Sashe 107
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kankame shi Harleen ya yi yana rokonsa da ya kyaleta haka nan ya isa. Ai cikin fushi ya hankaɗe Harleen ya yi baya-baya ya bugu da Abba suka yi baya zasu faɗi Faryan ya tari Abba. A fusace Aryan ya ce. "Dik wanda ya sake matsowa nan sai na kashe shi!". Yana wani irin huci ya faɗa. Ihu Rimsha take yi tamkar maƙoshinta zai fashe, ta daku iya dakuwa ba tare da tasan shin a kan me ma ake jibgarta ba.
Daga bayansa aka rike wayar wutar, a fusace ya juya da sufin kaiwa wanda ya rike ɗin duka. 4 eyes suka yi da Ammie, bata bari ya yi wani motsi ba ta ɗaukesa da wani gigitaccen marin da ya sanya shi ɗan ɗauke wuta....... "Ka haukace ne? Ko wani kwayan kasha? Kasheta zaka yi ne?!"....... Cikin tsawa ta faɗa alamar ranta ya kai kolokuwar ɓaci.
Sake mata wayar ya yi tare da juyawa, cikin fushi ya nufi door, a lokacin Faryan da Harleen sun fita da Abban da numfashinsa yake ƙoƙarin ɗaukewa, su dik a tinaninsu tsanar da Aryan ya yi wa Rimsha yasa yake yi mata wannan duka, shiyasa dik suka tashi hankulansu.
Waje ya fito da sauri har yana haɗawa da gudu tamkar zai tashi sama. Ƙasa ya sauƙo, motarsa ya shiga, da gudu ya tada ya bar gidan, dan in ya tsaya billahil lazi zai iya haɗawa da Ammie ɗin ma.
Kan Rimsha Ammie ta yi, dik ta yi laushi, ko motsin kirki bata yi baiwar ALLAH. Ɗagota Ammie ta yi ta rungume a jikinta, ita ma dik ya farfashe mata jiki da bulala har da jini kamar Seraph. Faryan Ammie ta kira tare da bashi umarnin ya ɗauketa sai hospital da gaggawa. Ai da sauri ya ɗauketa babu ɓata lokaci, dan numfashinta ɗaukewa yake yi ya sake dawowa.
Kai tsaye CPH ya wuce da ita dan a cetota. Ammie kuma ta nufi room É—in Abba dan su tattauna wannan matsala.
E kam akwai matsala sosai fa. To mu je wajen team DOL, watakila kafin mu dawo su Rimsha sun samu farfaÉ—owa, ko ita Seraph waye zai kaita asibitin? Ga shi ya rufeta a É—aki! Ya kuma fita cikin fushi saboda marin da Ammie tai mashi, ko ina ya nufa? Fatana ma kada ya je ya yi haÉ—ari a irin wannan yanayi.
-----------------------------🔥
DOL.
Wasa-wasa kwanaki uku suka shuÉ—e babu su Lion babu labarinsu, domin kuwa bluetooth da suka sanya ma dan samun infamation ma ya yi disconnected, su Arya sun daina jiyo motsinsu, hakan ba karamin gigitasu ya yi ba, dikkansu sun shiga damuwa, V har da kuka, ita kuwa Arya a fili zaku ga tamkar bata damu ba, amma a cikin zuciyarta da sunan wannan my sterious É—in nata take wuni take kwana, dik ta damu, ko abinci bata ci, ga wayoginsu a sansanin basu tafi da shi ba.
Arya ce ta fito daga cikin tantinsu sanye cikin uniform ɗinta, fuskarta har ya ɗan rame, bata cin abinci sosai, bata da natsuwa, da daddare kwana take yi manne da laptop ɗinta a kusa da ita, komai ƙanƙantar ƙara ta ji sai ta duba ta ga ko su Leo ne, ga shi a garin musayar wuta sun harbe drone ɗin da ta tura masu. Ta yi ƙoƙarin tura wani amma ta gagara kama ainahin saitin in da suke, yanzu kwanaki uku kenan basu san a wani hali suke a ciki ba.
