← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 227

Sashe 151

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ruwan sama yaf-yaf-yaf ya fara sauƙa a kansa, iska mai ɗan sanyi ya fara kaɗawa, alamar an yi babban ruwa a nesa da su. Lokaci guda hadari ta taso gadan-gadan, iska mai karfi da guguwa suka turnuƙe dajin, tsawa da walkiya ya fara yi. Hakan yasa dikka sojojin suka koma kusa da tantunansu except Leo dake tsaye bai motsa ba. A cikin ransa yana saƙa yadda za'a wayi gari ace sun gyara duniyar nan, sun tsabtacesa daga dik wasu gurɓatattu.

Noor ne ya fito daga cikin tantinsu sanye da army trouser da tactical tshirts a jikinsa. Yana fitowa dik sojojin dake wajen suka ƙame tare da fara sara mashi........ "Ina Leo?". Ya faɗa a dake.

Arya dake cikin tantinsu ne ta fito da sauri jin ya ambaci sunan Leo, tana fitowa ta ƙame game da sara mashi. Jinjina mata kai ya yi....... Ɗaya daga cikin sojojinsu ya ce. "Sir Leo yana bakin ruwa". Nan ma kai ya jinjina alamar to.

Sai ya nufi hanyar bakin ruwan, har ya É—an yi step 2 sai kuma ya juyo, kai tsaye ya nufi cikin............

Likes comments and share fisabilillah.

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️

QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥

🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

For more information 08161390581 Whatsapp me only.

STEP 1🔥

2025-12-12.🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E_____________ 51 & 52

DEATH OR LIFR (DOL)🔥

Sai ya nufi hanyar bakin ruwan, har ya É—an yi step 2 sai kuma ya juyo, kai tsaye ya nufi cikin É—akinsu Arya É—in. A tsakiyar É—akin ya tsaya, ya zuba mata idanu, tana zaune saman electric mattress É—insu, ta sanya bluetooth a kunne, dik iskar dake tashi bata da labari.

Angelina dake zaune gefenta ne ta taɓata game da cewa. "Ke". Ɗago kanta yi daidai lokacin da take cewa. "Kai ma muryanka na da daɗi ai causin.......". Gagara karisa maganar ta yi a lokacin da idanunta suka sauƙa a kan angry face ɗin Noor.

Da sauri ta zabura ta miƙe tsaye, wani irin mugun kallo ya dallah mata wanda bai san ya yi ba, in a harsh way ya ce. "Da waye kike waya?"...... Da sauri ta cire bluetooth na kunnenta, hannunta na ɗan kerma, dan gabaɗaya yadda ya ɗaure faska ya razanata, murya na ɗan rawa ta ce. "Wani..... Wan.... Wani brother ɗina ne".

Wani kallo da ya wurga mata ne yasa ta haÉ—iyi yawu gwad...... "Ashe kina da brother kenan?". A faÉ—a...... Kallonsu Angelina da Manassa suke yi, while Manassa na ta faman rikita hankalin Vash dake cikin tantansu, ta gama ce mashi wai ta gani a in da yake ana ruwan sama, kuma zata kawo mashi ziyara daren yau, dik ta rikita bawan ALLAH, wlh ya yarda aljana ce.

"No, he's my Aunty's son, tare muka yi school, mother É—insa sister É—in dad ne.......". Hannun da ya É—aga mata ne yasa ta haÉ—iye sauran maganar. Cikin fushi ya ce. "Kuma kike cewa he have a sweet voice ko?"..

Tsuru-tsuru ta yi da idanu, dan bata zaci ya ji ba, kuma wlh ita ba da wata manufa ta faÉ—a ba, kawai guy É—in ya ce mata your voice is so sweet shi ne ita ma ta ce naka ma da daÉ—i, kun gane irin wannan abin ai? Wai ka É—an mayarwa mutum magana mai daÉ—i, ashe sarkin kishi kuma lover boy É—inmu ya jita.

Jama'a watau family ɗin Noor duniya ne, lovers ne, ga kishin balai da iya shagwaɓa.

Kai ya É—an jinjina. "Your voice is so sweet". Ya maimaita yana É—an jinjina kai....... Zata yi magana daga cikin wayar guy É—in ya ce. "Vanisha are you okey?".

Ta ɗan zazzare idanu a kan face ɗin Noor kafin ta ce. "Nothing Yosif"..... "I hear like kina magana da wani, who's he?"......... Ƙara zazzaro idanunta a kan Noor ta yi. Daidai lokacin su Angelina suka mimmiƙe tsaye suna kallonsu. Wani irin kallo Noor yai mata like ki bashi amsar da waye kike magana!.

ÆŠan tattauna lips É—inta ta fara yi. "Yosif bye". Tana faÉ—a ya katse kiran. Muryarta na É—an rawa ta ce. "My Romeo.......". Bai jira jin me zata ce ba, waje ya nufa cikin fushi.

Da gudu ta rufa mashi baya, a tsakiyar wajen tantin nasu ta tare gabansa, kamar zata yi kuka ta ce. "Please my Romoe, isn't what you're thinking......".

In a harsh way ya ce. "How do you know that I'm thinking something? Or you're hiding something for me right?!"...... Kai ta fara girgiza mashi, kawai tasan yadda ya fita nan ne zai yi tinanin ko soyayya take yi da wani, shiyasa ta ce isn't what he's thinking, amma ya sake fassarata ta wani sigar.

Raɓawa gefenta ya yi zai wuce, a lokacin ruwan saman ta fara karfi sosai. Da gudu ta juya, ta ruga ta faɗa bayansa, ta ƙanƙame shi tightly, hakan yasa dikkan sojojin dake kallonsu suka yi ƙasa da kai dan girmanawa a garesa. Tsalle ta yi ta haye bayansa, ta saƙalo wuyansa.

