← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 205 OF 227

Sashe 205

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saura kuma su barsu a wannan karamin sansani da suka kafa su karɓi kuɗin fansa, waɗan da aka wuce da su babban sansani sai su haura watanni 6-7 a wajen, wasu ma ko an kawo kuɗin fansa basa sakesu, saboda ba'a basu umarnin su sake su ɗin ba, daga sama ake juyasu suma, haka zasu ajiye mutane suna lalata da su, basa zuwa kama mutane haka kawai sai an gama tsara masu ga waɗan da zaku kama, idan kun kamasu ku ware kaza ku turasu babban sansani, kaza ku karɓi kuɗin fansa daga ƙaramin sansani, dik karshen wata waɗan da suke basu umarni suna kiransu su yi lissafi da su, dama already sun san adadin kuɗin da suke baiwa masu basu umarni dik wata. Dik watan ALLAH akwai adadin kuɗin da suke baiwa manyan ƙasar masu ɗaure masu gindi, miliyoyin miliyoyi suke basu, su kuma manyan su basu kayan aiki, bindigu masu inganci, kayan abinci, kayan more rayuwa da kuma wayoyi masu tsada, sannan ga kayan shaye-shaye da suke basu kala-kala, komai ana zuwa da jirgi helicopter a sauke masu kayan abinci, jirgin bata sauƙa ƙasa, a sama take tsayawa ta sake masu makamai da kayan abinci game da dik abin da zasu buƙata.

-----------------------

Bin dik wani lungu da saƙo na wannan ɗaki da drone ɗin Leo ya yi, basu gane cewa drone bane, dan na faɗa maku kamar ƙuda yake....... Ya jima a wannan ɗaki yana kallon irin manyan ingantattun kayan aikin da suke da shi kafin ya fita ya sake shiga ɗakin kusa da wannan.

A nan kuwa mata ya gani, mata dayawan da a kallah zasu kai 250 haka, dik sun yi shunfuɗa dun kwakkwanta. Fita ya yi ya cigaba da yawace wajen da girmansa ya zarce yadda kuke tinani, nan yaga wasu matan suna zaune bakin wuta suna girki sanye da manyan hijabai har ƙasa, daga gani ba tambaya kasan waɗan nan sun zama ƴan gida, sun yi jimawar da duniya ta manta da su a wajen, sun sadaukar da rayuwarsu sun mance da iyalansu ma bakiɗaya, ALLAH sarki, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ALLAH yai maku sakayya, ya bi maku hakkinku, dan na tabbatar kuna da yara da ƴan uwa.

Leo bai san lokacin da ya ɗaura ɗayan hannunsa a kan bakinsa ba, ya kusa suman tsaye saboda tashin hankali, yana jin ta'addanci ta'addanci bai taɓa zaton karfin ta'addancin ya kai har haka a arewacin ƙasar ba, a wannan waje yaushe ƙananan sojoji ƴan bar one zasu iya fito na fito da su? Tsakiyar wannan dokar daji, gaba daji baya daji, ba zaka taɓa zatan akwai ran ɗan adam a wajen ba, ia ilahi, sun kafa wajen kafawar da suna iya ganin dik motsin da zai shigo masu, kafin sojojin su iso in da suke already suna ganinsu ta computers ɗinsu, kafin sojojin su farga sun kewayesu sun masu rubdugu.

Wannan ai sai sojojin da suka samu horo biyu suka amsa sunansu sojoji, sannan a haɗa da air force, a masu ɓarin makauniya na wuta sama da ƙasa, ai masu ruwan boma-bomai sau ɗaya shi ne za'a iya masu ba'a zauna tura ƙananan sojoji masu tasowa ana kashesu a banza ba.

Miƙewa tsaye gabaɗaya Leo ya yi tare da juyawa Arya baya, ya ɗan dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi saboda tsananin ciwo da sara mashi da yake yi, musifar ta zarce tinaninsa.

Sai da ya É—auki good 5 mins a haka, ya saita natsuwansa kafin nan ya juyo, ya dawo ya sunkuyo kanta, ya sauke ajiyar zuciya ya fi sau uku, damtsen hannunta ya É—an buga kaÉ—an game da cewa. "You really try, and i really appreciate".

Sosai ta ji daɗi har cikin ranta ganin yau ya yabawa aikinta...... Ni kam na ce bama dole ya yaba maki ba, irin wannan ɓarna da kika bankaɗo ai wlh ba dik kai ba, za'a tara sojoji 1000 ba'a samu biyu masu kwazonki ba ɗiyar daddynta.

Mai da kallonsa a kan laptop É—in ya yi yana tunanin lallai zai yi aiki tare da Arya, dan ta fi dik mazan nan amfani, team 1 ne kawai suka É—arata kwazo a wannan tafiya, amma dik sauran wlh ta fisu jajircewa, lallai zai yi aiki da ita, yana son mutum mai jajircewa.

Cigaba da kallon wajen ya yi, a cikin wani tanti suka gano wani waje tamkar makaranta, ga board da komai, kuma ga alamar rubutu a jikin board É—in, amma ya gogge ba su iya gane me ake karantarwa a wajen ba, amma tabbas makaranta ce wajen karantar da Æ´an ta'adda.

Babban abin da ya ƙara baiwa Leo mamaki shi ne yadda suke pacaka da ruwar roba bama pure water ba, sun fi bayin ALLAH na cikin gari yin rayuwar ƴanci da jin daɗi. Dik da basu ga ainahin cimarsu ba, amma sun fahimci cima mai kyau suke samu, dan sun ga buhu-buhun shinka ta waje, foreign rice kenan.