Dik suna zaune jigum-jigum, Angelina dai ta sanya bluetooth a kunne tana sauraran kiÉ—a, wani lokaci ta taka rawa, idan ta gaji ta zauna.
Gajiya da zama a cikin ɗaki Arya ta yi, dan tana kara shiga tashin hankali da damuwa ne. Waje ta fito bayan ta ɗauki ɗan karamin pistol da aka basu dan kare kansu. Kai tsaye wajen kogin ranar ta nufa, tana tafiya tana ƴan waige-waige, tana jin kamar alamar motsin wani abin ne a bayanta, tana jin kamar dai ana biyota, idan kuma ta juya sai a ɓuya ne yasa ta fara tafiya slowly.
Sai da ta isa dab kogin, da karfi ta juyo tare da É—aura hannunta a saman pistol gun É—in nata, ta yi readyn koma menene ta gani zata harbesa ne. Ga manakinta sai bata ga kowa ba. A matsayinta na jami'a sai ta yi amfani da kwakwalwarta, ta motsa tamkar ta juya tare da rungumo hannayenta a kirji.
Aikuwa tana motsawa kamar ta juya sai ga mai binta a baya ɗin ta bayyana, daga bayan wata bishiya katuwa ta fito. Ai wani irin razana Arya ta yi ganin yarinyar, na faɗa maku yarinyar kyakkyawa ce sosai, ga idanunta manya-manya fafare tas. To yau gashin kanta a watse yake, ya zubo mata ta gaba har baya, kuma gashin nata yana da mugun tsawo, dan ya wuci mazaunanta sosai, kuma yarinya ce ƙarama sosai.
A farko da Arya ta ga motsi a bayan bishiya ana ƙoƙarin fitowa har ta zaro bindigarta, amma ganin yarinyar yasa ta mayar da bindigar bayan ta dawo daidai daga razanar da ta yi. Ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗan kyafta idanunta dan ta tabbatar ba almara bace.
Yau yarinyar yadda kuka san aljana ko mahaukaciya haka ta bayyanar mata. Dik da ta ji tsoron yarinyar, amma hakan bai hanata takawa a hankali ta nufi in da yarinyar take ba. Shiru yarinyar ta tsaya bata motsa ba har Arya ta iso in da take.
Durkusawa a gabanta ta yi tare da riko hannunta, cikin harshen turanci ta tambayeta yau kuma me take so?. Kwace hannunta ta yi tare da nuna mata alamar yunwa take ji, abinci take son ci. Ajiyar zuciya Arya ta sauke, miƙewa ta yi tare da kama hannunta suka nufi wajen sansaninsu.
Ai tana isa da ita wajen da gudu su Angelina suka yi kanta suna faÉ—in a ina Arya ta samo kyakkyawar yarinya haka? Kamar aljana, V mai kuka tuni ta goge hawayen, a gaban yarinyar ta tsaya, sai kuma ta ce. "Arya wannan yarinyar ta yi kama da commander Nirash, ta wani gefen kuma sai naga kamar Romeo É—ina, kamar suna kama, ko dan ina kewansa ne?".
Angelina ce ta ce. "No da sir Nirash take kama"....... Siririn tsaki Arya ta ja tare da wucewa cikin ɗaki, biscuits da wani ɗan ƙaramin kwalin drink ta ɗauko, bata amsawa kowa ba ta zo ta kama hannun yarinyar, a saman wani dutse da Manassa ta ajiye a wajen kofar tantinsun dan zama ta zauna tare da zaunar da yarinyar a ƙasa.
Biscuits ɗin ta buɗe ta miƙa mata, ai da karfi yarinyar ta kwace biscuit ɗin har sai da Arya ta razana, dannawa a baki ta yi har da laidar tana kara zazzare masu idanu. Dikkansu sun tsorata musamman Manassa da dama bata wani yarda da yarinyar ba. Zuba mata ido suka yi suna kallon yadda take danna biscuit ɗin a baki, da alama yunwa yana neman kasheta ne.
