← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 207 OF 227

Sashe 207

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Siririn tsaki Arya ta ja tare da kama hannun Jehan suka fito daga cikin ruwan, bathrobe É—inta ta sanya game da É—aukar sauran kayanta suka nufi sansanin nasu. Sai dai suna isa suka isko gabaÉ—aya fulanin a tare waje guda, sun durkusa a kan gwiwowinsu, dik sun yi tsuru-tsuru da idanunsu da suka yi jajir, ido ya raina fata, sun ci jibga a hannun sojojin AZURE. Zaynish ne ya umarci sojojinsu da su tattabkesu da bulala, su zanesu da kyau sai sun gane wajen wuta suka kawo kansu.

Aikuwa sojojin suka ciro zabga-zabgan bilalu suka rakasu, suka fara basu a jikinsu, suka daka masu tsawa kan su taru waje guda, sannan suka dinga zane masu jiki har wajen huts ɗinsu suka je suka kamo waɗan da suka gudu suka dawo da su, zanesu da kyau suka yi, Leo yana ɗaki ko leƙowa bai yi ba, Noor ma yana ɗaki da V dake barci, while Vash yana ta baya yana waya da su Ammie. Shi ma Zaynish ya fito yana waya da Aunty Ummie ne Fulanin suka iso kansa da sanduna, wai zasu dakesa, aikuwa ya ce bashi da lokacinsu, ya umarci sojojinsu da su zanesu, kada su harbesu da bindiga ko su ji masu ciwo, a'a, bulala zasu masu shi ne daidai da su, dan rashin duka ne yake damunsu.

Ganin dik suna durkushe a tsakiyar tantunan nasu suna kuka ne yasa Arya dawo da kallonta a kan Manassa kafin ta ce. "WaÉ—an nan ne suka zo kashe mu É—in?"...... Waige-waige Manassa ta fara yi..... "Yeah su ne".

Tsaki Arya ta ja game da wucewa cikin tantinsu tana jan hannun Arya, dan in ta tsaya tana iya sumar da mutum, dik takaici ya rufeta. A gurguje ta shirya dan tasan Leo na jiranta, a hanzarce ta ɗauko breakfast ɗinta suka ci tare da Jehan, ta dinga baiwa yarinyar a baki har sai da ta tabbatar ta ƙoshi, sannan ta ci nata, bayan sun kammala ta ɗauko biscuit daga rucksack ɗinta ta baiwa Jehan kan ta ci, sannan ta jawo laptop ɗinta.

A gefenta Manassa da Angelina suka zauna, Angelina ta ce. "Manassa ina son sir Zaynish fiye da yanda kike tinani, ya haÉ—u fiye da yadda kike tinani, jiya kin san har mafarkinsa na yi?". Wani irin harara da Arya ta dalla mata bata san ma ta yi shi ba, ta É—auke kallonta daga kansu ta mayar kan laptop É—inta.

Manassa ta ce. "Gaskiya ya haÉ—u, amma fa zaki sha bakar wahala a kansa, dan naga ko kallon mutane baya yi, ga fuskansa kullum a tamke"...... Angelina zata sake yin magana Arya ta katseta da cewa. "Aiki nike yi, kuna damuna da shirmen banza, ku je waje idan hira zaku yi".

Harararta Angelina ta yi game da cewa. "Bari ki ga wani abu Manassa, ke kula Arya ki yi abin dake gabanki babu ruwanki damu". Ta faɗa tare da jawo wayarta. Number Aunty Ummie ta fitar, kira ta danna mata tana cewa Manassa. "Sister ɗinsa ce, daren jiya sun yi waya, bana jin yarensu but na fahimci sun shaƙu sosai, tana da kyau matuƙa, kin ganta kuwa? Kamar tauraruwa, har cikin raina ina sonta sosai". Angelina ta faɗa a lokacin da wayar ya fara ringing.

Zazzaro idanu a kanta Manassa ta yi. "Ke ina kika samo nunber sister É—insa kuma?". Cike da mamaki Manassa ta tambaya..... Yatsa Angelina ta É—aura mata a saman lips É—inta alamar ta yi shiru, shirun ta yi a daidai lokacin Aunty Ummie ta É—aga kiran tana sallama.

