Sashe 74
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai bayan sun dawo gida ya duba wayansa ya ga saƙonta, one side smiling ya saki kafin ya rubuta mata reply kamar haka, na faɗawa daddy abin da muka yi daren jiya ne shiyasa ya kara sonki, ya ji zaki haifa mashi jika da wuri....... Da jin haka sai ta ji ta yi danasanin hana Noor kanta da ta yi, dan yadda daddy ya damu yake son jika gaskiya bata kyauta ba da ta zama bata bari sun kama hanya ba, amma da ta tuna ai Noor zai dawo gobe, suna da lokaci a tare, sai kawai ta ji daɗi.
In kara takaice maku labarin nan after one day su Noor dik suka yi wa AZURE diran mikiya, a rana guda dik suka dawo saboda basa wasa da lokaci. Harta Zaynish ya dawo, amma fa kafin ya dawo sai da ya saita gidan Ummie, tin daga kan uwar mijinta, uban mijin nata, wannan shegiyar Auntyn nasu, gabaÉ—aya kannen mijinta tattarasu ya yi, ya basu capital warning, ya ce masu wlh a kan Ummie ba irin hukuncin da ba zai masu ba, zai iya sanya bindiga ya harbe mutum kuma ya harbe banza! Shi ba sojan Nigeria bane a yanzu, karkashin ikon gwamnatin AVARIS yake! Yakamata su san wannan, dan haka su shiga hankalinsu.
Ko da zai dawo kuma bai bari Ummie ta sanar masu cewa ya koma ba, ya ce mata kada ta gwada masu ya koma, dan zasu iya cigaba da yi mata iskanci, yanzu dai biyayya sama da ƙasa ake yi mata, har amarya da aka sha jinya aka dawo, yanzu zaman lafiya take da Ummie, ai dik wanda ya sha dukan soja so ɗaya ko a mafarki ba zai so ya sake haɗa hanya dashi bama bare duka, mutanen da in suka mareka sai ka ji kamar ba'a duniya kake ba, kunnenka ya daina jiyo sautin komai, dole amarya ta natsu. Yanzu dai Ummie ta samu saukinsu sosai, kannen mijinta mata Aunty sama Aunty ƙasa, marasa kunyar karya, ai komai waje yake samu, yanzu dai dik sun haɗa malaman jikinsu, wata mara kunyar kaunar Faisal ɗin ma wai son Zaynish take yi, ta tattaro kayanta dik ta dawo wajen Ummie, sai ladabi da biyayya take yi mata, har aiki dik ita take yi mata, burinta kawai ta dinga ganin Zaysh da har ya gama zamansa a gidan bai taɓa ɗaga ido ya kalleta ba, magana wannan baya yi wa mutane kuma baya amsa nasu idan sun yi mashi, idan kun ji Zaysh yana magana to da Ummie ne, bayan ita sai Faisal da suke waya, idan ba su ba sannu baya haɗa shi da kowa.
Da Ummie tai mashi maganar aure zai ce ta zaɓa mashi mata kowacece in dai ita ta zaɓa mashi zai aureta. To kannen Faisal sun ji haka shiyasa suka makalewa Ummie dan ta zaɓawa Zaysh su, suka kirkiro halin kirki na karya, ladabi tamkar kaza a cikin miya. Shi dai Zayah har ya gama hutunsa ya koma kallo wannan bai haɗa shi da su ba, da zarar ya fito ma zasu gudu cikin ɗaki, suna tsoron haɗa hanya da shi, sai dai su dinga leƙansa ta window har ya fita, idan yana gidan amarya bata zama a waje, tana ɗaki, sai ya fita take fitowa ta yi aiki da sauri ta koma ciki.
Da ya koma Ummie ta ce masu ya yi tafiya ne zuwa Niger zai je ya ga gida ya dawo, bata faɗa masu ya koma ba, ya kara bunƙasa mata shagonta, yasa an kawo mata abays daga Egypt, Dubai and Turkey sosai da kuɗin da su Noor suka bata, ya gyara mata kasuwancinta kafin ya koma. A takaice kun ji yadda Ummie take ciki. Idan na ce zan tsaya rubuta maku komai labarin ba zai gudu sosai ba, ainahin labarin yana gaba, yanzu dik sharar fage ce, so ba zan tsaya ɓata lokacina a kan abubuwan da basu da muhimmanci sosai a labarin ba, fatan kun gane?.
To a yanzu dai dikkan sojojinmu sun dawo barrack, sun kuma dukufa a kan aikinsu, shirye-shiryen tafiya mission suka fara yi ba kama hannun yaro, a cikin kwana biyu da ya rage masu su tafi sai da suka shiga practical, aka kara horar dasu, sannan aka faÉ—a masu mission É—insu na farko.
Daga nan suka dawo suka ƙara shiri, tin da Noor ya dawo basu haɗu da V ba, saboda gagarumin aikin dake gabasu, ko waya basa yi, ita ma bata damu ba, saboda shirin da suke yi ita ma, zasu fara aiki a yanzu, za'a gwada kwarewarsu, shiyasa ita da Arya and Angelina suke ta faman shiri, ita kuma manassa idan baku manta ba na faɗa maku ita Surgeon ce, ba jami'a bace, idan kun ji Surgeon General ko Surgeon Brigadier yana nufin likitan dake kula da rundunar dake karkashin Brigadier ko General ɗin ne, to ita Manassa Division Surgeon ce, watau likita mai kula da majinyatar runduna na musamman, ita zata yi aiki ne a medical corps na soja. Dan haka dole zata tafi Mission da su Noor, saboda sune runduna na musamman, dik idan sojiji zasu tafi mission ana haɗasu da kwararrun surgeon saboda in sun ji rauni, an harbesu ko sun faɗa wani waje sun ji ciwo sai ayi jinyarsu, so a taƙaice ita Manassa ba jama'a bace, likitar sojoji ce.