Ganin zata ci har da ledar ne yasa V ta yi gaggawar sanya hannu zata kwace ledar, ja da baya yarinyar ta yi ta hanata tana cigaba da danna shi a baki, ta cika kumatu tap tana kara zaro dara-daran idanunta masu kalar sanyin nan, ita ma jade eyes gareta.
Wani irin damƙa Arya ta kaiwa hannun yarinyar, tana ƙoƙarin kwacewa ta hanata tare da sanya ɗayar hannunta ta zare ledar biscuit ɗin kafin ta saketa. Zabura yarinyar ta yi zata kwace ledar daga hannun Arya, miƙawa V Arya ɗin ta yi tare da cewa ta jefar da shi.
Da sauri V ta miƙe da shi ta je ta jefar ta dawo. Yarinyar tana ƙoƙarin zabura ta bi bayan V sai ta kware ta fara tari. Da sauri Arya ta buɗe drink da ta ɗauko mata, a natse ta kai mata saitin bakinta. Da karfi yarinyar ta kwace ta sanya baki, bata ita sha daidai ba, rabi na zuba a ƙasa rabi na bin bakinta. Ƙoƙarin gyara mata Angelina ta yi, sai dai ina, ta ja da baya dan a tinaninta kwacewa zasu yi.
Arya da bata iya jurar hakan ne ta damketa, ta matseta ta gyara mata. Ai tin da ta kafa baki sai da ta shanye tas sannan ta cire. Mamaki ne ya kamasu, Arya ta ce. "Mu kara maki?". ..... Bata san me suka ce ba, sai kallonsu kawai take yi. Miƙewa V ta yi ta ɗauko mata wani biscuit ɗin.
Yarinyar tana gani ta miƙe ta nufi V zata kwace, ita babu ruwanta da kakin dake jikinsu, bata san wani abu wai soja ba.
Riketa Arya ta yi gam tare da cewa V ta fasa mata biscuit ɗin ta zare ledar........ Wani irin ihu ta kurma saboda rike da Arya ta yi, tana ƙoƙarin kwace kanta, ita dai a barta ta isa ga biscuit ɗin. Arya bata saketa ba sai da V ta fasa mata shi. Ana bata ta hau dannawa a baki.
Ganin haka yasa Arya ta ce su ɗauko mata abincin safenta da bata ci ba, da ruwan sha. Angelina ce ta miƙe ta nufi cikin tantin. Su dai sojojin dake gadinsu suna ta faman kallonsu, suna tsaitsaye tamkar saƙaguna. Angelina ta dawo ɗauke da abincin cikin plate.
Yarinyar tana gani ta zabura ta miƙe, kamata Arya ta yi zata zaunar, ina ai ƙoƙarin kwacewa ta fara yi, ganin haka sai ta saketa dan ta ga gudun ruwanta. Kwace abincin a hannun Angelina ta yi, a tinaninsu zata zauna ta ci ne, sai suka ga akasin haka, domin kuwa tana kwacewa ta juya da gudun gaske ta kutsa cikin daji ta hanyar da suka bi suka zo.
Miƙewa Arya ta yi, da gudu ta rufa mata baya dan ta ga ina zata je, sai dai kuma bata yi taku biyu ba laptop ɗinta dake ɗaki ya fara kara. Ai da gudun gaske ta juyo, su Angelina dik da gudu suka watsa izuwa cikin ɗakin, su kansu sojojin dake tsaronsu da gudu suka nufi cikin ɗakin.
ALLAH sarki abin da suke jira ne kwana uku kenan, watau samun location ɗin su Leo. Da gudu ta isa gaban laptop ɗinta, wani irin zubewa a ƙasa ta yi, hannunta har yana rawa wajen tsayar da alert na laptop ɗin kafin ta shiga kan drone ɗin nata.