← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 227

Sashe 145

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan a cikin jinin akwai sinadarin erythropoietin, sinadarin da ke samar da jan jini, a likitance ana ce mashi red blood cells, sannan akwai sinadarin fetal hemoglobin da suke cirewa, wannan nau’in haemoglobin ne da ke cikin jinin jariri, wanda ke da ƙarfin ɗaukar iskar oxygen fiye da na manya. Sannan akwai sinadarin mesenchymal stem cells, da interleukins & growth factors, sai alpha fetoprotein, wanda a hankali zan faɗa maku me suke yi da waɗan nan sinadaran, tare daku zamu zaƙulo komai mu warware In Sha ALLAH. Kun ji na jinin, to shi kuma ɓargo fa?.

Akwai sinadarin wharton's Jelly da suke amfani da shi a ɓargon jariri, wannan wani abu ne mai kama da jelly da ke cikin ɓargon ƙashin jariri wansda sai sun firgita jariri jikinsa ke sakin wannan sinadarin ta yadda in sun kashesa zasu iya samu, wannan sinadari yana ɗauke da hyaluronic acid da collagen, a yanzu ba zan faɗa maku me suke yi da sinadaran nan ba, dan tashin hankalin zai maku yawa, amma gaba zaku ji komai In Sha ALLAH.

To bayan wannan sinadari na wharton's akwai glycosaminoglycans, da kuma chondroitin sulfate, sannan akwai exosomes, da umbilical cord stem cells da dik suke amfani da shi daga cikin ɓargon ƙashin jariri, wanda in muka natsa cikin labarin zaku ga komai dallah-dallah da idanunku, zan daure in rubuta maku komai, ba zan rage koda abu ɗaya ba In Sha ALLAH! Yadda na tsara labarin nan, dik taɓa zuciyansa ba zan canza ba, na sha kuka wajen rubutasa tamkar raina zai fita, amma haka na daure, ina typing ina kuka saboda tashin hankalin ya kai tashin hankali, ace da jinin jariri suke haɗa wasu magunguna, jaririn da bai ji ba bai gani ba, bai san komai ba, ba imani ka ɗauki jariri kasa inji ta marƙaɗa shi, ya rab, wai wani irin zuciyace a kirjinsu 3D?.

Ga wasu sinadaran da suke cirowa daga ɓargon ƙashinsu, ya ALLAH, ko waɗan nan sinadaran kuma me suke yi da su? Alƙalamina zai waware maku komai.

Kwashe komai tas suka yi, suka fita da jinin izuwa wani ɗaki dake kusa da wajen, a nan suka ajiyesu cikin wani katon freezer, sannan suka fito daga cikin wajen, sai gobe za'a fara ƙoƙarin haɗa magunguna, dama kashe jariran kawai suke yi cikin tsakiyar dare yadda babu ma wanda, zai gansu.

Suna fitowa SECTION D Dr James ya koma. Su Dr Kamal kuma suka koma gidansu, wlh bawan ALLAHN nan Dr James tamkar ba jarirai rai biyar ya danna cikin inji ta niƙasu ba, ko kaɗan bai damu ba, ya shiga cikin ɗakin da su Zinta suke, tana barci ya saɓeta a saman shoulder ɗinsa ya fito, kai tsaye gidansu ya koma, dama in baku manta ba ɗazun ya ce mata anjuma zai sake yin abin da ya yi da ita ai, to shi ne ya zo ɗaukarta.

Ya ilahi, me suke yi da waɗan nan sinadaran da suke cirewa daga ɓargon ƙashin jariri? Mesuke yi da sinadarin cikin jinin jaririn? Daga gani abubuwa masu muhimmanci da tsadar gaske suke yi da su, ki tsaya ki karanta abin da suke yi da sinadaran. Watakila kema kina amfani da wannan abin bisa rashin sani! Sai ki san me kike amfani da shi!.

Tambaya shin idan su Maya suka farka zasu gane an É—auki jarirai guda 5? Ko ba zasu gane ba? Idan suka gane me zasu yi? Wani mataki zasu É—auka? Ya rabbi, idan kana raye babu abin da ba zaka gani ba, ya ALLAHU ka kawo mana karshen dik wata fitina, ALLAH ka dubemu da idanun rahama.

Likes comments and share fisabilillah.

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

For more information 08161390581 Whatsapp me only.

STEP 1🔥

2025-12-12.🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E_____________ 49 & 50

WS-HOSPITAL.

Kai tsaye room É—insa Dr James ya wuce da ita, bai direta a ko'ina ba sai a saman bed É—insa. Toilet ya wuce, sai da ya yi wanka saboda wajen jini da suka je, ya tsabtace jikinsa fes, sannan ya dawo cikin É—akin, jikinsa sanye da bathrobe ya haye saman bed É—in, jawota jikinsa ya yi, ya fara sarrafata cikin salon kwarewa.

Can cikin barci ta ji ana taɓa mata jiki, a hankali ta waro idanunta, kai tsaye sai saman face ɗinta, dik da cewa dim light ne a kunne, amma tana iya ganin fuskansa sosai. Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa. "Sir"......... Ɗan kwantowa kanta kaɗan ya yi. "Da sir yakamata ki dinga kiran mijinki ne?". Ya faɗa yana shafe cikinta.

Kai ta girgiza mashi, fuska É—aure da kyakkyawan murmushin nan nata da bana fatan in daina ganinsa a kan fuskanta ta ce. "Sorry oga".

Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali, yana jin wani irin azababben sonta na ƙara shigarsa matuƙa, shi kaɗai yasan irin matsayin da take da shi a cikin zuciyarsa, ita ma ita kaɗai tasan irin son da take yi mashi.

"My oga please ka kaini in ga darling ka ji?". Ta faɗa cikin raunin murya, da alama da yaron nan a ranta ta yi barci, sun gagara mancewa da shi ko na second ɗaya ne....... Ɗan rintse idanu ya yi, ya ji haushi, tana neman ɓata mashi darensa mai daɗi. Can ƙasa ya ce. "Zuwa da gobe idan muka tashi aiki zan kaiki ki gansa". Ya faɗi hakan ne kawai cikin tsananin mayen sonta da yanayin da yake ciki, amma batu na gaskiya ba zai iya kaita in da darling yake ba, dan izuwa yanzu cutar ta gama yawace gangar jikinsa, dik wanda ya kusancesa zai kamu ne, suma 3D sai sun yi using care overall da oxygen dan kada su shaƙi iskar numfashinsa a ɗakin da yake a ciki, suna shaƙa zasu kamu a cutar ne suma.

Jin cewa zai kaita wajensa gobe ne yasa ta fara murna tana farinciki, nan ta saki jiki, ta bashi haÉ—in kai, sosai ya yi romancing É—inta, ya gigitata ya sanya ta har da kuka, amma kamar É—azun ne, bai tare da ita ba, iya wasa ya yi har ya yi realizing abin dake damunsa, ya samu natsu sosai.

Ɗaukarta ya yi suka shiga toilet, kun sansu da kunya sosai, sai faman ɓoye fuska take yi, shi kuma shugaban marasa kunya na duniya, wai ta mashi wanka, ta ce a'a ita kam ba zata iya ba.

Suna shiga cikin jaccuzi ya jawota jikinsa, daga shi sai shorts, ya so cire shorts É—in ma ta dinga mashi magiya kada ya cire, saboda son da yake yi mata ya hakura ya shiga cikin ruwan da shi.

Mara kunya dik ya cire mata kaya, yasa dik ta takure waje guda, tana ta faman dukunkunewa, ya jawota jikinsa, haka ya dinga wasa da ita a cikin ruwan nan, sai da ya sake realizing round 2, sannan ya ce su yi wanka, dare ma ya yi.

A natse suka gudanar da komai, ya bata bathrobe ɗinsa ta sanya, yau tana jin tamkar wacce akaiwa kyautar duniya da abin dake ciki, sai murna take yi. Ɗaukarta ya yi, sai kan gado ya direra, tana ce mashi zata sanya kaya a jikinta, ai ina, jawota jikinsa ya sake yi, ya ja masu bargo. Can ƙasan maƙoshi ya ce ta yi barci sai da safe in zata koma wajen babies ta sanya kayanta, yanzu taka tare da mijinta ne, ya hutar da ita sanya wani sleeping dress.

Soyayya, soyayya shegiyar aba ce, sai ta kwanta luff a jikinsa, yana É—an shafa bayanta har barci tai awon gaba da ita, shi ma ba jimawa barci ta É—aukesa. ASUBA TA GARI.

---------------------------🔥

Washegari da su sister Zinta suka zo basu fahimci an É—auki jarirai guda biyar ba, saboda in baku manta ba Dr Mark ya cire gadan babys É—in ai. Kamar kullum, shirye-shiryen yi wa dikka jariran wanka suka fara yi. Zama sister Zinta ta yi a gefen gado tana É—an dafe mararta dake murÉ—a mata a hankali.

A kusa da ita sister Maya ta zauna tana faɗin. "Sis lafiya kika zauna?"..... Tana ɗan dafe ciki ta amsa da. "Cikina na ciwo, ina ganin menstruation ɗina ne, dama tin daren jiya nike expecting ɗinsa"..... Siririn murmushi sister Maya ta yi kafin ta ce. "Na ƙosa nima in fara wannan period ɗin dan in ji me kike ji da kullum kike kukan ciwon ciki idan zaki yi"........ "Uhm da kin fara zai isheki ne, ga ciwo ga wahala". Ta kai karshe tana ɗan kwanciyar rigingine ko zata ji sauƙin ciwon da cikin nata yake yi mata.

Nasan yanzu tambayoyi sun gama cika maku kai kan cewa ya aka yi sister Maya bata fara period ba kuma bayan shekarunsu ɗaya da sister Zinta ko? Kuma ace 18 years old bata fara ba, abin da mamaki ko? To haka ne, yadda kuka ji ne, Maya bata period, bata taɓa yi ba, bata san ya yake ba. Kun tina cewa Dr James ya ce zai auri sister Zinta, ita kuma sister Maya zai mai da ita PA ɗinsa? Kun tina wannan magana?.

To ba Maya kawai ba, dikka nurses dake cikin wannan hospital É—in basa period! Zinta ce kawai take yi! Amma saura nurses É—in dikka shiru ne, ga shi dai shekarunsu É—aya watau 18 years, amma basa yi. To dikkansu 3D sun cire masu mahaifa ne, babu mahaifa kuma ai kunga babu zancen period ko? Su dama dan su yi aiki 3D suka kyankyashesu ba dan su haihu ba, shiyasa 3D É—in suka cire mahaifansu gabaÉ—aya, to sister Maya na daga cikin waÉ—an da aka cirewa Mahaifan.
Chapter 145 · 0% Book details