Tin Leo na mamaki har ya daina, ɗan ƙara rage tsawonsa ya yi game da cewa. "Keep watching they're movements, idan wani sabon abu ya bayyana ki sanar dani, and dik abin da kika gani wanda bamu gani a tare ba make sure you write it down for me, bari in yi meeting da su Zaynish, i will be back in the next 2 hours". Ya kai karshen maganar game da miƙewa tsaye.

Waje ya nufa cikin zafa. Bayansa ta bi da kallo tana jin tamkar ta jawosa ta dawo da shi ya cigaba da magana a kurkusa da ita kada ya dakata, amma ba yadda ta iya, tana gani har ya fita. Yana fita ta ce. "Jehan come close to me in baki yi barci ba".

Da sauri ta ɗago kai jin ta ambaci sunanta, bata jin turanci, bata gane me Arya ta ce ba, sai da ta nuna mata alama da hannu sannan ta miƙe ta zo kusa da ita, a gefenta ta zauna, Arya ta ɗan jawota jikinta tana faɗin. "Zan koya maki computer my girl"...... Ita dai Jehan bata ji komai ba, kallon laptop ɗin kawai take yi. Arya kuwa ta cigaba da aiki, wani lokaci idan ta yi pressing wani abin sai ta cewa Jehan wannan abu kaza yake nufi, dik da yanrinyar bata jin yaren amma tana fahimtar nufin Arya tin da in tana mata bayani tana gwadawa da hannu.

A can kuwa, Leo ya yi wa Noor message kan ya kira Vash and Zaynish su same shi a ɗaki yanzun nan. Ba'afi 5 mins ba sai gasu sun bayyana. Umarni ya basu kan su zazzauna, a dake suka karɓi umarni, suka zazzauna suna fuskantar juna.

Cikin natsuwa ya zayyana masu dik abin da ya gani a cikin wannan daji ɓangaren aikin su Arya. Hakika hankulansu ya yi mugun tashi, amma sai suka daidaita natsuwarsu, Noor ya ce. "Okey, the reason why our seniors always saying North is different? Oh, kenan they already knows that akwai gagarumin matsala?".

Vash ya amsa da. "Of course, but keep all this aside, let's focus on wancan hayakin, mu gano menene, wannan case ɗin babba ne, sai mun fara gano hayakin mecece a wajen can before mu takalo faɗa da waɗan can riƙaƙƙun yan ta'addan".

Jinjina kai suka yi, sun gamsu da kalaman Vash, dole su fara da batun hayakin nan, dan waɗan nan riƙaƙƙun ƴan ta'addan sai sun shirya masu.

Gyaran murya Leo ya ɗan yi wanda yasa dik suka ƙara natsuwa suka kuma yi tsit. A natse sosai ya ce. "Zamu raba aikin nan yadda zai fi yi mana sauri da kuma sauƙi"......... Basu gane nufinsa ba, sai suka bisa da kallo suna jiran dogon bayani.

"Kowani soja a cikinmu zai É—auki jami'a É—aya su yi aiki a tare, hakan zai tafi daidai, zamu tafi da fly drone É—insu na sirri, idan mun je wajen hayakin zamu rabu ne kashi huÉ—u, kowanne zai kama hanyar da zai bi, a kan hanyar da zai bi zai saki wannan drone, jami'ar da suke aiki da ita zata na duba mashi hanyar da yake bi É—in tana bashi information a kai, hakan zai sa suma matan su bada himma, for now kunga su ukun dik basu bada himma ba, É—aya ce mai fafutuka".

Jinjina kai suka yi, sun yi na'am da wannan shawara....... A kan Noor Leo ya tsayar da idanunsa kafin ya ce. "Bayan aiki ban ce ku ɓige da wani abin ba, dan ma dai an ɗaura ne ba halin in haɗata da wani da na maka canji".

Noor ya gane karatun, watau Leo ya gano cewa shi lover boy ne, shi ne har da yi mashi gargaɗi, siririn murmushi ya ɗan yi kafin ya ce. "Amma ai ya halatta idan ta binciko mun abu mai ma'ana in na ji daɗi in bata sumbata a cheek ko?"...... Kunnensa Zaynish ya kama, ya ɗan murɗa kafin ya ce. "Da a iya wannan zaka tsaya to da sauƙi, nasan halinka sarai, zama ka iya mantawa da aiki kuke yi ka zarce wani wajen, ni shawarata a rabasu, a haɗata da wani ɗin kawai tin da a bakin aiki muke, shi ma a haɗa shi da wata".

Vash na murmushi ya ce. "Wannan shawara ta yi, kawai a rabasu"...... Buge hannun Zaynish Noor ya yi game da cewa. "In ga yadda za'ayi a haɗa matata da wani kato! Ni da kayana? A ina aka taɓa hakan?". Yana tamke fuska ya faɗa, wai dan ma su san ba da wasa yake yi ba.

Shi dai Leo bai ce masu komai ba, ya jawo laptop É—insa, ya fito da sunan dikka sojojin da suka zo da su wannan Mission É—in, sojoji bar one su 34 ne, sai bar 2 team 1 and team 2 su 8, sai kuma su Arya su 4, dik in an haÉ—a su 46 kenan.

Fito da information a kan su Arya ya yi, ya zari V daga cikinsu ya turawa Noor Information ɗinta ta email ɗinsa kai tsaye ta sauƙa a laptop ɗin, a ƙasan information ɗin ya zayyana mashi aikin da zasu yi tare, dokokin aiki da tsare-tsaren da ya dace!.
Chapter 205 · 0% Book details