A wannan rana irin ta yau dikkan jami'an da aka yaye zasu tafi Mission ɗin da aka sanyawa suna DEATH OR LIFE (DOL) kenan a taƙaice. Gabaɗaya sojojin da suka yi imani da cewa mutuwa ba'a bakin komai take ba sune a tsaitsaye a cikin hall na AZURE. Tabbas Noor ya yi mamakin ganin V a cikin tawagarsu, bai yi zato ba, ita ma bata taɓa zaton da su zata tafi ba, sai kallon juna suke yi daɗi tamkar su kurma ihu.
Dikkan jami'an babu alamar wasa a tattare dasu, dikkansu a shirye suke tsab wa mutuwa. Zasu tafi wannan mission na farko ɗin ne a karkashin ikon Brigadier General na ƙasa, shi zai kula da mission ɗinsu na farko, dan haka yasa ƙananan sojoji suka fara shirya masu rucksack ɗinsu, watau wannan jaka katuwa ta sojoji, wannan jaka da kuke gani tana ɗaukar abubuwa fiye da tinaninku, a matsayinsu na masu tafiya Mission ga abubuwan da aka shirya masu a cikin wannan jaka.
Combat uniform na yadi nai karfi da kwari, akwai tactical shirt wasu rigunar aiki ne ta musamman, sai jacket ɗinsu saboda sanyi. Bayan uniform akwai combat trousers da ake basu, yana nan kalar kayan sojiji, amma shi wando ne mai tarin aljihuna fiye da uniform ɗinsu. Akwai manyan gloves ɗinsu dan kariya ga hannuwa daga yankar wuƙa, zafin ɗaukar bindiga musamman a lokacin yaki idan bullet na fita daga bindiga yana masu zafi a hannunsu, to wannan kakkarfar gloves ɗin zai taimaka masu sosai.
An baiwa kowani soja body armor, ballistic vest ɗai-ɗai, body armor rigar kariya ce daga bullet, kazalika dik an basu plate carrier dan sanya ƙananan wuƙarsu na soja, ƙaramin bindiga and wayarsu na na ujila da sauran abin da ba'a rasa ba. Kowani soja an bashi helmet wasu ballistic helmet, waɗan nan huluna ne na soja dan kariya ga kai daga wajen buguwa da sauransu.
Sannan dikkansu an basu camouflage, wasu kuma ghillie, kaya ne dan ɓoyewar sojoji a lokacin yaki, kamar ciyawa haka aka yi kayan, idan sun sanya ba zaku taɓa cewa mutane bane, musamman idan suka kwanta, sai ku zaci shuka ce a wajen, dik dabarun yaki ne. Dik an basu tactical belt dan ɗaukar ƙananan kayan aiki da holster.
Sannan dikkansu sojojin an basu service rifle, wasu assault rifle, bindigu ne wanda dayawan sojoji dasu suke amfani. Sannan mutum uku daga cikinsu watau manyan cikinsu an basu pistol gun, Leo kuma sidearm, ƙaramin bindiga ne da zasu iya rikewa da hannu ɗaya dan kariya ta kusa ko faɗar gaggawa, uku daga cikinsu da aka bawa sun haɗa da Leo, Noor and Zaysh, su ne position one to 3 ɗin.
Sannan an basu rocket propelled grenade, kayan ne da aka yi dan lalata manyan abin hawa masu ƙarfi, in case ko ƴan ta'addan suna da motocin yaki ko abin hawa su ce zasu gudu, to zasu yi amfani da wannan dan lalata shi. Sannan kowani soja an bashi optics wasu kuma scopes dan hangen nesa, saboda ya taimaka masu wajen inganta daidaito harbi ko ganin nesa, zasu iya duba nesa ko su hango me abokan gaba suke yi. An kuma basu bipod dan ya rinƙa daidaita bindigarsu a lokacin harbi.
Kowani bindigarsu an mashi suppressor, na Leo , Noor and Zaysh kuma an masu silencer, hakan yana rage amon karar harbi da flash light da yake kawowa, hakan zai taimaka kada abokan gaba su riskesu da wuri. An basu wasu mahaukatan flashlight, mutane ukun nan kuma weapon light, wasu irin light ne masu balain haske wanda in suka haska sai waje dik ya zamto tamkar rana, baku ganin torchlight na sojoji ne? Hasken balai garesa, ga shi da haska nesa sosai, in suka dalla shi sai ya kashe ido.
Dikkansu an shirya masu night vision goggles ta yadda ko a cikin duhu tana amfani da ƙarfin intensification na haske, komai duhu in dai yana fuskansu zasu iya yin aiki kuma zasu iya ganin abu!. Sannan dik an sanya masu ɗan karamin thermal imagers, na'ura ce ta gano zafi ko a cikin duhu, idan abu mai zafi ya nufosu zai yi alerting nasu da sauri.
Sannan dikkansu an mallakawa kowannensu handheld radio dan sadarwa ga juna, ƴan rundunan zasu dinga amfani da shi saboda sanarwa ga juna halin da suke ciki, an yi masu connecting na shi dikka, in ɗaya ya yi magana dikkansu zasu ji, kuma zasu dinga karɓar umarni daga ogansu Leo, fatan kun ganesa?.
Dik da wannan sai da aka kara masu da headset with boom mic, shima dik na sauraran juna ne da magana da su kai tsaye, gudun ko ta kwana ne, ida wancan baya bada abin da akeso sai su É—auki wannan.