← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 227

Sashe 23

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A yau zaku yi 200 push-up, 100 sit-ups, 80 burpees, 30 squats da kaya a baya, dik wanda ya kasa kammalawa a cikin mintuna 20, sai ya sake farawa daga farko". Sai ya rabasu team by team best on yadda suke 4-4 a É—aki.

Kun san meyasa yanzu yake rabasu team-team? Dan ya lura idan ya rabasu ya sanya masu kamar gasa suna zagewa, babu wanda yake É—aukar last, har Noor dagewa yake yi, kun san abu da gasa takan sa mutun ya yi har over acting ma.

Dan haka bayan ya rabasu team-team, sai ya ce. "Dik wanda É—an team nasu ya yi karshen gamawa, to dinka team É—in zasu sake farawa ne daga farko, team da suka yi karshe kuma, zasu yi frog jump 500 feets". Babbar magana.

Ai su Leo dik kai kallonsu a kan Noor suka yi, while shi ma su yake kallo, bawan ALLAH tin da yake bai taɓa push-up, ta ya za'ayi yau kawai ya fara kuma a zaci zai iya. Da sauri ya kawar da kallonsa daga kansu, dan yasan sai ya ja masu ɗaukar last.

Suna can suna tinani Captain ya ce. "Ready!....... Start"...…...... Cikin zafin nama kowa ya fara na shi, team ɗin su Unays sun zage, su ma su Zaysh sun zage sosai. Take suka fara haɗa gumi, amma dik da haka basu tsaya ba. Noor kam yana dai yi ne kawai, amma ba daidai yake yi bama, dan ko yadda ake ajiye hannu bai iya ba.

Da Captain ya ga dayawa daga cikinsu basu iya ba, sai ya ce wasu sojoji su koya masu. Cikin minti ɗaya wasu dakakkun sojoji suka yi wa wajen ƙawanya, take suka fara bankare su Noor, dan kun san koyarwa waɗan da suka sha horo kam ba a hankali zai biku ba. Tin Noor yana daurewa har ya fara kuka. Zaysh and Leo ne kawai suka iya jurewa, a wannan karon Unays ma bai iya ba, kuma bai iya jurewa ba, dan Unays ma dai renon ice cream ne, iyayensa manyan ƙusa ne a Naija, shi kuma Zaynash kun san dole zai iya, saboda wahalar da suka sha hannun Auntynsu, bawan ALLAH wuya tabi jikinsa already.

Shi kuma oga Leo yana da alaƙa kakkarfa tsakaninsa da AZURE wanda a nan ba zan faɗa ba, sai mun yi gaba, baa banza Captain Onbish yake jinsa a ransa ba, bugu da kari yana da alaƙa da manyan Generals na GIDAN SOJA ɗin, musamman GAT, wannan side ɗin na bari ne saboda wani sirri na labarin gaba zaku ji me alaƙarsu, amma suma basu san alaƙar ba fa, bugu da kari tin ainahi yana gym ba yau bane farau!.

Tin da Noor yake a gidan soja bai taɓa shan wahalar horo irin na yau ba, kafafunsa da hannunsa dik sun yi tsami, ya sha kuka sosai, ya kuma ci wahala, ya wahalar da team ɗinsa, dan sau uku su Leo suna maimaita wannan horo, tin suna hakuri har dikkansu idanu ya fara raina fata, yau harta Vash sai da ya yi ta kuka, Leo and Zaysh basu yi kuka ba kam, amma dai sun ɗanɗana a jikinsu, idanunsu ya yi jajir tamkar wuta, tin daga nan Leo ya kudurta a ransa cewa in dai haka ne daga yau Noor ba zai sake sanyasu faɗuwa ba, dan fa ba karya yau sun wahala, sama da 2 hours suna maimaita wannan horo, tin suna iyawa har dikkansu suka gaza, dik saura teams ɗin sun kammala horonsu sun bar wajen, amma su suna nan.

A ransa Leo ya ce lokacin gyarawa Noor zama ya yi, dan ba zai lamunta ba, babu abin da ya fi kona mashi rai irin last da team nasu ta ɗauka a yau, ya ji matuƙar zafin hakan. Da Captain yaga dik sun zube a ƙasa sun kwanta sai ya ce yau zai ɗaga masu kafa, amma wlh gobe dole sai sun kammala dukkansu a kan lokaci. Vash ya yi kuka har da majina, shi kan Noor ai faɗin irin kukan da ya yi ma ba zata yiwu ba, shi kuma Zaysh tin idanu na jajir har ta ciki da kwallah. Leo ne kawai bai yi kwallan ba, an dai ji jiki.

A tinanin vash za'a yafe masu sauran lokacin da ya rage ace su je É—aki su huta tin da sun gaji, sai ya ga akasin haka, saura awa biyu lokacin sallar jumma'a ta yi, a yau in suka yi sallar jummaa shikenan horo sai gobe, na faÉ—a maku ranar Jummaa suna da gajeran lokaci ne.

A wannan awa biyu da suka rage Captain ya É—aukesu suka nufi filin horo, ba zai iya yafe masu wannan awa biyun ba ko da zasu mutu. Dik sauran team sun kammala nasu har sun tafi horon sake koyan magana da ido.

Su kuma yanzu za su yi escape run, É—aÉ—É—aure masu fuska da hankey aka yi, aka É—aukesu a mota zuwa wani waje mai nisa da basu san ina aka nufa da su ba, kafafu da hannayensu dik zogi yake yi masu.

