← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 176 OF 227

Sashe 176

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A yadda ya yi magana yasa su Zaynish sun ji lallai ko zasu mutu ba zasu marawa karya baya ba, lallai zasu aiki dan cika alƙawarin da suka ɗauka. Cike da taƙaici Zaynish ya ce. "Hakika ba zamu zama karnukan farautar manyanmu ba! Lallai ba zamu karɓi umarnin rufe bakinmu a lokacin da ake zalunci ba, ba shakka sai dai a kashemu amma a kan gaskiyanmu!!".

Noor ya ce. "Dama ai mu mutuwa ba wata aba bace a wajenmu, sai da muka tabbatar cewa mutuwa ta fi takalmar sakawarmu sauƙi a wajenmu kafin mu yarda mu sanya wannan kaki, dan haka mu matattune dama, lallai zamu tsaya a kan gaskiya!".

Vash ya ce. "Ba zamu taɓa bari a cigaba da cutar da al'umma ba, zamu zama sojoji na farko da suka fara gyarawa kowa zama a ƙasar nan!"....…. Leo ya ce. "Idan sun san wasu ai basu san wasu ba, ba zamu ki karɓar umarninsu ba, dan umarninsu doka ce, amma muna da damar yin abin da muke so a bayan idanunsu ba tare da sun sani ba ai, daga yau babu wani ɗan ta'adda da zamu sake kamawa mu mayar barrack, dik kashe shegu zaku yi".

Zaynish da ya fito daga Afirka me bai sani ba? A ƙule ya ce. "Abinda ko mun sha wahala, mun je yaki, a yakin har mu rasa ƴan uwanmu sojoji, mu sha wahala mu kama ƴan ta'addan mun kaisu ma bayan kwanaki sakesu ake yi wahalarmu ta tashi a banza, dan haka ina tare da kai, dik a daji zamu kashesu kisa mafi walaƙanci, mu jefa gawarwakinsu cikin manyan tekuna, in mun koma mu ce dik sun gudu, that's all".

Noor ya ce. "Wannan umarni da ƙananan sojoji basa samu yasa suke shan wahala, suna filin daka amma wai suna jiran manya daga sama su basu izinin harbi, sai su tsaya ayi ta harbinsu! Abin taƙaici, amma zamu gwada masu kwarewa a kan aiki, zamu canza hukumar soja na duniya bakiɗaya".

Vash ne ya ce. "Ni wani kafurin ne ma ya kawo dokar idan kana filin daga ma sai ka nemi izinin harbi?"....... Zaynish ya ce. "Kafuran suna dayawa ai, amma zamu kafa tarihi a hukumar soja wanda ko mun mutu Æ´an baya zasu yi amfani da salonmu, zamu canza hukumar soja a duniya bakiÉ—aya kamar yadda Noor ya ce, zamu bawa duniya mamaki, sai mun É—ara FIVE LION In Sha ALLAH".

Leo ne ya ce. "FIVE LIONS, kai watau AZURE ta jima tana yaye gwarazan maza fa"......... Noor ne ya ce. "Ni fa ina ganin IRON FIST ma daga AZURE suka samu horo, dan wani lokaci aikinsu yana mun kama da namu fa".......... Vash ne ya amsa da. "Ban san meyasa nike son tarihin FIVE LIONS har cikin raina ba, sojojin da suka shiga tarihin duniya a lokacin baya, sojojin da suka bada mamaki".

Leo ya ce. "Ina tinanin AZURE ta hora IRON FIST gaskiya, saboda nima irin aikin da suke yi yana bani mamaki, amma ni fa ina ji a jikina IRON FIST ba mugaye bane kamar yadda duniya ta É—auka, kawai gwamnatin duniya ne ta nunasu matsayin azzalumai saboda suna rusa zaluncinsu"........ E mana, jama'a jinin IRON FIST yana magana, kaifin kwakwalwarsu gado ce, kun ji yana hasashen ba mugaye bane.