Cikin harshen turanci Angelina ta ce. "Hello Aunty"...... Mamaki ne ya É—an kama Aunty Ummie jin turancin turawa, sai kuma ta tina kila daga wajen aikin su Zaynish ne, dan haka sai ta natsu sosai saboda ta iya fahimtar turancin, kunga ba wani iyawa sosai ta yi ba.

Cike da girmamawa sosai Angelina ta ce. "Good morning Aunty"....... "Morning how was your night?". Cikin rawar murya Aunty Ummie ta faÉ—a....... Angelina na murmushi ta ce. "Cool. My name is Angelina, from AZURE barrack, babban friend É—in sir Zaynish, shi ne ya ce in kiraki mu gaisa". Cike da tsoron abin da zai je ya zo na karyar da ta yi mashi ta yi maganar.

Aikuwa washe baki Aunty Ummie ta yi, abinku da jininmu mutanen amana, kun sanmu da alkunya, Aunty Ummie ta ɗauka budurwarsa ce ya ce ta kirata, ta ɗauka kunya ce yasa Angelina bata ce ita budurwarsa ba ce, aikuwa ta yi matuƙar farinciki, ta tarbi Angelina da kalamai masu daɗi, cikin zolaya ma ta ce. "Ko dai kece surukar tawa?".

Angelina murmushi sosai tamkar ba zata dakata ba, ta ji matuƙar daɗin yadda Aunty Ummie ta karɓeta, sai ta ce. "Eh...... A'a..... Kawai na kira ne in gaidaki, muna aiki, in ba damuwa zan iya dinga kiranki muna gaisawa Aunty?".

Aunty Ummie ta ɗauka Angelina kunyarta take ji yasa take mata kwana kwana, bata san nan yaran GAT basu san kunya ba, kawai tsoron Zaynish take ji yasa taki sakan jiki su sha hira. Cike da nuna kulawa Aunty Ummie macen kirki ta ce. "Ko baki kirani bama ni zan dinga kiranki ina jin ya kike! Tin da daga ke har shi kunki faɗa mun kece surukata to ki kula mun da shi sosai, kada ki bari komai ya damesa, sannan ki saki jikinki, ni Auntynku ce gabaɗaya, dake da shi dik ɗaya na ɗaukeku". A goggece ta yi turancin, amma zaka iya fahimta sosai. Ta faɗa a cikin ranta tana cewa. "Watau already yana da budurwarsa, kunya ce yasa yaki faɗa mata, amma da jiya ta ce zata samo mashi mata shi ne kenan yau yasa budurwar tasa ta kirata, lallai ma, to tasan me zata yi mashi ɗan ƙaniya". A fili kuwa murmushi kawai take yi tana sauraran Angelina ɗin.

Angelina ta fahimci turancin Aunty Ummie sosai, sai ta ce. "Thank you so much Aunty, i really appreciate"....... Cike da zumuÉ—i Aunty ta ce. "Ki tura mun hotunanki ta Whatsapp mana, ina son ganinki kanwata".

Sosai ta ji daɗi game da rungume Manassa da ta kafeta da kallo tana faɗin bari ta tura mata yanzu, ita ma Aunty Ummie sosai ta ji daɗi, da haka suka yi sallama cikin mutunta juna da girmamawa. Whatsapp Angelina ta shiga, a take ta zaɓo hotunanta tsala-tsala masu kyau ta tura mata guda biyu, sai ta ɗauko wanda suke su huɗu gabaɗaya ta tura mata game da ce mata su ƴan huɗu ne ga sauran sisters ɗinta.

Aikuwa Aunty Ummie na online, da sauri ta buɗe hotunan, har hannunta na rawa wajen ganin ta buɗe. Ya rabb, tana yin tozali da ɗiyar GAT ta ji Angelina ta kwanta mata a rai, yarinyar ta haɗu, bata damu da yanayin shigarta na ƙananan kaya ga kai ba ɗan'kwali ta saki gashi har baya ba, ita dai yarinyar ta kwanta mata tin da Zaynish da kansa ya ce ta kirata ai shikenan.

