Sashe 224
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Arya ta zuba mata ido tana kallonta, sai ta ji tana sha'awar addinin, musamman yadda taga Leo a cikin addinin, sai take jin zata iya bin wannan addini, addini mai natsuwa da haifar da kwanciyar hankali. Shiru ta yi tana tinanin yadda za'ayi ta koyi addini, ya za'ayi ta yi register, wajen waye zata yi? Dan ta É—auka register ake yi a shiga.
Tana zaune har Jehan ta idar da sallah, ta ware hannu ta yi addu'a sosai, sannan ta shafa game da miƙewa ta koma kusa da Arya ta zauna. Arya na son tambayarta game da addinin amma bata san da wani yare zasu yi magana ba tin da bata jin na Jehan ita ma bata jin nata, sai ta yi deciding ta fara koya mata turanci da kuma reading, wannan tunani yasa ta fara ƙoƙarin koyawa Jehan karatu da kuma turanci.
Daidai wannan lokaci Angelina ta shigo ta ɗauki mouse ɗinta ta fita, kai tsaye tantin Zaynish ta koma, tana zuwa ta zauna a gaban laptop ɗinta, ta jona mouse kafin ta laluɓo number Aunty Ummie a wayarta.
Bugu É—aya tai mata Aunty Ummie ta É—auka, cikin girmamawa Angelina ta ce. "Hello Aunty ina wuni"...... Aunty Ummie dake hospital tana bin layi ne ta amsa da. "Lafiya lou sister É—ita, ya aiki ya gida dasu mama?"...... Angelina tana murmushi ta amsa da. "Sunanan lafiya sun ce in gaisheki".
Dik da Aunty Ummie bata jin daÉ—in jikinta hakan bai hana ta saki murmushi ba jin cewa iyayen Angelina na gaisheta, bata jin dadin jikinta haka ta daure ta biyewa Angelina suka dinga hira har lokacin da Angelie taga Zaynish zai shigo cikin tantin, da sauri ta cewa Aunty Ummie. "I will call you back Aunty". Bata jira amsarta ba ta katse kiran.
Take ta haÉ—e natsuwanta kafin ya shigo. Yana shigowa a gefenta ya zauna game da kai hannunsa ya jawo laptop É—inta, a natse ya hau duba abin da yawakana. Har around 3 suna tare, sai 3:30 ne Aunty Ummie ta kira numbersa.
A natse ya fara bin wayar da kallo, ita dai tana ta kallonsa, watau natsuwar Zaynish daban take a cikin sauran sojojinsu bayan Leo, ko shekara goma zaka zauna da mutum biyun nan Leo da Zaysh ba zaka iya faɗar ainahin halinsu ba, Zaysh yana da kamewa da sirri matuƙa, zurfin cikin bala'i ne da shi, a yanzu dik duniya mutane biyun nan kawai ya yarda dasu, team 1 nasu da Aunty Ummie, ko uncle ɗinsa bai yarda da shi ba, yana dai bashi girma, kuma dik duniya team 1 da Aunty Ummie kawai suke sanin me yake ciki, Aunty Ummie ma wani abin yana ɓoye mata, kamar yanzu da ya ɓoye mata suna daji, and ko su Leo wani abin yana ɓoye masu kamar yadda Leo ɗin ma yake ɓoye masu wani abin, kunga Leo ya ɓoye masu batun aikinsa na shi da Arya, baka isa iya gane ainahin zuƙatan mutane biyun nan ba, dik abin da ka ga ka sani a kansu to su suka yi ra'ayi suka faɗa maka, suna da banbanci wasu halaye, Leo yana da saurin fusata, Zaynish yana da hakurin sai ka turasa bango, Leo idan ya fusata ya yi faɗa komai ya wuce, Zaynish ba'a saran mumini sau biyu a rami ɗaya haka yake, in ka mashi sau ɗaya, ya hakura har ka turasa bango to fa ko waye kai zai zubaka a kwanton shara ne, dik basu da yawan magana, amma in suka fara magana Leo yana faɗar magana kai tsaye daga zuciyansa, ba ruwansa tai maka daɗi ko kar ta yi maka shi dai ya faɗa, ma'ana baya tauna magana, yana da ɗabiar IRON FIST na baka da wuta kuma baka da aljanna bare su ji shakkar mutum.
Zaynish ba shakkar kowa yake ji ba, kawai dai É—abia ce ta namu na Æ´an Afrika, sai mun tauna magana muke yinta, dan haka baya magana kai tsaye, sai ya tauna, idan yaga faÉ—arta ya fi alkhairi zai faÉ—a, idan kuma ya ga faÉ—arta ba alkhairi bane yana fasawa. Dik suna da dogon nazari a kan abu, kuma in suka yi nazari suka yanke hukunci sai an sara masu, suna da mugun natsuwa, Zaynish yana da girmama nagaba da shi sosai, yana da ladabi, Leo baya ji guy É—in nan, ya raina kowa, gani yake kowa a kasan shi yake, zaka iya nunawa Zaynish iko ya É—auke kai ya rabu da kai, ka kuskura ka nunawa Leo iko in ta zo da tsautsayi sai dai wani ba kai ba, dikkansu idan suna son abu soyayyar gaskiya suka iya, basu iya rayuwar munafurci ba.
Hannu ya miƙa ya ɗauki wayar, ya katse kiran nata tare da shiga account ɗinsa, ya sayi kati na kamar 10k a kuɗin Naija, sannan ya bi kiran nata. Cikin sanyin murya ya ce. "Assalamu alaiki"...... Daga ɗayan ɓangaren ta amsa da. "Wa'alaikumussalam"........ Wani irin natsuwa ya kara yi, cikin nuna kulawa ya ce. "Aunty Ummie lafiya na ji muryarki haka? Baki da lafiya ne?".