Noor ya ce. "Ai manyan duniya zasu aikata fin haka ma, da zarar ra'ayinka ya sha banban da nasu to fa kai ne É—an ta'adda kuma mugu, su kuma asalin Æ´an ta'adda mugayen basa kiransu da hakan saboda ra'ayinsu iri É—aya"...... Kai kawai Zaynish ya girgiza, daga nan bai sake yin magana ba, ya yi shiru, suka cigaba da hira suna tafiya, sai da suka kusa isa wajen tantunansu ne Noor ya ce.

"Zaynish lafiya ka yi shiru?". Nisawa ya É—an yi tare da cewa. "Babu komai bro". Noor bai yarda ba, ya matsa ya rike Zaynish tare da tsayar da shi suna fuskantar juna, suka dakata da tafiya, cike da kulawa ya ce. "Bro, now we're one family, bamu da iyaye da Æ´an uwa a nan, bamu da kowa, why not ba zamu haÉ—a kanmu, mu rungumi juna ba?".

Matsawa Vash ya yi, ya dafa kafaÉ—ar Zaynish yana faÉ—in. "Ka faÉ—a mana damuwarka mu yi maganinta a tare"...... Baya Leo ya koma ya jingina da jikin wata bishiya yana kallonsu bai yi magana ba. Nisawa Zaynish ya yi kafin ya fara basu labarin yadda Æ´an ta'adda suka kashe mashi dangi, iya shi da sister É—insa kawai suka rage, ya basu labarin komai bai rage ba.

Sun yi matuƙar tausaya mashi, Noor ya rungumesa game da cewa. "As from today we're your family also, ba kai da Aunty Ummie bane kawai, akwai mu, we are brothers now! Zamu tsaya da kai dik wuya dik daɗi, promise that kaima kana tare damu"........ Ajiyar zuciya ya sauke tare da rungume Noor. "We're brothers now!". Matsawa Vash ma ya yi, suka rungumi juna.

Shi dai Leo yana gefe yana kallonsu bai tanka ba....... Wani irin haushi karnukan hannunsu suka fara yi, hakan yasa Noor janye jikinsa a miliyan ya ja da baya, ya tsorata da kukan karen. ÆŠago kai Leo ya yi yana faÉ—in. "Me yake damun karnikan?". Ya faÉ—a tare da kuna light É—in hannunsa a kansu.

Shiru Leo ya ɗan yi game da cewa su Noor su yi shiru, dan karnuka basa haushi banza, bare ma karnukan da aka baiwa horo irin wannan....... Tsit suka tsaya karnukan na cigaba da daka haushi. Lokacin guda cikin zafa Zaynish ya ture Leo tare da damke wukar da wani mutun ya zo ta baya zai daɓawa Leo ɗin.

Take wuƙar ta fasa mashi tafin hannu dan bai sanya hand gloves ɗinsu na aiki ba, janye wuƙar baya mutumin ya yi, hakan yasa ta kara pasa tafin Zaynish. Kafin DOL su motsa sai ganin wasu jiga-jigan mutane huɗu suka yi sun bayyana kewaye da su, suna sanye da bakaken kaya na manyan ɓarayi, suna wani irin haki, da alama gudu sosai suka yi kafin su cim masu.

Siririn tsaki Noor ya ja tare da cewa. "Ku zo da wuri mu baku a jikinku muna son komawa kafin gari ya waye"....... Zazzare wuƙaƙen hannunsu mutanen suka yi, miƙawa Vash igiyar karen hannunsa Zaynish ya yi, ya sanya hannu ya tsaga rigar jikinsa gida biyu, ya ɗaure hannunsa dake zubar da jini, har lokacin haske wata tamkar kamar rana yana haskasu.

Komawa baya Vash ya yi ya jingina da jikin wani ƙaton dutse dake wajen, ya barwa mazajen AZURE filin su fafata shi kuma ya rike karnuka. Haɗe bayansu Zaynish, Noor and Leo suka yi suna kallon mutanen.

Kansu mutane suka yi da wuƙaƙen, hakan yasa suka dare suka rabu. Wani irin faɗa suka fara gwabzawa na nuna banbanci kwarewa, sai dai sun yi mamaki ganin mutanen sun iya faɗa irin wanda ake koyawa sojoji.