Tana buɗe hotonsu su huɗu sai ta ruɗe, a take a wajen ta ce lallai Zaynish ya samu mata, ai ko dan fatan da take yi na ya haifa masu yara dayawa zata so ya auri Angelina, ALLAH yasa a haihuwar farko ta haifa masu ƴan huɗu kamarta, su biyu iyayensu suka haifa, ga shi ita bata taɓa haihuwa ba, shiyasa ta matsu ya yi aure ko daga gefensa za'a samu haihuwar, ta matuƙar matsuwa ya yi aure, dan haka tana jin Angelina ƴan huɗu ne ta ce shikenan ga matarsa.

Cike da farinciki ta dinga yabon kyan Angelina ta hanyar yi mata typing ta tura. Angelina ta ji mugun daÉ—in wannan abin, ta dinga yi mata godiya, Aunty Ummie ta tsare hotonsu su huÉ—un da kallo, lokaci guda ta ji V ta kwanta mata a rai bayan Angelina, V akwai shiga rai sosai, sai addu'a take yi ALLAH yasa rabon Zaynish ne Angelina, ALLAH yasa tashin farko su haifa mata Æ´an huÉ—u dikka maza, sai ta sake haifa masu Æ´an huÉ—u dikka mata, addu'a sosai ta dinga yi kafin ta turowa Angelina hotunanta kala uku ita ma, É—ayan ita da Zaynish ne wancan zuwansa gida hutu suka É—auka, biyun kuma ita kaÉ—ai ne a shagonya.

Wai jama'a a ina Angelina ta samo number Aunty Ummie ne? Ku bini in faÉ—a maku. Datsan wayar Zaynish ta yi, kun sansu mayun computer, a nan ta ciro number, shi bashi da number mutane dayawa ma, daga na uncle É—insa, sai na Aunty Ummie, sai kuma nasu Leo watau sojojin da suka taho Mission tare, aikuwa number Aunty Ummie ne kawai ya yi saving da special suna, sauran kowanne sunansa ya sanya mashi, dan haka ta É—auki number, da farko ta zaci budurwarsa ce ganin irin sunan da ya sanyawa number, sai da ta shigar da number laptop É—inta ta yi bincike, a nan ta samo hoton Aunty Ummie da aka yi register sim É—in, sai taga ai hoton matan jiya ne, nan ta gane ashe number sister É—insa ce ba budurwa ba, kun ji yadda aka yi.

Angelina ta yi murna matuƙa, ta dinga kallon Aunty Ummie tana ƙarawa, ta kira Manassa kan ta ganta, tsare hoton da kallo Manassa ta yi, sai ta hau yaba kyan Aunty Ummie, kai Aunty Ummie akwai shiga rai ita ma, saboda kyawawan ɗabi'unta.

Hoton Aunty Ummie da Zaynish Angelina ta sanya a wallpaper É—inta, ta dinga yabon African hair É—insa, na buzaye dake gwanin burgewa, ya rungumo shoulder É—in Aunty Ummie game da É—an rage tsawonsa ya kwanto da kansa ta gefen wuyanta, ya fita tsawo sosai, hoton ya yi bala'in kyau.

Tsaki Arya ta sake ja game da cewa. "Ku fice mun daga É—aki, kuna damuna da shirmenku".

Angelina zata yi magana sai ga wani dakakken soja ya tsaya a bakin tantin nasu, muryansa a fashe kato ya ce. "Sir Zaynish yana kiran Angelina, yana cikin tantinsa". ....... Zazzaro idanu a kan Manassa ta yi, sai kuma amsa da gata nan zuwa. Ko kallon in da suke Arya bata yi ba, ta kara jawo laptop É—inta dab ita ta fara duba drones da ta tura tana kallon Jehan dake gefenta time to time, dik wani information masu muhimmanci tana turawa Leo, a lokacin shi kuma yana waya da Aryan, sai kara mashi kwarin gwiwa Aryan yake yi.
Chapter 207 · 0% Book details