"Eh to ina zazzaɓi ne, na zo asibiti a dubani, ba wani ciwo bane"..... Kai ya ɗan jinjina, sai kuma ya ce. "Ina yaya Faisal?"......... "Ya dawo jiya yana gida". Shiru ya ɗan yi, ya ɗan yi mamakin jin amsarta, sai kuma ya ce. "Yah Faisal yana gari kuma bai kaiki hospital ba, meyasa?"....... "Babu komai, jiya fa ya dawo da daddare, ya gaji yana barcin huce gajiya".
Tin daga kan yanayin maganarta ya gane karya kawai ta yi mashi, saboda bata saba karya ba, in ta yi sai ya gane. Nisawa ya ɗan yi kafin ya ce. "Bari in kirasa mu gaisa". Ya faɗi hakan ne dan ya fahimci gaskiyarta, baya son ya ce tai mashi karya saboda na ce maku yana da girmama manya, amma yana da hanyoyi da dama da yake bi dan gyarawa manya kuskure idan suka yi cikin sauƙi.
Da sauri ta ce. "A'a kada ka kirasa yanzu, please ka bari sai anjuma in na koma zan haɗaku, yanzu yana barci ne"..... Ya gama gano akwai matsala, yadda muryarta ke rawa take ƙoƙarin hanasa kiran....... Kai ya jinjina kafin ya ce. "To yanzu dai an gama dubaki ne?".
"Am..... In.... To .... Dama likita ne ya ce yana son yin magana da mijina, kuma yayanka yana barci shi ne na kira ka yi magana da shi matsayin yayanka". Ta faÉ—a murya na rawa.......... ÆŠago idanunsa a kan Angelina dake kallonsa ya yi, mamakin Aunty Ummie yasa ya ji kamar ana kiran sunansa a waje, a ransa ya ce faÉ—a suka yi da Faisal É—in ne? Menene yakefaruwa da har take son ya yi magana matsayin mijinta? Me yake damunta? Lallai akwai gagarumin matsala.
Jin ya yi shiru ne yasa ta ce. "Ba wani abin bane fa, nasan halinka yanzu zaka É—auka ko wani abin ne"...... Uhm ita da bata yi karatu bane wai take shirin yi mashi wayau, dik da dai ance babba kam babba ne, amma ai ta kwafsa tin a farko, babu rami me ya kawo batun rami da zata ce babu wani abu dan tasan zai É—auka akwai wani abin, akwai É—in kenan.
Nisawa ya ɗan yi, ya mai da kallonsa kan laptop na Angelina dan ya ga giftawar wani abin ta gaban drone ɗinsu, hannu ya kai saman mouse ɗinta kafin ya ce da Aunty Ummie. "Babu komai, haɗani da likitan, sannan kafin nan faɗa mun meyakefaruwa da Yah Faisal? Please kada ki ɓoye mun".
Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ce. "Gaskiya zan faɗa maka shi ne matsala muka samu da shi, ya dawo gida tin last week ba jiya ba, ya dawo da makudan dukiya, da na tambayi in da ya samesu sai ya ce a haƙar gold yai nasarar samun wani dutse mai daraja ya kai kasuwa, ban yarda da shi ba, na damu sosai, da na tsananta damunsa da tambayar ya faɗa mun gaskiya ina mashi nasiha shi ne ya fara faɗa, ya ce mu koma sabon gidan da ya saya a GRA, na ce ni ba zan koma gidan da ban san da kuɗin me aka saye shi ba, shi ne ya yi ta faɗa wai ina zarginsa, ya ɗauki amaryarsa suka koma can, ni suka barni a tsohon gida wai idan na ga dama in dawo sabon gida in samesu, shi ne takaicin yasa kirjina ya fara ciwo har dai na ɗan kwanta gajerar jinya, yau naga abin yai yawa na zo asibiti".
Tin da ta fara magana ya shiga dogon nazari, gabaɗaya ya ji abin yai mashi some how haka. Sai da ta gama jawabi tas, sannan ya ce. "Haɗani da likitan, sannan kada ki koma sabon gidan, ki jira kira daga gareni tukun nan". A takaice ya faɗa....... Kai ta jinjina alamar to, still ya fahimci akwai abin da take ɓoyewa ba iya maganar kenan ba, amma ya gano bakin zare a iya ɗan wannan bayani da ta mashi, dan haka a haɗa shi da likitan bayan sun gaisa ya ce mashi. "Dr ina son sanin me yake damunta".
Likita ya hau mashi bayani sosai. "Ta kamu da ciwon zuciya saboda tsananin damuwar da take ɓoyewa a ranta, sannan hawan jini yana gab da kamata, shekarunta sun yi kankanta da damuwar da take tarawa kanta, dole kullum kirjinta ya dinga ciwo sosai"....... Ni kam na ce ba dole ta damu ba, ga rashin haihuwa, ga kishiya, ga bala'in dangin miji, ga ba uwa, ba uba, uncle ɗinta ɗaya tilo gidansa babu daɗin kai ziyara saboda bala'in matarsa, babu ta in da Aunty Ummie ke juyawa ta samu saukin rayuwa face wajen Zaynish kawai, shi kaɗai take kira ta ji daɗi, kishiya ta balbaleta da masifa, ta daketa ta zubar mata da ciki, mijin dake bin bayanta yanzu ya samu abin duniya true color ɗinsa yana shirin bayyana, ya ALLAH, ina ake son wanna baiwa ta tsoma kanta ta ji daɗi ne? Ta ji da zafin rashin haihuwa ne ko damenene?.