A wani waje mai cike da yashi aka saukesu, sannan Captain ya umarcesu da su koma sansani a cikin mintuna 70. Babbar magana, zazzare idanu suka fara yi, dan bama su san a ina suke ba, kallon juna suka fara yi, Captain kuma ya nemi waje saman bayan mota ya zauna, a natse ya ce lokacinsu ya fara daga yanzu.

Shiru suka yi suna ƙoƙarin ganin sun yi amfani da kwakwalwarsu......... (Dik yadda aka yi manyan sojoji suna tantama a kan kaifin kwakwalwar room 1 ne yasa suke son gwadasu, dan kuwa wannan horo sauran teams ɗin basu yi shi ba, akwai dalilin da yasa su aka masu hakan!.)

Sun ɗauki a kallah mintuna 5 a tsaye, sannan suka ɗan motsa, Captain ne ya ce masu. "In dai ɗaya daga cikinku bai isa sansani a ƙasa da mintina 70 ba to tabbas zaku sake farawa dikkanku, dan a cikin team kuke har yanzu".

Da jin haka yasa suka sake kallon juna. Leo kamar ba zai yi masu magana ba, amma da ya tuna ko ya yi kokarin ya koma bai kulasu ba in suka tsaya a baya shi ma za'a sake dawo da shi ne, tina haka ne yasa ya ware tafukan hannunsa yana rarraba idanunsa a kansu. Da sauri Noor ya matso ya É—aura nasa hannun a kan nasa, Vash and Zaysh da sauri su ma suka É—aura. Shiru Leo ya yi for 2 mins kafin ya ce masu. "Think with your brain". Yana kai karshe ya wuce gaba. Da sauri suka biyo bayansa.

Mamaki ne ya kamasu ganin daji ne a gabansu, bayansu duwatsu, gefen da gefensu bishiyoyi, da sauri Vash ya ce. "To ta wace hanya muka zo?"........ "Ta wannan dajin na gaban, cikin ciyayi kenan". A cewar Noor.

Da sauri Zaysh ya ce. "Kenan sai mu bi tayan mota ai".........Murmushi Noor ya yi tare da cewa. "Yes mun samo hanya, cikin sauki ma zamu koma"....... Vash ne ya amsa da. "Ashe ma ba wani wahala zasu ruÉ—amu". Murna suka fara yi sun samu mafita, har da wucewa gaba suka fara neman tayar motansu.

In a cool way Leo ya ce. "Before they brought us here, they kept driving around in circles to confuse us about the route, so following the tire tracks isn't the solution!!"....... Take murnarsu ya koma ciki, watau kenan sun shirya wahalar da su.

Noor ne ya ce. "Brothers me abin yi to?"...... Vash ne ya amsa da. "Gaskiya our senior are very smart, wato suka yi ta kewaye da motar dan sun san zamu ce zamu bibiyu taya"........ Zaysh ne ya capke da cewa. "Jahili baya yin AZURE BARRACK, dik wanda ka gani a nan É—an baiwa ne!".

Noor ne ya ce. "Mu yi ta tafiya kawai zamu samu hanya"....... Zaysh zai yi magana suka ga Leo ya juya ya koma baya in da Captain yake zaune a saman mota. A É—an nesa ya tsaya tare da kurawa motar idanu na 1 minute kafin ya juya ya dawo in da suke, gaba ya yi, kallon juna suka É—an yi kafin su rufa mashi baya. A bakin fita dajin gaban nasu ya tsaya, ya É—an lumshe idanunsa yana tinanin in da gate na parking lot na barrack É—insu yake, da ya tina gabas take fuskanta, sai ya tina motar da kawosu tana fuskantar yamma ne, hakan na nufin da suka fito barrack daga gabas sun juyo yamma ne, in kuwa haka ne barrack É—insu yana ta gabas ne. Bashi da tabbaci, amma yana tsammanin haka ne.

Dan haka cike da yakini da yarda da kai ya wuce gaba tare da cewa su Noor su yi sauri dan lokacinsu ya ja. Zuba mashi idanu suka É—an yi suna mamakin hanyar da ya nufa, dan su dai iya kallonsu basu ga alamar barrack É—insu a wajen ba. Amma sai suka yi hakuri suka bisa. Tafiya suka fara yi tin suna hira jefi-jefi kafafunsu na yi masu zafi har suka yi shiru.

Sun yi tafiyar good 40 mins kafin su isko hanyoyin sun rabe biyu, tsayuwa suka yi a wajen suna kallon Leo, shi kuma ƙoƙarin tinano yanayin hanyoyin da suka bi a lokacin zuwa ya yi, dik da cewa idanunsu a rufe, yana iya tina kwana nawa suka yi a lokacin da suke cikin mota, tabbas kwana biyar suka yi, a farkon kwanansu sun fita barrack ba jimawa ne, kuma shi kaɗai ne kwanar tsakani da ALLAH sauran kwanan dik an yi ne dan a rikitasu.

Idan kuwa haka ne to kwana zasu yi, É—ayar hanyar zasu bi, kuma daga in da suke babu nisa da barrack. Dan haka sai ya bi hanyar da ta rabe ta yi kwanar. Jikinsu dik ya jigata, da kyar suke tafiya a yanzu. Sai dai duna yin kwanar basu wuce tafiyar 10 mins suka yi ba sai ga barrack É—insu sun hango. Ai tsabar murna Noor bai san lokacin da ya wastsake ba, cikin farinciki ya rungumi Vash, sai suka daure suka É—aga kafafu dan karisawa.
Chapter 23 · 0% Book details