Aikuwa cikin fushi ya dawo da ita ta gabansa, da karfi ya yakiceta daga jikinsa, ido cikin ido ya kalleta, ga ruwa na zuba a kansu, a fusace ya ce. "Kada ki sake taɓani, ina baki wannan umarni ne ba amatsayin masoyinki ba, sai a matsayin oganki!!". Yana gama faɗin hakan ya saketa tare da tureta gefe, ya wuce ya nufi bakin ruwa.

Abinku da bata taɓa faɗa da shi ba, durkushewa ƙasa a wajen ta yi, kuka ta fara yi, ALLAH sarki bata san komai ba sai soyayyansa, slowly ta kifa kanta a ƙasa, wani irin kuka ne ya kubce mata. Da gudu Angelina da Manassa suka yo waje. Angelina ce ta watsa da gudu ta yi kanta, a cikin ruwan ta je ta rungumota tana bata hakuri.

Takaici tamkar Arya dake tsaye a bakin tantin ta rufesu da duka, sun zubar mata da mutunci a cewarta, siririn tsaki ta ja tare da komawa ciki abinta.

Daidai lokacin Unays ya fito, ganin Angelina a cikin ruwa ne yasa ya yi gaggawar shiga ciki shi ma, ya isa daidai lokacin da Angelina ta ɗago V, sai dai V na ta famar langwaɓewa tana a barta a cikin ruwan ita kam. Sai hakan ya zamana kamar ta fi karfin Anglina ta gagara ɗagata.

Ganin hakan yasa Unays ya ce. "Let me help you, bari in kai maki ita ɗaki". Ya faɗa yana matsowa zai ɗauketa wai irin shi zai taimakawa Angelina ko zai zamu ya sace zuciyarta, taƙi kulashi ne, yana ta neman dama....... Matsawa baya Angelina ta yi tana faɗin thanks.......... Hannu yasa zai cicciɓi V, sai kuma ya tsaya cak, da sauri ya ja da baya daga kusa da ita kallonsa a kan Noor dake nufosu tamkar wani zaki, shi da Leo duns bubbuɗe kamar zakuna, ya nufo wajen yana dallahwa Unays ɗin wani irin mugun kallo mai kama da ka taɓata kaga yadda zan yi da rayuwarka.

"Ki ɗauketa kawai". Unays ya faɗa yana ƙara ja da baya game da mai da kallonsa a kan Angelina ɗin. Ta yi mamakin jin ya fasa taimaka mata, ita kanta V mai kukar ta yi mamaki. Slowly ta ɗago kai karaf suka yi 4 eyes da Noor. Ƙara ɗaure fuska tamau ya yi, ya ɗauke kallonsa daga kanta, ya zo ya wucesu tare da Leo.

Angelina ta gane karatun, watau Noor ne ya hana Unays É—aukar V, ya ALLAH kaga wata soyayya da kishi ga fushi a gefe, kai Noor akwai rigima wlh, ya dai yi fushi, amma ba zai bari wani ya kusantota ba........ Sai dai ita V É—in bata gane ba, ta zaci ya daina sonta kenan, shiyasa take ta faman kuka.

Arya kuwa tana komawa ciki ta hau aikinta na duba drone da suka tasa a wannan daji, ta share su V, a cewarta basu da hankali sam-sam.

Tantin Leo suka shiga shi da Noor, a saman electric mattress ɗin Leo suka zauna, Noor ya yi ƙasa da kai tamkar mai tinanin wani abu, kallo ɗaya Leo yai mashi ya ɗauke kai tare da faɗin. "What are you thinking?"....... Nisawa ya ɗan yi. "My Jeliet, na wuceta tana kuka, zuciyana tamkar ba zai iya ɗauka ba".

Wani kallo Leo ya wurga mashi like baka da aikin yi, daga nan yai shiru bai yi magana ba. A daidai lokacin Arya ya faɗo ɗakin bakinta ɗauke da excuse, sai da ta faki idanun Leo ta dallah mashi harara kafin ta ƙame ta sara mashi. Noor ya ganta sarai, a cikin ransa ya ce. "Ban san me yake tsakaninsu ba, kullum sai Arya ta harari brother ɗina, anya ba son shi take yi ba?".

Shi kuwa Leo yana zaune shiru bai motsa ba bare ya É—ago ya kalleta, a dake ta ce. "Sir, there's something you should come and see!". Kai kawai ya É—an jinjina ba tare da ya É—ago ba. Juyawa ta yi ta fita, amma kafin nan sai da ta dallah mashi mugun harara.

Tana fita ya miƙe tsaye, kayan jikinsa ya fara ragewa, shi kuwa Noor ya gyara ya kwanta cike da tinanin V a ransa. Pjs jade color kalar idanunsa Leo ya sanya a jikinsa, ya tara kitson kansa ya ɗaure da kyau kafin ya sanya winter coat a saman pj's ɗin, sannan ya sanya beanie, beanie wata hular sanyi ce irin mai laushi sosai ɗin nan. Bayan ya kammala ya fita ya nufi room nasu Arya. A lokacin Angelina ta yi ta maza ga ɗauki V sun shige cikin tantin nasu.

Zaune ya isko Arya gaban laptop É—inta tana duba dajin da kyau. Jin kamshin perfume É—insa yasa ta É—ago kai, zuba mashi idanu ta É—an yi, while shi kuma yana kallon gaban screen na laptop É—inta.
Chapter 151 · 0% Book details