba kansu zuwa team by team dan su kwaci kansu su kuma yi wasa da hankulan abokan gaba, na biyu suka fito da dabarun ɓuya, na uku suka haɗa kai a wajen dan ganin sun yi nasara. Abin ya yi matuƙar bawa manyansu mamaki, like wow, suna da basira. Sai ma da Captain ya ga suna yi wa juna magana da ido a lokacin da suka ɓuɓɓuya a wajaje tantunan dake wurin, magana sosai suke yi da ido na yadda zasu yi su tsira, kai abin ya bawa Captain mugun mamaki, bai taɓa zatan kwakwalwarsu zata yi sauri basu dabara da mafita ba, sai ga shi kuma sun yi.