Mutane su huɗu, su kuma su uku haka suka fara gwabzawa. A tare mutane biyu suka yi kan Noor shi kaɗai, kaucewa wuƙar da suke ƙoƙarin caka mashi ya fara yi, while shi kuma Leo ya kwace wuƙar nasa mutumin ya jefar, sun fara faɗar hannu, wani punch Leo ya kai mashi a bayan kunne wanda yasa ya yi baya-baya ya faɗi ƙasa.

Ganin ya faɗi ne yasa ya daka tsalle, ya taka wani dutse dake kusa da Vash, ya ƙara tsalle game da juyawa ya daki ɗaya daga cikin masu kawowa Noor hari da wuƙa, a wuya ya dakesa da ƙafansa, sai ga mutumin ya faɗi ƙasa. Dafa shoulder ɗin Leo Noor ya yi, ya daka tsalle ya taƙa ɗayan mutumin a fuska da waɗan nan shaggun tauraran takalman nasu, baya-baya ya yi ya faɗi ƙasa.

Dafe shoulder ɗin Noor Leo ma ya yi, ya daka tsalle tare da juyawa ya taka mutuminsa da ya taso yanzu yake ƙoƙarin nufosu, watau ya farfaɗo daga punch da ya sha...... Da karfi Leo ya riko waish ɗin Noor tare da ɗaga shi sama, Noor ɗin ya ware kafarsa ɗaya ya kaiwa mutumin da suke faɗa da Zaynish duka a gefen wuya, wannan duka ɗaya ba tashi Noor yai mashi, dan wannan shegen takalman nasu ya daki maƙogwaron mutumin wanda yasa ƙashin wajen ta ɓalle, kun san takalmansun nan ba karamar taurice da ita ba.

Zaynish bai iya faÉ—a da mutumin sosai bane saboda yankar da suka mashi a hannu, so da hannu É—aya yake faÉ—a shiyasa Leo ya taimaka mashi ta hanyar É—aga Noor ya daki mutumin.

Yana sauke Noor ɗin ya yi tsale ya yi backtorn ya taka ɗayan mutumin da ya taso yanzu a kai sai da ya koma ya zube a ƙasa. Tsalle Noor ya yi ya taka tsakiyar bayan Leo dake duƙe, ya ware kafafunsa ya daki guy da ya sake miƙewa a ciki, hakan yasa guy ɗin ya sake komawa ƙasa, ya durƙusa kan gwiwinsa yana nishi sama-sama tamkar yana son sumewa ne.

Dirowa ƙasa Noor ya yi, yana dirowa Leo ya miƙe tare da dafa shoulder ɗin Noor ɗin, ya daka tsalle tare da ware kafafunsa ya sake kaiwa guy ɗin dake durkushen wani mugun duka a gefen wuya da kafarsa, hakan yasa guy ɗin yanke jiki ya faɗi baya numfashi.

Dirowa ƙasa Leo ya yi tare da fara karkaɗe hannunsa alamar sun gama da su dikka........ Vash ne ya cire bindigar dake wajensa yana faɗin. "Dik ku kashesu, ba za'a rasa mai sauran numfashi a cikinsu ba"........ Hannu Leo ya ɗaga masu game da cewa. "Ku kamasu mu koma da su sansani, ina zargin ta yadda aka yi suka iy faɗar sojoji, lallai ba ƴan ta'adda bane kawai!".

Noor dake haki kaÉ—an-kaÉ—an ne ya ce. "Ina zargin navy ne!"...... A natse Zaynish ya amsa da. "Tabbas na zargi hakan nima"....... Vash ya ce. "Okey kenan Navy sun san da zaman filin da muka je yau kenan?".

Leo dake ƙoƙarin zare belt na wandonsa ne ya amsa da. "Suna da sani mana, sun san komai, kawai sun mayar da kansu karnukan farautar manyan Avaris ne shiyasa basa ɗaukar mataki"..... Zaynish ya ce. "Okey, watau sun ga shigarmu wajen?"...... Kai Leo ya jinjina alamar yeah sun gani. Cike da takaici Zaysh ya ce. "Okey, Navy na gadin ɓarnar manya ƙasa ba wai su dakatar da ɓarnar ba, watau masu gadinsu suka mayar da jami'an?".
Chapter 176 · 0% Book details